Free chapter Β· Read without an account
Chapter
*_MASARAUTAR FADAKATAM_*
*_Na Maryam Umar Abdullahi_*
( _Maman yusuf_)
*____________________________________*
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*ππ»
***
*____________________________________*
π ΏοΈAge_ 11
*AMAREN BANA*
*DR MMN YUSUF (LIKITAR MATA)* π©Ίπππ
*** call or Whatsapp
*Shawara gareki amarya* π§ππΌ *akan babbar matsalar da take damun mu ta addabemu watau ciyon sanyi ( infection)*
Shin kinsan illar da sanyi yake da ita ajikinki kuwa?? hmmm sanyi Yana haifar Mana da matsaloli Kashi Kashi ciki kuwa harda rashin kwanciyar hankali agidan mazajenmu , miyasa yanzu matsaloli sukayi yawa agidajen aurenmu ne ??? Wannan tambaya ce da kowacce mace yakamata tayiwa kanta saboda yadda abun yazama ruwan dare ,musamman duba da iyayenmu kakaninmu Sam basu fuskanci irin wannan matsalar ba to mu mi yake kawo Mana rashin zaman lafiya da mazajenmu ne duk da mafi yawanmu auren soyayya mukayi sa'banin iyayenmu da mafi yawa auren Hadi ake masu Amma sunfimu kwanciyar hankali shin Ina matsalar take ne ??????
Tabbas duk maccen da take da ciyon sanyi to zataci gaba da fuskantar matsaloli agidan aurenta , saboda sanyi Yana tafiyar da duk wata ni'imar mace yana hanata jin sha'awar mijinta Yana Hana jin Dadin auratayya tsakaninta da mijinta , zata dinga jin ciyo wajan saduwa wani lkcn har da mijin ma zafin zai rinka ji a maimakon yaji Dadi , kinga kuwa doli akwai k'atuwar matsala musamman in kinada kishiyar da zaiji Dadi a wajanta,
Ciyon sanyi Yana haifar da ciyon Mara Mai tsanani Yana Hana haihuwa idan yayi yawa ajiki yanasa mace budewar gaba Koda kuwa budurwace wadda Bata taba sanin namiji ba to sanyi kansa gabanta ya bude ,yanasa tusar gaba, kuraje, kaikyin gaba, da sauransu ,
Shawarata anan itace kowwace amarya Budurwa ko bazawara ta tabbatar tayi amfani da maganin sanyi kamun komai ,saboda duk.gyaran da zakiyi to aikin banza ne matukar kinada sanyi to ba gyaran da zaiyi maki wani tasiri yadda akeso zai kasance kinyi 'barnar kudinki a banza ne kifara yin maganin sanyi kamun kiyi komai ,
Ina matan da suke cewa duk abunda zanyi amfani da shi na kayan Mata bayamun aiki ????? To kusani bakomai ne matsalar ba sai (infection) matukar kinada sanyi to ba abunda zakiyi amfani dashi kiga aikinsa saidai kiyi ta barnar kudinki a banza ba biyan bukataππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
Wannan yasa nazo maku da sahihin Kuma ingantaccen maganin sanyi na Mata da maza , maganine da yake fara aiki cikin gaggawa matukar kikayi amfani dashi to kinyi bye bye da matsalar sanyi da izinin Allah ,kina fara amfani dashi to kema zakiji canji ajikinki ,
Na Sha ne da sabulun tsarki da Wanda Zaki dafa kina tsarki sai Kuma oil Wanda Zaki rinka shafawa ,
Na.maza Kuma gari ne Wanda za'a rinka dafa mashi cokali daya atace asha ruwan da ikon Allah kun rabu da matsalar sanyi kenan , don Yana da kyau in kinada sanyi to.kiyi magani keda mijinki tunda abune da ake dauka kar kiji sauki shikuma yanada shi kinga anyi ba'ayi ba kenan ,
TAKUCE YAR MUTAN SOKOTO MMN YUSUF MAI KAYAN MATA πππππππ
Don samun ingantattun magunguna na nemini ta wannan number *** pls in Baki shirya siya ba kibari sai kin shirya kimun magana plsπ€π€π€π€π€π€
......................Wasa Wasa sai da AZIZA da gimbiya HIDAYA suka kwanta ciyo sosai saboda rashin yarima ZAHIRR, inda hankalin matar Malamin duba ya tashi sosai ganin shugabar ta da 'yar ta kwance cikin mawuyacin hali , kuma ba abunda zata iya akai ,da k'yar da lallashi gimbiya HIDAYA ta Fara dawowa dai dai inda ta k'udirta sanyawa kanta dangana ko don kula da lafiyar Aziza , zata ci gaba da Taya d'an nata da addu'a don samun cikar burinsu baki d'aya ,
Yau kimanin wata ukku kenan da tafiyar yarima ZAHIRR ,tun suna damuwa har suka sanyawa ransu dangana ,sai dai gaba d'aya Aziza ta canza ta koma wata miskilar k'arshe kullum zaka ganta shiru shiru kamar Mai tunani ,duk wannan k'iriniyar da rashin ji ta daina ,Aziza Mai yawan fara'a da dariya ,wadda ko Ido kuka had'a sai ta kasheka da murmushinta Mai burgewa Amma yanzu duk ta canza abune Mai matuk'ar wahala yanzu kaji maganarta ma bare akai ga zancan murmushi ko dariya , tun Umminta na Mata fada har ta gaji ta Sanya Mata Ido , Abu d'aya suke samun sauk'inshi in har suka zauna suka nuna Mata wannan tafiyar da yarima ZAHIRR ya yi, yayi ne don samun ku'butar da mahaifinta Malamin duba daga azzalumin sarki ZULAIMU ,to a wannan ranar zasuga farin cikinta sosai, saboda a duniya ba abunda Aziza ke so irin yau ace taga mahaifinta , wannan buri na ta Yana d'aga hankalin umminta , wani lokacin har ya sanyata kuka , tana tsoro tana matuk'ar jin tsoron ranar da zasu rasa Malamin duba ba tare da cikar wannan burin na 'yar ta ba , in hakan ta faru Bata san wane hali Aziza zata tsinci kanta aciki ba, irin yadda ta kwallafa ranta akan mahaifinta, ,
Haka Nan suka ci gaba da rayuwa yau fari gobe bak'i suna rayuwa ne kawai Amma Sam Babu farinciki a cikinta ,saboda farincikin nasu baya tare dasu , a haka suka shafe shekara shidda cikin wannan Hali , a kuma lokacin ne farin ciki ya Fara doso rayuwarsu in da suka Shiga shauk'i da dokin dawowar yarima ZAHIRR ,kullum Zaki gansu suna faman shirye shirye dawowar yarima ZAHIRR zancansu d'aya biyu yarima ZAHIRR , sai a wannan lokacin walwalar AZIZA ta dawo gaba d'aya yanzu zamanta yafi yawa inda gimbiya HIDAYA don Basu da wata fira sai ta yarima ZAHIRR,
*Masarrafar horo* a lokacin da nayi arba da yarima ZAHIRR baki da hanci na saki Ina kallon abun al'ajabi da tsoro ,
Zaune yake Akan wani dutse inda ya tank'washe k'afafunshi ya mik'ar da hannuwanshi saman k'afafun nashi , idon shi a rufe Yana sanye da dogon wando Mai fad'i sosai irin Mai Kama da bujen nan jikinshi ba riga inda duk wata k'ira ta mazantaka ta gama bayyana a jikinshi ,jikinshi ya bud'e sosai yayinda jikin yake a murd'e irin na asalin jarumai ,gashin kanshi ya sauko ya rufe mashi fuskarshi , duk yadda naso na ga fuskarshi abun ya gagara saboda yadda gashin ya sauko sosai a fuskarshi, alamunshi sun nuna addu'a yakeyi , ya Jima a haka kamun wani bafade ya shigo wajan cikin girmamawa ya duk'a yace
"Ya shugaba na lokacin atisaye yayi , har shugaba ya k'araso"
Ba tare da ya motsa ba ya jinjina kanshi alamar amsawa ,da sauri hadimin ya tashi Yana fad'in " a fito lafiya shugaba" daga haka ya bar wajan cikin sauri,
Sai da ya shafe wasu mintuna kamun ya mik'e tsaye subuhanallah namijin gaske kenan dogo ne sosai Yana da d'an jiki sosai sai dai jikin nashi a murd'e yake irin na jaruman da suka amsa sunansu , Wanda a kallo d'aya zaka fahimci tsananin jarumtar dake tare dashi, kamanunshi da mahaifinshi sun sake bayyana a tare dashi , bambancinsu d'aya ne sarki KUNTARU bak'i ne yayinda yarima ZAHIRR ya ke fari Tass Kamar mahaifiyarshi,a cikin shekarun nan ya Zama cikakken saurayin da a kallo d'aya zaka dauka yayi shekara ashirin da biyar ko da shida sai dai ba haka bane a wannan lokacin yake cika shekara goma Sha Tara ciff,
a hankali cikin tafiyarshi ta Isa da zallar izzar mulki dake cikin jininshi ya nufi inda babban Malamin ke jiranshi,
Kwanci tashi asarar mai rai a yau yarima ZAHIRR ke cika shekara shidda da rabi a masarrafar horo inda wata shida cif ya rage mashi ya dawo gida , inda yayi dai dai da lokacin da Allolin zinari suka dibama yarima ZAHIRR don yak'ar azzalumi sarki ZULAIMU, shiri sosai mutanen garin RIGASA keyi na murnar dawowar yarima ZAHIRR ,gefe d'aya sun Fara Shirin yak'ar sarki ZULAIMU,
________________________________
Gudu yakeyi sosai gudun ceton rai ya had'a zufa sosai yayin da ko'ina na jikinshi ke rawar tsoro , Yana gudu Yana fad'uwa ya na tashi ,yayinda wasu manyan k'ayoyi da Bai ta'ba ganin irinsu ba suka ci gaba da Huda mashi kafafu duk inda ya taka sai dai yaji ya taka k'atuwar k'aya Mai tsananin dafi da zafi , Yana cikin wannan gudun da ihun neman d'auki ya ga wani haske ya bayyana a gabanshi acikin hasken ya ganshi ya fito rik'e da wata shar'be'biyar takobi Mai tsananin haske da kaifi , inda mutumin ya Fara tunkaroshi gadan gadan , ja da baya ya Fara Yana ihu da neman d'auki Bai ankara ba sai jin yayi yayi Karo da wani k'aton dutse ,juyawar da zaiyi sai ganin wani k'aton kwazazza'bi yayi gabanshi Mai matuk'ar zurfi da fad'i waje ne da in mutum ya fad'a to tun kamun Ya Kai k'asa zai riski ajalinshi saboda girmanshi da zurfinshi da wasu kifiyoyi da suka Yi mashi k'awanya ko ta Ina , a razane ya d'ago kanshi ya dubi wannan saurayin kamun yayi wani motsi saurayin ya daga takobinshi ya fille mashi Kai inda gangar jikinshi ta Fara gangarawa cikin wannan kwazazza'bin, ........ A firgice ya farka da wani irin ihu Wanda duk Wanda yake cikin sashen na sarki ZULAIMU sai da ya jishi, a guje dakarun da ke tsaron k'ofar sarki ZULAIMU suka nufi inda yake suna masu zare takubbansu da Shirin ko ta kwana , suna zuwa bak'in k'ofar suka tsaya suna masu jiran umurni daga shugabansu , inda amintaccen sarkin ZULAIMU ya kutsa kanshi cikin turakar sarki Yana dube dube kasancewar har lokacin sarki ZULAIMU na zunduma ihu Yana laluban kanshi ,ya had'a uban zufa ,da sauri dogarin ya k'arasa kusa dashi cikin tashin hankali ya Fara magana,
"Allolin zinari su baka nasara ya shugaba mi yake damunka haka ne kake irin wannan ihun bayan ba kowa a cikin d'akin Nan, mi yake faruwa ??,"
Tsitt sarki ZULAIMU yayi Yana sauraren amintaccen bawansa kuma Mai bashi tsaro , ajiyar zuciya Mai k'arfi ce ta k'wace mashi ganin Ashe Yana raye , Ashe mafarki ne yakeyi , Amma wannan wane irin mafarki ne, idan bai manta ba shekaru arba'in da biyu da suka wuce ya ta'ba irin wannan mafarkin kuma ba abunda ya canza tsakanin wancan da wannan , a lokacin ba'ayi mashi sarautar waziri ba , tabbas akwai wata a k'asa tunda har ya sake maimaita mafarkin Nan ,a zabure ya sauko daga saman gadonshi bai damu da dare ba ya Sanya rigarshi ya fita daga d'akin inda ya nufin d'akin tsafinshi don yin bincike , da sauri wannan dogarin ya bi bayanshi ,
Madubin tsafin shi ya d'auko ya Fara bincike akai , kamun ya dubi wannan bafaden yace "inason gobe a taramun duk bokayen da ke cikin wannan garin ,Ina son kamun na fito fada a tabbatar da kowa ya zo akan lokaci , "
duk'awa yayi yace "umurninka abun cikawa ne ya shugaba," daga haka ya fito daga cikin d'akin ya nufi inda yaranshi suke...........
Ban yarda iklass k'amshi ta karanta wannan page din baππππππ