Free chapter · Read without an account

Chapter one

by Rukayya Ibrahimlawal · RIKICIN MASOYA

SHINFIƊA

Yabo da godiya su ƙara tabbata ga Allah Ubangijin talikai mai kowa da komai, ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani iko tare da baiwar rubuta wannan littafi.Tsira da aminci su tabbata ga Manzon tsira Annabi Muhammad (S.A.W)

Allah ka karo Aminci ga sahabbansa da iyalan gidansa, ka sanya mu a cetonsa Ranar gobe kiyama.




TSOKACI

Wannan labari mai taken Rikicin masoya Ƙirƙirarren labari ne mai haɗe da Labarin da ya ke faruwa a gaske.Labari ne Akan wasu masoya guda biyu masu tsananin don junansu duk da yawan Rikici da Rashin fahimtar juna da ke tsakaninsu.

Labari ne da ke kunshe da salon soyayya na dabam soyayyar gaskiya, riƙon Amana da sauransu.




GARGAƊI

Ban yarda wani/wata ya sauya mun labari ta wata fuskar ba,domin wannan labari yanada matuƙar Amfani da tasiri a gurina.




  Page 1⃣


A jami'ar Bayero University Kano da misalin ƙarfe 12 na rana.

Tafiya ta ke cike da nutsuwa tana rungume da wani file a ƙirjinta, da alama takardu ma su muhimmanci ne a ciki.


Cike da nutsuwa ta ke tafiya yayin da fuskarta ke ɗauke da fara'a, lokaci zuwa lokaci ta kan yi smiling wanda hakan ke ƙarawa innocent face ɗinta kyau.


Da dukkan alamu tana tunanin wani abun da ke sanya ta nishaɗi ne.


Ba ta yi aune ba kawai sai ji ta yi ta yi arangama da mutum, takardun da ke hannunta duk suka watse a ƙasa.


Kallo ɗaya ta yi wa gayen ta ɗauke kai tare da durƙusawa tana tsince takardunta.


Shi ma saurayin sunkuyowa ya yi ya durƙusa a gabanta suna facing juna yana taya ta tsince takardun.


Ɗago madaidaitan idanuwanta ta yi ta zuba masa su da zimmar za ta yi masa magana amma sai ta kasa.


Wani irin kwarjini ya mata ga kuma ƙirjinta da ta ji yana harbawa da ƙarfi.

Shi ma kyakkyawan saurayin hakan ce ta faru da shi, da ƙyar ya iya buɗar baki ya ce "Ki yi haƙuri 'yar budurwa, wallahi ban lura dake ba ne sai ji na yi mun yi arangama na san wannan babban zunubi ne pls ki yafe min."


A Lokacin har sun kammala mayar da takardun cikin file ɗin, ta miƙe da zimmar wucewa ta jiyo sanyayyar muryarsa yana ba ta haƙuri.


Sabreen kasa ɗaga ƙafarta ta yi saboda wani abu da ya tsirgar mata tun daga kanta har cikin ɗan yatsanta na ƙafa, ƙoƙarin saita nutsuwarta ta yi sa'annan ta wuce da ɗan sauri ba tare da ta waiwayo shi ba.


Haka saurayin ya ci gaba da tsayuwa a wurin, ya ma rasa wanne yanayi yake ciki, ga baki ɗaya yarinyar ta tafi da imaninsa.


Dafa kafaɗar sa da aka yi ne ya dawo da shi hayyacinsa.

"Asim me kake yi tsaye a nan kuma? Daga cewa kayi mantuwa a hall zaka je ka ɗauko, shi ne ka maida gari naka?"

Abokinsa Ashik ya faɗa.

Murmushi Asim ya yi ya ce "Bakomai friend mu je na ɗauko sai mu wuce koh?" Ya ƙarashe zancen da tambaya.


Shi ma Ashik ɗin murmushi ya yi duk da bai yarda da cewa bakomai ba "to" kawai ya ce suka juya zuwa hall ɗin da suka kammala lecture mintuna biyar da suka wuce a ciki.


Ita kuwa Sabreen takawa ta yi zuwa Bus stop na jami'ar a ƙafa,sauri kawai ta ke ta ƙagu ta ganta a gida.


Ta ƙagu ta ɗora idonta a kan Lily guy, haƙiƙa ta yi missing ɗin shi sosai sai ga shi Umma ta mata waya tana sanar da ita ya zo, shi ya sa take ta murmushi idan ta tuna yau za ta sha dariya sosai tunda ga Lily guy ɗinta ya zo, akwai hira yau.


Bus ɗin ta shiga zuwa gida kamar kullum.

Da fara'arta ta shiga gidan tun daga ƙofar shiga parlourn ta ke ƙwalla masa kira "Lily guy! Kana ina ka zo ga ni na dawo, Lilynah!" Ta faɗa a daidai lokacin da ta murɗa handle ɗin ƙofar parlourn.


Lily da yake kitchen yana taya umma aiki tare da sanya ta nishaɗi ya jiyo muryar Sabreen tana kiran shi da gudu ya ƙaraso parlourn hannunsa riƙe da ludayin miya yana faɗin "you're highly welcome my Angel, Sabreen I miss u alot."


Murmushi ta yi tana Faɗar "Lilynah I'm badly miss u, ya su Mama da bros Jb da fatar suna lafiya?"

Kafin ya amsa ta Kuma jefo masa tambaya "Me kake yi da ludayin miya a hannu?"

"Umma na ke tayawa aiki a kitchen." Ya faɗa

Nan fa hira ta kacame da ma Lily iyayen surutu wanda ko da ba a tambaye shi ba zai faɗa bare an tambaye shi.


Bayan Ya ɗauko littafin da ya manta a hall suka fito tare shi da Ashik, kai tsaye wurin motarsa suka nufa da nufin zuwa gida, sai dai a yau ba ya jin zai iya driving fuskar yarinyar nan ta ɗazu kawai yake gani tana gifta masa kamar walƙiya.


Saboda haka ya ce "Ashik ka yi driving ɗin ba zan iya ba." A kasalance ya yi maganar.


Ashik ya lura Amininsa na da wata damuwa a yau amma ya ƙi sanar da shi, don haka ba gardama ya karɓi mukullin saboda ya lura Amininsa ba ya tare da nutsuwarsa a yanzu. 


Jan motar ya yi zuwa gidansu Asim da ke ƙofar gadon ƙaya, suna ƙarasawa daf da gate ɗin ya danna hon da gudu maigadi ya zo ya wangale masu gate ɗin katafaren gidan ya shigar da motar ciki, sai da Ashik ya daidaita tsayuwar motar sa'annan ya dubi abokinsa wanda har lokacin bai ma san motar ta tsaya ba saboda ya yi nisa a tunaninsa.


Girgiza kai Ashik ya yi alamun tausayawa, yana lura da abokin nasa tun da suka shigo motar har suka iso gidan bai ce uffan ba sai faman tunani yake, yana ta zabga murmushi shi kaɗai.


Dafa kafaɗarsa Ashik ya yi, firgigit ya dawo daga duniyar da ya faɗa ta tunani tare da begen yarinyar da a yau ya fara ganinta.


"Munzo gida sai ka sauka daga motar koh?" Ashik ya faɗa tare da fita ya zaga ya buɗe wa abokin nasa murfin motar kana ya miƙa masa mukullin, ya masa sallamaa tare da zaro nasa makullin a aljihu ya ja motarsa da ya bari a gidan ya fice cike da tausayin Amininsa duk da bai san damuwarsa ba.

*****************


Sabreen kuwa hira suka sha sosai ita da Lilynta, ba su suka tashi ba sai da aka kira Azahar sa'annan ya tafi masallaci ita kuwa ta ɗauki jakarta ta shige ɗakinsu don yin Sallah.


Da ya dawo masallaci ne suka zauna suka ci abinci a tare cike da ƙaunar juna suna yar hirarsu, har umma na tsokanar su da cewa "Ko 'yar gida za a yi ne Lukman?"

Dariya ya saka ya ce "Me kika gani ne Umma?" 

Ta ce "Na ga wannan shaƙuwar taku kai da ƙanwarka ta yi yawa, gwanda mu haɗa ku aure kawai mu huta da wannan shagwaɓar da a ke yi wa Lily."


Sabreen da kunya ta gama cika ta cire hannunta daga abincin ta yi ta miƙe ta bar wurin, har ta kusa kai ƙofar ɗakinsu sa'annan ta waiwayo ta ce "In dai da Lilynah ne na yarda da wannan haɗin ko yau ma a yi." Tana gama faɗa ta shige ciki da gudu tana dariya.


Umma da Lukman suka saka dariya. Umma ta ce "Shakiyiya ki dawo mana miye na guduwa bayan kin faɗa?"

Asim kuwa tun da ya ƙarasa falon bai tarar da Mom ba, kai tsaye ya wuce zuwa ɗakinsa ya faɗa kan luntsumemen gadonsa.


Da ƙarfi ya runtse idanunsa don har zuwa yanzu hoton yarinyar ke yi masa gizo a ido, yana tuna yadda suka yi arangama da ita.

Sanye ta ke cikin wata doguwar riga Baƙa ta ɗora farin hijab iya gwuiwa a kai. 


Ga dukkan alamu yarinyar tana da kamun kai da nutsuwa, ganin farko da ya yi mata ya ji a ransa cewar ya samu kalar matar da ya ke so kuma wacce ta dace ya aura.


A ransa yana addu'ar Allah Ya Sa su sake haɗuwa, haka ya ci gaba da saƙe-saƙensa har a ka kira Azahar ya tashi ya ɗauro Alwala ya wuce masallaci don yin sallah.

********"*********** 


Sai around 11 o'clock sa'annan Sabreen ta gudu zuwa ɗakinsu don yin barci, saboda tun ƙarfe tara na dare da Lily ya shigo gidan suka barƙe da hira su duka har su Umma da Abba suka gaji suka je suka kwanta, ya rage saura ita da Lily yanzun ma guduwa ta yi bacci ya dame ta.


Haye ɗan madai-daicin gadonsu ta yi ta kwanta, sai dai me?

Fuskar gayen nan na ɗazu kawai ta ke gani tana mata gizo sai kuma ta fara tunani, 'Wane ne shi? A makarantar yake kuwa? Ni ban taɓa ganinsa ba sai yau.'

Can kuma ta ja wani uban tsaki "mtsww! To ni koma wane ne ina ruwana da shi? Aikin banza kawai mutane ba kwa kallon gabanku idan kuna tafiya." Ta faɗa tana gyara kwanciyarta.



Share & comment

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol