Free chapter ยท Read without an account

19.

by Nusaiba ยท SARAUTAH TAH CE

๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘


*SARAUTA TAH CE*




*Ga masu son a tallata masu HAJA kofa a bude take ku matso kusa domin bunkasa kasuwancin ku*








*DATA...๐Ÿ—ฃ๏ธDATA...๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธDATA...๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ*



*INA MASU SON SIYEN DATA AKAN FARASHI ME SAUKI? YAU GA GARABASA TA SAMU๐Ÿ’ƒ๐Ÿป DATA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA๐Ÿฅฐ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป NUCEEYLUV NA MUKU MARABA DA SIYEN IYA KUDIN KA IYA SHAGALIN KA๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป*



*500MB - N200*

*1GB - N300*

*2GB - N600*

*3GB - N900*

*5GB - N1500*



*1 month validity*


Call๐Ÿ‘‡๐Ÿป or cht me private๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป


***


*ANA TURO KUDI TANAN๐Ÿ‘‡๐Ÿป*


Via....1445626295 Nusaiba Mustapha Access bank.


*BANA KARBAR KATI PLS๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜*



*KUNA TURO KUDI ZAKU JI ALERT DIN DATA INSHA ALLAH BABU BATA LKCI๐Ÿ™…๐Ÿปโ€โ™€๏ธ KO BANA ONLINE KU KIRA DIRECT A SAKO MAKU DATA๐Ÿ˜น๐Ÿ‘Œ๐Ÿป*








*Free page*







*Wattpad*

@nuceeyluv






By

Nuceeyluv๐Ÿ˜˜





19...



Kyawawan idanuwan sa farare Kal ya zube mata su akan fuskar ta tana bcci batare da tasan yyi Hakan ba, yareema yaseer ya Dan Jan numfashi Yana kauda Kai hade da yatsina fuska tun dazu ya dawo baya zuwa Inda take bayan tafiya d yyi me nisa sai kuma ya dawo yana Bata rai Kamar Wanda aka sashi dole yazo.


Sake juyowa yyi yana karewa 'yar maidaidaiciyar fuskar tata kallo a karo na uku Yana tabe baki sai kuma ya gyara zaman sa Yana dan kishingida a gefen dutsen d take kwance ya dora kansa a hankali Yana matsawa can kada ma ya hade kusa da ita.


Bilqees har yanzu bcci take Hakan yasa batasan ma dawar garin ba. Sanyin asuba ne ya fara ratsa bilqees dake kan Dutse tana bcci.


Bude idanuwan ta tayi a Hankali tana Kara rufesu, take Kuma ta mike d sauri kirjinta na bugawa lkcn data tuna a yadda ta kwanta jiya d Kuma yadda yareema yaseer yyi tafiyar sa ya barta, Hakan yasa ta tsorata sosai tana karewa dajin kallo sai kukan tsuntsaye kkeji ba Wani motsi Kuma. Juyowa gefen ta tayi da nufin sauka ta wajen sai kuma taja Baya d sauri saura kadan ma ta fadi Allah ya tsare,


Ba komai ya firgitata ba sama da ganin yareema yaseer kwance a daidai Inda ta tashi Yana bcci hankalin sa a kwance hannun sa a saman kirjin sa. Mmki ne ya kama ta, mutumin d yyi tafiyar sa to yaushe Kuma ya dawo? Meyasa ya dawo? Bata da Wannan amsar Dan haka ta tsurawa fuskar sa ido tana kare Masa kallo a tsanake.


Karo na farko kenan data tsaida hankalin ta a kansa tana yi Masa kallon kurulla.


"Why are you staring at me?"


Taji ya furta Hakan a nutse har yanzu kuma idonsa a lumshe. Ja Baya tayi d sauri yanzu kam duka ta zame zata fada baya domin dama saura kiris


"Innalillahi"


Bilqees ta furta Hakan d sauri tana juyewa kasa zata fadi yareema yaseer ya rikota da sauri Allah ya taimaka Bata fadi ba saura kiris ta fada jikinsa ya zame Yana sakin hannunta hade d maka Mata harara yace,


"A garin kallon gulmar ki Zaki Karya kanki."


Kunya da takaici ne ya kama Bilqees tana turo baki hade da aika Masa da martanin hararar tace,


"Aka gaya maka Nima bansan lkcn daka kalleni bane? Inajin a jikina ka gama karemin kallo daga sama har kasa"


ta Ida mgnr tana sake ballo Masa harara ta dauke kai. Mmki ne ya kama shi saidai be nuna Hakan ba ya mike kawai Yana kade jikinsa yyi bayan dutsen Inda yake kyautata zaton d ruwa a wajen.


Tsaki bilqees taja tana kama kanta hade d cije lips d Dan karfi har yanzu ji take kamar kasa ta bude ta shige haka takeji Dan kunya ya kamata tana kallon sa mtwss. Ita gsky bataso Hakan ba Sam.


Toh Amma wai waye shi? Wannan tmbyr itace Nan farkon furucin data farayi Masa lkcn da tunanin sa ya bace, ya kamata ta maimaita ta yanzu da tunanin sa ya dawo waye shi? Daga Ina yake? Dan wanne gari ne? Dan bazai yiyu suyita zuba tafiya batare da sunsan Ina suka sa gaba ba...


Juyowa tayi firgigit gefenta lkcn da taji ya watso mata ruwa d alama Alwala yyi, hararar ta yyi yana dauke kai beyi mgn ba ya tada sallah kawai a wajen Yana kabbara. Harara bayansa tayi a yatsine itama ta mike tayi baya Inda taga yyi anan ta tarar da karamin kogin dake wajen Inda ruwa ke bulbulowa ta cikin duwatsu.


Tara tayi a Wani ganye me fadi data lankwasa ta sake mtsawa can gaba anan tayi fitsarin ta, kafin ta dawo ta daura Alwala a nutse sannan ta taho Inda ta barshi. Lkcn yake sallama bilqees taja gefe itama ta tada tata sallar hade da kabbara.


Juyowa tayi bayan ta sallame anan ta ganshi zaune Yana aswaki d Wani itacen bishiya daya karyo, saiya tuna mata da lkcn da yake cikin batan tunani koyaushe ya tashi sai taga Yana aswaki har itama ta fara kwaikwayon Abinda yake tana goge baki abin ya birgeta d takejin bakinta wasai ga Karin haske ba Wani bashi idan mutum yyi aswaki.


"Waye Kai?"


Bilqees ta furta Hakan a takaice yyinda yareema yaseer yaji tmbyr tamkar daga sama, saidai miskilin ko juyowa beyi ba bare tasa ran amsar Sa,


"Nace waye Kai? Daga Ina kke? Dan wanne gari ne Kai? Ya kamata nasan wa'annan Abubuwan bawai muyita tafiya batare da munsan Inda zamu sa gaba ba."


Kamar bazaiyi mgn ba sai kuma yyi tunanin ya kamata by now ace yabar wannan kauyen domin yyi missing masarautar MANARAS, yanaso ya isa gida kan lkci domin ya gano manya-manyan jiga-jigan munafukan da sukayi sanadin barinsa masarautar uwa uba besan a wanne hali

Ummi da Abba harma da sister suhaima suke ba, dauriya kawai yake Amma zuciyar sa cike take d tarin Abubuwa barkatai Wanda yake bukatar yyi clearing dinsu ,


Hakan bazai faru ba har sai ya samu damar ficewa daga Wannan kasurgumin dajin Wanda besan ta Inda zai fita ba Saida taimakon Allah Dana bilqees.


"Kayi hakuri idan bakason tmbyr ne daga yau bazan sake furta maka wa'annan tambayoyin ba."


Bilqees ta furta Hakan tana shirin tashi zuciyar ta cike d tunanin kodai bayason komawa asalin sa ne??


"Adamawa."


Yareema yaseer ya furta Hakan a takaice Yana juyowa a hankali ya dubeta. Shidin take kallo Hakan yasa tadan wara ido kadan sbd yadda taga gaba1 yanayin sa ya canja, alamar damuwa da kunci sun bayyana akan fuskar sa, sai kuma taga kamar ya Dan canja ya koma babban mutum, Hakan ya sata shiga shakku.


Amma dai ta maze tana gyada Kai a nutse tace,


"Adamawa? Sunan gari ne? Ko kuwa sunan tambarin Ahalin ku ne?"


Ta furta Hakan cike d Rashin fahimta Dan batasan Kuma inane Adamawa ba. Zuba mata ido yyi na wasu few seconds kafin ya dauke kai sannan yace,


"Sunan gari."


"Ikon Allah, Wallahi ban San garin ba. Amma tunda ka furta sunan gari tazo gidan sauki, matambayi baya Bata muyi gaba akwai Wani bababn kogi a gabanmu Inda ake shiga kwale-kwale dake fitar d mutum daga Nan saimu fara tmbyr garin ko Allah zaisa mu dace."


Gyada mata Kai yyi a nutse yana mikewa beyi mata mgn ba kawai yyi gaba. Hararar bayansa tayi a Hankali tana mgn kasa2 tace,


"matsalata dakai Wlh ka cika miskilancin banza..."


Gani tayi ya juyo Hakan yasa ta dauke kai da sauri tana tafiya a gefen sa. Kwafa yareema yaseer yyi shima ya dauke kan nasa kawai yaci gaba da tafiya.


Sannu-sannu Bata hana zuwa saidai a dade ba'a je ba, cikin ikon Allah sai gasu a gabar kogi

Tun daga nesa suke hango mutane na safa da Marwa ta wajen alamar akwai 'yar kasuwa a gun. Kowa na harkar gabansa. Suna isa wajen bilqees ta dubi yareema yaseer d har yanzu Beyi mgn ba tun dazu tace,


"Jirani bari nazo."


Kallon ta yyi d mmki, kafin yyi mgn ma harta bar wajen, Dan dole ya tsaya jiranta a wajen Yana kallon masu siye d siyarwa ta wajajen gun. Bilqees data bar wajen gurin masu Saida fruit ta nufa, bakin zaninta ta bude Nan ta dauko kudin cinikin ta data kulle ta dubi me lemon tace ya Bata d sauran kayan itatuwan irinsu ayaba da tuffa d Kuma abarba.


A leda aka zuba mata ta dawo Inda ta barshi Yana tsaye kikam. Bilqees ta dubeshi a tsanake tace,


"Muje can mudan zauna kafin mu fara tmby ko?"


Banza yyi d ita domin be kalli ma Inda take ba. Dawowa ta wajen sa tayi tana tsayawa gabansa tace,


"Bakaji Abinda nace bane?"


Hararar ya aika mata Yana Bata rai sosai yace,


"Waya baki izinin zuwa wajen mutanen can?"


Gwalo ido bilqees tayi tana ja Baya a hankali tace,


"Na maka mgn fa."


Binta yyi d mugun kallo yace,


"Kuma na baki izinin kije? Kin manta Abinda ke kanki ne waii?"


Ya furta Hakan d Dan karfi. Cikin sauri ta girgiza kai tamkar zatayi kuka Tace,


"Abinci fa naje siyo Mana? Shine nayi lefi?"


Ta furta Hakan bakinta na rawa ranta a bace ta juya fuu tayi hanyar wata rumfa ta shige ciki tana Jan numfashi yadda kallo ya fara dawowa kansu shine ya Kara Bata haushi sai ya dinga yi mata fada kamar Wani ubanta.


Ransa ne ya Kara baci Yana Kara tunowa da waye shi din, idan a masarauta ne ta isa tayi Masa haka? Ko kallon takalmin sa ma Bata da izinin yi bare shi kansa d zata dinga yin gaban kanta batare daya Bata umarni ba...


Toh Amma laifin shi ne da har yanzu be fada mata asalin waye shi din ba. Tsaki yaja me ciwo zuciyar sa babu dadi ya isa cikin rumfar da take zaune, tana ganin shi Amma ta dauke kai tana bare ayaba tasa a baki hade da lumshe ido haka kawai tanajin yunwa bazata kashe kanta ba.


"Bilqees"


Ya furta dakyar kamar bayason mgn.


Dukda taji kiran sunan har cikin ranta Amma haka tayi banza dashi tana sawa a ranta shima yaji Inda dadi.


hakan kuwa ya Kara soya Masa zuciya yana Kara Tuno da hadaddun 'yan matan sa d suke rububin samun damar yyi masu mgn Yana Shan kamshi Amma jibi Wannan tatsitsiya da ita ruwan kauye wai itace Yana mgn tana dauke Masa Kai???? Lalle duniya d fadi take, soon....very soon...zai gyara mata zama.






*A lallaba da Wannan pls๐Ÿ‘๐Ÿป*





*Zaki iya biyan kudin ki yanzu a saki a paid group*



It's 300 via... Access bank 1445626295


Nusaiba Mustapha


Then show your evidence ta Wannan number๐Ÿ‘‡๐Ÿป



***.




*Haka zalika Zaki iya turo katin 300 MTN ta Wannan number ****

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol