Free chapter · Read without an account

14

by Fadimafayau · Fajaruddeen

Fatiha ta jima tana mita aranta kamin tai tsaki ta miƙe tai inda suke zama.


  Rai duk atunkushe ta gaidashi abinka da psychologist tuni ya fahinci akwai damuwa yaɗan murmusa aransa yace mata se abarsu ƙaramin abu su babba ne gurinsu.


  Ƙanwata ya kirata ta kalleshi batare da ta amsa ba yace am sorry kwana biyu banzo ba bankuma kira naji ya kike ba aranta tace ashe yasan be kyauta ba.


  Banzo bane sabida mahaifina beji daɗi ba duk na rikice jiki na rawa cikin nuna nadama take tambayar me ya sameshi tun yaushe.


  Faɗuwa yai yau kwanansa biyar kenan a asibiti muna sa ran ko yau ko gobe ma asallameshi dik se taji babu daɗi taita Allah ya sawwaƙe yana amsawa da amin.


  Kinsan me yasa ya faɗi ta girgiza kai yaɗan murmusa ya tambaya ne ba dan daman ta bada amsa ba dan yasan bata da ita.


 Any way abinda nazo mu tattauna kenan nan ya bata labarin auren da fasawa gami da dalilin fasawa ta jinjina abin aranta gami da afili shiru ya ratsa.


  Can yace Fatiha zaki iya aurena ta dube shi kawai pls kiban amsa zaki iya aurena ban ɓoye miki komai ba game da abinda nasani akaina sedai kawai ina da tabbacin iyayane sune suka haifen duda banda tabbacin niɗin sun haifen lokacin da sukai aurene ko kuwa kasuyi.


  Kiban amsar da take ranki karki damu wallahi bazan zargeki ba dan kince bazaki auren ba dan nasan kina da hujja me ƙarfi.


  Indai har kanajin zaka iya aurena ni babu wani aibu dazaisa in kasa auren ka ta faɗa ya dubeta ni kuwa fatiha mezai sa ince bazan aureki ba a'a yah karkayi bincike kace bazaka iya .


  Bazan bin cike ba Fatiha ki faɗan da kanki wallahi kinji na rantse miki zan yadda da kome kika faɗan bazan taɓa tunanin kin ɓoyen wani abu kamar yadda na ban ɓoye miki komai ba sedai ni bazan ce ki yadda da abinda nace miki ba ki fara bin cikawa.


  Murmushi tai bana buƙatar bin cike domin bani ma da wanda zai bin cika min wanda zan aura dan ba wanda ya damu da rayuwata karka damu.


  Naji yimun bayani na miki alƙawarin ba abinda zaisa in fasa aurenki tai shiru kamin ta fara.


Ni haifaffiyar kaduna ce.....


Thanks for reading 😍


Fatiha ta cigaba.


  Mahaifina sunansa Abdurrashid muktar haifaffen kano ne komai nasa na kano ne.


  Malam muktar shine mahaifinsa wanda ya kasance yanada mata biyu umma salamatu da umma Barira ko waccensu tana da nata yaran umma Barira ce uwar gida tanada yara biyar sai umma Salamatu wadda take itace amarya tana da yara takwas ita ce kuma mahaifiyar mahaifina wanda shine na huɗu a ɗakinsu.


  Gidansu mahaifina shahararren gida ne a unguwar su da maƙotansu koma ince a garin kano baki ɗaya daga nisan duniya in kace akawo ka gidan Malam muktar sarkin mayu za'a kawoka yar gidan kakana wato mahaifinsu babana.


  Shine sarkin mayun garin nasu sana'arsa ita ce bada magani babu lefi Allah ya hore masa dan maganin nasa yana ci sosai kamar yankan wuƙa indai ya baka insha Allahu zaka warke saidai fa in mutuwa ce to ba yadda za'ayi.


  Kasantuwar yanayin gidansu mahaifin nawa yasa mutane basa san mu'amala dasu duda kuwa sunsan da fewar maitar gidan ba me cutarwa bace dan kuwa bazaka taɓajin ƙorafin wani ɗan gidan ya kama wani a waje ba.


 Duk wanda ya isa aure ayaran iyalin akan yaɗashi aure da ƴar uwarsa ko ahaɗata da ɗan uwanta domin kuwa mutane basa yadda kan su basu auren yaransu ko kaɗan hakan baya damunsu domin kuwa suma ba lefi suna da dangi masu yawa ta inda wani be rasa abokin aure.


  

 Da yawa cikin ƴaƴan kakana basu da sha'awar sana'artasa duda kuwa yanasan ace yasamu Magaji cikinsu Baba musa ne ma wani zubin yakan nuna kulawa ga yaga yadda mahaifin nasu ke abubuwa.


  Cikin masu ƙin sana'ar mahaifin nasu harda mahaifina wanda shi ya zaɓi sana'ar fatauci dan karatun ma yaƙi duk yadda mahaifinsu yai yaƙi domin iya primary bn kawai yayi itama daƙyar ya ƙarasa hakama na addini ba wani nisa yai ba dan ko hizifi guda ba'ace ya haɗa ba tunda ya samu na sallah ya dena zuwa.


  Cikin iko da ni'imar Allah sai kasuwancin nasa yai albarka domin kuwa komai ya taɓa sai yazama kuɗi hakan yasa mutane ke cewa ai shi ɗin akwaishi da nasibi.


  Ganin Allah ya sanyawa kasuwancin nasa albarka ne yana samu sosai yasa mahaifunsu ya buƙaci da yai aure nan yace yanasan ya nemi yar gidan ƙaninsa wato Batulu domin alokacin kusan itace sa'ar aurensa duk yarane ƴan.


  Saidai fa kwata kwata Batulu bata cikin tsarin matan da Abdurrashid yake ganin sun dace da burin zuciyarsa na mace hakan yasa yace shifa gaskiya bayasanta duda kuwa yasan afaɗin garin kano babu mai bashi ɗiyarsa ya aura anman haka ya nuna shifa tabbas baya santa.


 Hakan yasa mahaifinsa zuba masa ido kawai yace aƙyaleshi inyaje yaga ya rasa matar aure zaizo da kansa yana neman auren batulun yana bada haƙuri.


  Fatiha ta ɗan numfasa kamin ta cigaba inbaka mance ba nace maka mahaifina Fatauci yake.


A harkar fataucinsa babu garin da baya zuwa cikin Nigeria wani zubin har maƙotan Nigeria fataucinsa ya kaishi garin makurɗi fahintar da yai kasuwanci agarin da riba yasa har shago ya kama inda in yazo yake zama masaukinsa.


  Yakanyi watanni agarin kan ya waiwayi gida hakan yasa yasaba da mutane da yawa musanman ƴan unguwar da yake zaune domin shiɗin akwaishi da saurin sabo saboda mutun ne shi mai faran faran da jama'a ga zaulaya.


  A garin makurɗin ne Allah ya haɗashi da wata yarinya mai suna sakina wadda gidansu ke lokon da ya kama haya daga gaisuwa wani zubin kuma sukan ɗanyi hira dan takan ganshi agidansu wajen yayanta har suka saba indai ya ganta saiya zaulayeta.


   Sannu ahankali shaƙuwa ta shiga tsakaninsu dan haka kawai takan fito susha hira ita dashi koda yayan nata basa nan kafin wani lokaci sun fahinci irin soyayyar da suke ma juna .


  Sakina haifaffiyar garin makurɗi ce mahaifinta ɗan kano ne aikine yakaishi makurɗi har ya haifesu daɗin zama yasa ya kasa dawowa gida kano sedai suzo da ziyara duk ƴan uwansa suna garin kano shida yayansa ne kawai anan makurɗin wato Alhaji sule wanda shi kasuwanci ne ya kawoshi nan makurɗin.


  Iyayan sakina su bakwai suka haifa shida mata sai ɗaya namiji yayin da kuma alhaji sule yake da yara uku duk maza hakan yasa suke san ɗiya mace da yara domin su haihuwar ba me yawa suka samu ba.


  Ganin mahaifin sakina yana da yara masu yawa yasa matar Alhaji sule ta nemi da subata biyu ta riƙe sukako ji daɗi dan ba wani arziƙi suke dashi ba Salima da Sakina suka basu wanda Sakina ce babba dan inda take Ss 1 zasu tafi 2 yayin da ita salimar ke a JSs 2.


  Akoyaushe burin Hajiya Shatu shine sakina tai candy su aurawa Babban yaron su ita ita kuma salima su aurawa ɗan autansu itadan harma sun sanarwa da iyayansu sakinar sun kuma yi murna sosai.


  Yadda suka riƙe su sakina riƙone na amana kamar yaransu suka ɗaukesu habu abinda su sakinan zasuce sun rasa sedai ma ace sunfi jin daɗi anan fiye da agidansu dan gidansu suna da yw yayin da kuma mahaifinsu bai da ƙarfi sosai.


 Saidai fa kan kowa ya ankara soyayyar Abdurrashid tai ƙarfi azuciyar Sakina wanda har batajin zata iya rayuwa ba dashi ba sun shaƙu irin shaƙuwar da mai rubutu bazai iya rubutawa mai karatu ya fahinta ba.


Sakina suna Ss1 3rd term Abdurrashid ya nuna shifa yanasan ya futi ai aure dan ya jima da shiryawa ta nuna itafa tafisan tai candy abinka da shi ba wani mahincin illimin yasani ya dage harseda ya juyo da hankalinta ta amince abinka da shi namiji ne kuma ya girme mata.


Yayin da shikuwa tsoron girman yarinyar yai da yadda yaga tana kuma kyau ga farin jinin samari hakan yasa yakeso suyi auren kar aje amasa ƙafa dan yanasanta sosai in yai sake ya rasata yasan zai sha wuya.


Ganin dai ya takura da batin auren yasa ta cire kunya ta tunkari mariƙiyar tata da batun hankalun Hajiya shatu yai mugun tashi dan tasan shirun su ya tasarma rushewa na haɗa auren zuminci dan yadda tasan sakina da kunya tunda tazo mata da batun auren take so tasan tabbas tana matuwar san yaron.



Duk yadda ummanta mahaifiya da mahaifinta suka so fahintar da ita kan kartai butulci taƙi ta nuna itafa Abdul kawai takeso ganin haka yasa kowa yai fishi da ita kowa ya fita sabgarta duk dan ta mance da batun Abdul ɗin saidaifa kamar ƙara mata sansa suke dan lokacin da kowa ya fita sabgarta shine yake kwantar mata da hankali yake kuma nuna mata irin san da yake mata yake kwaɗaita mata irin daɗi da kulawar da zata sha agidansa akuma gurinsa hakan sai ya ƙara ninka shaƙuwarsu.


Ko makaranta ma Sakina dena zuwa duk kuwa da yadda ada ta ɗaukaki karatu ta bashi mahinmanci duk ta faɗa ganin kar yarinyar mutane ta cutu tumda iyayanta sun musu kara yasa Alhaji Sama'ila da kansa yasamu mahaifinta yace shi gurinsa babu komai suma karsuji komai ai sakina ɗiyarsa ce dan haka bazai mata auren dole ba akwai wasu yaran ƙanne da yayyenta se ayi zumuncin.


Haka iyayanta suka haƙura duda basu soba Alhaji sama'ila ya wuce gaba wajen auren nata.


Koda mahaifinta yasa aka masa bin cike akan Abdurrashid ɗin nan suka gano ko shi waye da sana'ar mahaifinsa nanfa hankalinsu ya tashi nan suka saka Sakina a gaba suka mata bayani da fatan tace ta haƙura bama sai an mata dole ba.


Buɗar bakinta tace ina ita ai a musulunci babu maita sai kanbun baka wanda kuma dan mahaifi nada kanbun baka ba yana nufin cewa ɗan sa yana da shi ba dan haka Abdul ɗinta ba dole bane yana dashi taji ta gani tanasam sa zata aureshi.


Duk zagi da hantara da iyayenta ke mata haka ta rufe ido taƙi haka suka haƙura da faɗan dan sunga ba zaiyi ba suka koma lallashi da nasiha anman ta ƙi sairaronsu.


Ganin ta bijire ta nace yasa mahaifinta da mahaifiyarta suka ce sun janye hannu dags kanta basu ba ita tace itafa taji ta gani dan tanaji aranta fishi ne kawai sukai in lokaci yaja zasu haƙura aganinta.


Alhaji Sama'ila ne da matarsa su sukai mata komai aka kaita ɗakinta wato ɗakin mijinta anan makurɗin inda zata zauna bashi da nisa sosai da gidan iyayanta.


Sakamakon Alhaji Sama'ila sun saba da riƙe mace yasa lokacin bikin cikin yaran da sukazo daga kano suka roƙi Balaraba da ta bar musu ɗiyarta Hadiza su haɗa da Salima ƙanwar sakina tunda mahaifin Hadizan ya rasu aiko Balara taji daɗi nan ta bar hadiza kan sauran kayanta za'a aiko Driver yazo ya ɗaukar mata.


Watansu Sakima takwas da aure suka taso suka dawo kaduna dam kasuwamcin sa alokacin yafi ci a kadunan.


Zaman aurensu zamane me ban sha'awa domin indai ka gansu sai sun baka sha'awa abu guda ke damunta shine rashin haihuwa musanman yadda dangin Abdul suka takura mata danma ba gari guda suke da su ba.


Shekarar sakina ta biyar da aure sedai Allah bai bata haihuwa ba abin duniya duk ya isheta dam in tazo kano gidan su Abdurrashid iyayansa da ƴan uwansa suyi ta mata gori banda hantara dan abunne ya haɗe gs haushin yaƙi ƴar uwarsa ya aureta ga haushin kuma rashin haihuwa.


Akoyaushe taje kano da kuka ko da takaici take dawowa haka ma in waninsu yazo da ƙunci suke barinta Fahintar hakan yasa Abdul rage mata zuwa kanon kazalika in sukazo baya zuwa ko ina dan in yananan basa iya mata hakan ya maya daɗi sosai yakuma ƙara mata san mijin nata.


Sedai matakin Abdul ya ƙara tura tsanar sakina ga dangin nasa suka ƙara sama ransu tafa shanye musu ɗan uwa.


Seda suka shekara shida suna shirin shiga ta bakwai sannan ta samu ciki murna gurin ta ba'a magana haka ma Abdul dan zanma iya cewa yafa fi sakina murna.


Alokacin kuwa Abdul ya zama babban Alhaji dan kuwa Arziƙinsa sai san barka dan tun suna shekara ta huɗu da aure sukaje saudiyya shida matarsa.


Watanta tara ta haifi yaronta santalele me kama da mahaifinsa yaci sunansa Abbakar aiko an kashe kuɗe ranar suna alokacin sakina ta kuma tabbatar wa Abdul ita yake so ba wani abu nata ba dan alokacin se take ganin kamarfa sabon shafin soyayya ya buɗe agareta da yaronta.


Haihuwar Abubakar se ta zama kamar an buɗe mata haihuwar dan tana yaye shi ta Haifi umar sannan usman datai na huɗun ne ta roƙi yasa mata sunan mahaifinsa shine yasa Ibrahim nanmafa taga jalala a family ɗinsu wai besa sunan mahaifinsa ba se nata ita dai ta toshe kunnenta kawai.

Tun haihuwar Ibrahim se yazama kamar an rufe mata haihuwar sedai alokacin bata wani damu dan tana ganin su Abbakar agabanta kuma alokacin babu me kiranta juya dan ta aje har huɗu.


 Seda ta shekara takwas dan har ma sun cire rai suna zaton ko ta gama ne sannan ta kuma samun ciki murna gurin ma'auratan kai kace haihuwar fari ce.


  Alhaji Abdul alokacin ma dai yafi Hajiya sakina murna sanshi aduniya yanasan yara musanman ma ace Sakinansa ce zata haifa masa.


  Lokacin da sakina taje asibiti akace mata macece tai murna sedai fa Abdurrashid yafita murna danshi akwai da san ɗiya mace duk se ya ƙagu Sakina ta haife masa me kama da ita.


 Tun cikin na yaro yake waƙar Fatiha zai samata.


 Tun farkon cikin abubuwa marasa daɗi ke samun mahaifina akasuwancinsa na asara.


 Abinka da ƴan gargajiya nanfa danginsa suka hau faɗin anya ba hannu aka saka masa ba tunda da lokacin da auri sakina arziƙinsa haɓaka yai bare suce itace me farar ƙafa.


  Yanayin yadda yake asarar yasa ya fara yadda da hannun akasa masa abinka da wanda be wani illimin addini me nisa ba .


 Ran Litinin mahaifiyata ta fara naƙuda hankali tashe mahaifina ya ɗauketa sukai asibiti dan Allah ya temaka lokacin yazo dan lokacin yakan yawan tafiya hakan ne ma yasa ya ɗauko kakarsa dan kar haihuwar tazo yazama ita kaɗaice agidan.


 Basu jima da zuwa ba nurse ta fito take faɗa masa ai ta sauka ta samu ɗiyarta mace murna gurin sa ba'a magana ya miƙe yana faɗin zan iya shiga in ganta tace eh dan asibitin kuɗi ne ita kaɗai ce aɗakin.


 Wayarsa ce tai ƙara ya dakata ds shiga ya ɗaya muryar yaronsa ya tsinkaya yana faɗa masa ai wuta ta tashi a kasuwa cikin shagunan da suka kama harda nasa bakuma yajin akwai mamora kasa shiga ɗakin yai ya koma ya zauna daɓas hankali tashe yana faman innalillahi wa'inna ilahi raji'un yayin da kaka kuma keta faman faɗin kai ita dai wannan yarinya batazo da arziƙi ba yayinda shi bama jinta yake ba dan shi kaɗai yasan me yakeji aransa.


  Ya jima azaune kamin ya miƙe zai bar asibitin nurse ɗin ta fito riƙe da baby ta miƙa masa ya amsa yana shafa kanta ya shiga ɗakin da matarsa take wato ummana ya mata sannu sannan ya faɗa mata abinda ya faru hankalinta ya tashi yace shi zai je dan ganin ya ake ciki seda yamin huɗuba da Fatiha ya kwantar dani gefen ummana yana shafa kaina kamin ya fice.


   Koda yaje alokacin hankalinsa ya kuma tasha dan be yi zaton abin yakai haka ba dan babu wani abin mora komai ya ƙone abinka da wanda ya nema da gumin sa yai kuka sosai dan yasan zafin dukiyar sa.


  Yayin da Danginsa daga kano ke ta faman cece kuce kanwai yarinyar nan ita ce silar komai duba da tun randa aka samu cikin yake tafka asara kama da haihuwar ta.


  A cewarsu wai na kwaso babbar maita daman akan samu haka wani maitarsa tafi ta kowa zafi.


  Ummana ce ta sayi ragon suna ganin ko maganar bayau zatonta sabida matsalar da ya faru dashi ne dan batasan tayar masa da hankali.


  Watana uku a duniya mahaifina ya tattaro iyalinsa daga kaduna zuwa kano dan kasuwan cin kadunan yaƙi ci.


  Lokacin da muka dawo kano yana da gida anan rijiyar zaki da yasa ƴan haya kan mu dawo ya tashesu nan mukai masauki.


  Alokacin rayuwa tai mana zafi dan kuwa komai yafaƙi ci hakan yasa ummana tace tunda gidan da muke ciki babbane kuma unguwar tanada daraja mai zai hana ya saida gidan ya siya mana ƙarami anan gaida sauran kuɗin sai yaja jari sosai yaji daɗi kuwa dan hakan yayi yaja jari.


  Babu lefi kasuwamcin yana garawa sai dai duda haka ba kamar da ba alokacin ida shekara guda harda watanni ina yawona ka ina sai dai tun alokacin mahaifiyata ta fahinci mahaifina baya shiga sabgata dan ko abu yace ummana ta masa in tace Fatiha takema abu yanzu zai balbaleta da faɗa wai tana sangarta ni yai waje cikin fishi.


   Ranar da akasa za'a yaye ni alokacin ne akai wata gobara a sabon gari ciki kuwa harda shagon mahaifina hankalinsa ya tashi sosai dan kuwa har faɗuwa yai.


  Duk wanda yazo daga gidansu Abdul ɗin wato mahaifina jaje sai kaji suna shaguɓe kan wai sanadiyya ta komai ke faruwa dashi ahankali mahaifina ya gama yadda da batun ƴan uwan nasa duba da hujjojinsu abinka da wanda bai wani illimi mai ƙarfi ba.


   Ya riga ya gama yadda da cewar indai har abin farin ciki zai sameni to tabbas abin takaici zai sami me ɗaukan nauyina sabida wai nice na gaji wata yayar kakarmu domin maitarta mai zafi ce itama haka abubuwa ke samin mijinta indai zai faranta mata maganin abun kawai shine fita sabgata da nunan tsana.


  Duda kuwa duk yaron da aka haifa ana karya masa maitarsa saidai acewar su irin tawa tafi ƙarfin karyuwa.


Alokacin inada shekara uku aduniya aka haifa min ƙani wanda yaci sunansa Aliyu tun lokacin ko faɗa mukai da yaro se yaita cuta ko dan iyayansu sun canfa ne oho hakan kuwa ya ƙara tunzira mahaifina da ƙara tsanata aduniya babu wanda nake tsoro kamarsa dan kuwa yana ganina zai hau muzurai yakuma hauni da faɗa gashi lokacin kakana yarasu wato mahaifinsu su babana bare ace zaiyi maganin abun su kuma yaransa basu wani san komi kan sana'ar tasa ba.


  Mahaifina bai shawara da mayaifiyata ba ya saida gidan da muke ciki na gaida tun tanajin jita jita bata yadda ba har seda ya zo da akori kura yace wai kaya za'a kwashe zamu koma gidansu wato gidan kakana dan daman duk mara ƙarfi kawai shatar guri yake ya zauna shida iyalinsa dan gidan akwai girma.


 Koda ummana tai magana ya hauta da faɗa wai ai duk lefinta ne da ta haifo masa masifa haka kawai yana zaman zamansa ds arziƙinsa ta haifo masa tsiya alokacin ummana tai kuka sosai na bijirewa iyayanta dan tasan baƙin cikin da tasasu ke bibiyarta.


 Lokacin Aliyu nada shekara 3 inada 6 ummana ta nemi akaini makaranta Abbana da kansa yakaini dan har lokacin be gama cire hannunsa akaina ba nan yakaini primary ta gwamnati da ke unguwar tamu nai murna sosai dan kuwa akwaini da san karatu.


  Banda yaya mace se yayye maza tun haihuwata nake yar gata agunsu komi suka samu na Fatiha ne ko Ali dake ɗan auta basa ji dashi sabida sunasan mace ni kaɗai kuma suke dani hakan yasa sabida yarinta banwani damu da rashin kulawa ta mahaifina ba.


 Sesai lokacin dana shiga primary ƴan ajinmu kowa kance babansa ko Abbansa yai masa kaza yai masa kaza sai na fara damuwa nagane bawai fa iya kulawar yayye nake buƙata ba ta uba ma itace mafi a'a la.


 Babana bai sati da kaini makaranta ba ya tafi Nijer da kuɗin gidan da ya seda dan sayo shinkafa dan yaji labarin alokacin cinikin shinkafar ke garawa.


 Cikin rashin sa'a duk wanda ya sayi shinkafar se ya dawo masa da ita dan kuwa duk ciki tai hunhuna alokacin mahaufina ya fidda hannunsa akaina dan ya riga ya gama yadda da soki burutsun danginsa.


 Tun tasowata mahaifiyata ta koyar mun da komi nagani insa mass albarka hakan zai sa komada dagaske ne inada kanbun bakan to babu wani abu da zai sami wannan abin da ya birgeni hakan kuma nake.


  Tun bayan asarar shinkafar da yaine yace shifa ina yama dena neman kuɗin inje inci kaina da kaina badai dukiyar sa ba tunda dai inrasa wa zanma zalunci sai ubana.


 Kwata kwata ya dena zuwa ko ina sedai yaci yashi yaje salla ya dawo ya shige ɗaki yai kwanciyarsa.


 Ummana ita take mana komi da temakon yaya Habu in yaje makaranta ya dawo yakanyi buga bugarsa ya kawo ahaka muke rayuwa.


 Kamin wani lokaci aka samu wanda sukai convincing ɗin mahaifina cikin danginsa kan cewar dole sai ya auri ƴar danginsa arziƙin sa zai dawo aiko dai ya yadda nan akasa lokacin bikin nasa shida Batulu wadda akai akai ya aura abaya yaƙi dan kuwa har lokacin batai aure ba.


  Duk wainar da ake toyawa ummana batasan anai ba sai ran kai amarya ta samu labari dan ba gida guda muke dasu batulunba bacin ma haka mu bama shiga sabgar ƴan gidan dan sun ware ummana.


 Aikuwa ranar tai kuka sosai taita masifa mahsifina ya mata banza zan iya cewa shine karo na farko dana ga faɗan ummana.


 Washe gari ta kwashemu mukai makurɗi saidai fa bata wani samu karɓuwar kirki ba bare ta musu bayanin me Abdul yake mata dan babu fuska duda dai bakamar daba da suke korarta satinmu guda acan ta tattaro mu muka dawo kano dan tabar Yah Habu da yah Ummaru akano sabida su suna exam.


  Ina primary 6 matar babana ta haifi ɗiyarta mace inda Abba na yasa mata Sakina aikuwa taita masifa baza'a sama ɗiyatta sunan kishiyarta ba nan yaita rantsuwa ba sunan matarsa yasa ba kawai dan yanasan sunan ne tace to taji anman wallahi baza'a ɓoyeba dole kowa yace mata sakina yace Yaji yagani.


 Duk soyayyar da mahaifina kema ɗiya mace se ya ɗiba ya ɗora kan ɗiyarsa sakina dan ya jima yanasan mace.


  Mahaifiyata bata ankara ba sai labari taji wai zai koma kaduna anman da iya amaryarsa zai tafi tai kuka iya kuka har ta godewa Allah dan kuwa tasan bata isa ta hanashi ba inko ba haka ba yanzu aji kansu.


  Tun daga wannan lokacin da yabar kano se lokaci lokaci yakanzo hayan watanni ya ɗan kawo abinda ba'a rasa ba yaɗanyi kwanaki ya tafi wanda in yazo ɗin mu hankalin mu atashe shi nasa atashe dan in yazo yadinga masifa kenan ta bagaira bare dalili seda yakai ya kawo kar cikin mu babu me san zuwan nasa.


Kusan ina Jss ne ya dawo kano inda yazo gida wurjan jan bayan wajen wata takwas da ya kwashe bezoba yaita mun masifa wai duk sanadinane wallahi in ban sake masa mara ba yai kasuwancin sa zai koreni daga gidan ya cireni cikin yaransa.


 A wannan zuwan ne yace ya cireni amakaranta yakuma hanani fitowa koda tsakar gida ne indai yana nan sedai innaji fitarsa masallaci in maza in abunda zan in koma ɗakina.


  Alokacin bamu san me yasame shi bakuma musan asarar me yaiba har ya dawo kanon.


  Alokacin babu lefi yayyena sun tasa su ke ciyar damu yayana usman shine yaban jari yace ba talla ba indunga zuwa bakun lokon mu ina suyar ko waina kuma awara na zaɓi awara duk wanda yake gida acikinsu to zaka sameshi gurin awarata suna tayani zama hakan yasa babu me kawon wargi in ba ita kazo siya ba kawai kazo surutu ne yanzu zasu nuna maka hanya.


  Kwanansu biyar mahaifina agida ya kwashi amaryarsa da iyalinta suka bar gidan bamu san inda suka koma duda de har yanzu suna kanon sedai lokaci lokaci yakanzo anman ya dena kawo mana komai sedai ya kwashe abinda yayye na suka kawo yai gaba dasu.


 Idan ummana tai magana yahauta da masifa yana faɗin shida da yake kawowa me yasa bata magana se yanzu da yaranta ke kawowa to daɗinta bafa ita kaɗaita haifesu ba kuma ayanzu ai haƙƙin ci dashi yana kansu.


  Ana haka yayana ya kammala makaranta yah Abu da yah ummaru inda yah Habu yasamu aiki da FG suka tura su jigawa shi kuna ya ummaru yake kasuwanci babu lefi yana samu.


  Lokacin danai candy yah usmanma ya kammala karatunsa yana koyarwa a secondry babu lefi yanzu ta fi mana da yayyena suka biyamun kuɗin jamb cikin ikon Allah naci aka ban abinda na nema agric naita murna.


  Alokacin damuwata biyu ce ta farko itace ta mahaifina yadda kullum kamar ƙara masa tsanata ake wanda lokacin da ya samu labarin ai naci gaba da karatu harnai candy na cigaba da jami'a yaita bala'i wai zai koren daga gidansa.


  Sai abu nabiyu shine afamily ɗinmu kaf wanda suke sa'oin aurena mata an musu aure mazan da suka rage kuma ba wanda yake sha'awar aurena dan tsoron kar masifa ta dinta afka masa.


 Yah Bashir ya dage shi zai auren iyayansa sukace zasu tsine masa inaji ina gani ya auri Badariyya duk da kuwa har yanzu yanasona sedai ba inda muka iya.


 Tun ina primary bani da wata ƙawar kirki dan uwa ta samu labarin ɗiyarta na abota da Fatihan gidan sarkin mayu tuni zata raba mu.


 Hakama ina secondry rimi rimi zamu fara ƙawance da yarinya tazo gidanmu se ta fara tsorona tunda dai gidanmu gidan mayu ne hakan yasa kaf rayuwar karatuna nake nikaɗai banda wata ƙawa ko aboki.


 Tun rashin saurayi na damuna har ya dena sabida ada babu fitar da zan banyi saurayi ba sedai fa yana zuwa gidanmu zai dena zuwa wani zubinma ƴan gidan ke korarsa.


 Hakan yasa kawai na rungumi ƙaddarata nake komai nawa ni kaɗai har ko yaushe kake gani na anan ni ɗaya dan bansan in saba da mutane su gujeni inzo ina damuwa.


 Yayye na duk sunyi aure ina level 1 going to 2 babban yayi aure yah Habu dansu yah Usman sun rigashi aure.


 Duk da sunyi aure basu fasa ɗaukan nayun karatunmu nida su yah Ibrahim ba sun jima da hanani yin awara sedai dan banasan cika tambayarsu dansuma ba wani ƙarfi garesu ba yasa naƙi denawa.


 Ayanzu nice kamar ƴar auta dan ko Ali da yake ƙarami da ya samu abu to yanzu zai kawon gabaki ɗayansu tausayina suke danma ummana ta hana da tuni ina Jigawa gurin yah Habu tace ina bazai yiwu daga aurensa akaimasa yarinya budurwa ba.


  Fatiha tai shiru kamin tace wannan shiene ataƙaice wace ce Fatiha.


  Cigaban labari.


 Shiru kawai Fajar yai yana kallon ta hankalinta ya tashi kodai shima tsoron nata yake ne tace daman nasani indai kaji ni wace tuni zaka sauya ra'ayi ta faɗa tana share hawayen da ya zubo mata.


 Yai murmushi ba hak bane Fatiha kawai tausayin kine ya cikani ya hanani magana ai shi so baruwansa da waye mutum kuma shi so na gaskiya shine kaso mutum ka rungumi komi nasa ka maidashi naka sanki a jina yake bazan denashi ba kamar yadda ummanki bata yadda da maitaba haka nima kawai ki fara amsa sunan Amaryar Deeni tai murmushi dagaske.


 Ba wasa nake ba ki faɗan yaushene Abban naku ke zuwa zanzo in sameshi eh to bashi da taka mai mai lokacin zuwa sai dai in yazo zan kiraka awaya in faɗa maka.


  In zaka zo karka zo da mota karkayi wata shiga me kyau in yafe mene sana'arka kace koyarwa yace sabida me tai murmushi sabida in kaje da mota bazai baka aurena ba inkaje da shiga me kyauma haka zaiji tsoron kar kaima ƙaddarar data faɗamasa ta faɗa maka dsn haka zaice zai baka Sakina ƙanwata.


 Inko yaga baka da komi ko kusa ka kaɗan bazaima sakina sha'awar auren ka ba dankuwa yanasanta da yawa.


 Ok kin bani satar amsa suka sa dariya gami da sauya wata hirar zukatansu cike da annashuwa musanman Fatiha dan Fajar duda yasan mahaifinsu zai amince sedai ta wani ɓarin yana tsoron mahaifiyarsa kar taƙi amin cewa.


Koda Fajar ya koma gida baima mahaifiyar sa maganar Fatiha ba sai da ya bari mahaifinsu ya dawo sannan ya faɗa masa komai game da game da fatihan yace ba komai indai ya tabbatar yana santa shikenan ba komai.


 Sai dare suna cin abinci sannan mahaifin nasa ke faɗawa ummam nasu.


  Salima ya kira sunanta ta amsa gami da maida hankalin ta gunsa daman maganar Deeni ne kan aurensa na samo masa yarinyar da nakesan ya aura taji daɗi aranta aƙalla dai ya sa hannu akan Deeni sanin halin sa yasa ko tambayar sa wace yarinyar ko a ina ya samo masa ita batai ba.


  Kwana uku da yin maganar su Fatiha ta kira shi take faɗa masa cewar Abbansu yadawo yako ji daɗi aransa yace zaizo kan ya tafi.


  Da yan macin ranar da sukai waya da Fatihan ne ya shirya tsaf cikin shigar farin yadinsa da yasha guga wanda inkai ba mai mu'amala bane da ya dudduka bazaka taɓa banbance shin mai tsada bane ko mai arha duda kasancewar simple shiga yai saidai yai kyau sosai kwarjinin sa da zatinsa ya kuma bayyana.


  Fajar Dogo ne bacan ba shi ba fari bane bakuma baƙi ba kalarsa wasu kekira da ruwan tarwaɗa sumar kansa akwance take luf akansa wanda ko bai taje ba ko bai aske ba zaka ganta akwance yayin da sajen fuskarsa ke ƙara masa kyau da kwarjini duda yana yawaita aske shi sai dai kan wani lokacin ya kuma kwanciya a fuskarsa.


 Hancinsa da idanunsa duk na mahaifinsa ne wanda idanunsa suke dara dara hancinsa har baka ataƙaice dai Fajar mai kyau ne kyansa ke jan mata da yawa wajen kamuwa da soyayyarsa.


 Sau da dama shike haska kaya inya saka ba kaya ke haska shi ba hakan yasan ko wacce irin shiga ya ɗauki hankalin mai kallonsa.


  Kai tsaye bakin titi yai dan tarar ɗan sahun da zai kaishi unguwar su Fatihan.


  Ji yai ana Malam ya juya jin kamar ya san muryar murmushi yasaki ganin Faiza ashe dai zan ɗauki murya itama murmushin tai kamin su gaisa yace daga ina haka naje gidansu Fadila ne suka ɗan taɓa hira nan take bashi haƙuri kan abinda mahaifinta yai ya nuna mata ai komai ya wuce ya kuma nuna jin daɗinsa na yadda yaga ta saki ranta tana rayuwa ta masa godiya kan admission ɗin da ya samo mata yace ba komai sukai sallama yai gaba.


 Ta jima tana kallon sa har ya ƙule sannan ta share hawayen da tuni fa yanzu tana gidansa yana kiranta mamata tana kiransa mijina Allah ka ciremin san wannan bawan naka ta faɗa sannan tai gida.


  Har unguwar su Fatihan mai adaidaita sahun ya kaishi abakin lokonsu maiɗan sahun ya ajiye shi inda ya sauƙa ya miƙa masa kuɗin nan ya hangi Fatihansa tana suyar ta sai yanzu fa ya tuna bai ce mata yau zai zo ba ya ɗan jima yana kallon ta yadda ya ganta fes duda ba kwalliya tai ba sai yaji ta burgeshi aƙalla ita ɗin mai tsafta ce.


  Gurin ya ƙarasa tana ganinsa ta diririce shi kuma yahau dariya haba tawan mene haka kuma daga gani na sai ki wani daburce yah Ibrahim yatoso lafiya dai Malam yai ɗan murmushi Ibrahim ko eh nine fatiha tai mamaki yadda ya iya gane yayan nata da sunansa bai bari ya kuma magana ba dan yaga ɗan zafi ne yai saurin cewa pls gurin Abbanku zaka min jagora Fatiha tai saurin cewa yawwa yah kuje ɗin.


 A hanya yake faɗa masa abinda ya kawo shi Ibrahim yaji daɗi ya godewa Allah da baisa ya kwafsa ba wajen yima Fajar ɗin rashin mutunci.


  Daman kasanni ne inji Ibrahim nop but taban labarinku tace daka kai sai ita duda ka bata 8yrs but jikinka baya nunawa Ibrahim yai dariya ai sun rainani ita da Ali Fajar yai dariya haka ƙanne suke ai shima yai murmushi inda yai dedai da zuwansu ƙorar gidan Ibrahim ya shiga bari in maka iso to Fajar yace.


  Babu yabo babu fallasa yadda mayaifin nata ya amsheshi kamar yadda ta faɗa aiki da sa'arsa ya tara tambaya kamin ya ɗora da ince kasan me zaka aura dan banasan se abu yai nisa kace na munafunceka Fajar yace yasan komai ya yadda ya amince yakuma ji yagani mahaifin nata yace to kaje zan sanar mata da matsaya ta inna gama nazari to yace sukai sallama.


 Yana fitowa daga ɗakin zauren yaci karo da Fatiha yace sana'ar fa tai murmushi yah Ib. Yace zai jire nan suka sami waje suka hau hira wanda sai bayan lisha sukai sallama da juna cikin shauƙin ƙauna ya tafi tai gida.


  Cikin kwana biyun nan duk hankalinsa atashe yake ya kasa kwanciya sabida zullumin kar Abban Fatiha yace bazai bashi ita ba dan sai ayanzu ya kuma fahintar irin son da zuciyarsa kema Fatihan wato zazzafan sone wanda bayajin ya taɓa ma wata irinsa wanda kuma yasan babu wata mace da zai iyama irin wannan son shi kansa har mamakin irin yadda yakejin ta aransa yake.


 Kwana biyun nan sabida fargaba har faɗawa yai duda yanajin kamar mahaifin nata bazai ce bazai bashi ita ba sedai yana tsoron kar yace sedai ya bashi Sakina ƙanwarta.


💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol