Free chapter · Read without an account
Fita ta 5
by M.Kwalisa · DADI KAN DADI
DADI KAN DADI
M.Kwalisa
Fita ta 5
A lokacin da Hajiya Laura take Jin kamar ta fizgo santalelen saurayin dake tsaye a gabanta,Ya saki baki galala Yana kallon santala-santala jajayen cinyoyinta dake kyalli a cikin hasken wutar dake cikin dakin.
A lokacin Kuma Hon. lawali mijin Hajiya Laura ya yi fakin din motarsa a harabar gidan.
Ta tawo cikin azama kamar zata fada masa,a lokacin da numfashin muntasir yake Kai komo a tsakankanin hakarkarinsa. Wannan tarkone mai wahalar fita santalelen saurayi ya tsinci kansa daki guda da cikakiyar mace mai jini a jika.Ga mamakinsa sai ya ji wandonsa ya daga.
Akwai matsala.
Ya soma neman nutsuwarsa ya rasa.
A lokacin Alhaji Lawali ya shigo cikin falon farko na tangamemen gidan yana sallama gami da fadin.
"My sweetheart.. " shiru ya gaida kunuwansa.
Hajiya Laura ta Kara tunkaro muntasir, ganin haka ya ja baya cikin tsoro gami da fadin. "Kiyi hakuri ban taba aikata abinda kike son na yi ba. Hasali ma bansa yadda ake yi ba"Ta zuba masa shanyayun idanunta tana dubansa.
"Ni zan Koya maka..."
Binta sudan ta hango shigowar Alhaji Lawali, gabanta ya fadi,ta ja dogon tsaki shi kenan shirinta ya lalace. Cikin sauri ta nufi dakin da su Hajiya Laura suke ciki ta tura kofar cikin sauri.
Jin bude kofar ya saka Hajiya Laura tayi saurin Kai dubanta, ganin Binta sudan yasa ta sauke numfashi.
"Yaron nan yaki bada hadin Kai..." Cikin sauri ta karasa gareta.
"Gwara da bai bayar ba, don Alhaji ya dawo".
Ta dubeta cikin mamaki "Shi Daya ce sai 12 dare" Cikin azama ta fice daga dakin.
Binta sudan ta dauke wayarta tana jan tsaki. Shi kenan shirinta ya lalace. Amma a juri zuwa rafi.
"Kana iya tafiya Dan saurayi ka yiwa kanka asara sulala ..."Muntasir ya juya cikin azama zai fice har ya je bakin kofa ya ji murya Binta sudan tana cewa "Saura naji labari a wajen wasu cewar Hajiya Laura ta neme ka"Ga mamakinta sai taga muntasir ya dubeta ya yi Murmushi kafin ya sa Kai ya fice.
Tun daga falo yake jiyo surutu da sambatu na Alhaji Lawali,Ga mamakinsa sai ya ji dariya ta kwace masa.
Duk wannan abun ya faru ne,kafin muntasir ya farka rana tsaka ya gansa kwance da wata tsaleliyar budurwa kwance tsirara akan gado Daya, a cikin tsakiyar dokar daji.