Free chapter · Read without an account

4️⃣

by Ramlat Abdulrahman Manga · ABIN DA YA BAKA TSORO

ABIN DA YA BAKA TSORO...🦋

       (Arrow Of Destiny)

بسم الله الرحمن الرحيم

*EWF*

3️⃣


Kamar yadda suka yi tsammanin suka kuma zata haka ce ta faru domin zaɓe, cikin nasara da yadda suka tsara kome ya tafi, Sadi Ahmad ya samu dan majalisar wakilai. Daga nan ne wasu abubuwan da shi kan shi ba zai ce ba, suka shiga cikin al'amarin shi ya manta da kome bai da abokin sama da Lawali sai ya kasance Lawali ya zame masa kamar Uba sai yadda yayi da shi idan kana son ganin shi sai ka fara ganin Lawali kafin ka gan shi.


    Sai ya kasance ko lokacin iyalin shi bai da shi, Lawali shine yake da lokacin Azumi matar Sadi. Kusan bata nuna damuwar ta amma a hankali idan ka zauna da ita zaka fahimci rashin lokacin Sadi yana mata ciwo.


   Sadi yana da yan uwa hatta Mahaifiyar shi tana raye domin su ma manyan mutane ne sosai a damagaram, sai dai wani abu daya da yasa suka watsar da Sadi shine tun bayan rasuwar mahaifin su, da farko an bar gadon su akan ayi ta juya musu, da farko ya amince har aka fara. Sai dai kasancewar bai gayawa Lawali ba har aka samu lokaci, shi kuma Lawali dan makotan sune irin yaran nan da basu jin magana, tun yaranta, duk da an ce sai hali yazo daya ake abota, kowanne su yana da dabi'ar shi.


  A lokacin Sadi shi yana jami'a, a maradi shi kuma Lawali yana bin yan siyasa dan bai wani nutsu yayi karatu ba, shi kuma Sadi mutum ne me zurfin ilimin addini da ilimi zamani, sai Allah yasa yana da wata irin baiwa ya iya magana, bawai surutu ba a'a shi mutum ne da matukar zai tsaya a gaban ka toh ba makawa sai ya tab'a zuciyar ka da iya kalaman shi.

   

  Haka yasa yayi farin jini a wurin mutanen makaranta har ya gama, idan suka samu Hutu yana zuwa gida anan ne suke haduwa da Lawali suna kafa hiran siyasa, a hankali Lawali yayi ta cusa mishi ra'ayin siyasa, tun baya so har dai wani zuwan shi lokacin sun kunsan gama makarantar ya dauke shi zuwa office din shugaban jam'iyyar da suke rike da mulki lokacin da suka je yayi dan hira da Sadi, ba karamin al'amari hiran ya zame mishi ba, sai ya fahimci matukar ya dauki Sadi in right hand toh dole ya dauki Lawali domin shi yasan me ake kira siyasa da wannan yanayin ya haɗa su yayi musu bayani, ea farko Sadi yaki amincewa sabida gidan su Babban gida ne kuma yana jin tsoron Mahaifiyar shi da Babban Wan su me suna Aboubakar, shahararren malamin Addinin Musulunci ne a Nijar din, shi yasa yaki amma haka suka yi ta lallashin sa har ya gama makaranta a lokacin ya tunkari gidan su da maganar siyasa, kallon mahaukaci suka mishi, babu wanda ya kula shi har ya gama Haukar shi, rigima kala kala da tijara da rashin mutunci, wanda ya ja Kannen shi da suke bin shi Jamil da Nura suka ce a raba gadon yayi yadda yake so, duk da Uwar su Hajiya Zinnaira bata so haka ba, haka suka raba gadon aka bashi na shi yayi tafiyar shi ya bar gidan tun da ya bar gidan basu kuma ganin kafar shi a kofar gidan ba, yana karkashin ikon Lawali.


  Ko auren shi babu wanda yasani a cikin yan uwan shi, Sadi mutumin kirki ne, haduwar shi da Lawali akan tafarkin siyasa ya zama wani irin gurbataccen mutum, sannan mu'amalar shi da Matar shi Azumi me suna Hamdiya yayi baya ainun ba dan kome ba, sai duk lokacin da ya kusanceta zai ji baya jin gamsuwa kamar yadda ya samu a wurin mahaukaciyr nan, baya jin kome na jin dadin aure, idan yana son ya nutsu dole sai yayi kamar yana tare da mahaukaciyar nan yake jin dadi.


★

Haka rayuwar Baaba me kosai ya cigaba da tafiya, tsawon wata biyar. A kasuwa kuwa taimakon mahaukaciyar da tayi ya kara mata kima da daraja, wanda yasa baki daya ake mata kallon uwa. Allah ya sanya albarka a cikin kasuwancin ta.


   Yau sun dawo ta leka dakin mahaukaciyar wacce suke kiran ta da Yarinye. Kura mata ido tayi ganin itama kallon ta take, idan ba gizau idanun ta yake ba, Yarinye ta kara girma shigowa dakin tayi ta zauna.

"Yarinye kar dai...?"

Ta kasa magana, tana kallon kirjin ta da cikin ta da yayi wata irin tasowa. Lekowa Rabe yayi yana faɗin.

"Baaba me kosai lafiya dai?"

"Rabe yarinyar nan ciki ne da ita"

Ta fada cikin matsanancin damuwa.

"Toh Baaba a zubar mana"

"Kul" ta fada tana kallon Yarinye, mikewa tayi ta nufi dakin Malam, ta zauna shiru tana kallon shi kafin ta ce mishi.

"Malam"

"Na'am Balkisa"

"Yarinye juna biyu gare ta"

"Alhamdulillahi. Allah ya albarkaci abin da zata haifa"

"Malam!"

"Balkisa bawa baya wuce ƙaddaran shi. Allah ya albarkaci abin cikin ya zama me tausayi da jin kai"


"Kaddaran zata mata nauyi" ta fada cikin matsanancin kuka.

"Ita bace ta tsarawa kan ta kome ba, Allah ne ya tsara ba tsari na ba, kuma ba tsarin ki bane, haka zalika ba tsarin ta bane, kin san yadda Allah ya tsara rayuwar abin cikin da mutuwar shi? Toh tsaya me kike bukata?"


"Ina ga a zubda!"

Kallon ta yayi ya ajiye casbin shi sannan ya ce mata.

"Idan aka zubda me zaki cewa Ubangiji? Kin san Arzikin shi ne? Sannan idan aka zubda baki san zai nemi Allah ya bi mishi hakkin shi ba? Tayiwu wani bawan Allah ne Ubangiji ya kawo mana shi domin ya share mana hawaye tayiwu babban hafizin Alqur'ani ne, don Allah idan kina son bada gudummawar ki toh tabbas sai kin zama jajjirtacciya akan cikin jikin Yarinye a yanzu ita bata da damuwa ko ta rabu da cikin amma Kefa? Nauyi na uwa ya hau Kanki reno uwar da D'an naki ne, Allah ya san yawan ladan da zaki samu, akwai mutanen da suke shiga aljanna ba tare da an duba mizanin su ba, baki fatar ki zama daya daga cikin su ne?"


Sharrr hawaye yake tsere akan fuskar ta, kafin ta ce mishi.

"Ina so Malam"

"Dole ki rungume su uwar da cikin"

Zama tayi ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, abin da mugun ban tausayi ne.

"Allah yasan abinda ya shirya sai ta turo miki Rabi'u ya kuma baki ikon tafiyar da kasuwancin ki, ke kika gaya min fa Allah ya albarkaci kasuwancin ki, me kike tunanin idan kika yi wannan aikin me dinbin lada?"


Murmushi yayi yana jin shashekar ta, mace kome girman ta, sai ta nuna maka ita din yarinya ce. Yasan tana tsoron abinda gaba zata haifar ne, amma bai ga wani mutum da ya wuce ƙaddaran shi ba, dan haka ya nutsu yayi ta mata nasiha yana nuna mata illar abinda zata yi da kuma yadda Allah zai iya nuna mata iyakar ta, wannan bangare yayi nasarar tusa mata Tauhidi da iklasi, har ta amshi al'amarin da hannu bibbiyu. Haka ta fito ta samu Rabe har ya sauke dafa dukan da suka daura sawan suna dawowa ya haɗa wutar.


   Haka Baaba me kosai, tayi ta juya al'amarin har washi gari inda ta fadawa Mudansiru da Ghali, suma sun kadu sosai, dan haka suka ce Allah ya sauke ta lafiya, bayan kwana biyu da basu labarin halin da ake ciki suka hada mata kusan CF dubu ashirin da hudu suka bata, kin karba tayi sai da suka yi da gaske. 

Wani kaddarar bata saka bawa a halin kunci amma tana iya saka shi a wani ma'auni na daban da zai tsaya da kafar shi, tun daga ranar Ghali ya dauki nauyin idan zata tafi bayan ta sayar da kosai zai zuba mata nama ta bata ya ce a kaiwa Yarinye. Sannan ya ware mata tantakwashi ya bata nasu.


  A hankali yan wurin suka ji labarin masu shagunan gefen wurin haka suka hada mata kayan masarufi ranar Baaba tayi kuka kamar me, domin dai sun nuna mata suna tare da ita kuma suna tare da ita Yarinye.


   Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, koda cikin ya tsofa haka suka kaita asibiti a lokacin aka yi ta musu fada akan basu kawo ta awo da wuri ba, ita dai Baaba bata iya magana ba, sai basu hakuri tayi ta yi.


     Haka suka gama suka dawo gida, a kofar gidan suka samu Ali yana zaune yana jan zuciya.

"Aliyu me aka maka?"

"Babu kome"

"Toh mu shiga cikin gidan"


 Haka ya shiga cikin gidan ya zauna yana kallon yarinye, ya jima baya shigo gidan daga makaranta sai makaranta, yau ma fada suka yi da Buhayyah, ya sashi fitowa kuma koda su buzu suka tare shi cewa yayi sai yasa an kore su. 


  Haka yasa dan dole suka bar shi. Kofar gidan Baaba ya zauna, duk da cikin su daya da Buhayya amma baki daya basu dogon shiri ba tare da sun yi fada ba, haka yasa baki daya basa zama inuwa daya.


  "Baaba me kosai bata da lafiya ne?"

Ya tambayi Baaba.

"Eh Aliyu"

"Allah ya bata lafiya"

"Amin Ya Allah"


  Dake tana samun kulawa daga cimma me kyau zuwa tsafta sai gata baki daya tayi fess da ita, sai dai kawai rashin lafiyar da yake damun ta kawai. Aliyu bai bar gidan ba sai da magariba ya wuce gidan su, babu wanda ya mishi fada, dan dama ba fadar xa a mishi ba, kuma gwanar fadar ma ba shiri suke ba.


    Haka ya bashi damar dibi kayan ciye-ciyen shi yana kawowa Yarinye idan Baaba bata nan, ya zauna a wurin Malam su yi ta hira, dake Yaro ne me kwazo sai gashi ya makalewa malam yana karatu, a lokacin ba zai wuce shekaru goma sha biyar ba, karatu sosai suke da malam, tun Baaba bata sani ba. Har ta zo tasan Aliyu yana shigowa karatu, Aliyu shi ya bawa malam shawaran ya fito waje su kafa majalisar karatu, duk da malam bai so ba, amma haka suka bude zauren karatu Yara, da shi aka fara.

   

      Allah cikin ikon shi aka fara zuwa, tsakanin sa da Yarinye shakuwa ce ta musamman. Idan ya zauna ita shi zai ta surutu amma ita bata magana sai tayi ta murmushi. Allah ya haɗa jinin su sosai ko Rabe bata kulawa kamar Aliyu. Allah ya taimaka malam bai yarda sun zauna a haka ba, domin tun da Baaba ta gaya masa maganar cikin yake zama yayi rubutu a wanke ana saka mata zuma tana sha, wanda ba karamin taimakawa yake ba musamman lokacin haihuwa, wani lokaci idan malam bai rubuta ba Aliyu ko Rabe wani ke rubutawa. Wanda shima ya dawo gaban malam karatu sosai.


  Karatun da ya fito da malam har jama'ar unguwar suka san da zaman shi. Sanadin haka sai gashi har da manyan maza suna zuwa daukar karatu.


   Cikin Yarinye kuwa shanye watan haihuwan yayi har aka fara damuwa, malam ya cewa Baaba.

"Ki kwantar da hankalin ki lokacin shine bai yi da fitowa ba, yana cika zai diro duniya"


  Kusan rabin kudin da Baaba take samu ya kare sayayyar haihuwar, wanda kusan kayan maza take saya.

*TOP-NOTCH WRITERS*


  

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*


 _Kasancewar bikin kanwata ake ta biyar me suna Zahrah sai kaiwa da komawa nake Hankalina yana kan Babbar kawata Farisah tsaki nayi na wuce can na kuma dawowa na zuba mata ido cikin takaici mahaukaciya ta zare_


  _Malama kin zo biki ne ko kin zo karanta chat kin yi shiru kin b'ata shiru_


  _Wani banzan dariya ta saka min tana d'age min gira_

  

_Hmmm Bestie wai ke ko irin karance-karancen social media baki yi irin su Wattpad,Okada, Arewabooks baki yi?_ 

  _Sake baki nayi ina kallon ta. When rabona da Hausa Novel Allah na tuba tun Iyatuh Abba tana karanta a gidan Radion B.R.C tabe baki nayi na ce mata_

   _Ke rabani da kayan wahala rabona da Hausa novel tun zamanin Iyatuh Abba_

   

_Innalillahi!, Tace tana kallona kafin ta ce. Jasmin yanzun don Allah duk cigaban da aka samu baki san da shi ba? Lallai kin wuce yadda nake tunani kin gani wuri na karanta book din da nake fama da shi_


  _Cikin mamaki na wuce na dawo na zauna kusa da ita nace mata don Allah daura ni a hanya ina ganin kowa na karance-karancen amma ban dani_


   _hmmm lallai zata fashe... Toh saurara da kyau nan da kike gani na karanta books nake na marubuta daban daban amma idan ana dara ana fidda uwa... Kin ga last na ga The Governor's Wife, one to three, after ma gama na karanta Zaytoonah.... Abun dad'i sai na cikaro da Affiyah da Unaisah_


  _Allah Aunty Rukayyah kina karanta online hausa novel ne? Lallai toh ai yanzu ina karanta Zayn Malik Jiya na gama karanta Zanen ƙaddarata,_ 

_Kanwata Amaryan da muke bikin ta ta saka mana baki a she ba banza yarinyar nan ta nace daga gama sakandare tace a direta gidan miji_


_Amarya Zahra toh kuwa nima Zayn Malik nake karantawa musamman rigimar Hajiya da Uncle Bashir, da Zayn da Abul amma kin san zata fashe on October?_


  _Don Allah fa_

  _Hmmmm gamayyar marubutan nan sun hade wuri guda za ta fashe sun fitar da sunan Team din su_


_Aunty Don Allah ya sunan Team din?_

_TOP-NOTCH.... Za ta fashe a books uku Sahla A Paris, Bani Da Laifi Abin da Ya baka Tsoro_


_Wow da gaske?_

_Zan Miki karya ne?_

_Ina da number Mai_Dambu bari na duba nasan zata daura a status...._


_juyawa tayi ta kalle ni ina bin su sa kallo ke kuma ko garzaya Wattpad ko duba Ribar Uwa, Mutum Mugu, Wadata, Uwargidan Bahaushe, Bororoji,Kallabi does story sun tab'a ni_


  _Kut nace sannan na cigaba da cewa don Allah ga Iphone dina daura Wattpad ke kome ma daura min nima ta fashe dani_


 _Tabbas za ta fashe amma fashewar alkhairi....._


_Books din da zasu zo kamar haka_

1- Sahla A Paris

2-Bani Da Laifi

3-Abin Da Ya baka tsoro.

Dukkan su Uku 1k

_Guda daya_ 350

_Guda Biyu_700

_Guda Uku_ 1k


_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_


_and send evidence to does number_

*****

Or

**** or ****

_Dukka zaku iya tura shaidar biya_


_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_


**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah

*+22784506476*


_Welcome ta Top-notch Team_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.