Free chapter · Read without an account

5.

by Nusaiba · SARAUTAH TAH CE

👑👑👑👑👑


*SARAUTA TAH CE*






*Free page*





*Wattpad*

@nuceeyluv






By

Nuceeyluv😘





5.....






*MASARAUTAR MANARAS*



A zabure ta kalleshi batayi mgn ba saidai kawai tana jiran taji ta bakinsa ne, sarkin gida dake durkushe gabanta ya sake waiwayawa kafin ya juyo cikin magana kasa2 yace,


"daga majiya Mai karfi naji cewar maimartaba sarkin MANARAS na shirin daurawa yareema yaseer aure Nan bada jimawa b..."


"Wannan mgnr banza ce"


cewar kwarkwarar sa'adiyya da fuskarta ta fara canja launin fushi tace,


"yareema yaseer din da baya kasar yaushe aka shirya Hakan da zaiyi aure? Nifa d kaina na sanya Masa tsanar auren Nan, na Kuma cusa Masa kaunar Zina a zuciyar sa, sannan kace min za'ayi Masa aure? Toh taya? Yaushe ma ya shiryu da har zaiyi tunanin aure? Kasan irin karfin kafin da nayi a kansa kuwa? Gsky bakaji daidai ba..."


Kwarkwara sa'adiyya ta karashe mgnr zuciyar ta na zafi hankalin ta ya fara tashi. Cike da girmamawa sarkin gida yace,


"ai ranki shi dade shi kansa yareeman baisan da zancen Wannan auren ba, Wannan duk shirin maimartaba ne."


Mikewa tsaye kwarkwara sa'adiyya tayi zumbur hankalin ta a mugun tashe sai dukan hannun ta take a hankali tana safa da Marwa a Tsakanin Inda suke, jikinta har Wani rawa yake ta juyo a fusace tamkar ta fashe da ihun takaici tace,


"yanzu duk kokarin da nake naga na raba Tsakanin maimartaba da yareema yaseer Ashe Duk aikin banza ne? So yake ya lalata min shirina? Duk zaman da yareema Yazeed yakeyi a fada Hakan be wadatar dashi ba sai hango sa yake acan wata duniyar daya gama lalacewa a titi?? Kaii bazaiyi yiyu ba Wlh. Karyane ayimin Wannan kutsen cikin plans dina."


Ta furta Hakan tana me wucewa cikin can dakinta ko takan sarkin gida Bata bi ba Hakan yasa shima ya mike Yana maida Jan kyallen sa ya fice a sace kamar yadda ya saba.


Tana shiga kuryar dakinta ta kada Wani Shantu take Wani siririn farin hayaki ya fito ta ciki Yana yin sama ya bace bat.


Boka Markus dake tsaka da tsafinsa yaga alamun kiran kwarkwara sa'adiyya sbd bayyanar Wannan farin hayaki, Hakan ya shaida Masa cewar lalle tana neman sa, duban lkci yyi yaga har dare ya fara shiga, Hakan ya Tabbatar Masa da cewar lalle kiran Nan bana banza bane, take ya mike yana gyara rawanin sa hade da shiga futuk irinta malaman fada sannan yyi wuf ya fice Yana bin hanyar da zata sada shi da wajen haduwar su shi da kwarkwara sa'adiyya.


Zaune ya sameta harta rigashi zuwa kafarta daya kan daya tana girgiza ta ya karaso a nutse yana zama kan Dan buzun sa na sihiri yace,


"Ranki shi dade lpy kike nemana a cikin Wannan daren?"


Juyowa tayi a fusace dama bashi take facing ba, tace,


"boka Markus ya mukayi da Kai?"


Cike da daurewar Kai yace,


"ban fahimci abinda kikeso kice ba ranki shi dade"


Tsaki kwarkwara sa'adiyya tayi kafin tace,


"Taya akai ka bari sarki ya fara tunanin daurawa yareema yaseer Aure? Bayan ka sanar dani babu Wani lakani dazai Karya sihirin yareema yaseer sama da ya sadu da matarsa ta Sunna shiyasa ma muka cusa Masa tsanar aure damma kar Azo da batun Hakan Amma kwatsam sai naji mummunan lbri cewa maimartaba na shirin yi Masa Aure????"


Shiru boka Markus yyi Harta gama kafin yace,


"Ranki shi dade Inaga Wannan duk Mai sauki ne..."


"ban gane ba"


ta katse shi rai bace, boka Markus ya gyara zamansa kafin yace,


"Sam Bai kamata ki daga hankalin ki haka ba, kin manta da kudurin kawar dashi da aka shirya idan ya dawo ne? Ai kafin a kaiga auren ma an kawar dashi saidai a maida auren Nan kan yareema Yazeed badai yareema yaseer ba"


Numfashi sa'adiyya ta sauke fuskarta na fara washewa tace,


"Kanada tabbacin auren kan Dana zai juye?"


Girgiza Kai boka Markus yyi cike da tabbaci, sa'adiyya ta mike a tsanake tace,


"lalle kuwa zanje na fara shiri tun yanzu kafin lkci ya kure."


Tana gama fadin haka ta fice daga wajen.




*KAUYEN JIRAGO*


"Yau rafin ba mutane da yawa"


cewar Shema'u, bilqees tace,


"ai kinsan dayake yau kasuwa wasu sun tafi tun safe Nima anjima zanje kasuwar"


Shema'u tace,


"kamar kinsan Nima zanje goron da nake sarowa ya kare"


bilqees tace,


"nikuma saura kadan kawai inaso na karo ne kada yyi karacin"


"an gaishe da bilqees Mai kayan marmari"


cewar Shema'u tana dariya. Dan murmushi bilqees tayi batace komai ba.


Sana'ar bilqees kenan Saida kayan marmari irinsu lemo, ayaba, kankana, gwanda da sauran su. Ta zabi Hakan ne sbd rufawa kansu Asiri ita da innarta da sauran yayunta da Suma suke a wahale gidan mazajen su, tana tausaya masu sosai a dalilin haka ma ta kyamaci auren gani take duk kanwar ja ce Kuma ta yarda akan Hakan duba da yadda mahaifin ta ke gudanar da nasa halayyar a gida sai Hakan be Wani Bata mmki sosai ba akan Abinda ake yiwa yayunta.


ko yaushe takan kasa su a tire taje dandali dashi kullum Inda sauran ke Saida abinsu itama ta jeru wajensu da kayan marmari tana tallata abinta, Toh dayake mazan wajen na son yi mata mgn sai kaga sunata siya ko bada niyya ba...ita Bata San ma sunayi ba domin har a wajen basa ganin fuska a wajenta saidai su siya kawai a Hakan Suna kare mata kallo ba damar mgn.


Saida suka gama wankin tass kafin suka dawo gida, a gurguje bilqees ta shirya inna habi ta miko mata abincin Rana da akayi tace,


"ya kamata kici Wani Abun kafin ki tafi"


girgiza Kai bilqees tayi tana shafa man habiba na 'yar karamar roba data siyo masu a kasuwar GWAB'E. Tace,


"banajin cin komai inna"


inna habi ta dubeta a tsanake kafin tace,


"akan mgnr dazu ne?"


Shiru bilqees tayi batace komai ba, inna habi tace,


"kamar koyaushe bilqees Ina Mai baki hakuri, da ki Kara yin hakuri akan halayyar mahaifin ki wata Rana sai lbri bilqees."


Hawayen da take dannewa ne suka zubo cikin yanayi na kuka da Jan zuciya Tace,


"Inna mena tarewa baffa ne a gidan Nan? Meyasa ya tsane ni haka inna? Dama wai Dan Adam na zabar Abinda za'a halitta Masa ne?? Ko kuwa mu da muke 'ya'ya mata ba mutane bane...??"


Ta Ida mgnr tana fashewa da kuka Mai cin rai.


Jawota inna habi tayi tana lallabata a hankali tace,


"Yi hakuri bilqees, komai yyi farko zaiyi karshe, sannan komai lokaci ne, wata Rana ko ance yyi da kudi ma bazai iya aibata halittar 'ya'ya mata ba bilqees, kisa a ranki haka tamu kaddarar take

Jarrabawa ce daga Ubangi ya kamata mu kasance masu hakuri a koda yaushe Allah Kuma na son bayin sa masu hakuri domin mahakurci mawadaci"


Haka dai inna habi ta dinga lallashin bilqees harta samu bilqees ta yarda ta tsakuri abincin kafin ta mike ta shirya a nutse sannan tayi mata sallama a lkcn har Shema'u ta biyo mata suka wuce kasuwar daga Nan.




*MASARAUTAR MANARAS*



"An gaishe da dawisu uban ado, yareema yaseer Mai jiran gado sarkin gobe da yardar Allah, gaba salamun baya salamun...."


fadawan masarautar suka fara yiwa yareema yaseer kirari lkcn da motar data dauko shi daga airport tayi parking Yana ciki a hakimce jikinsa sanye da Wani irin tufafi na sarauta yanayin zanen da akayi Hakan zai bayyana maka asalin waye shi, da kuma tsadar yadin da akayi amfani dashi Wanda fadar kudin kayan zaisa ka kafa jari Mai tsokar gske.


Kansa sanye yake da wata irin hula Mai daukar ido manne da tambarin masarautar MANARAS Hakan ba karamin Kara tatso da tsantsar kyawunsa yyi ba ko makiyi saiya yaba.


Yafi minti 30mins zaune a cikin motar ko motsi beyi ba Kai kace sarkin ne da kansa irin yanayin yadda yareema yaseer ke gudanar da kasaitar sa na matukar birge mutane da kuma shayin sa domin komai nasa cike da kasaita yakeyi, a hankali ya zuro kafarsa daya zuwa kasa sanye take da Wani irin takalmi na Alfarma Saida ya bada tazarar lkci kafin ya sanyo dayar kafar waje a lkcn har wasu fadawan sun baza babbar rigar su Suna jira ya mike aikuwa Saida ya Bata lkci kafin ya mike dakyar


wohoho...yareema yaseer kenan da ga Abdallah Usmanu Yusuf maimartaba sarkin MANARAS. Nan fa aka ci gaba da zabga kirari,


"takawar ka lfy yareema...fari kke tass Wanda babu algus a ciki sukari kke fes bakayi farin banza ba yadda jikin ka yake haka zuciyar ka take fara tass karyar mahassada suga bayanka Allah ya tsare gabanka da bayanka yareema yaseer sarkin gobe da yardar Allah...."


dukkanin daukacin masarautar MANARAS babu Wanda besan da dawowar yareema yaseer ba Hakan yasa aka shirya gagarumin shagali na tarbar yareema yaseer babban da namiji ga maimartaba sarki Abdallah.


Iyakar dannewar kishi yareema Yazeed yyi kafin ya iya yake yana kokarin maida fuskar shi kamar koyaushe irinta kamulallun bayi hade da nuna tsantsar kulawa ga yareema yaseer da bayyana farincikin dawowar sa. Ya

Isa gaban yareema yaseer lkcn daya shigo fada cike da murna ya mika Masa hannu yana fadin,


"barka da dawowa Dan uwa"


girgiza kai yareema yaseer yyi alamar amsawa kafin ya wuce gaban sarki domin kwasar gaisuwa.


Wani irin tukuki ne ya tokare wuyan yareema Yazeed Amma ya daure yana ci gaba da yake yareema yaseer ya durkusa cike da biyayya a gaban maimartaba Yana yi Masa gaisuwa a matsayin sa na maimartaba kafin su kebe ayi gaisuwa ta Tsakanin da da uba.


"Sarki ya Amsa Kuma Yana godiya hade da nuna farincikin saukar yareeman masarautar MANARAS lpy."


Bafaden sarki Wanda shine bakin sarkin ya bawa yareema yaseer amsar gaisuwar da yakeyi.


"Godiya muke, Allah ya Karawa sarki Daraja yaja kwanan sarki"


sauran Wanda suka rako yareema yaseer Suma suka furta Hakan cike da girmamawa Suma.


Neman izini yareema yaseer yyi sbd yanason shiga cikin gida, bafaden sarki yace,


"an baka dama Yareema sarki na maka ban gajiya."


Mikewa a nutse yareem yaseer yyi ya taho cike da takun sa na kasaita yabar fadar gaba1.


Kusan mutum biyar ne suka bishi da harara Wani daga ciki na yiwa na kusa da yareema yaseer inkiya da wata irin alama ta munafukai wato bafaden sa Musa....





*Tofah😳 bafade Musa ma Ashe Ana cikin....uhum bari dai nai shiru🤐, su Kuma sauran suwaye da suke binshi da harara?? Uhum bari dai na Kara yin shiru...😹🤐🤐 Ai yanzu aka fara wasan💃🏻*






*Albishirin ku🗣️🗣️🗣️ tuni wasu mutane suka fara biyan kudin su na SARAUTA TAH CE, me kike jira? Idan har kinada dama ki biya abinki a wuce wajen🙅🏻‍♀️🙅🏻‍♀️🙅🏻‍♀️*




*Zaki iya biyan kudin ki yanzu a saki a paid group*



It's 300 via... Access bank 1445626295


Nusaiba Mustapha


Then show your evidence ta Wannan number👇🏻



***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.