Free chapter · Read without an account

PART 1

by ABUBAKAR MUHAMMAD · RAINON ALJAN.

[9/4, 12:15 PM] A.M.G GRAPHIC DESIGN.: *👹👹👹👹👹



 *RAINON ALJAN* 


* 


🌖🌖🌖🌖🌖🌖

   (ĆŠaukar fansar *Fidal* )




👹👹👹👹👹👹


NA;-A.M GOZAKI.

_________________



ELEGANT ONLINE WRITER"S

  

  PAGE 1.

……………………………






 Hajiya Hasina ta kasance Ć´ar garin borno tare da iyayenta,sannan babanta attajirin mai kuÉ—ine wanda yayi Ć™aurin suna,bayan ta kai shekara 25 aduniya allah yayi ma mahaifan nata rasuwa a wani hatsarin jirgi daya afku dasu,haka ta cigaba da rayuwa ita kaÉ—ai a cikin gidan sai Ć´an aiki dake tare da ita.




 A cikin abokan baban ta na wajen kasuwanci,akwai wani attajiri mai suna alhaji tukur mai shadda,alhaji tukur amintacce ne ga mahaifin Hajiya hasina,inda yake taimakonta wajen gudanar da hurÉ—oÉ—in kasuwancin ta,tun da yanzu duk É—umbun dukiyar ta zama tata.




A hankali a hankali har ya yanke hukuncin ya tuntuɓeta yaji idan zata aureshi,domin yana son ta kasance kusa dashi kodan saboda ƙarancin shekarunta ga kuma dukiya mai yawa da take juyawa a gida ita kaɗai.




 Daga Ć™arshe hajiya hasina ta amince ta aureshi,ansha bikin su cikin kwanciyar hankali da lumana.




Daga gidan alhaji tukur kuwa,yanada mata biyu Aliya da jamila,wadda kowaccen su tana da Ć´aĆ´a biyu,Aliya tana da Mahmud da mansur,sai jamila tana da munawwara da mannir,kuma dukkanin Ć´aĆ´an sun haura shekara ashirin da biyar a duniya,gashi dukkanin su babu na kirki daga su har iyayen nasu mata,haka alhaji tukur yake ta haĆ™uri dasu.




A haka hajiya hasina tazo gidan babu mai son ta,dukkanin ƴaƴan gani suke taya dad ɗinsu zai auro sa'ar su a matsayin abokiyar zaman iyayen su,haka hajiya hasina ta cigaba da rayuwa a gidan babu mai ƙaunar ta sai mijin ta,shiyasa ko falo bata iya fitowa koda yaushe tana cikin bedroom ɗinta.


  *BAYAN WATA TAKWAS.*


  Hajiya hasina ce ta tashi misalin karfe biyu na dare domin ta shiga toilet,tasowa tayi daga kan bed cike da magagin bacci tana hamma,wuqil taga kamar wani ya wuce ta gaban windown dakinta,dayake babban falo dayane a gidan sai bed rooms da akayi na kowace mace a gidan da ma ya'yan, a É—an tsorace ta tsayar da hammar da takeyi tayi duba izuwa windon amma bataga kowa ba,É—an É—aga kafaÉ—a tayi haÉ—i da É—an taÉ“e baki sannan ta Ć™arasa room toilet É—inta,ta É—auki kamar minti goma haka sannan ta fito dauke da alwala domin yin nafilar dare kamar yadda ta saba,ta kabbarra sallah kenan taji kamar ana Ć™us Ć™us daga waje,amma hakanan ta share tamkar bataji ba har saida ta gama sallar,addu'a takeyi idon ta a duĆ™e na tsawon lokaci,dagowar da zatayi ta Ć™ara ganin wani ya Ć™ara gittawa ta wajen window É—in ta, daga nan ne fa ta fara faÉ—in "waye anan?"miĆ™ewa tayi ta nufi tagar don ganin ko wanene ke daga wajen,tana zuwa daidai window É—in taji daga waje wasu suna faÉ—i ciki Ć™us Ć™us "ka gane mansur,kai ka tsaya nan ka kalle mana kada daddy ya fito ya kama mu,ni da mahmud zamu shiga ciki mu kasheta da pillow yadda babu wanda zai tunanin kasheta akayi,kaga data mutu sai musan yadda zamu Ć™waci dukiyar ta wajen wancan tsohon",wani dogon numfashi hajiya hasina taja,zaro idanu tayi haÉ—i da daÉ—e bakinta kada su gane taji su,namfa ta fara tunanin ya zatayi ta kuÉ“uta daga hannun waÉ—annan mugayen azzaluman,wata sabuwar dabara ce ta fado mata,nan take ta nufi window data bulla ta baya, a dai dai lokacin ne taji suna kokarin buÉ—o Ć™ofar su shigo,a firgice ta Ć™arasa wajen tagar domin fita kada su risketa,ta buÉ—e ta zura Ć™afarta É—aya kafin ta fidda É—ayar har sun buÉ—e Ć™ofar,innalillahi ta fara faÉ—i tana Ć™ara sauri domin dura wa,mannir ne ke faÉ—in"ke dawo munafuka,sai mun kamoki kibar wani Ć™oĆ™arin guduwa don mun ma rufe gate É—in"haba koma ta kan maganar shi tabi,da gudu ta nufi wajen gate inda suma suka zagaya don shawo kanta duk da sun san bazata iya fita ba tunda gate É—in kulle yake,sannan katangar gidan doguwa ce bazata iya tsallaka ta ba,itako hajiya Hasina tana zuwa taga gate a kulle,ta Ć™wanĆ™wasa ma mai gadi amma inaaa, bai tashi ba don saida suka É—irka mai maganin bacci sannan suka kulle Ć™ofar haka daddyn nasu shima maganin bacci suka bashi shiyasa bazai iya sanin abinda zai faru ba,.


 Ga tsohon ciki haka tay ta Ć™oĆ™arin buÉ—e Ć™ofar amma abu ya gagara,ga shi sun kusa zuwa inda take,cikin iko na Allah kawai Ć™ofar nan ta buÉ—e, ashe da suka tashi rufe gate É—in basu murÉ—a key É—in a daidai ba,kawai ya É—an maĆ™ale ne,aiko tana fita suna zuwa gurin,mansur ne yace "yaya mahmud kunga dare ne,kubarta kawai ko Ć´an shaye shaye sun isheta,kawai mu koma ciki"mahmud ne yace "dalla kauce matsoracin banza,kai mannir mu bita mu kasheta idan ba haka ba bamu sani ba tana iya tsira,gobe ta dawo ta jiĆ™a mana aiki,kasan dad yana iya saka Ć´an sanda su kama mu kamar wancen karan"mannir yace "hakane kuma fa,muje kawai"nan take suka fita cikin sauri suna haske haske don neman ta inda tabi.


Ita ko hasina gudu kawai take gashi babu hitila hannunta,ga wani baƙin duhu saboda gagarumin hadarin dake niyar tasowa,shiyasa bama tasan inda take nufa ba, tana dai gudun cetar rayuwar ta da na ɗan dake cikin cikin ta ne kawai.


Mahmud ne ya dalla falleliyar hitilar dake hannun shi ta wani ɓangare,su manau yacema "kai gata tacan wajen,mubita tun kafin a fara ruwan nan ta ɓace mana".



hasina gudu take tana waige iya ƙarfinta,kwatsam taci karo da wata bishiya dake gabanta bata kula ba,nan take ta dafe goshinta da hannu ɗaya,inda zafin buguwar da tayi yasa juwa ta ɗauketa ta faɗi nan gurin



…………………………

Shin faɗuwar da Hasina tayi zasu isketa a gurin koko zata tsira daga uƙubar su,don jin cigaban ku biyoni a page na 2.


Yawan comments É—inku yawan typing.


Ina son naji yanayin comments É—inku akan wannan page É—in,shin lbrn ya É—auki saiti koko.?


🌖🌖🌖🌖🌖🌖


Daga ni mai baku nishaÉ—i a koda yaushe *.GOZAKI*

[9/4, 12:15 PM] A.M.G GRAPHIC DESIGN.: RAINON ALJAN

……………………………

(É—aukar fansar *fidal*)




Na:- *Gozaki* 



 *ELEGANT ONLINE WRITER's* 📚📚.



  

  PAGE 2.

……………………………




 Mahmud ne ya fara zuwa inda ta faÉ—i yana ta haske haske amma bai ganta ba,yarfa hannu yayi yace a É—an fusace "oooo shet,lallai ko ina kike saimun nemo ki",haka suma sauran suka Ć™araso gurin amma ko alamun inda tayi basu gani ba,mannir ne yace "ku muje gaba nasan dama  bazata tsaya nan ba"da gudu suka suka nausa can gaba suna nemanta.



Hajiya hasina kuwa ashe ta shiga wani kwalbati dake kusa da bishiyar data bige ta ita,kwanciya tayi sosai ciki ta yadda indai ba wajen suka leƙa ba bazasu taɓa ganinta ba,ta daɗe a gurin bata ɗago ba saboda tana tunanin suna nan basuyi nisa ba.


 Wata gagarumar iska ce ta taso hadari ya gangamo wadda tasa su mahmud tsorata amma duk da haka basu haĆ™ura ba suka cigaba da nemanta ido rufe.


Itako hasina dake Ć™asan kwalbati (lambatu),ganin za'a fara ruwane yasa taji tsoron ci gaba da zama cikin ramin don kada a fara ruwa,cike da kula ta fito daga cikin ramin,ba zato ba tsammani taji ana faÉ—in kunga munafukar can mu kamoto" habawa tana jin haka ta tabbatar da sune,aiko da tayi wata juyawa ta ranta a na kare kudu take suna biye da ita,sun É—auki lokaci suna É—auki ba daÉ—i amma sun kasa kamata saboda tsananin gudun da takeyi domin cetar rayuwar ta.



Dayake unguwar da suke tana kusa da wani daji wanda suke kira da dajin sulbana,dajin sulbana daji ne wanda yayi shekara da shekaru ba'a samu wani É—an adam daya shiga dajin ba saboda tsananin haÉ—arin dajin,basu ankare ba sai ganin su sukayi gab da wannan dajin suna niyar faÉ—a mai,itako hasina bama ta kobi takan haÉ—arin dajin ba ta wafta kai tsaye,inda waÉ—annan samari suka tsaya cak haÉ—i da wani murmushin gefen baki na mugunta,mannir yace "haba wannan ta mutu kawai,bama sai munsha wahalar binta ba kada muma muje mu mutu a banza" atare mahmud da  mansur sukace "hakane fa"suka wani Ć™yalĆ™yace da wata mahaukaciyar dariya,sannan suka bar gurin dasauri kada ma wani mugun abin ya same su a gurin.



Hasina ta daɗe tana gudu bata tsaya ba saboda tana tunanin har yanzu suna biye da ita,saida ta ƙara yin nisa a cikin dajin sannan ta gane cewa sun fa koma,sannan ta tsaya tana ta faman hakin gudu,zama tayi a inda take tsaye duk da cewa batasan a ina take ba ballantana tasan kan ma ta zauna.


Allah sarki,hadarin daya gangamo ne ya fara zubo da ruwa yaf yaf yaf,gashi bata da ko mayafi ballantana ta ɗan tare dukan ruwan,ga wani sanyi dayake hura mata jiki, haka taita ƙanƙame wa tana rawar sanyi inda ruwan sama ya zuge da uban yawa gashi babu inda zata fakewa,sai dai ta ruga ƙarƙashin wata bishiya ta raɓe domin ruwan ya ɗan rage bugun ta,ɗan kwali ta kwanto daga saman kanta ta rufa dan rage dukan ruwan.


Tun misalin 2:30am na dare ake tsugaga ruwannan ba'a tsaya ba sai wajen ƙarfe uku da rabi na dare,wannan dalilin yasa Hasina tayi mugun galabaita tamkar bazata rayuba.


Bayan É—auke ruwanne bacci É“arawo ya sace ta a nan inda take rakuÉ“e da bishiyar,amma duk da tana baccin nan rawar É—ari kawai takeyi kyaf kyaf kyaf,haĆ™oranta na sama suna karo dana Ć™asa,bata farka ba sai wajen Ć™arfe takwas na safe,ta farka ne a firgice tana faÉ—in "lahaula wala Ć™uwwata illa billa"tana faÉ—in hakan ne saboda ganin inda take zaune,wurine dake É—auke da kawunan Ć™warangwal na mutane dama jukkunan Ć™warangwal É—in gasunan fululu, shiyasa taji tana taka wani abu jiya da dare kamar duwatsu,nan take ta miĆ™e tsam duk ta firgice gabaki dayanta.



 Ta É“angaren gidan alhaji tukur kuwa,yana can duk ya ruÉ—e wajen nemanta bai ganta ba,Ć´aĆ´an shi da matan shi ya tara yana tambayar su ,aÉ—an fusace yake cewa "Ina Hajiya Hasina ne??na duba ko ina a gidan nan ban ganta ba" matan nashi ma kallon sama da Ć™asa suka fara yi mishi,Jamila ce tace "ai babu wanda ka bama ajiyar ta a nan,Ć™ilama ta tafi karuwancin ta ne can waje kazo kana wani tsare mutane da tambaya"tana ida rufe bakinta taji saukar wani azababben mari mai ratsa Ć™waĆ™walwa,wata Ć´ar Ć™ara ta saki tana faÉ—in "ni ka mara saboda waccan ballagazai??to wallahi zakazo ka sameni"ya É—aga hannu zai Ć™ara mata ta tashi ta gudu daga gurin tana ta Ć´an maganganu,Alhaji ne ya koma kan su mahmud yana tambayar su,mahmud ne yace "mufa dad muna can wajen birthday partyn aboki mu acan muka kwana,kama daina tambayar mu don bamu san komi a kaiba"mahmud na gama faÉ—in haka ya juya ya kama gabansa inda suma Ć´an uwan nashi suka mara mishi baya,itama aliya da munawwara suka tashi suka barshi nan yaji da matsalar shi shi kaÉ—ai,haka dad ya zauna yana ta tunanin tana ina,zuciyar shi har wani zafi take mai.



 Ta É“angaren Hasina kuwa,da gudu ta tsatstsalake Ć™warangwal É—in na ta bar girin jikin ta tsuma kawai yake,namfa wani sabon tsoro ya bayyana a cikin ranta dama kan fuskar ta,haka ta cigaba da nausawa cikin dajin saboda ko tace zata koma baya batasan ta ina zata fara ba,gashi tana son tayi sallar asuba ga yunwa tana masifar ji,cikinta wani Ć™ugi kawai yake mata,haka ta cigaba da tafiya kamar baza ta kai ba.


Tana cikin tafiyar ne ta shiga wani yanki,inda bishiyoyi ne dogaye sosai inda gurin yayi tsit tamkar babu halitta koda ƙwarine a gurin,haka taita daga kai sama tana kallon wannan dogayen bishiyoyi,gabanta faɗuwa kawai yake jikinta duk bai bata ba......


……………………………

Yawan comment yawan typing.


Sannan wannan littafin na kuÉ—i ne ba kyauta ba.


N200 kachal.


FREE PAGES ZASU CIGABA DA ZUWA MUKU HAR PAGE 5.


🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰👹👹👽



daga mai baku nishaÉ—i a koda yaushe *A.M GOZAKI*


***

[9/4, 3:14 PM] A.M.G GRAPHIC DESIGN.: RAINON ALJAN

……………………………

(É—aukar fansar *fidal* )



Na:- *Gozaki*




 *ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚📚




 **PAGE 3* 

 *……………………………* 



  Sama sama take jin wasu iface iface kamar daga nesa,natsuwa tayi sosai don jin daga ina ake wannan ihun,bata ankara ba sai dai taga wasu kalar mutane suna ta sakkowa daga dogayen bishiyoyin nan,wasu kuma taga suna ta tuÉ—aÉ—owa daga cikin dajin izuwa nan inda take,wani kalar sauti mutanen ke fiddawa ji kake "wu wu wu wu wu",adadin mutanen a Ć™arance zasu kai mutum 70,maza da mata yara da tsofaffi,gasu dukkanin su bente ne kawai suka É—aura sai matan da suka rufe Ć™irjin su da sarrafaffen ganye,amma sauran sassan jikin nasu a waje yake.



Namfa Hasina ta shiga tashin hankalin da bata taÉ“a tunani ba a rayuwar ta,ganin yadda mutanen ke buÉ—e baki duk fiĆ™a gasu baĆ™aĆ™e sosai da jajayen idanu,riĆ™e suke da wasu irin mugayen makamai.



 Wani wada ne daga cikin mutanen ya hura wani Ć™aho dake hannun sa,nan take gabaki É—ayansu sukayi tsit,daga wani É“angare ne na mutanen suka fara bubbuÉ—a ma shugaban su hanya,daga can nesa naga yana tahowa a saman wata Ć™atuwar giwa,daga gefen shi kuma ga wasu Ć™osassun mutane manyamanya suna tafiya a Ć™asa suna take mai baya.


Hasina waiwaigawa ta fara yi tana neman hanyar guduwa,ganin sun zagaye tane yasa ta fashe da kuka tana faÉ—in "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,wannan wace kalar Ć™addara ce haka ta same ni?? ya Sarkin da baka barin zalunci ka fiddani daga sharrin waÉ—annan halittun marasa imani" tsit ta rufe bakinta saboda wani Ć™aton mashi  da ya cake a kusa da Ć™afafun ta saura Ć™iris ya same ta Allah ya kare,Ogan su ne yake faÉ—i da wata murya tamkar aradu "Wannan babban rabo daga ina haka,yaushe rabon da mu É—anÉ—ana naman Ć´an adam,lallai yau akwai shagali da daddare kenan, hahahaha"ya wani É“alle da wata Ć™atuwar dariya suma mutanen sa suka fara ihu suna jin daÉ—i,can ogan ya É—aga hannu kowa yayi shiru,sai ya nuna ta da mashin dake hannunsa yace "ku kama ta ku kaita wajen tukubar gashi,don naga zatayi maiĆ™o"cikin bin umurni waÉ—annan Ć™attin mutanen dake take mai baya suka kamo hasina,kuka take tana Ć™oĆ™arin fizge hannayen ta amma tamkar bama dasu takeba,haka suka jata har madafar su,É—aureta sukayi a jikin wasu itace dake kafe a tsakiyar rana sannan suka tafi suka barta a nan gurin,ga wata masifaffiyar yunwa dake damunta,ga zazzaÉ“i ya kamata saboda ruwan da ya daketa jiya da daddare.


Daga can gefe wani tsohone É—an kimanin shekaru tamanin,zaune yake a Ć™ofar wani É—an É—aki dake kusa da inda ake sarrafa duk wani nama da aka farauto,da alamun shine mai kula da gurin,kallon hasina kawai yakeyi yana girgiza kai,yana cikin kallon ta ne yaga bakinta yana É—an motsi kamar tana son yin magana amma ta kasa,tashi yayi ya nufi inda take yana cewa "mi kike son faÉ—a ne Ć´ata??"Ć™ara maimaitawa tayi a hankali tace "ruwa ruwa"cike da tausaya mata yaje ya kawo mata ruwan,sosai ta banki ruwannan saboda irin matsanancin Ć™ishin da takeji,duk da cewa tana buĆ™atar abinci,amma bata tambaya ba saboda tayi tunanin ya bata ruwan ne don kada ta mutu suyi asarar namanta kawai cemai tayi "nagode baba,Allah ya biyaka"bai kobi ta kanta ba ya juya ya koma inda yake zaune.



Ta É“angaren su dad kuwa,dad gaba ki É—ayanshi ya fita hayyacinshi,duk yabi ya firgita neman Hajiya Hasina domin ba Ć™aramin sonta yakeyi ba,kodan saboda yadda yake samun kyakkyawar kulawa daga gareta,gidan radio,gidan television,Ć´an sanda da sojoji sun bazu a garin mai duguri nemanta kawai sukeyi,don Alhaji tukur har Ć™yauta ya saka ta Naira million biyu ga duk wanda yaji inda take kokuma ya ganta,amma haka aka wuni har dare yayi ba'a samu masaniyar inda take ba,haka Alhaji Tukur ya koma gida cike da baĆ™in cikin rashin nasarar samun Hajiya Hasina.



Har yanzu dai Hasina tana nan gurin a É—aure,gashi har 7:00pm na dare tayi bataci komi ba sannan bata samu magani ta sha ba,da Ć™yar takeyin numfashi,tana cikin wannan halin ne wannan dattijon ya Ć™ara zuwa gurinta yana cewa "sannu kinji,amma keko baiwar Allah mi ya kawo ki wannan dajin mai matuĆ™ar haÉ—ari haka"namfa ta fara Ć™oĆ™arin furta wani abu amma ta gaza cewa komi,da tsohon nan ya lura da halin da take ciki nan take ya kwance mata É—aurin sannan yace "yawwa zauna na kawo miki abinda zaki ci,sannu kinji"É—an É—aga mai kai kawai tayi,shikuma ya je É—akinshi ya É—auko mata kayan itace (fruit) saboda akwaisu a dajin sosai,dandai ita bata Ć™arasa inda suke bane ta shiga tarko,yana kawo mata su namfa ta fara cin su hannu baka hannu Ć™warya saida ta kusa cinyesu tas duk da cewa suna da yawa,sannan ya bata ruwa tasha sosai,nan take baki ya buÉ—e hankalinta ya dawo jikinta gode ma wannan tsoho ta fara har saida ya dakatar da ita,sannan ya kalleta ya Ć™ara maimaita tambayar shi ta É—azu,yace "Ć´ata keko wace Ć™addara tasa kika  shigo wannan dajin??kodai bakisan matsalolin dake cikin sa bane??" namfa Hajiya Hasina ta kwashe duk labarin abinda ya faru da ita tun daga farko har Ć™arshe ta ba wannan dattijo,ya tausaya mata sosai don har saida yaÉ—anyi Ć™walla saboda tasayi,sannan yace mata "yanzu zan taimakeki,gashima kina É—auke da tsohon ciki, kai"É—an girgiza kai yayi sannan ya Ć™ara cewa "kafin mutanen nan su dawo ki sauri ki bar gurinnan,saboda indai suka dawo suka taddaki a nan lallai saikin mutu,saboda sun daÉ—e basu haÉ—u da nama mai kyau irin naki ba,zasu cinye ki ne batare da jin magiyar da zakiyi musu ba"hasina ta tsorata sosai da maganar tsohon nan,É—an waro idanu tayi haÉ—i da tambayar tsohon tace "yanzu baba taya zan iya barin nan?? bayan ban ma san inda zan nufa ba,kadama na faÉ—a ma wasu can daban"É—an murmusa mata yayi sannan yace "kalli can"wata hanya ya nuna mata,itakuma tabi hannun shi da kallo don ganin hanyar,sannan yace "idan kika miĆ™e wannan hanyar bazaki kauce ba har saikin kai inda hanyar ta rabu biyu,É—aya tabi dama É—aya kuma tabi hagu,to idan kika bi wadda tabi dama itace zata maida ki har saman hanyar da kika shigo cikin dajin nan,idan kuma kika bi ta hagu zata kaiki inda bazaki taba fita ba har abada,saboda itace hanyar da zata kaiki sansanin aljanu,sannan babbar matsalar itace idan kika manta kikai tako koda É—aya ne a hanyar hagun to lallai kinfa shiga kenan bazaki iya komawa ta damar ba koda ace kina son hakan"wani dogon numfashi taja haÉ—i da furzo wata iska mai Ć™arfi daga bakinta,sannan tace "in sha Allah zan kiyaye,nagode sosai baba,Allah ya taimakeka kamar yadda ka taimakeni"cike da mamaki yake jin maganar ta,kallonta yayi yace "amma Ć´ata najj kin cewa Allah,minene wannan kuma??" É—an duĆ™ar da kanta tayi cike da mamaki take É—an kaÉ—a kanta,saboda yadda tambayar shi ta É—aure mata kai,sannan ta É—ago ta kalleshi tace "baba Allah da kaji na faÉ—i Shine Wanda Ya halicci gabaki É—aya duniyar nan da duk wani abu dake cikinta,Shine sarkin da baya mutuwa,koda yaushe a raye yake har abada,shine wanda ya halicce ka ya halicceni,sannan shine sarkin daya baka dama ka kawo wannan shekarun baka mutu ba,shiyasa a koda yaushe muke roĆ™on buĆ™atun mu a gurin Shi" bayan hasina tazo dai dai nan a zancenta tsohonnan jikinshi duk yayi sanyi,sannan ya kelleta yace "yanzu yarinĆ´a taya nima zan koma É“angaren Allah É—in,koda yake ma ni na makara,tunda har na kusa mutuwa shekaru sun ja" murmushi Hasina tayi sannan tace "baka makaraba baba,shi Allah a koda yaushe yana maraba da duk wanda yakoma É“angaren shi,yanzu bari na baka kalmar shahada"namfa Hasina ta karanta mashi kalmar shahada sannan tace yai ta maimaita kalmar a koda yaushe tunda yanzu babu lokacin da zata koya mashi sauran abubuwa,nan take tsohon nan yace "Ć´ata tunda nake ban taba jin daÉ—in da nakeji a daidai wannan lokacin ba,gaskiya na gode Allah ya albakace ki"hasina taji daÉ—i sosai,É—aki ya shiga ya É—auko mata wasu fruit É—in masu yawa ya bata domin tayi guzuri,sannan yace mata "ki tafi da sauri yanzu nasan suna kan hanyar su ta dawowa,nagode sosai,sannan ya sunanki ne?"tace "suna na hasina,sannan kaima daga yau sunanka khalid"haka sukayi sallama cikin farinciki,ta kama hanya,shiko É—an tsoho sai faman maimaita sunayen yake saboda sun burgeshi sosai.



Hasina ko gudu gudu sauri sauri haka take tafiya saman wannan hanya,sai wajen ƙarfe tara na dare ta isa inda hanya ta rabu biyu,tsayawa tayi tsakanin hanƴoyin tana tuna maganar kaka khalid,har zata bi dama ta fasa tajuya zata bi hagu namma ta fasa,wannan kokonton ya shigeta ne saboda a lokacin da yake faɗa mata ƙa'idojin hankalinta yana kan dawowar mutanen can,kada suzo su tarar da ita,shiyasa bataji ƙa'idojin da kyauba.....

……………………………


1-shin wace hanya hasina zata bi,zata tuna koko a'a.???


2-Shin mutanen dajin nan ya zasuyi idan suka tarda Hasina ta kuɓuta.???


Yawan comment ɗinku shine ƙwarin gwiwa ta.


Sannan paid book ne N200 Kachal.


duk maiso yamin magana ta PC ta number dake ƙasa👇👇👇👇



 *GOZAKI* ✍🏻


***

[9/4, 3:15 PM] A.M.G GRAPHIC DESIGN.: RAINON ALJAN

……………………………

(É—aukar fansar *fiÉ—al* )



Duk wanda yake son ya cigaba da samun littafin nan,zai tura N200 ta wannan account É—in 1594865657,ABUBAKAR MUHAMMAD GOZAKI, ACCESS BANK. Idan kuma kati ne za'a tura ta wannan number É—in MTN ***.

GLO ***.

Domin karantashi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.



Na:- *Gozaki*



 *ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚📚


 *PAGE 4*

 *……………………………*




   Tana nan cikin waswasin wace hanya ya kamata tabine kawai tajiyo sauti daga can baya inda ta baro,kasa kunne tayi dakyau don jin wannan sautin minene,a hankali take jin sautin mutanen nan da suka kamata yana Ć™ara kusanto inda take,wani É—an ruÉ—ewa tayi ta rasa ina zata shiga ta É“uya,don tasan lallai ita suke nema,tunanin haÉ—arin shiga hanyar da bata daceba da kuma tunanin haÉ—arin muten dake nemanta yasa tama kasa motsawa daga inda take tsaye na tsawon lokaci,bata ankara ba sai dai ta gansu dab da ita riĆ™e da mugayen wuĆ™aĆ™e,cike da razana Hasina ta ruga zata bi hanyar dama domin tseratar da rayuwar ta,nan take wani baĆ™in hayaĆ™i ya fito daga hanyar dake É“angaren hagu ya ja Hasina da Ć™arfin tsiya,wanda Ć™arfinshi yasa saida mutum biyar suka mutu murus daga cikin tawagar masu cin mutanen dake son kama Hasina,nan take suka tsorata,ogan su yace cikin babban murya "maza kowa ya juya kafin baĆ™in hayaĆ™in nan ya dawo"namfa dukkanin su suka juya domin cetar rayuwar su.


Da komawar mutanen wajen sansanin su,basu zame a ko'ina ba sai inda kaka Khalid yake domin jin taya ya bari Hasina ta kuÉ“uta bayan sanin cewa shike tsare da ita,zaune suka taddashi yana ta maimaita kalmomin da Hasina ta faÉ—a mashi,cike da jin haushin tsohon ogansu ya same shi ya mai wani bugu nan take kaka khalid ya sume sannan ogan yace "ku kaishi É—akin azaba,yau sainaji dalilin da yasa burina na shekaru ya kuÉ“uta daga gareni"nan take É—aya daga wannan manyan mutanen ya saÉ“a shi a wuya ya kaishi wani É—aki dake shirye da kayan azaba kalakala saboda masu laifi,saman wani tafasashshen ruwan acid aka É—aureshi,inda zafin zai cigaba da bugun fatar jikinshi har izuwa ranar da zai faÉ—i gaskiyar abinda ya faru.


  *Bayan sati É—aya.* 


  Misalin Ć™arfe biyar na yamma ne daddy na zaune a parlour cike da tunanin halin da Hasina take ciki ne yaji jikinshi yana wata irin kyarma,nan take zufa ta fara tsatso mashi,su mahmud suna can cikin É—akinsu suna ganin abinda ke faruwa amma babu wanda ya motsa daga inda yake,wasan kafta kutse suke tayi abinsu (ludo),zailani mai gadi ne ya shigo don kiran alhaji cewa yana da baĆ™i a waje,da gudu ya Ć™araso inda daddy yake zaune cikin mawuyacin hali,faÉ—i yake "Alhaji alhaji lpy,innalil lahi wa'inna ilaihi raji'un"yana gama faÉ—in haka ya cicciÉ“e shi izuwa wajen mota,a lokacin ne munawwara ta shigo gidan ta dawo daga makaranta,wani waro idanu tayi cike da tsoro ta ruga inda dad yake tana faÉ—in "zailani mi ya sami dad É—ina?dad ka tashi don Allah",dayake itace Ć™arama a gidan shiyasa suke juya tunanin ta,amma batason abinda akema dad a gidan,zailani ne yace mata "wllh nima na shiga ne zan kirashi yayi baĆ™i naganshi a wannan halin,amma yanzu tunda kinzo ki tuĆ™a motar izuwa asibitin"É—an É—aga kai kawai tayi sannan ta shiga tayima mota key ya buÉ—e gate ta fita,baĆ™in dake wajene suma hankalinsu ya tashi,nan take suka ja motocin su suka bi bayan motar da alhaji ke ciki izuwa asibitin.


Da isar motar munawwara ta fito da sauri ta kira wani doctor akawo gadon da za'a É—ora dady a kai,cikin É—an lokaci wasu nurses suka gunguro emergency bed É—in aka É—ora dad sai emergency room don binciken mike damunshi.


 Ta É“angaren Hasina wadda tayi sati É—aya zungur a sume kuwa,idanuwan ta tafara buÉ—ewa a hankali tana lumshe su,saida ta É—an É—auki Ć´an daĆ™iĆ™u sannan idonta ya buÉ—e gaba É—aya,wasu manyan baĆ™aĆ™en halittu masu fukafukai ta gani suna shawagi a samanta,nan take ta tashi daga kwancen da take a firgice.....




Ku biyoni shafi na gaba don jin wane kalar halittu ne waÉ—annan,sannan miyasa suka hanata bin waccan hanyar da zata kaita har gida.


More comment more typing.



👹👹👹



***

@GOZAKI✍🏻

[9/4, 3:15 PM] A.M.G GRAPHIC DESIGN.: RAINON ALJAN

……………………………



Na:- *Gozaki* 



Paid book N200 only.


Acc:-1594865657

ABUBAKAR MUHAMMAD GOZAKI, ACCESS BANK.


MTN:-***.

GLO:-***.


 *Duk wanda ya tura nashi sai yamin magana ta pc na sakashi a sabon group É—in RAINON ALJAN PAID FANS.*




ELEGANT ONLINE WRITER's📚📚



Last free page

    PAGE 5

……………………………





 Nan take ta tashi daga kwancen da take a firgice,miĆ™ewa tayi cike da tsoro tana kallon waÉ—annan halittu dake mata yawo a sama,tana cikin wannan yanayi ne kwatsam taga wani baĆ™in hayaĆ™i ya bayyana a gabanta,aÉ—an tsorace ta ja da baya tana faÉ—in "haz biyal lahu wa nimal wakil",nan take taga wannan baĆ™in hayaĆ™i yayi baya amma duk da haka bai bar gurin ba,can kawai taga yana sauyawa izuwa halittar É—an adam ahankali ahankali,bayan ya gama komawa mutum sak,cike da mamaki take ganin yana ranĆ™wafa kanshi gareta cikin wata murya mai sautin dake cika ko'ina yana faÉ—in "barka da zuwa duniyar jinnu yake mai girma uwar sarauniya,kada kiji tsoro don bazamu cutar dake ba,yanzu haka ma sarki ne ya turo naje dake gabansa ranki ya daÉ—e",nanfa jikin ta yayi wani sanyi ,tajita a yanayin da bata taÉ“a jinta ba,wai ace itace aljani yake ranĆ™wafa ma har yana cewa uwar sauriniya,to mike shirin faruwa ne???"haka dai tai tama kanta tambayoyi a cikin ranta,cikin firgici taji Ć™afafuwan ta suna rabuwa da Ć™asa ahankali,kafin ta buÉ—e baki tayi magana sai dai ta ganta a wata kalar duniyar da bata taÉ“a ganin wani guri mai makamancin kyawun shi ba,wata Ć™atuwar fada ce wadda babu kowa a cikinta sai dai kayan alatu na gwalagwalai dake ta walwali suna kashe mata ido,namfa kallo yakoma sama tama manta cewa a duniyar aljanu take,kalle kalle kawai take tamkar wata sabuwar baĆ™auyiya,sautin da ya bigi dodon kunnen tane yasa ta dawo cikin hayyacinta,wata kalar sarewa ce ake busawa mai matuqar daÉ—i da ratsa zuciya,haka dai hasina tai ta waige waige amma bataga kowa ba,saida aka É—auki lokaci ana busa wannan daddaÉ—ar sarewa sannan taga wata Ć™atuwar Ć™ofa tana buÉ—ewa a hankali.


Ta bangeren daddy mara lafiya kuwa,likitoci har sun auna shi sun gano cewa hawan jininshi ne ya hau sosai,munawwara ce dake tsaye a bakin operation room É—in tana jiran sakamakon daga doctors É—in,doctor mus'ab ne ya fito daga cikin room É—in,da dauri ta tareshi tana faÉ—in "doctor ya daddy na yake?? ya tashi kuwa??" É—an murmushi doctor yayi sannan yace "ki kwantar da hankalinki,hawan jininshi ne ya hau shiyasa,amma zai samu sauĆ™i in sha Allah"kuka munawwara ta saki haÉ—i da duÉ—awa inda take tsaye tana faÉ—in "dad kada ka tafi ka barni,ka jure dad É—ina"doctor ne yace mata "amma ina Ć´an uwanki? ko ke kaÉ—ai kika zo ne?" É—an É—aga mai kai kawai tayi sannan ta cigaba da kukanta.



Ta ɓangaren hajiya Hasina kuwa,tsaye take tana kallon ƙofar nan dake buɗewa a hankali.....


……………………………


PAGE 6 zai zo muku a sabon group É—in rainon aljan na waÉ—anda suka biya É—ari biyunsu.




@GOZAKI✍🏻

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.