Free chapter · Read without an account
Page 3
***
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️Maimoon☘️☘️
Khadijat Isiaka Muhammad
(Mum sayyid)
Page 3
____"Sunan babansu Mami Abubakar ya haifi yara takwas Ibrahim,Sulaiman,Usaini,Hassan, Maryam,Zakiya,Fatima dakuma autarsu Aisha, sun taso cikin gata da jindadi kasancewar babansu yanada rufin asiri kuma sunyi karatu dai dai gwargwado na addini dana islama babansu matarsa daya Hajiya zulai...
Yarsu Maryam ta taso da farin jini sosai manya da yara suke zuwa tun bata isa aure ba suna neman aurenta amma Abbansu yace suyi hakuri ta kamalla karatu daga nan sai su nemi yardarta, Ita kuma Maryam basu san tana da wanda take so ba'a gida kasancewar bai taba zuwa gidansu ba sai dai su haddu a makaranta sai kuma lambarshi dasuke waya don abbansu ya siya mata waya sbd haka tsarin gidansu yake indai ka kusa kammala karatu za'a siya maka waya a baka saboda jin lafiyarka in kana maka ranta, sosai suka shaku da Muktar har basa son rabu, bayan ta kammala karatu abba yace ta bawa manemanta dama su fito takira Muktar ta gaya masa yace kinsan halin dana ke ciki bawai munada wani abu bane ni da mahaifiyata kuma bamuda kowa sai Allah sai yayyen mahaifina gashi har yanzu ban samu aiki ba,kin sani sai shagon askin danake lalabawa kina ganin in na zo Abba bazai koreni ba tunda kun fimu hali, Na hanaka irin wanan maganganun amma kakiji, ni sonka nake ba abin hannuka ba kuma zan nunawa iyayena zan iya zama da kai a koh wani yanayi don haka ka shirya ranar juma'a in an sauko daga masallaci ka zo ka gaishe da Abba, toh shikenan Maryam Allah yayi mana jagora suka cigaba da hirar soyayah mai dadi har sukayi sallama....."
"Ranar juma'a bayan sallah sai ga Muktar da abokin Mussadiq sun zo cikin suturarsu wanda su a ganinsu sun dauko wanka da kaya masu kyau nan kuwa kayan duk sun fara kodewa ya kira Maryam a waya gamu a kofar gida tace toh ta turo Aisha ta shigo dasu fallon Abba, da sallama suka shiga Abba ya amsa musu yana cewa ku zauna mana suka zauna tare da zamowa suna gaisheshi, ya amsa yana cewa waye sirikin nawa Mussadiq yace gashi nan, masha Allah yasuna sirikin nawa kuma a wani anguwa kake, sunana Muktar Adamu ina anguwar rigiyar lemo ne nida mahaifiyata kasancewar ni kadai ta kaifa kuma mahaifina ya rasu tun da dadewa sai kanenshi da yayenshi ne suka rage, Masha Allahu "Allah ya jikanshi da rahama", wani aiki kakeyi Malam Muktar, nayi karatu sai dai ban samu aiki ba amma ina lalabawa da aikin aski ne a yanzu dashi muke samun rufin asiri nida mahaifiyata, what; abba yace hmmm zan nemeka,in kun tashi tafiya ku rufe min kofa zan shiga daga ciki ya fada fuska a daure, mungode abba sai anjima koh amsawa bai tsaya yayi ba ya shige ciki rai bace, jikinsu a mace suka fita yana kiran Maryam bata dauka ba sai ya yanke shawarar tafiya in yaso in taga kiran ta neme shi......"
"Zulai" "Zulai" ina amsa maka Alhaji ta fito cikin sauri lfy dai koh, ina koh lfy kinga wanda yarinyar nan ta aiko wai ya zo neman aurenta kuwa, A'a meye yay.....ya katseta wai harni zata kawowa mai aski don raini toh ki tabatarda kin gaya mata kar in sake ganin kafarsa a gidan nan in ba haka ba daga ke har ita ranku in yai duba sai ya baci wlh na gaya miki kin dai jini ,,,haba Alhaji meye don yaron nan ya zo neman aurenta ai yana ma da sana'a tunda ba zaman banza yake ba kuma naga koh kai ai daga baya Allah ya azurtamu bayan wahalhalun da muka sha don hk shima Allah zai warware masa inda rai ai da rabo alhaj.......kiyi min shuru na gaya miki kafin ranki ya baci shashasha kawai na dai gaya miki ni dai fuuuuuuu yayi waje yana cewa na tafi office,,, a dawo lfy tace tare da zama tana mamakin hali irin na dan adam mai manta dah inba haka ba ai Alhaji bai kamata yayi irin wanan zancen ba tunda shima gidansu shi kadai ne mai halin cikinsu kuma shima baidade dayin arzikin ba don ita kadai tasan wahalar data sha a duniya don me zata kyamaci talaka tunda bashi ya zabi talaucin ba Allah ne ya dora masa bawai don baya sonsa ba kawai jarabawace, Ni kam zan kara karfafawa yata ta aureshi insha Allah
***