Free chapter · Read without an account
05
🦽👨🏻😭SUN GUJE NI😭👨🏻🦽
(SANADIN CUTAR LAKKA)
IT BASED ON TRUE LIFE STORY.
LABARI DA RUBUTAWA:FARIDAT HUSAIN MSHELIA(UMMU-JIDDAH).
SHAFI NA BIYAR.
ZUCIYA BA TA DA ƘASHI.
Ta ƙwallara wani ihu jin ta yi baya za ta faɗi ƙasa, dan sam ba ta san shine ya shillo ta zuwa ƙasa ba,
kawai ta sadakar
idon nan na ta ya yi sama tsabar tsoratar da ta yi amman sai ta ji ta sauka a hannun mutum wani wawan ajiyar zuciya ta yi cikin tsiwa ta ce"kai amman wallahi kai ɗin nan baƙin mugu ne",
"Oh haka ki ka ce?"
"Eh mana yo ba kaine ka ja reshen da na ke kai ba tsabar kai ɗin baƙin mugu ne ka tsorata ni tare da firgita ni?",
Ɓame ma ta baki ya yi da yatsun hannun shi guda biyu ya yi saurin sakin ta ta faɗi a ƙasa cikin dakewa ya ce"yanzu kin ga aikin ainihin baƙin mugun da ki ke faɗa"ya juya da niyyar shigewa ciki ya bar ta a wajen amman jiyo kukan ta wanda ke nuna alamun kamar ta bige ya sanya shi dawowa tare da tsugunnawa yana duba ƙafar ta da ta ke riƙe da shi alamun tana jin zafi,
Ja ya yi da ƙarfi dan ya san buguwa ce ta yi ƙara sosai har zanin da ta yi ɗaurin kirji ya faɗi ƙasa,tsura ma kirjin ta ido ya yi ya shagala sosai hankalin sa ya yi nisa har tana mi shi magana bai ji ta ba,
Girgiza shi ta yi sannan ya dawo daidai ta dalla mi shi harara tare da cewa"kai kam an yi ɗan iska,yanzu B...... ɗi na ka ke kallo haka daman sai ka ce wani maye?",
Shiru ya yi mata can ya sunkuce ta bai ajeta ko'ina ba sai kan gadon su tare da cewa "bari yau in cire rainin da ke tsakanin mu da ke yau tunda na ga alamar kin raina ni dayawa gashi yau har zagina na ga kina yi",
"Ni....wallahi bani ba ce"ta faɗi hakan tana mai fashewa da kuka dan Hajiyar ta ku duk rashin kunyar ta ba ta saba tarayya da maxa ba sai mijin ta shi ɗin ma tunda ya amshe budurcin ta ƙazantar ta ya hana shi kusantar ta dan ko da ya ji wani shauƙi na son kasance wa tare da ita, yana shaƙar warin da jikin ta ke fesar wa saboda rashin aske gashi sai ya ji sha'awar ya gushe,(ƙalubale gareku mata masu adon sa kaya amman bakya lura da aske gashin matsematsen ki da na hammata haɗa da yawaita wanke gashin kan ki,shin kin san komai iya wankan ki in kina barin gashi ajikin ki kina yin gumi kaɗan dole aji kina wani irin tashi,shin kin san duk iya sa turaren ki ƙamshin turaren daban bashin bashin ki daban haba ƴar'uwa shi fa aure da ki ke gani ana yin sa ne dan samun kwanciyar hankali,shi kuma tsafta da gyaran jiki suna daga cikin muhimman ababen da ya kamata ku dinga dubawa ya na kuma da gayen muhimmanci ki banbamce tsakanin gyara da shafa su janbaki da hoda dan hjaka mata a kula).
Jin ta ɓarke ma sa da kuka ya sa ya dalla ma ta harara"ke a ganin ki ke har wata mace ce da za'a ji sha'awa har ayi rububin son kasancewa da ke?
"Eh mana dah ni ba macen ba ne amman ka lallaɓo za ka min iskanci",
"Zan dai karɓi haƙƙina kuma wallahi ko yanzu na so zan karɓa da ƙarfin cin tuwp amman kasancewar ki wacce ta rako mata duniya ya sa sam ba najin wani shauƙi a tattare da ke",
"Oho dai" ta furta hakan cike da tsiwa ganin yanda xa ta fita daga ita sai kayan bacci ya sa ya janyo ta "ki yi gaggawar cire kayan nan dan na bacci ne sannan ga jikin ki duka a waje",
"To wai ina ruwan ka ne da rayuwa ta ni fa wallahi na tsani mutum mai shegen sa ido da takurar tsiyaa haba!ta shige za ta fice ya fixgo ta,
Ji ya yi gabaki ɗaya ran shi ya ɓaci ta yaya ya je ya gama wahala a kasuwa ya dawo gida amman ya kasa samun kwanciyar hankali a gidan sa,shi ba ga samun kyakykyawar tarba daga mata ba,ba daddaɗan abinci ba,ba kwalliya ba sannan kuma ba magana mai daɗ amman kullum ya yi magana sai a dinga bashi haƙuri ana cewa yarinta ne watarana xa ta bari,
"Yaushe za ta gyara? sai yaushe zai san daɗin aure s sai yaushe zai samu tarairaya daga matar shi kamar yanda kowani namiji ya ke samu idan ya yi aure?
"Babu rana in dai da wannan kucakar ne"
dafe kan shi ya yi da hannu bibbiyu saboda yanda ya ji yana sara mi shi, damuwa ta cunkushe a ƙwaƙwalwar sa,ita ganin bai ce mata komai ba ya sa ta tsallake ƙafar shi za ta wuce ya fyaɗe ta ta faɗi a ƙasa,cikin shan mur ya ce"wallahi xan yi maganin ki raeesat insha Allahu sai kin nadamar abinda ki ka aikata a gareni",
Miƙewa ta yi tana karkaɗa jiki cikin rashin kunya ta e"kan ka ake ji ...."tuɓe rigar ta yi ta nemi wani zani falle ɗaya ta ɗaura,
sanin ba ta yi wankin da ya bar mata ba ya sa ta shige sashen surukar ta(Mahaifiyar Yusuf),tana ganin ta ba ko riga ta ce"Ra'isat lafiya?Ina rigar ki?,
Fashe ma ta da kuka ta yi tamkar wacce Yusuf ya ma ta duka rarrashin ta ta fara haɗe da janye ta su ka shiga cikin ɗakin ta dan gidan gida ne babba wanda ya ƙunshi sassa daban-daban kuma kowa ya san yanda babban gida ya ke ƙaramar magana sai a juya ta ta koma wa ta daban,
"Yusuf ɗin ya ma ki wani abu ne"ta gyaɗa ma ta kai cikin kukan munafurci ta ce"Mama Yusuf ba ya so na kullum cikin zagi da hantara mi ke ina hakuri da shi ,daga na yi magana kuma ya ce min daman ni ba zaɓin ran sa ba ne ke ce da umma ta ku ka matsa mi shi dan dole a ka yi auren",
"Yanzu haka dukana zai yi saboda na haɗa wankin kayana ban yi ba dan kaina na ciwo shine na gudu nan",
Yusuf ɗin?Maman Yusuf ta faɗi hakan cike da mamakin halin ɗan yau,
"eh shi fa mama"ta faɗi hakan tamkar ba ita ce wacce ta gama rushe wa da kuka yanzu-yanzu ba,
"To ki yi hakuri ƴar nan ki koma ɗakin ki insha'Allah zuwa anjima zan shigo sasar na ku in gari ya rufa,sai na sassaɓa mi shi fiye da tunanin ki daga yi mi shi AUREN GATA shine zai dinga wulaƙanta ki to kuwa zai gamu da ni,zan mi shi faɗa kin ji",
Ɗaga kafaɗa ta yi alamun ba zata tafi ba cikin tsiwa ta ce"a'a walle ni ba inda za ni ƙafata ƙafar ki matuƙar kin ga na koma gurin shi,haka kawai dan ba ƴar ki za'a da ka ba shiyasa ki ke ƙoƙarin aika ni ga mahalaka ta, to wallahi in kin gan ni a lahira kaini aka yi"fir ta ƙi tafiya ta tsaya tana ma sirikar ta rashin kunya,
Hakuri kawai Maman Yusuf ta cigaba da ba ta jin irin kalmomin da ta ke fitar wa daga bakin ta na rashin kunya ya sa ta ji gwiywar ta ya yi sanyi dan ita dai ta san Yusuf mutum ne wanda ba ya son raini so ba zai taɓa yarda ya ɗauƙi wannan salon iskancin na ta ba,
Amman duk da haka ba za ta taɓa yarda ya zamto namiji mai duka ba saboda ba ya daga cikin ɗabi'un mutanen kirki idan kuma ya saba shikenan barin sa xai ma sa wuya,
Duba ta kai gun Ra'eesat wacce ke tsaye akan ta ƙiƙam sai ka ce doki,girgije-girgije ta ks tana hararar ta gefe ido tare da magana ƙasa-ƙasa, ta girgiza kai kawai kafin ta ce"to ai sai ki samu waje ki xauna tunda kin cika taurin kai amman ni kam babu inda zani yanzu a sani a gaba da magana acikin gidan nan"
kallon sirikar ta ta tayi sheƙeƙe tare da turo baki gaba sannan tace"da dai kin taimaka mun tafi kafin ya samu ya fice gantalin sa da sunan sallah dan yana daɗewa bai dawo ba,in kuma kina son in fasa ƙwai kowa na gidan nan ya san me ake ciki ne to bismillah",
A tsorace Mahaifiyar yusuf ke Kallon Ra'eesat cikin zuciyar ta ta ce "Ashe daman haka yarinyar nan ta ke ba ta da mutunci ah lallai Yusuf yana haƙuri",
"Muje mu"cewar Ra'isat wacce ta shige gaba tana umurtan mamar Yusuf ta biyota a baya,
jin ba ta biyo ta ba ya sa ta ce"Allah mama gara ki biyoni dan in kin ƙi zuwa zan fasa ƙwai",
Bin bayan ta ta yi jikin ta duk a sanyaye...........
Hajiya Ra'isat na gaida Masoyan ta musamman AHALIN GIDAN "SUN GUJE NI"
More comments
more typing.....
*UMMU-JIDDAH*