Free chapter 路 Read without an account
CHAPTER FOUR
by Ummubasheer 路 MAHAIFIYA TA
*Page 15~19*
*DEVOTED 2 RAHMAT MUH'D NALELE*{Aunty'n Luv}馃槏
*Aunty na Rahmat wannan shafin sadaukarwa ce gare ki, Allah he k'ara miki lafiya, Allah ya k'ara basira da hazak'a kwarin ido tare da laushin hannu, Allah ya kare ki daga sharin mahassada, Ameen, Kiyi ta suburbud'o mana litafin LEEKITAN ZUCIYA {zoka gyara tunani na}* *Taki mai k'aunar ki a koda Yaushe Ummu Basheer*馃挅
*GIBSON JALO BARRACK*
*Cikin* Gibson jalo Barrack Wanda yake Army Barracks Road, wani had'aden Office ne Wanda ya tsaru sosai, Zaune yake akan kujera yana wani aiki a laptop, yana sanye cikin Uniform na sojoji, Saif kenan ba k'aramin haduwa yayi ba, phone d'in shi ne yayi ringing a hankali ya d'auka, koda ya d'auka baiyi magana ba daga k'arshe cikin Voice d'in shi me rud'ar da y'an mata yayi magana.
"Ok Sir"
Iyakan abin da naji yace kenan ya cigaba da aiki, can phone d'in ya k'ara ringing, sai da yaja k'aramin tsaki sannan ya d'aga.
"My Saif hope kana lafiya"
Wani taikaici ne ya kama shi kawai sai ya katse wayar, wai meyasa yarinyar nan ta cika naci, bai tab'a ganin mace me nacin *FEENA* ba, Saif ke wnn maganar a zuciyar shi yayin da ya mik'e ya d'auki wani k'aramin briefcase ya fito Office d'in, yana fitowa wani soja ya karb'a briefcase d'in cikin sauri tare da Sara mai wucewa kawai yayi, yana zuwa parking lot Wani soja ya bud'e mai mota ya shiga sannan sauran securities din shi suka shiga mota tare da barin cikin barrack d'in.
Yakubu Shopping Plaza motocin suka shiga kasancewar d'aya daga cikin su yasan abin da Ogan nasu keda bukata kawai sai ya shiga ciki, bai dad'e ba sai gashi ya fito rik'e da manyan ledoji, motar da Captain Saif yake ciki ya bud'e front seat ya ajiye, sannan ya juya back seat inda Saif ke zaune yayi mai magana alamar sun gama, d'aga mai hannu kawai Saif yayi sannan motocin suka bar gurin tare da d'aukar hanyar Unguwar 80unit, gate man ne ya wangale musu Gate motocin suka shiga sukayi parking a gurin parking lot da aka tanada Wanda cike yake da motoci masu shegen tsada, Fitowa yayi har yayin da wani ke d'auke da briefcase da leddoji, suna zuwa k'ofar parlour'n Saif ya karb'a tare da danna code d'in shiga parlour'n ya shiga.
Salma dake buga game tana ganin shi ta daina Cause ta San baya so, Gaishe shi tayi tare da karb'an leddojin ta shiga kitchen inda Ummi take.
"Mutum sai muskilancin tsiya wallahi matar ka ta shiga uku" Salma tace murya k'asa- k'asa
"Ke kuma da Waye ne"
Turo baki tayi"nida ya Saif mana, daga shigowar shi ya katse min jin dad'in game"
"Allah ya kyauta"Ummi ta fad'a yayin da take karb'an leddojin, fresh milk ne a robobi masu sanyi sai Fura a Jere cikin Wasu had'adun robobi, d'ayan ledar kuma gasashiyar kaza ce sai d'ayan fruits ne irin na gwan-gwanin nan Wanda an riga an fere tare da slicing d'in su in to different shapes, Murmushi Ummi tayi tana k'ara jin son d'an ta a ranta, kullum idan ya tashi aiki sai ya kawo mata wannan k'a'ida ne.
Kitchen d'in ya shigo tare da gaishe ta cikin sanyin murya, amsawa tayi tana sa mai albarka.
"D'azu Yarinyar nan Feena ta kira ni ta gaishe ni, Yarinyar akwai hankali, shiyasa naso ka Aure ta kaga sai Mu k'ara kulla zumunci"
Swan water ya d'auka a fridge yasha kad'an ya ajiye bai ce komai ba sai dai ya b'ata rai.
"Ni a yanda naso ma ku dai-dai ta kanku kawai"
Duk da ran shi a b'ace yake hakan bai hana shi sanyaya murya ba gurin cewa"Ummi karki damu Insha Allah zan samu matar Aure but please a bar maganar Feena"
"Toh Allah ya kawo ta, amma irin wacce nake so"
Murmushi yayi ya fita jin abin da tace, ko sai Yaushe zata cire abin a ranta oho, ya fad'a a ranshi.
*Rugar Gerei*
Najma ba'a son ranta ba taba Abba hakuri, anan ma sai da tasha zagi, taci kuka har ta hakura.
Da yamacin Ranar wata Alhamis ne ta shirya cikin doguwar riga na less anyi shi fitted gown, gashi purple colour sai ya haska fatar ta, light make up tayi sannan tasa purple hijab iyakar gwiwar ta, flat shoe tasa sannan ta nufa gurin Mami dake surfen massara.
"Mami dan Allah ki bari na k'arasa miki sai na tafi"
"A'a ki barshi, kije ki kaima Maman Yusra wannan kud'in adashin dan kinsan yanzu ba son ajiye kud'i nake ba"
"Nifa kawai bana son inga kina aiki ne, gaskiya nan gaba masu aiki zasu dinga komai ke kuma kina hutawa"
"Allah ya nuna mana lokacin idan kinyi Auren"
Turo baki tayi cikin shagwab'a"nifa bazan yi aure in rabu da MAHAIFIYA TA ba"馃槡
Dariya Mami tayi"Ai ko dole wata rana kiyi Aure Mu Rabu"
Buga k'afa ta fara tana cewa ita dai bata yarda ba, nan dai Mami ta rarrashe ta har ta tafi.
Tana shiga gidan su Yusra ta gaishe da Maman cikin kunya sannan ta mik'a mata kud'in, ganin yanda Najma ke jin kunyar ta yasa tace ta shiga d'aki Yusra na ciki, dama kamar jira take ta shige da sauri, Yusra dake kallon wani film a Bollywood na Madhubala sai ganin Najma tayi da sauri ta tashi tana murnar zuwan ta, zama sukayi suna kallon film suna hiran RK da Madhu, sai gurin K'arfe shida ta tashi da niyyar tafiya gida, Yusra ce ta kalle ta cikin wasa da dariya tace"Wato na gane wayon ki dan kin ga Ya Muhseen ya kusa dawowa daga k'walo shine zaki gudu koh"馃槀
"Ke dilla can ba hk bane"馃槖
"To meye ne, ai dai Umman da kike jin kunyar ta tasan komai "馃槤
"Oho ke kika sani"馃槡ta fad'a bayan ta fito d'akin sallama tayi ma Umma Yusra na dariya ta raka ta wace, kad'an ya rage suyi karo dashi, yana sanye cikin kayan k'walo green, sunkuyar da kanta tayi, Murmushi yayi tare da yin magana k'asa k'asa"Beauty na zaki ji ma mijin ki ciwo fa"
Murmushi tayi"Afuwan ban sani ba"
Yusra dake gefe ta kwashe da dariya, Hararan ta Najma tayi"ka ganta koh"馃槖
"Sorry my love and only,ke Wuce ki bamu guri" ya fad'a ma Yusra
"Ba sai kun Kore ni ba asha love lafiya, ama Aminiya kar ki manta a gidan surukai kike"馃槀
Ai ba shiri Najma tayi waje da sauri sai yanzu ta tuna inda suke, Yusra ce ta biyo bayan ta tana mata magana, ko kulla ta bata yi ba, ta shige gida, Yusra na juyowa gidan su taga Ya Muhseen inda suka barshi.
"Ah ya Muhseen baka shiga gida ba?"
"Ina zan shiga bayan kin koran min beauty na"
Dariya tayi tana bashi hak'uri suka shige gida.
*Jalingo Street*
Wani kyakyawan matashin saurayi ne naga ya nufo inda Saif yake zaune, Masha Allah nace ganin Yanda Saif yayi kyau sanye yake cikin blue check d'in riga da black jeans yana sanye da sunglass ga gashin kan shi ya kwanta luf bak'ikirin kwanin ban sha'awa hk ma sajen dake kewaye da fuskar shi duk da fuskar ba alamun ko murmushi.
Saurayin nan ne ya mik'a mai hannu sukayi musabaha,
"Captain ya garin ko ya aiki zance"
Kamar da dutse yayi magana dan Saif phone d'in shi kawai yake dannawa.
Idan da sabo to ya saba da halin Aminin nashi"Captain ko dai kayi budurwa ce kuke charting irin wannan dane-dane hk"
A fusace ya d'ago kai"Kai fa d'an iska ne *SULTAN* ni na fad'a ma hk"
Dariya yayi"Maida Wuk'ar, wasa nake ai nasan kana nan a gwauron ka, nidai na kusa angwancewa da Baby na Salma"
Tsaki yaja domin shifa matsalar shi da Sultan kenan shegen surutun shi.
Mik'ewa yayi suka shiga cikin gidan Wanda kusan estates ne guda.
A wani babban parlour suka zauna inda wani dattijo ke zaune Duk gemon shi furfura ne, cike da girmamawa suka gaishe shi ya amsa cikin fara'a, sannan sukayi ta hira da wasa irin na kaka da jika, sai dai Saif shiru yayi musu kawai jifa jifa yana d'an sa musu baki har Kaka kece mai"Wai kai baza kayi aure bane sai mun bada sadakan ka"
Kwashewa da dariya sultan yayi, hararan shi Saif yayi yana Jan tsaki"Lokaci ne baiyi ba" yace.
"Allah yan nuna mana lokacin"
Duk suka amsa da "Ameen"
*Wane ne SAIFUDEEN?*
SAIFUDEEN ALIYU SULTAN shine cikaken sunan shi, Mahaifin shi Alhaji Aliyu d'an Asalin Fulanin Adamawa state ne, Mahaifin shi Alhaji Sultan cikaken d'an kasuwa ne, matan shi biyu Hajiya Maryam da Hajiya Nafisa, Hajiya Maryam yaran ta uku maza , Bilyamin, Aliyu sai Huzaifa, Hajiya Nafisa yaran ta biyu Haidar da Maimuna, Hajiya Maryam da Nafisa suna zaman lafiya sannan sun rik'e yaran su, ba'a gane wacce ta haifa d'aya daga cikin yaran saboda duka yaran nasu ne, Alhaji Sultan yaba yaran shi ilimin addini dana boko, Bilyamin engineer ne yayi Aure yana da yara Maza Had'u da mace d'aya, Sai Aliyu da ya karanci Businesses, but baiyi aure ba sai da Huzaifa da Haidar sukayi, sannan ne ya had'u da y'ar k'anwar Hajiya nafisa suka fara soyayya, sunan ta Rukkaya, a haka dai har manya suka shiga ciki aka sa ranar aure, har da Maimuna wacce ta samu miji yana aiki a Lagos, Lokacin daurin aure nayi aka d'aura auren Aliyu da Rukkaya, Maimuna da Ishaq, aka d'auke ta zuwa Lagos inda zata zauna.
A unguwar shagari pest 1 suka zauna inda Aliyu ya Gina gidan shi mai kyau, Alhaji Aliyu mutum ne mai kirki da sanin ya kamata, yana da son talakawa da son taimakon su uwa uba kuma addinin da yake dashi domin Duk yawancin musaba'qa da akeyi akan gayace shi yaje gurin gashi da kyauta, Sab'anin Hajiya Rukkaya wacce ta tsani talakawa, bata son su rab'e ta, tana da girman Kai da nuna isa da nuna ita d'in wata babba ce, shekaran su d'aya ta haifa kyakyawan yaron ta namiji son kowa k'in Wanda ya rasa, aka sa mishi suna SAIFUDEEN, a lokacin ne matar Alhaji Huzaifa ta haihu ita ma namiji aka sa mishi sunan Mahaifin su wato Sultan.
Hajiya Rukkaya ta d'auki son duniya ta d'aura ma yaron ta Saif, tana nuna mishi gata da so bare kuma ta jima bata samu wani cikin ba har sai da tayi shekaru Takwas, sannan ta haifa yarinya me kyau taci sunan Mahaifiyar ta wato Salma, tun daga nan haihuwa sai ya tsaya, to Dama da yake wayayiya ce cewa tayi tafi son yara biyu ma, kuji ta fa.
Saif da Sultan sun shak'u da junan su domin makaranta ma d'aya sukayi tun daga primary har secondary to anan ne suka rabu domin Saif makarantar sojoji ya shiga shi kuma Sultan us fara karantar medical Doctor, Sultan maman shi ta k'ara haihuwa yara har uku mace da maza biyu.
A lokacin da Allah ya k'ara bud'a ma Alhaji Aliyu shine ya gina wani had'aden gida a unguwar Manyan masu kud'i da y'an siyasa wato Unguwar 80unit, Baban gida ne sosai na bene, Wanda akwai babban parlour'n k'asa da bedroom biyu sai Upstairs bedroom uku da wani parlour'n a gefe me d'auke da bedroom shine na Alhaji Aliyu, Bedroom d'in sama kuma akwai na Ummi (Hajiya Rukkaya) sai na Salma. A parlour'n k'asa akwai babbar kitchen da store, sai dining area, daga waje ta d'an gefe akwai garden da swimming pool, Sai daga can d'ayan side d'in had'aden flat ne mai d'auke da 3 bedrooms, akwai kitchen a parlour'n da Dining Area, akwai wani corridor Wanda yake d'auke da office da gurin exercises Wanda yake malakin Saif ne,
Kyakyawa ne Saif ya had'u iya had'u fari ne Tass me d'auke da saje zagaye a fuskar shi, Yana da Sexy eyes ga red lips d'in shi masu kyau, Saif Saurayi ne d'an kimanin shekaru 27 a duniya yana da daraja manya sai dai miskili ne na k'arshe ya iya dressing, ga son tsafta Sam mata basa gaban shi domin aikin shi kawai yasa a gaba har yakan cema Sultan bashi da aikin yi idan yaga yana soyayya, a yanzu hk ma Sultan da Salma soyayya suke me zafi sai dai Ummi ta kafe tace sai Salma ta gama makaranta dan tana FCE MODEL ne ta riga ta gama Secondary 2yrs back, kuma Sultan yace za ta cigaba da zuwa idan anyi auren amma tak'i yarda wai saura 1yrs ai, ba yanda Daddy (Alhaji Aliyu) baiyi da ita ba amma tace a d'an k'ara jira ai tana son Sultan kawai dai a Tsarin ta tafi son y'ar ta ta gama karatun ne.
SAIFUDEEN cikaken soja ne, yana aiki cikin barracks na Gibson Jalo Barracks, mutane na son shi saboda kwarewa a aikin shi sai da dai matsalar shi muskilanci, Tunda ya fara aiki iyayen shi ke fama dashi akan yayi aure sai da dai baiga wacce yake so ba, Ummi tasha kawo mai pictures na y'an mata da yaran k'awayen ta but yace ba wacce tayi mai, Ummi nada wata k'awa Hajiya Amina wacce take da yarinya guda d'aya safina ana ce mata Feena ita ce ke son Saif but shi ya tsane ta kuma ta nace mai, Ummi nason Feena ne saboda y'ar masu kud'i ce.
Saif da Sultan aminan Juna ne suna shiri sosai, sai dai muskilancin Saif yana sa ba komai yake iya fad'a ma Sultan ba, koda yana cikin matsala ne, idan kuma Sultan d'in ya gane sai ya tambaye.
Wannan kenan.
Cigaban labari
Zaune yake a office d'in Sultan cikin shigar farar shada yayi masa kyau kasancewar ranar juma'a ce, shiyasa yayi shigar but bai fiye sa manyan kaya ba.
Dr. Sultan ne ya shigo office d'in cikin Mamaki yake cewa"Yaushe kaxo shine baka sa an kira ni ba?"
Tsaki kawai yayi, nan Sultan ya gane saboda baya son takura mishi ne idan yana aiki.
Musabaha sukayi sannan ya mik'a mai ruwan Faro me sanyi, sai da Saif yasha kad'an sannan ya d'an kalla gefe cikin sanyin murya yace"Ina bukatar Aure!"
*{My Beloved Mother}*
*UMMU BASHEER CE*馃尮