Free chapter · Read without an account
6
by Khadija · MATAR MAHAIFINA
MATAR MAHAIFINA*
♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
~Labari da Rubutawa~
Na
MAMAN AMATULLAH
💫
Wannan littafin na kuɗi ne za ki bi ya nera ɗari biyu(200)ta asusun banki 0003187186 Khadija Salisu ja'iz bank ko ki turo katin MTN na nera ɗari biyu (200) ta wannan lambar *** ga mai ne man ƙarin bayani sai ya tuntuɓe ni ta lambar da ke sama.
FREE PAGE
Shafi na 41-42
Da ya ke ya san garin sosai be wani sha wahalaba sai gasu a k'ofar gidan guri ya samu ya ajiye motar sa sannan suka fito,abin ka da gidan masu zaman kansu kowa shiga ya ke babu izini,dan haka suma duna fitowa kai tsaye suka kutsa kai cikin gidan tana gaba yana binta a abaya,babu kowa a tsakar gidan ga dukkan alamu kowacce tana ɗakinta ana ware gajiyar jiya,,kai tsaye ban garan Hajiya jamila suka nufa,,sallama tayi a ƙofar ɗakin lafin ta ɗaga labile ta shiga,,kwance ta tarar da magajiya a saman kujera,tana waya,,tana ganin Juhaina ta faɗaɗa murmushinta tare da cewa ina zuwa zankiraka anjima,,tana ajiye wayan ta tashi zaune tana "Ƴar halak kink'i ambato yanzu nake maganarki araina,ashe kina tafe" Itama murmushin tayi tare da gaisheta tace "Ai kam dai hajiya ina tafe bama ni kaɗai bace tare da baƙo nake" "Baƙo kuma amman shine kika barsa bakice ya shigo ba,maza je kice ya shigo",tana daga zaune ta ce yaya wai ka shigo,shi ma da sallama ya shigo tare da ne man guri ya zauna,gai sawa sukayi da magajiya,magajiya ta dubi Juhaina alamar tana son ƙarin bayani,kafin Juhaina ta ce wani abu tini Junaid ya karbe da cewa, "Ni yayan ta ne,na jima ina nemanta,jiya nazo wucewa ƙwatsam sai na ganta a bakin hanya to shine na ɗauketa muka tafi tare yanzuma tazo ɗiban kayan ta ne da zata koma gida da zama ne" Daga jin wannan batu tini fuskar magajiya ta sauya,kafin ta dubi Juhaina ta ce "Baki sanar dashi duk abin da ke faruba na baki da izinin barin gidannan har sai kin biyani duk kuɗaɗe na" Wani irin kallo Junaid ya yi mata tare da cewa "Tayi min bayanin komai kuma yanzu zan mayar muki da kuɗinki har da riba,kinaso na baki madarar kuɗin ko kuwa na turo miki ta banki? Baki ta taɓe tana ganin kamar wasan yara ta ce "Aa kabani madarar kuɗi na sani ko duk bige ce," Be tanka mata ba yasaka hannu a aljihu ya ciro rafa ta ƴan dubu-dubu rafa shida ya miƙa mata hannu na rawa ta ƙarɓa tare da cewa shida fa nake gani? Eh ki riƙe har da riba, ke tashi ki ɗauko kayanki mutafi tin da an biya ta,ya faɗa yana duban Juhaina tare da mi ƙewa,itama miƙewar ta yi tare da cewa to hajiya saduwar Alkairi,,to Juhaina Allah ya tsare hanya zamuyi kewarki dan munsaba,babu komai Hajiya idan da rabo wata ran za'a ƙara gaisawa,tana kaiwa nan ta fice zuwa ɗakinsu babu kowa ciki ga dukkan alamu su Ruky basu dawo ba,sai ba taji daɗi ba dan taso suyi sallama,,dama ko mai nata a haɗe yake a jaka sai abin da ba'a rasa ba dan haka bata jima ba ta fito,yanan tsaye in da ta barsa karɓan jakar hannun ta ya yi tare da cewa sukenan muje ko? Eh su kenan amman akwai abin da zan karba a gurin Hajiya,bata jira cewar saba ta wuce dan kar ma ya tambayeta,nan kuwa ita lambarsu Ruky zata karɓa duk da bata da waya,duk ran da tayi waya zata ne mesu,dan sunyi zaman mutunci,ba ta jima ba ta karbo ta fito hajiya na ƙara jaddada kewarta,ha dai sukayi sallama da ita ta fi ce amota ta samesa,tana zuwa ta shiga yaja mota sukabar gurin ajiyar zuciya ta sauke tana k'ara yuwa Allah godiya da yarabata da wannan gurɓatacciyar rayuwar da ta kusa faɗawa,ju wowa ta yi ta dubi Junaid ta ce hakika baki na baze taɓa gajiyawa ba da nuna godiyata a gareka, nagode kwarai da gaske Allah ya ƙara arziki Allah ya tsareka daga dukkan sharrin mai sharri, Amin ya amsa tare da cewa, kinga godiyar ta yi waya haka ai yiwa kaine,ke tamkar jinina ce haka nake jinki,dan haka bana son wannan godiyar daga yau kinji, to yaya ai godoya ta zama dole,,haɗe rai ya yi tare da cewa ni kuma nace banaso idan kuma kinaso kiga ɓacin raina to kici gaba Allah ya huci zuciyar ka na dena,,be tanka mata ba ya kunna ƙira'ar Sudes, ido ta lumshe tana sauraron ƙira'ar sudes,can ta tsinci miryar sa yana bi,sosai taji zaƙin miryartasa na ratsa, ji tayi kawai ta tsinci kanta da son kallonsa,ido ta buɗe a hankali ta sauke ganinta a kansa,yan da yake motsa dan ƙaramin bakinsa ba ƙaramin ƙayatar da ita abin ya yi ba,sosai ta shagalta da kallonsa da kuma sauraron sa yan da yake karatun kamar wan da ya tashi cikin larabawa,jikin sa ne ya basa ana kallonsa duban gefen ta ya yi yaga yan da take kallonsa ko kiftawa babu,murmushi ya yi ya cigaba da duban hanya,,ita sam bama tasan yana yiba,dan ya gama ta fiya da ita,,duban ta ya sake yi a karo na biyu har yanzu shi ɗin dai take kallo,murmushi ya sakeyi tare da hura mata isaka,da sauri ta dubesa gira ya ɗaga mata tare da cewa wannan kallonfa karkisa na kasa tuki mana,cikin kunyar da ta dabai bayeta ta ɗauke idonta tana murmushi,ɗayan gefen ta mayar da kanta tana,faɗaɗa murmushinta,shima be ƙara cewa ko mai ba har suka ƙaraso gida,..
WANENE JUNAID?
Cikaken sunansa shine Junaid Aliyu Ahmad shi haifaffan garin Abuja ne amman asalin iyayensa duk fulanin Adamawa ne,yanayin nema yakai mahaifinsa Alhaji Aliyu Ahmad can Allah ya yi zamansu a can,sunan mahaifiyarsa Hajiya Aisha, yana da kanne guda biyu Farhat da Farhana mahaifin Junaid zuwa yanzu shararen dan kasuwa ne wan da duniya ta san dashi,bama nan ƙasarmu najeriba dan haka yana da arzki sosai,,sannan shi mutun ne mai son ƴan uwansa yana kuma son kyautatawa na ƙasa dashi dan haka nema mutanen dake ƙarƙashin sa suke matuƙar jin daɗin sa,sabi da shi mutum ne me sauƙin hali,sosai, Hajiya Aisha mahaifiyar Junaid macece mai son kanta da ƴaƴanta sam bata son talaka ya rabeta,balle ace har ya shigo cikinsu,amman in dai ka zo neman temako ne tanayi sosai duk wan da yazo tana iya kokarinta,tin da ƙuru ciyarta Alhaji Aliyu ya yi fama matuka dan ganin ya rabata da wannan halin sai dai kash abin yaci tira,bayan wannan bata da wata matsala macece ita mai jajircewa wajan tarbiyar yaranta dan haka nema dukkansu sun samu tarbiya mai kyau,sai dai ajizanci irin na ɗan Adam,,tana matukar son Junaid duk da ya kasance ɗan fari kuma duba da irin kunya ta fulani amman duk da haka tana nuna masa so, *JUNAID* yaro mai hanlaki da nutsuwa kyakkyawa ajin farko san ko wacce budurwa,dan ya haɗa duk abin da kowacce mace ke buri samu kyau kuɗi uwa uba ilimi,dan yana da haddar Alƙur'ani da wasu littattafai da dama,sannan ya yi digiri ɗinsa na farko a jami'ar dake kasar saudi in da ya dawo gida nageria ya yi digiri ɗinsa na biyu a nan Abuja,in da zuwa yanzu shi ƙwararren me zane-zanen gidaje ne da manya-manyan titinan sama,wan da ba anan ƙasarmu ba hatta ƙasashen waje suna Alfahari dashi ba dan kishin ƙasar sa da yake yiba da tini ya koma kasashen turawa da zama,wannan dalilin yasa be fiye zama a gida ba sabi da ya nayin kiraye-kiraye da yake samu daga gurare da ban-da ban,,yan zumma wani aiki ne ya kawosa KD saura kwanaki uku ya koma A buja,duk da dama Kaduna kamar gida take a gurinsa,yana yawan zuwanta sannan yana da abokan karatun sa,a cikinta wannan shine taƙai taccen tarihin Junaid,abin da ban faɗa ba ku bini bashi a cikin labarin,...
Cigaban labarin
Washe gari...
Comments and Share pls😍
Mmn Amatullah ce🥰
[03/09, 22:20] Alaweeyyah 1: ♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
*MATAR MAHAIFINA*
♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
~Labari da Rubutawa~
Na
MAMAN AMATULLAH
Wannan littafin na kuɗi ne za ki biya nera ɗari biyu (200)ta asusun banki 0003187186 khadija salisu ja'iz bank ko ki toro katin MTN na nera ɗari biyu ta wannan lambar *** ga mai neman ƙarin baya ni sai ya tuntuɓe ni ta lambar da ke sama.
FREE PAGE
Shafi na 43-44
Tin da ta tashi yau haka ta ke jinta cikin farin ciki,musamman idan ta tina da yana yin Junaid jiya,sosai ta ke sake tsin tar kanta cikin annu shiwa,sai dai ta kasa gane me hakan ya ke nufi dan gaskiya bata jin so ne,ba zeyiwu a ce so ya kamata cikin kwana biyu kacal ba,dan ko jiya da wannan tinanin ta ƙwana a ranta na ta karɓi soyayyar sa ko kuwa,dan tana ganin ita dashi akwai tazara mai nisan gaske kwatan kwacin tazarar dake tsakanin sama da ƙasa,,yan zumma zaune ta ke a falo,ta lula duniyar tinani,tin da ya fita tin safe bata sake ganin saba,duk sai taji kewar sa ta kama,ga tinanin sa da ya hana zuciyar ta sakat,zuwa yanzu ta fara yar da zuciyarta itama ta kamu,da san sa,a fili kuma ta ce dama haka so yake shiga tashi ɗaya,murmushi tayi tare da rufe fiska,kai kace wani yana kallonta ne,kiran sallar da aka fara yi ne ya tashe ta daga gurin ta koma ɗaki,tana shiga ɗaki yana shigowa,shima alwala ya yi ya wuce masallaci,,sam bata ji motsin shigowarsa ba,bayan ta idar da sallah ne ta fito falon,dan kallon tv yana ɗan rage mata kewa,,ledojin da ta gani ne zube a ƙasa suka bata mamaki dan ita dai tasan lokacin da tashiga ciki bata bar suba,har zata je ta duba sai kuma wata zuciyar ta ce idan kuma wani mugun abu ne fa,cikin sauri taja da baya,har da ɗan gudunta zata koma ɗaki,ba tayi zato ba ta tsinkayi muryarsa yana me ya faru kike gudu haka,ai ina ko juyowa ba tayi ba ta k'ara kwasa da gudu,zuwa ɗakin ta jiki na rawa ta sawa kofa key,dan ta tsorata da gaske,dan ko motsin buɗe kofa bata jiba sai magana, Junaid dake tsaye yana kallon ikon Allah abin ba ƙaramin dariya ya basa ba,,takawa ya yi a hankali, zuwa kofar ɗakin nata kwankwasawa,ya yi,yana cewa ke ni ne fa wai wannan wanne irin tsoro ne haka,ki buɗe Junaid ne, ajiyar zuciya ta sauke jin muryarsa,sakkowa tayi daga saman gadon ta ƙaraso bakin kofar cikin tsoro ta ce waye? Ninefa Junaid ki buɗe na ce,wata ajiyar zuciyar ta ƙara saukewa dan yanzu ta tabbatar shine bu ɗewa tayi,har ya bar gurin mayafinta ta ɗauka,ta fito zuwa falo zaune ta samesa,da sallama ta shigo,zama ta yi a ɗan nesa dashi,tana Yaya sannu da dawowa,duban ta ya yi tare da cewa yauwa sarkin tsoro,baki ta turo tana cewa to ba kai bane ka tsorata ni, ido ya ɗan zaro tare da cewa "Nikuma Aa ni kam babu ruwana dama a tsorace nazo na sameki wai ma me yasa ki gudu ne? To ba wannan ledojin na gani ba bayan kuma ni da na tashi ban barsu a gurin ba" ta ƙarasa maganar tana turo baki, me Junaid zeyi ban da dariya,sosai ya yi dariya,ita kuma ta samu abin kallo dan hani tayi ya yi mata ɗan karan kyau,sai da ya yi me isar sa kafin ya ce " Yanzu ke ban da abinki ai kin dai san basu da ƙafa balle sukawo kansu kin san ajiyesu a kayi,to ni na ajiyesu lokacin da na shigo kina ɗaki ina ajiyesu na wuce masallaci,shi kenan sai ki dena jin tsoron su,sarkin tsoro" Ya k'arasa maganar yana dariya "Cike da shagabar da ita kan ta batasan lokacin da ta yi ta ba ta ce Allah ka ga ni kade na yimin dariya" yan da tayi maganar sai da ta ratsa zuciyarsa, "To shi kenan na dena yan zu tashi ki ɗauko ledo jin ki fito da kayan ciki" ta shi ta yi ta ɗauko ledojin ta fara dubawa,ɗaya hijabai ne a ciki ɗaya kuma dohayen riguna ne dayar kuma abin cine da sauran kayan ciye-ciye, "Wa innan kayan na kine duka kiyi amfani dasu,miƙomin nawa abincin,dan yinwa nakeji sosai" Abincin ta ɗauka ta miƙa masa tana cewa " Yaya wannan ɗawai niyar ba tayi yawa ba" Harara ya dalla mata kainta ta sunkuyar k'asa tare da cewa "Kayi hak'uri Nagode Allah ya ƙara buɗi Allah ya rabaka da sharrin maƙiya" Amin ya amsa ya cigaba da cin abinci tare da cewa "Inason magana dake idan kina da lokaci" "To Yaya ina sauraronka" "Ke baza kici abincin ba? "Zanci amman sai anjima" Duban ta ya yi tare da cewa "Nalura dake bakyason cin abinci,kar ki bari an jima na bin cikeki baki ciba" To tace na murmushi, co kalin hannunsa ya ajiye ya dubeta sosai kafin ya kira sunanta *JUHAIINAA* sosai taji yan da ya kira sunanta har cikin ranta,ya yi mata daɗi, na'am ta amsa tare da kallonsa yan da taga ya kafeta da ido ne yasa ta sukuyar da kanta,ƙasa, cigaba ya yi da magana "Dalilin da yasa na ce dake ina san magana dake akan maganar da nayi miki ne shekaran jiya,naji har yanzu baki bani amsaba,amman fa karki damu ba matsa miki na keyiba,kifaɗan gaskiya idan bakya sona kuma nayi miki alk'awarin babu abin da ze canza,tsakanina dake,dan haka karki ji komai" Kai ta ƙara sunkuyarwa ƙasa tana wasa da ya tsunta kafin tace "To Yaya idan nace bana sanka nayi k'arya kuma na yaudari kaina sabi da kai mutum ne me kyawawan Halayyah baka da wani aibu da har zan k'ika,amman kana ganin iyayenka zasu amince da ni duba da ni ba tsararka bace akwai tazara me nisa a tsakanina da kai" "Karki samu da muwa iyaye na duk suna da fahimta kuma zasu fahimce ni,kuma zasu karɓeki a matsayin ƴa nayi miki wannan alk'awarin" "To shikenan Allah yasa mu da ce" tana faɗar haka tayi shiru duban ta ya yi tare da cewa amin sannan ya ƙara da cewa to "Naji wannan amman har yanzu baki bani amsa ba kina sona ko Aa? "Ina sanka da duka zuciyata *I LOVE YOU JUNAID* tana kai wanan ta tashi da sauri tabar gurin cike da kunya har da ɗan gudunta, Alhamdullah! Alhamdullah!! Alhamdullah!!! ya faɗa yana dariya yana cewa "To ina zaki kuma? Ina ai ko joyowa bata yiba tayi ɗakinta, abincin ya ture gefe ɗaya dan farin cikin da yake ciki har yasa yaji ya ko shi,lallai zejewa da su dad da mom Albishir me daɗi dama kullum faɗan da suke yimasa kenan ya ƙi ya samu natar aure to yau dai Allah ya yi,kai Alhamdullah!
Tana shigewa ɗaki saman gado ta faɗa tana dry yau jin ta take kamar tafi ko wacce mace sa'a a rayuwar ta,
Cikin kwana biyu sun k'ara shakuwa sosai sabi da Junaid shi mutun ne mai nuna kulawa a soyayyah, yau sun tashi da shirye-sharyen tafiya Abuja,tin da ta tashi yau take tafaman jin faɗuwar gaba,sai dai tana ta faman addu'a a zuciyarta,,zaune take a falo sosai ta yi nisa cikin tinani ta yan da har ya shigo ba ta sani ba,zama ya yi a kujerar dake gefenta,ya tafa hannunsa a saman fuskarta ya ce "Lafiya kike irin wannan dogon tinanin haka?HMMM nisawa ta yi tare da cewa "Wallahi tin da natashi idan na tina da yau zan haɗu da ƴan uwanka da iyayenka sai naji gabana yana ta faɗuwa,anya kuwa Yaya kana ganin babu matala? "Karki damu kin kwantar da hankalinki kinji insha Allah babu wata matsala,zasu karɓeki hannu bibbiyu,banason ina ganinki cikin damuwa nima hakan yana jefani a danuwa,kiyi min alkawri kin dena wannan tinanin" "Insha Allah na dena Allah ya shige mana gaba" "Amin,amman ki ɗan yimin murmushin nan naki,ko naji sanyi a raina" Mirmushi ta yi tare da boye fiskarta a cikin hijabi, "yauwa ko kefa amman fa ban yar da da wannan wayon ba ana boyemin wannan kyakkyawar fuskar" "To ai ni kunyarka nake ji kadena yimin irin wannan kallon" "Taf kun yata fa ai kuwa kwanan nan zan rabaki da ita garama ki shirya dan ni bazan laminci wannan ba,ko dan kinga bani da iko da duk abin da kika mallaka,to amma kwana kadan zan zama ina da cikakken iko,kuma zanyi duk yan da nakeso kuma baki da ikon hanawa" "Nikuwa Yaya Meye abin da na mallaka wan da baka da iko a kansa? Murmushi ya yi tare da cewa zaki sanshi nan ba da jimawa ba" Cike da shagwaba ta ce ni ni Allah ban yar da ba sai dai yanzu a faɗa min" "Kinga mubar wannan maganar dan naga za ki fara wannan shagwabar taki,ke baki san kina cutar dani da ita ba" ido ta zare tare da cewa "Ni da kai na ya ya,ni Allah Aa ai ko wani naga ze cutar dakai sai in da ƙarfina ya ƙare,ballekuma ni da kaina" Yan da ta ƙarasa maganar cike da shagwaba kanar zata saka masa kuka" kai ya dafe yana cewa "Ya Salam baza ki gane ba kinga tashi ki k'arasa shiryawa muzo mu tafi tin kafin ki wargazamin lissafi" Baki ta buɗe da niyar yin magana ya dallah mata harara,babu shiri ta tsuke baki ta tashi ta nufi ɗakinta,yasan idan ya kyaleta to babu makawa duk maganar da za ta fito daga bakin ta cike da shagwaɓa zata fito,ita bata san hakan yana sashi shiga cikin wani yanayi ba,kai ya dafe, yana cewa wannan yarinyar ta cika rigima,,ta shi ya yi shima ya wuce nasa ɗakin,ya cigaba da shiri,,shima zuciyarsa cike da fargaba dan yasan tabbas sai sun ɗebota da mom ɗinsa kafin ta amince karfin guiwarsa dama dad ɗinsune kuma yasan yana gari to kome ze faru yasan zezo da sauki,da wannan tinanin ya cigaba da shiri,duk da dama shi ba wani abu ze ɗauka ba,,,
Sanye take cikin wata bakar Abaya wacce ta gaji da haɗuwa,sai a gogo dake daure a hannunta,sai naɗe kanta da tayi da ɗan mayafi,,nan na ƙara ganin zallan kyanta duk da batayi kwalliyaba,tana fitowa,yace wow masha Allah tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan kyakkyawar surar, murmushi tayi tare da cewa ngd amman dai ai bankai Yayana kyau ba" ido ya zaro yana "ke wane ni ai babu ko haɗi,cike da shagwaɓa tace "Allah ni ban yar da ba" "za ki fara ko to mubarta iya nan na yar da kingama shiryawa?,kai ta ɗaga alamar eh,to muje ko,jakar hannunta ya karɓa ya yi gata bi bayan sa,ni sai nagama kamar suna kama da juna lox
Tini suka ɗauki hanya suna tafe suna taɓa firarsu irin ta masoya,cikin abin da be wuci awa biyu ba sai gasu a wani katafaran ƙofar gida,wannan shi ake kira da Aljannar duniya gida ne kamar ba naheria ba tsayawa faɗar kyan gidan da taruwar sa bata lokacine iya harabar gidan kaɗai aka barka da ita abar kallo ce sabi tsurraine iri daban-daban iya ganin ka,sosai Juhaina ta saki baki tana kallon irin wannan kata farangida,ai bata gama tsikewa da lamarin ba sai da ta shiga falon gida,sai dai sam a zahiri bata nuna kauyan ci ba,da sallama ya shiga falon,da gudu wasu ƴan mata guda biyu sukayo lansa suna oyoyo babban Yaya wata mata shiyar dattijuwa dake zaune itama dariyar ta ke tare da cewa barka da zuwa my son oyoyo, shima rungume ƙannansa ya yi yana cewa nayi kewar ku ƴan k'annena, muma haka yaya ya hanya Alhmdllh,yana faɗin haka ya sakesu ya tafi gurin matar dake zauna yana faɗin I MISS YOU MOM ƊINA murmushi tayi tana me two dear,rungume ta yayi yana sosai fa nayi kewarki rabin rai na,my fest love,wani daɗi ta keji duk lokacin da taga ɗanta a kusa da ita,Dad dake sakkowa daga sama yace ni kumafa my son, ta shi ya yi har da ɗan gudunsa ya ƙarasa in da Dad yake ya rungumesa yana Dad kewar ka irin ba iyakar nan ,uba nagari,kansa Dad ya shafa yana cewa ya hanya,Alhmdllh Dad,to masha Allah hannunsa ya kama suka sakko kasa guri suka samu suka zauna,
Duk abin nan da ake Juhaina tana tsaye tana kallonsu cike da burgewa dan ba ƙaramin sha'awa suka bata ba,sai bayan da ya zauna ya tina da ita duban ta ya yi tare da cewa "ki ƙaraso mana kika tsaya anan,dukkansu bin in da ya kalla sukayi dan duk basu gan taba sai yanzu A hankali ta dinga takowa har zuwa gaban su kowa sai kallonta yake da kuma tambaya fal zuciyar kowa, ko da ta ƙaraso,a kasa ta zauna Dad ta fara gaisarwa sannan mom sannan suka gaisa da su Farhat,dukkansu angaisa babu yabo babu fallasa, mom ce ta dubi Junaid ta ce "my son wannan ɗin wacece ita? Daga shi har Juhaina sai da gabansu ya faɗi da jin wannan tambayar ta Mom,,,
Tofa my fans kuna ganin Mom zata amince kuwa?
comments and share plz
Mmn Amatullah ce🥰
[03/09, 22:20] Alaweeyyah 1: ♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
*MATAR MAHAIFINA*
♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
~Labari da Rubutawa~
NA
MAMAN AMATULLAH
💫💫
*
Wannan littafin na kuɗi ne za ki biya nera ɗari biyu(200)ta asusun banki 0003187186 khadija salisu ja'iz bank ko ki tiro katin MTN na ɗari biyu ta wannan lamabar *** ga mai ne man ƙarin baya ni ya tuntuɓe ni ta lambar da ke sama..
FREE PAGE
```Saura shafi ɗaya free page ya kare gamasu son cigaban labarin zasu biya ɗari biyu kamar yan da``` na faɗa ngd
Shafi na 45-46
Dad ne ya du bi Mom ya ce "Haba ki bari mana su huta ai duk abin da ki ke so kiji duk za ki ji saurin me ki ke yi" Baki ta taɓe tare da cewa "Tai shi ke nan" tin daga nan ta yi shiru bata sake cewa ko mai ba sai kuma gurin rin ya yi tsit,duk sai Junaid yaji ya tsargu dan haka ya mi ke yana murmushin ya ke ya ce "Mom Dad ni bari na wuce ɓangare na na ɗan watsa ruwa" "To shi kenan ka je idan an gama shirya teburin cin abincin za'a kira ka" Amsawa ya yi da to Mom kafin ya du bi su Farhat ya ce "Ku ɗauki kayan ta ku raka ta sama ku bata ɗaki itama ta huta kun ji ko" Da ya ke Farhat ta fi Farhana sauƙin kai tana murmushi ta amsa da to ya ya kafin ta dubi,Juhaina ta ce muje ko,jiki a matu ƙar san ya ye ta mike tsaye,ta bi bayan su,Mom ta bisu da kallo zuciyar ta fal da tambayoyi,sai dai dole ta jira lokacin da ze amsa mata su,,wani kata faran ɗaki suka kai ta iya gadon da ke ɗakin kaɗai abin kallo ne bale wadrop abin sai wan da ya gani,, Farhat ta ce "Bismillah shigo ko to ga ɗakin ki daga yau idan akawai abin da babu sai ki sanar dani na sa a kawo miki" Murmishi Juhaina ta yi tare da cewa "To nagode" "Karki da mu ƴar uwa wai ma ya sunan ki ne? Murmushi ta sake yi tare da cewa "JUHAINA" Wow suna me daɗi gashi ya da ce dana babban ya ya kamar yan da kuka da ce gaskiya bazan boye miki ba ke kyakkyawa ce" Nagode Juhaina ta faɗa tana murmushi, Farhana da ke zaune a gefe tana latsa waya baki ta ta ɓe tare da cewa, "Ke kuma kin cika surutu da yawa kawai daga ganin mutum sai ki ta faman zuba,mtsss" tsaki ta ja tare da ta shi tsaye ta fi ce, "Kinga kar ki damu da ita haka ta ke tana da wahalar sabo" "La ai ba bu mai ƴar uwa Nagode" "Au na manta ban faɗa miki sunana ba ni ɗai sunan Farhat ita kuma da ta Fita Farhana ta ke" "Masha Allah suna me daɗi" "Mun gode sister ni bari na fita na barki ki huta ko" Ah haba ke kuwa muna ƴar firar mu za ki ce za ki tafi" "Karki da mu ki huta yanzu zuwa an jima zan dawo musha fira" "To shi kenan nagode" nan dai Farhat ta wuce ita kuma ta fara kallon ɗakin tana jin jina haɗuwar sa sosai ta saki baki,ta ke kallo,a zuciyar ta ta ce lallai arziki yana in da ya ke irin wannan katafaran ɗaki haka,ƙwanciya ta yi a saman gadon wani laushi ta ji kamar auduga,ido ta lumshe tana sha ƙar ƙamshin ɗakin,ta ɗan jima a kwance kafin ta tashi ta shiga bayi,nan fa ta ƙara kashe kwar-kwatan idon ta wani abun ma bata san yan da aka amfani da shi ba,,wanka ta yi ta fito daure da alwala dan taji ana kiran sallah,,tana fitowa ta saka kaya tare da ta yar da sallah,ba yan ta idar zama ta yi a gurin ta ɗanyi tilawa har aka kira sallar isha,sai da ta yi sallar isha tare da addu'o'i sannan ta tashi daga gurin gefen gado ta koma ta zauna tana tinanin yanayin da ta ga mom ɗazu anya kuwa zata kar ɓeta,a matsayin surika,sosai ta lula duniyar ti nani ga kuma kewar Junaid da ta ke yi,tanan zaune taji ana kwan-kwasa kofa izinin shigowa ta bayar,wata mata shi yace ta shigo hannunta ri ƙe da tire,da sallama ta shigo,tana gai she da Juhaina tare da cewa dama abinci ne aka ce na kawo,mi, to nagode cewar Juhaina,kana ganin ta kaga mai aiki dan har da kayan aikin ma a jikinta,sannan ta sake duban juhaina ta ce Hajiya idan kingama ki danna wannan ƙararrawar zan zo na kwashi kwanikan,ta faɗa tana nuna mata,to jihaina ta ce tare da godiya,,tana fita Juhaina ta sauko,ta fara dubawa dama yiwa ta keji,abinci ne kusan kala uku, ban da far fesu na kayan ciki dana kaji,farfesun kawai ta ci sai tuwo kaɗan da ta ɗiba,,
Zaune su ke dukkansu a akan teburin cin abinci shiru ne ya ratsa gurin sai k'arar cokula da ke tashi,,har suka gama babu wan da ya ce ƙala wannan al'adar gidan ce,duk me magana ya bari sai anci abinci,suna gama wa gaba ɗaya suka koma falo aka ɗan ta ɓa fira,kafin Mom ta ce ""o yanzu ai za ka iya yi mana bayanin ko wacece ita ko",Dad ya amsa da cewa "Eh maganar mom ɗinku haka take kafa ɗa mana ita ɗin wacece? Duban su Farhat ya yi tare da cewa ku tashi ku bamu guri za muyi ma gana,to suka ce tare da miƙewa,suka bat gurin,zama ya gyara tare da duban Dad da Mom ya ce to da far ko dai sunanta Juhaina kuma ita ƴar kano ce sai dai mun haɗu da ita a kaduna ne,sannan ta shiga wani irin siraɗi na rayuwa tin daga kuruciya har girma,nan dai ya kwashe kaf labarin ta da ya sani ya faɗawa su Dad,amman be faɗa musu tayi zama a gidan karuwai ba,dan yana ganin wannan sirri ne,,sosai suka tau saya mata,musamman Dad Mom ta dubesa tare da cewa "To munji wannan,mun kuma tausaya mata amman me nene manufar kawo ta nan baɗai ka tema ke taba? Hmmm ni sawa ya yi tare da cewa Dad Mom bazan boye muku ba kallon farko na yiwa ya rin yar nan son ta ya shiga zuciya ta wannan da lilin ne ma yasa dana gano ta nakuma temake ta sannan na kawo ta nan dan inaso na Aureta, what Aurefa kana da hankali kuwa,ka rasa wacce zaka aura sai tsin tacciya wacce babu tabbas in tana da asali wacce har zama tayi a titi ita zaka ɗauko ka kawo min gida ama tsayin surika to baka isaba,kaji na faɗa maka tin wuri ma ka canza tinani" "Za ki yi shiru na yi magana ko kuwa za ki yi gaban kanki? cewar Dad shikuwa Junaid dama yasan haka zata faru dan haka ya ma rasa mezece ban da fargaba da tsoron rabasa da Juhaina da ya bai bayesa,, Dad ne ya dora da cewa "Ke wai wacce irin mace ce, harkullum ina nuna miki ra yuwa amman sam bakya ga newa to ki gaya min me ne ne aibu dan ya aureta,baga dai dukkanmu musulmai ne ke ko da ace ba addinin mu ɗaya ba yana da damar ya aureta balle kuma addinin mu ɗaya,dan haka ni banga wani ai buba" "Ai dama kai haka za ka ce to idan kai bakaga ai buba to ni na gani,dan haka in dai ni ce uwarsa to baze aure ta ba" "Au haka kika ce,to bari ki ji in dai ni ne uban sa sannan in dai ni ne mai faɗa aji a gidannan sannan ko wa da yake cikin gidannan a ƙar kashina ya ke to ze auri yarin yar nan idan kinga be aureta ba to shi ne ya ce ya fasa da izinin Allah,kinji na faɗa miki" "Haba Alhaji yanzu idan kace haka ni kayi min adalci kenan amman tin da ka ce haka ayi mugani" "Zakuwa ayi ɗin da yar dar Allah kuma zan baki mamaki ki dan kisan cewa ba dawasa na ke yiba" "To muzuba mugani" Tana kaiwa nan ta tashi ta haye sama, duban Junaid Dad ya yi tare da cewa ka tabbatar kana son ta itama tana son ka? Cikin rawar murya ya ce "Eh Dad ina son ta itama tana sona" "To shi kenan kar ka samu da muwa insha Allah zaka aureta gobe-gobennan da sauri ya kalli dad ya ce "Dad gofa to Mom fa?Kar ka damu da ita zan ji da ita kai dai kawai ka sanar da abokanan ka na kusa go be bayan sallar azahar za'a ɗaur A babban masallaci" Cikin matsanan cin farin ciki ya ce "Dad nagode Allah ya ƙara girma" Kar ka damu je ka abin ka,Junaid yana ta fiya ɗad ya fara kiran muta ne yana sanar dasu ɗaurin auren ɗansa gobe ko wa sai mamaki ya ke tare da tambaya sai dai ya ce kawai ba yason ya wahalar da na nesa ne,,
Junaid na barin gurin kai tsaye ɗakin Juhaina ya nufa,yana addu'ar Allah yasa ba tayi bacci ba,ya ko ci sa'a tana zaune tana tinanin sa ta kasa bacci taji ana kwan-kwasa, waye tana ta addu'ar Allah yasa shi ne,ba ta gama addu'a ba kuwa ta tsinci muryarsa,cikin zumuɗi ta zura hijabin ta ta ƙarasa ta bu ɗe masa,ajiyar zuciya ya sauke har tana jinsa,ji ya ke kamar ya rungumeta sai dai kashi ya fi so ta zama tasa kafin ya kai hannu zuwa jikin ta,wani murmushi ya sakar mata tare da cewa "Har yanzu ba kiyi bacci ba? Ta ya zan iya bacci bayan ka hana zuciyata sukuni" Ta ƙarasa maganar tana rufe ido murmushi ya yi tare da cewa "nima tin ɗazu kin hana zuciyata sa kewa ina can amman zuciyata na gareki" Zama ta yi a gefen gadon tana cewa "ya na ganka baki ya ƙi rufuwa ne? "Albishir ne dani guda biyu da ya zan baki kyauta ɗayan kuma sai kin biya" "To shi kenan a fa damin duka sannan sai a faɗamin farashi" "Aa fa za ki iya biya kuwa? "To me ze hana ka faɗa ka gani" ta ƙarasa maganar tana dry, "To albishir na farko Dad ya amin ta da Auren mu Albishir na biyun kuma kibini ba shi zuwa gobe insha Allah" Cikin farin ciki ta ce kai Alhmdllh, to banji ka ce mom ba? "Bazan boye miki ko mai ba mom ta ki amin cewa amman karki samu da muwa Dad ya ce na bar masa ko mai" Jiki a san ya ye ta ce "Kana ganin hakan babu matsala? "Babu komai insha Allah" Ta amsa da Allah yasa nan dai suka taɓa ƴar firar su kafin ya yi mata sai da safe ya wuce ɓan garansa,shima a daran ya sanar wa da duk abokansa na kusa kowa sai mamaki ya ke
Mom kuwa tin da ta koma ɗakin ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman kaiwa da komowa ta ke tana neman ma fita dan tasan tin da ya ce haka zance ya ƙare, zama ta yi ta da fe kai tare da ɗaga filo ta ɗauko wani tshon hoto,tana kallo tana hawaye,,ta jima a haka kafin ta mayar ta ajiye a in da ta ɗauko sa,
Washe gari aka ɗaura auren JUNAID DA AMARYAR SA JUHAINA AKAN SADAKI NERA MILIYON ƊAYA 1 million naira duk da auren yazo babu shiri amman ya samu halartar manya-manyan muta ne, da dama kuma guri ya cika sosai,can na hango an sha manyan kaya sai faman dariya ake,ga zugar a bo kai sun yi masa halacci,bayan an ci an sha ko wa ya kama gaban sa in da Dad ya wuce gida shi kuma ya tsaya sallamar a bokansa,,
Yan zummah dai ri ƙe ta ke da wannan hoton tana ta faman zubar da ƙwallah wani lokaci kuma kaga ta yi murmushi,Farhat da Farhana ne suka shigo da sallamarsu amman sam Mom ko motsinsu bata jiba,zama su kayi a gefen ta tare da dafata sai a lokacin ta dawo cikin tinanin ta du ban su ta yi tana goge hawaye, cikin sanyin murya Farhat ta ce "Mom ga dukkan alamu sun nuna kina cikin damuwa dan naga wannan hoton wan da ki ke kallah a kullum mu samman lokacin da ki ke cikin damuwa sannan ga hawaye a idonki" mom dan Allah ki faɗa mana damuwar ki" cewar Farhana' murmushi ta yi wan da ya fi kuka ciwo ta ce, kwarai kuwa wannan hoton shi kaɗai ne ya ke sani farin ciki idan na gansa,sannan kamar yan da kuka ce tabbas ina cikin da muwa","to wai mom me a cikin hotannan suwaye a jiki?sannan me ya ɓata ranki har haka? murmushi ta ƙarayi tare da duban hoton ta ce "Wata rana zan fada muku ko suwaye,wai Yayan ku ne ze yi aure" Cikin ɗoki suka ce "To mom me ye abin ɓacin rai a ciki?Naga kullum burinki kenan" Hnmm "Na fi kowa san naga Yayanku ya yi aure,to amman ba irin wannan ba,yarasa wacce ze auro sai marar asali wacce ya tsinta a titi,wai fa wannan yarinyar ze aura," "Wacce yarinyar kuma mom? Dauk suka faɗa a tare, "Yarin yar da yazo da ita jiya mana,wai ita ze aura" dukkansu iso suka zaro suna ita kuma mom? "To amman kuma mom ai kamar sun da ce da juna kuma ni banga aibun ta ba indai tana da tarbiya" cewar farhat "ke tafi can ina wani da cewa anan yana ɗan asali ita kuma ba a san daga in da ta fito ba,za ki ce wani sun dace sakarai da ke" cewar mom "Um gane min han ya dai mom wai makafi sunyi dare ai babu da cewa sai ƙaskanci," cewar Farhana "ai rabu da wannan dama duk halin su ɗaya, "To yanzu mom wanne mataki za ki ɗauka a kanta? "Ai na yan ke shawarar na koreta kawai yanzu yanzu tin kafin su dad ɗinku su dawo" "Ai mom hakan kawai za ki yi, ki sakko ƙasa yanzu zan kirawo miki ita,yawwa to kiyi sauri cewar mom "Haba mom dan Allah karki haka shifa ɗa na kowa ne" "ke dallah sakarai rufemin baki,ki kuma matsa ki bani guri" baya ta ja tare da cewa Allah ya baki haƙuri,,ko kulata mom bata yi ba,ta fice itama bayan ta tabi da sauri,suka sauko kasa...,,
Insha Allah page ɗaya ya rage free page ya ƙare,duk wan da yake son jin cigaban labarin ze iya biyan nera ɗari biyu kamar yan da na faɗa,.ngd
comments and share plc
Mmn Amatullah ce😍
[03/09, 22:20] Alaweeyyah 1: ♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
*MATAR MAHAIFINA*
♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
~Labari da Rubutawa~
NA
MAMAN AMATULLAH
💫💫
*
Wannan littafin na kuɗi ne za ki biya nera ɗari biyu(200) ta asusun banki 0003187186 khadija salisu ja'iz bank ko ki turo katin MTN na ɗari biyu(200) ta wannan lambar *** ga mai ne man ƙarin baya ni ya tuntuɓeni ta lamar da ke sama.
LAST FREE PAGE
~Daga yau free page ya ƙare ga me bu ƙatar ci gaban labari ze biya ɗari biyu kamar yan da na faɗa..~
Shafi na 47-48
A bo kan ango an haɗu guri ɗaya sai faman tso kanar an go ake,da ango kasha kamshi,irin wannan gaggawa haka wai me ye sirrin ne mutumina, da riya Junaid ya yi tare da cewa "Ai mutumina abin ba'a cewa ko mai a she haka soyaya ta ke da daɗi amman fa idan ka da ce da wacce ta ke sanka ni dai na da ce da tawa kuma ina yi muku addu'a ku da ce" Ya ƙarasa maga nar yana dariya ɗaya daga cikin a bokan ya ce "Ku fa jiye mun abin da mutumin nan ke cewa, ko yau she ma ya fara soyayyar da har ze faɗa mana yan da ta ke da daɗi" "Eh na ji dai ko yau na fara ai dai na fi wasu" Ya ƙarasa ma ganar yana kallon wani abokin sa da ya ke gegensa, "Kai malam lafiya kake wani kallona nifa banason saka ido,ni kaɗai ne a dakin da zaka kalle ni" Gaba ɗaya ƴan dakin dariya suka saka, Junaid ya ce "To ni dai banyi magana ba ban kuma kama suna ba ashe dai ka tsargu,tim da ka tsargu bari nayi magana a kanka, tin da ka zama tuzuru ka zauna she kara arba'in na doso ka amman ko budurwa ma baka da ita" "Eh na ji ɗin da nayi aure a kananun she karu ai gara na tsaya na mallaki hankalin kaina kai yanzu me ma ka sani a cikin auren? ya ƙarasa maganar yana harar Junaid, sake fa shewa da dariya abokan sukayi tare da cewa to kai ango kaji abin da Bash ya ce bama kasan meye auren ba to ya kenan? "Ku dallah ku rabu da shi an faɗa masa kowa ma irin sa ne me tsoron mata,kuma zan bashi mamaki nan da shekara ɗaya zaka dawo suna" Gaba ɗaya suka sake ɗaukan ihu, wan da aka kira da Bash ya ce "Ai ka ji irin jarabar ta ku ta yara to wallahi kabi yar muta ne a sannu" "Eh naji ni jarababbe ne amman dai garaa ni da wan da ba shi da jarabar ma sam" Nan dai suka yi ta ƴar tsama da ma sun saba in dai zasu hadu guri daya da Bash sai Junaid ya yi masa gorin aure dan duk ya girme musu,kawai dai yana da ƙaramin jiki ne,abota ce irin ta maka ranta lokacin da suka hadu duk sun mallaki han kulansu,, Bash shi ma Shahararen ɗan kasuwa ne kuma matashi,,wan da aƙallah ya dosowa shekaru arba'in amman ko budurwa ba shi da ita a cewarsa wai yanzu samun nagari a mata wahala ta ke gani ya ke ko wacce dan kuɗinsa suke sansa,dan ya taɓa ƴan mata a baya be ji daɗi ba wannan dalilin ya hana sa aure har yanzu iyayensa har sun gaji da faɗa...
Mi kewa Junaid ya yi tare da ɗaukan babbar rigar sa yana cewa "Abokai ni bari na je naga amarya ta dan ban da kewar ta babu abin da na keyi,ƙila zuwa anjima za ku iya ganina" Gaba ɗaya suka ɗauka da Ango Ango wato bama za ka bari a kai maka ita ba ko to wlh ka dai bi a sannu" Harar su ya yi tare da cewa to sarakan sa ido wato kuma Bash ya koya muku ko to naji kifaɗi duk a bin da kukeso ni dai yanzu duk babu sa'ana a cikin ku nayi gaba a cigaba da rungumar fulo" ya ƙarasa maganar yana dariya tare da fi cewa,...
Babu ko sallama haka ta banka ɗakin tare da kitsa kai ciki Juhaina da ke zaune ta buɗe jakar kayan ta tana gyarawa,ba karamin tsorata ta yi ba,da sauri ta ɗago kai tana duban,wan da ya shigo,Farhana ce tsaye a kanta ta wani riƙe ƙugu,tana yi mata wani irin kallo, jiki a matuƙar san ya ye,Juhaina ta mike tsaye tare da cewa "Farhana lafiya kuwa? Harara ta watsa mata tare da cewa "Kinga alamunta anan to babu ita,sannan duk abin da ki keyi ki ajiye kije mom na son ganinki" Ji ta yi gaban ta ya gaɗi to ta ce tare da ɗaukan hijabin ta ta saka tini Farhana ta yi gaba in da Juhaina ta rufa mata baya tana jin yan da ƙirjinta ya tsanan ta faɗuwa zaune ta samu mom a saman kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sai faman girgiza su ta keyi,, "Mom ga tanan" cewar farhana, tsu gunnawa ta yi har ƙasa tare da cewa "Mom ina yini" wani matsiyacin kallo ta watsa mata kafin ta ce, "Ke kinga ban kiraki nan dan ki gaishe ni ba,ko an faɗa miki ina da buƙatar gaisuwar ki ne,to ban da bu ƙata,kin san me yasa na kira ki? Kai ta girgiza tare da cewa "Aa mom" "To na kira ki ne a kam maganar yaro na duk kuma naji abin da kika kitsa masa wato sabi da kinga gidan dukiyi shi ne kika maƙale masa ko to bari kiji tun wuri ma ki sake tinani dan bazan taɓa barin ɗana ya auri tsin tacciya ba,dan shi ba sa'an aurenki bane,dan haka idan kina son kanki da arzki ki tashi tin kafin Dad ɗinsu da shi kansa sudawo cikin gidannan ki fice min daga gida idan kuma ƙinki zan sa afitar da ke ta ƙarfi kinji na faɗa miki" Cikin kuka ta ce "Mom dan Allah kiyi ha kuri wallahi ban san ina zan jeba idan kika koreni" "Toni ina ruwa na kije duk in da kike ganin ya yi miki amman zama a gidannan ya ƙare miki,maza ki tashi ki fice min a gidan tsin tacciyar mage,kawai,idan kuma ba haka ranki ya yi mugun ɓaci" Mi kewa tsaye ta yi tare da cewa "Mom zan tafi nagide da kwana ɗayan da kika barni nayi,Allah ya saka, sannan ta ƙarasa kuaa da Farhat da take ta zubar da ƙwallah rungume juna sukayi suna ƙara fashewa da kuka, cikin miryar kuka Juhaina ta ce "Ƴar uwa na gode kwarai da karamcinki gareni,Allah ya ƙaddara saduwar mu" "cikin kuka tace dan Allah ƴar uwa kada ki tafi,ina jinki a raina tamkar wacce muka fito ciki ɗaya" Murmushin ya ke Juhaina ta yi tare da cewa nima haka na kejin ki to amman kinji duk abin da mom ta ce dan haka kiyi hakuri idan da rabo wata rana zamu gana" ta ƙarasa ma ganar tana kuka, "Za ki ficemin a gida ko kuwa an faɗa miki nan gidan mutuwa ne" Mom ta faɗa cikin ɗaga murya, sakin juna sukayi ta fara ta fiya, Farhana ta ce "ke tsaya wa incan tsommo karan naki fa wa kika barwa? Juyowa ta yi tare da dawowa ba tare da ta ce ko mai ba,dan batajin zata iya magana sabi da kukan da yake cinta, "ke ina za ki dakata anan ai kingama hawa samannan kitsaya a in da kike yanzu zan kwaso miki tarkacen ki,ita dai bata ce ko mai ba ta tsaya sai sharar kwalla ta keyi,haurawa sama Farhana ta yi tana shiga ɗakin ta ɗauko jakar kayan a yan da ta ke ko zugeta ba tayi ba,tana fi towa ta watso wa Juhaina jakarta a jiki gaba ɗaya kayan jakar suka tarwatse,a ƙasa, ta ɗora da cewa "Gatsiyar ki nan sai ki kwashe ki kara gaba dan nan gidan ba masaukin irin ku bane, kamar daga sama suka tsinci muryar Junaid yana cewa "Ke Farhana ashe baki da kunya to babu inda zata itama nan gidan ta ne dan kuwa yanzu haka a matsayin mata take a gurina dan yanzu aka ɗaura mana aure,ni da ita" Gaba ɗaya falon mutuwar tsaye sukai sai bin Junaid sukeyi da kallo,ko wa ya kasa cewa,ƙala,ita kuwa Juhaina jitayi kamar bataji dai-dai ba, cikin fishi Mom ta ce "Me kunnuwa na suke jiye min eh my son kana so kace wannan abar ita ce matarka? "Eh mom yanzu haka daga wajan ɗaurin auren miki" "To wallahi ba ku isaba ya zama dole ta tattara yanata ya nata ta bar gidannan yau,ɗinnan, kaji na faɗa maka kuma a yanzu na keso ka saketa,ta fita ta barmin gida,bana so ka ƙara ko da ta ku ɗaya ne idan baka saki yarinyar nan ba,, "Baki isa ba nace baki isaba" cewar Dad da yasako kai cikin falon, ya ɗora da cewa "Aure tsakanin su sai dai mutuwa insha Allah amman yariga da ya ɗauru sannan ke baki isa ki raba shiba idan kuma har kikayi kokarin yin haka to tabbas za ki ga mummunan hukuncin da zan ɗauka a kanki,kuma yarinya zama daram a gidannan kin ji na faɗa miki" Shiru falon ya yi babu me cewa ko mai Juhaina dake durkushe ban da kuka babu abin da ta ke yi,
Baki mom ta buɗe da niyar yin magana idonta ya sauka a kan wasu hotuna da ke zube a gurin ƙafafunta,kafe su ta yi da ido kafin jiki na rawa ta kai hannu ta ɗauka,,tana kallon wa'in da ke jikin hoton,baki na rawa ta dubi Juhaina da ke tsugunne ta ce "Ke a ina kika samu wannan hoton? ta faɗa tana nuna mata,rinannun idanunta ta ɗago tana kallon hoton kafin cikin muryarta wacce ta da she ta ce, "Na wa ne" "cikin faɗa mom tace k'arya ki ke yi wannan hoton nawa ne aɗakina kika ɗauka" "Wallahi mom da abina na nazo" Duban farhana mom ta yi tare da cewa maza jeki ƙasan fulona ki gani ko hoton nan da nake yawan kallo yana nan" Da gudu ta haura sama gama makin ta tana ɗaga filo sai ga hoto,iri ɗaya da na hannun mom,da gudu ta fito tana mom mom,Wallahi gashi yanan, jiki na rawa mom ta karba ta duba shine kuwa, baki na rawa ta dubi Juhaina ta ce "Ke waya baki wannan hoton a ina kika samesa? Juhaina na kuka ta ce "Hoton Ummy na ce,wannan ita ce ma" ta karasa maganar tana nuna wata ƴar ƙaramar ya rinya dake jikin hoton,tini jikin mom ya fara rawa baki na rawa ta ce "me ye sunan ta? "Sunan ta Maryama" Cikin kuka me tsanani mom ta ce Wallahi ita ita ce Wallahi itace jini na ce kawai sai gani .sukayi mom ta faɗi sumammiya gaba ɗaya sukayo kanta a matukar ruɗe.....
Alhamdullah
Anan na kawo ƙatshen free page ɗina ga wan da ya ke son jin cigaban labarin ze biya 200 kamar yan da na faɗa,ngd
Shin me ne ne alaƙar mom da Juhaina?
Me yasa mom ta suma bayan ta ji sunan maryama?
Shin ya soyayayyar JUHAINA DA JUNAID zata kasance?
Shin ya ku ke gani haɗuwar Maryama da ƴarta Juhaina ze ka sance?
Shin me ne ne ma komar SA'ADE kuwa?
Dan jin duk wa ɗannan amso shin ku biyoni a cigaban labarin dan jin yan da zata kaya, duk akan naira ɗari biyu kacal (200) me neman ƙarin ba yani ga lambata ya tuntuɓe ni ***
Comment and share plz
Mmn Amatullah ce😍