Free chapter · Read without an account
CHAPTER TWO
by Ummubasheer · KE HASKE CE
*Tunda* LAILAH take a duniya bata tab'a ganin gida irin wannan ba wannan ai shine ake cewa aljanar duniya tun bata Shiga ba gidan ya tafi da tunanin ta. Inna Mairo ko sakin baki tayi tana kale kale Kayan su suka d'auka suka nufa cikin gidan straight Boys Quarter Hafiz ya kai su gurin ya had'u sosai dan d'akuna ne masu kyau nan ya bude musu wani suka Shiga gaba daya d'akin ya tafi da tunanin su cause komai na buk'atar more rayuwa akwai irin su fridge, Plasma, Kujeru da saitin gado sai A. C ga toilet din ya had'u.
Inna Mairo wacce suka zo tare ta kalle Hafiz tace"d'an nan kana nufin nan ne masaukin mu kamar a Saudiya"
Murmushi yayi"Inna nan ne zaku zauna Idan kun ajiye kayan muje in nuna muku cikin gidan"
LAILAH har lokacin mamakin irin wannan hadaden gidan take. Bayan sun ajiye kayan su ne ya Bi dasu ta wani gate karami mai kyau Wanda nan ne asalin gate d'in Shiga main parlour. Dai dai k'ofar parlour'n ya danna wasu number Wanda yace LAILAH ta rike code d'in saboda Idan Superstar basa nan code suke sawa Wanda shi kad'ai ne ya sani.
Shiga main parlour sukai Wanda sai da Suka kusa sumewa dan haduwa shi inna Mairo sai raba ido take LAILAH ko tasbihi take a zuciyar ta domin dai bata tab'a ganin irin parlour'n ba ko a film.
Nan ya nuna musu gurare a parlour'n sannan ya kai su kitchen Wanda ya tsaru iya tsaruwa ya nuna musu yanda za suyi aiki da komai na Electric.
Inna Mairo tace"kenan ba za muyi amfani da itace ko risho kenan"
LAILAH dariya tayi"Inna ai gidan nan baiyi kalar icce da risho ba"
Gaba d'aya sukayi dariya. Daga nan upstairs ya nufa dasu ya nuna ma LAILAH k'ofar d'akin kowane sai dai bai bud'e ba. Gaskiya ko'ina a gidan ya burge su. Aikin Inna Mairo shine shara da goge gogen guri sai wanke wanke. Sannan ita ce zata dinga ma masu aikin gidan abinci irin masu gadi da masu wanki a laundry da mai kula da flowers .
LAILAH kuma ita ce zata dinga masu SAMEER girki tare da kula da gyaran bedrooms d'in su. LAILAH aikin gyaran bedrooms baiyi mata ba dan a matsayin ta na mace bai kamata ita ce zata dinga gyara musu bedrooms ba.
Bayan Hafiz ya tafi ne suna Zaune a d'aki suna shirya kayan su a wardrobes Nan ta fad'a ma Inna Mairo damuwar ta dan ta d'auke ta kamar Hajaju. Inna dai nasiha tayi mata. Wani idea ne yazo ma LAILAH nan tayi dariya domin hakan ne kad'ai mafita.
Kasancewar sai a washegari zasu fara aiki yasa basu koma cikin gidan ba.
Washegari da safe da missalin k'arfe 9:00am Ranar Saturday.
LAILAH tayi wanka ta d'auki kod'aden kaya tasa ta d'auki wani garin gawayi Wanda daga gida tazo dashi domin wanke baki sai gashi ma Hafiz ya nuna musu toothpaste. Garin gawayin ta d'auka ta d'an shashafa a fuskar ta sannan ta d'auki jambaki ta shafa har kasan bakin ta sannan tayi wani katon cabin tasa kwalli. kayan nata ma sunyi mata yawa dan bata son shape d'in jikin ta ya fito sai tasa wani karamin hijab.
Inna Mairo na ganin ta tace"meyasa zaki bata kyawawar fuskar ki"
"Inna Mairo hakan ne kad'ai mafita. In canza kamani na yanda zasu k'yamace ni. Bana son suga kyau d'ina"
"Allah ya kare ki domin hakan shine daidai"
Allah yayi ma LAILAH kyau shiyasa ta b'oye kyaun ta.
Kasancewa ranar weekend ne yasa basu tashi barci da wuri ba. Inna Mairo ta fara aikin ta yayin da LAILAH ta fara had'a musu break fast. Dankalin turawa da plantain ta soya sai ferfesun cat fish sai ruwan Lipton Wanda yaji su na'a na'a da cita tasa a flask ta shirya komai a dining table.
Inna Mairo ta gama komai na aikin ta sai LAILAH tasa turaren wuta.
SAMEER ne ya tashi da yunwa dan haka da sauri yayi wanka ya shirya ya fito tunda ga sama yake jin k'amshin abinci yasan masu aikin da Hafiz ya kawo musu ne.
Kitchen ya nufa lokacin LAILAH tana goge electric Jin motsin mutum yasa ta juyo da sauri nan suka had'a ido Gaban SAMEER ne ya fad'i.
Da sauri ta sunkuyar da kan ta kasa bakin ta na rawa saurin k'ara kallon ta yayi jin zazak'ar murya amsawa yayi kawai ya nufa dining table.
AYAAN ne ya sauko downstairs sanye da kayan barci yasa earpiece a kunnen shi. Fitowa LAILAH tayi tana sauri nan suka ci karo da kai da sauri tace"kayi hakuri dan Allah"
Kallon ta yayi yana bata rai yana shafa goshin shi. Wucewa tayi shi kuma ya juya dining yana cewa"Amma da alama wannan itace y'ar aikin ko"
SAMEER dai abinci ya cigaba da ci bai kula shi ba sai da AYAAN ya sake magana"to aci ci kayi dai a hankali"
Hararran shi yayi"kai fa d'an iska ne. Duk ina jin ka"
"Wai ni ina wannan sarkin muskilancin ne ko bai tashi bane"
"Je ka duba karka ishe ni"
MAHEER ko na kwance cikin blanket yana barci a natse. Jin ringing d'in waya yasa shi juyi yana duba phone d'in yaga mom d'in shi ce bata rai yayi tare da ajiye wayar har ya sake ringing bai daga ba. Bayan 10 minutes ya tashi ya nufa toilet yayi wanka ya shirya sannan ya sauko downstairs wani irin k'amshi ne mai dad'i ya ziyarci hancin shi.
Sannu a hankali har ya sauko downstairs d'in. LAILAH ce ta nufa hanyar upstairs domin fara gyara bedrooms tana ganin shi tayi saurin gaishe shi ko kallon ta baiyi ba ya wuce yana yatsina fuska.
Mamaki ne ya kamata har tayi tunanin to ko kurma ne baya ji dan ko alamar yaji bai nuna ba.
*Iya yawan comments d'in Ku iya yawan typing din da zanyi dan naga bakwa comments*
*UMMU BASHEER CE*🔮
[11/22, 15:20] Vah💞Merah💖Haï💔Ek😘: *KE HASKE CE...*💡
*{The Story About Friendships, Love, Musicians and Betrayal}*🔮
*NA*
*UMMU BASHEER*
*^√^°DEVOTED TO^√^° Aisha Aliyu Garkuwa*
✨✨
✨
*^√^°BESTOWED TO^√^° Rahmat Muhm'd Rufa'i Nalele*
*&*
*Maimounath o.g*
*____________________________*
Allahuma aafini fii badani, Alhumma'aafinii fii sam'ii, Allahuma 'aafinii fii basarii.
*O Allah! Give me health in my body, O Allah grant me health in my hearing, O Allah grant me health in my sight. (Recite 3times)*
*____________________________*
*Page 5~6*
*LAILAH* tana zaune tayi tagumi tana tunanin yanda za tayi ta nemo musu abin da zasu ci yau tun safe babu abin da suka ci, Wasu hawaye ne masu d'umi suka zubo mata, Hajaju tana kwance tayi shiru nan LAILAH ta mik'e tasa hijab tace "Hajaju bara naje gidan Hanne"
To kawai tace mata, ita kuma ta fita, tana shiga gidan Hanne taga Hanne ta had'e rai, gaishe ta tayi ta amsa da k'yar.
"Dama kud'in wankin da nayi miki jiya, nace bari inzo ko kin samu"
"Ai ko dai banda shi sai dai kiyi hak'uri zuwa karshen wata"
Kamar LAILAH za tayi kuka dan tasan tana da shi kawai baza ta bata bane, Sai tace"Dan Allah ko abinci ne ki taimaka mana dashi wallahi kaka ta ba lafiya"
Tsaki Hanne tayi ta shiga kitchen ta d'auko wani dumamen tuwo miyar kuka duk yayi guda ta mik'a mata kwanon, godiya LAILAH tayi ta bar gidan.
Tana shiga ta ajiye kwanon gaban Inna tana cewa taci, Hanne ce ta basu, Allah sarki y'ar tsohuwa najin yunwa ai nan ta wanke hannu ta fara ci, sai kuma ta tsaya" kizo muci kin zauna"
Murmushi tayi"A'a kici kawai bana jin yunwa"
Cikin rashin yarda da maganar ta tace"haba LAILAH meyasa kinfi son inci dake kici, bazan iya jure ganin cikin yunwa ba dan hk ki wanke hannu muci"
Za tayi magana ta D'aga mata hannu alamar bata son gardama, nan ta wanke hannun suka fara ci suna hira kamar basu da damuwa.
*LAILAH shin Wace ce Ita*
*LAILAH RUFA'I* shine cikaken sunan ta, Mahaifin ta Malam Rufa'i shi kadai Maman shi ta haifa sun bashi tarbiyya na gari baiyi karatun boko ba saboda basu da hali sai dai yakan yi noma sannan yana da d'an k'aramin shagon provision, wata rana ya had'u da wata Kyakyawar budurwa mai suna Aisha, nan yaji yana son ta babu b'ata lokaci yaje gidan su ya nema da'a bashi izinin nemar ta, iyayen ta Fulani ne sai dai Baban su ya rasu daga ita sai Yayan ta, Haruna, an bashi izini har soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin su, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba aka sa musu rana, Rufa'i anan gidan Mahaifin shi aka gyara wani d'aki d'aya inda zata zauna.
Cikin ikon Allah ranar Juma'a aka d'aura auren Rufa'i da Aisha ta tare a d'akin ta, tana ma iyayen shi biyayya suma suna jin dad'in zama da ita, bayan wata tara ta haifa y'ar ta mai kama da ita Kyakyawa sai dai me jini yak'i tsayawa, a cikin dare ta amsa kiran Mahalicin Mu Allah, Malam Rufa'i yayi kuka na Rasuwar matar shi mai biyayya, hk dai ya rungume y'ar shi har akayi sadakar bakwai, Hajaju ita ce ke kula da LAILAH sunan da aka sama yarinyar kenan, madara suke bata har ta fara wayau ake had'a mata da koko, kafin Aisha tayi Arba'in da Rasuwa Mahaifin Malam Rufa'i ya rasu, shima sunyi kuka daga k'arshe suka d'auki hak'uri da dangana.
Bayan shekaru biyar LAILAH tayi wayau, Mahaifin ta na son ta yana nuna mata gata, kwatsam wata rana ya kwanta ciwo, ya d'auki tsawon wata hud'u ba lafiya sannan Allah yayi mai Rasuwa, Allah sarki LAILAH baiwar Allah, hk Hajaju ta cigaba da rainon ta tana tausaya mata, rabon gado akayi sai dai Haruna Yayan Aisha yabi duk hanyar da zai bi ya samu gadon nan duk da cewa dai kud'in duk ya k'are a magani amma har Gadon Maman ta ya had'ame, babu Wanda ya isa dashi dan mahaifin su ya rasu, Maman kuma bata da iko sai dai tayi shiru.
LAILAH da yake ba wayau ne da ita ba sai bata San meke faruwa ba Hajaju dai tayi bakin cikin hakan.
LAILAH Kyakyawar budurwa ce y'ar kimanin shekaru goma sha Takwas, mace ce mai shape sai dai kirjin ta ba acike sosai suke ba amma tana dashi dai-dai kuma a tsaye suke ga nipple, idanun ta farare ne tasss sannan suna da girma, lips d'in ta d'an k'arami Wanda ake cema kissable lips, sannan tana da gashin gira, kuma tana d'auke da dogon hanci, tana da gashi dan har baya yake tana nanade shi da ribbon tasa a dankalin ta sai ba'a lura, LAILAH tana da hak'uri da biyayya, ga tsoro ga kuma ta da surutu, gata da saurin kuka, akwai ta da son jiki sai kace mage, sannan tana girmana na gaba da ita.
LAILAH tana son kakar ta itace ta sa mata suna Hajaju wai a za taje Makkah idan tayi kud'i, tun tana yarinya take fad'in hk sai sunan ya bita, Tana son kakar ta da jin tausayin ta tun tasowar ta take ganin yanda kakar ta ke kula da ita tana nuna mata k'auna shiyasa ita ma take son ta.
Tayi primary and secondary school na government, yanzu ta gama s.s. two sai dai babu kud'in da zata yi S.s.c .e Examinations, dole ta hakura tana zaune a gida, sai dai tana zuwa islamiyya kuma tana da ilimin addini, izifin ta 40 yanzu tana zuwa hadda da islamiyya. Hajaju ce ke taimaka mata har ta samu wannan ilimin.
Bata zuwa gidan Iyayen Maman ta saboda ko taje Kawu Haruna ya dinga d'aure mata fuska kenan yana wani mata bak'ar magana, bashi da kirki ko kad'an shiyasa bata son zuwa gidan.
Suna fama da talauci dan sai su yini su kwana basu ci komai ba, shiyasa LAILAH ta dage tana d'an yin aikin wankau, ko tayi ma Wasu kitso a biya ta to dashi ne suke samun abinda zasu ci, Toh ba ko Yaushe bane take samun aikin shiyasa sukan zauna da yunwa. Wani lokacin ma sai a hana ta kud'in ta da gangar. Ko taje wurin Kawu Haruna ba taimaka mata yake ba.
LAILAH a rayuwar ta tana da burin zama mawak'iya ita burin ta kenan ta ganta tana rera wak'a especially ma dai na larabci. Sai dai tasan babu yanda za'a ta zama kawai dai mafarkin tane, bare k'auyen da suke k'auye ne sosai, suna fama da wahalar Rayuwa.
*Wannan kenan*
Cike da tafiyar k'asaita ya nufa parlour'n gidan nasu cikin sanyi ya bud'e k'ofar sai dai duhu ya mamaye ko'ina baya ganin komai phone d'in shi ya Ciro yana haske hanya sai ji yayi a kunna wuta ko'ina ya cika da Haske, mutane ne ya gani suna tafi tare da cewa"Happy Birthday MAHEER"
B'ata fuska yayi, da sauri AYAAN dake cikin Wasu suit black ya k'arasa kusa dashi tare da rungume shi, SAMEER ma rungume su yayi, shi dai kallon mamaki yake yi, nan AYAAN yaja hannun shi zuwa upstairs ya Ciro wata black suit ya mik'a mai"come on man its your Birthday day let celebrate, ka shirya pls" yana fad'in haka ya fita.
Tsaki MAHEER yaja tare da wurgar da kayan ya zauna, shifa ya tsani takura a rayuwar shi.
SAMEER ne ya nufa bedroom d'in dan sun jishi shiru ga kuma guests dake jiran fitowar shi Wanda friends d'in su ne kawai maza suka gayace su, Wanda shi MAHEER bai San da hakan ba.
"Friend we are waiting for you and you are not yet dressed"
Tsaki yaja baiyi magana ba har sai da SAMEER ya sake magana.
A fusace ya d'ago cikin wani irin voice mai dad'i amma da fad'a yace"Waye ne ya shirya wannan birthday party d'in, shin nace muku ina so ne? I don't like disturbance pls ku salame su now"
Cikin sanyin murya SAMEER yace"come on pls be a man forget the paste and let celebrate its your birthday party pls not for my sake for Allah's Sake"
Ganin yanda SAMEER ke mai magana cikin natsuwa yasa yaji ya hak'ura har ya shirya bayan ya d'auki lokaci mai tsawo.
A hankali yake saukowa daga stairs har ya sauko nan aka hau tafi, AYAAN da SAMEER ne suka sashi a tsakiya ya yanka wani cake mai hawa uku,gurin ya d'auki tafi sannan aka ci aka sha, AYAAN yayi wata wak'a mai dad'i Wanda ya shirya ma MAHEER na mussaman. Sosai yaji dad'in yanda Friends d'in nashi ke k'aunar shi da bashi lokacin su.
Bayan kowa ya watse ne na gansu zauna su uku a parlour'n suna buga game cikin niahad'i, AYAAN ko sai zuba surutu yake daga k'arshe kowa ya tashi ya nufa bedroom d'in shi cikin farin ciki.
Washegari
Wani mota mai kyau ce tayi parking a wani park, MAHEER ne ya fito cikin d'aure fuska sai dai yayi bala'in kyau.
Wata babban mota ce mai kyau naga wani driver ya bud'e mai ya shiga, wata mata ce cikin doguwar riga tayi rolling veil a kan ta tasa sunglasses Kyakyawa ce, kallo d'aya Nayi mata naga kamar su da MAHEER. Da kun ganta kun ga wayayiyar mace.
Kallon shi tayi ta cire sunglasses d'in fuskar shi a d'aure murmushi tayi"I'm wishing you happy birthday Son"
Ko kallon ta baiyi ba ta sake cewa"hope you're happy"
Nan ma bai kula ta ba sai ta mik'a mai wani present cikin wani k'aramin box anyi nade da foiling paper.
Bai amsa ba ama maganar da yayi ya ban mamaki" I don't need anything and pls don't come to see me again I'm being happy without you"
Idan da sabo to ta saba dan haka ta maida glass d'in ta, yayin da shi kuma ya fita motar, tare da nufar gida.
Shin suwaye wa'inan Kyakyawan samareen guda uku Wanda suke amsa kiran Superstars wato SAMEER, MAHEER da AYAAN?
*SUPERSTARS*✨
*SAMEER* Kyakyawan saurayi ne black handsome, ya had'u iya had'uwa, yana da natsuwa da hankali da sanin ya kamata, shekarun shi ashirin da biyar, Alhaji Sa'id da Hajiya Nuratu sune sunan Iyyayen shi su biyu iyayen su suka haifa, shida k'anwar shi Meenal, yana son iyayen shi yana ji da k'anwar shi domin farin cikin ta shine nashi iyayen shi na zaune ne a garin Kaduna.
*MAHEER* saurayi ne d'an kimanin shekaru ashirin da biyar, yana da kyau fari ne Sol mai d'auke da manyan idanuwa da jajayen lips, muskili ne na k'arshe tun yana yaro, sunan Iyayen shi Alhaji Muhammad Sani da Hajiya Aisha, Alhaji Muhammad sani Engineer ne shi kadai iyayen shi suka haifa Baban shi ya rasu, lokacin daya dawo daga karatu k'asar waje ya had'u da Aisha lokacin tana 200 level a University nan suka fara soyayya mai k'arfi har aka d'aura musu aure, suna zaune a Kaduna state, anyi auren kenan da wata biyu Aisha ta gano tana d'auke da ciki, bata so hakan ba saboda sun tsara rayuwar auren su cewa sai sun jima kafin su haihu, domin ita yanzu karatu take kuma har aiki take son yi dan hk basu shirya fara haihuwa yanzu ba, Alhaji Muhammad ma bai so hakan da dan yace haihuwa ai wahala ce.
Haka dai tana karatu tana rainon cikin har ya isa haihuwa ta haifa namiji, suka sa mai Suna MAHEER, tunda ta haihu sai tana barin MAHEER da y'ar aiki, ko Yaushe tana makaranta shi kuma Alhaji Muhammad yana aiki basu da lokacin d'an su, y'ar aiki ita ke kula dashi har ya kai shekaru uku lokacin Hajiya Aisha ta gama karatun ta zata fara aiki, Alhaji Muhammad ko har mantawa yake yana da d'a rayuwar su kawai suke irin na turawa, ana cikin hk suka ce zasu je K'asar Canada karo karatu dan hk suka barshi gurin Granny Mahaifiya ga Alhaji Muhammad, tayi musu fad'a akan me zasu tafi neman wani karatu su bar d'an su ai Wanda sukai ya isa, hk dai tayi fad'a har suka tafi.
Shekarar su hud'u acan dan koda suka gama karatun sai da suka fara aiki, Granny ce ta matsa sai sun dawo, shine fa suka dawo, lokacin da suka ga MAHEER yayi girma dan har ya gama primary, basu damu suce zasu karb'e shi ba, har bayan shekaru biyu da Dawowan su, rashin kula da suke nuna ma d'an su yasa tayi musu magana sai cewa sukai ta rik'e shi kawai har mahaifin shi na cewa ai su basu San tsakuran yara, aiki ya musu yawa, sosai Granny taji haushin hk har kuka tayi tana fad'a kuma tace ita zata rik'e MAHEER.
MAHEER ya taso da tsanar iyayen shi a ranshi domin yana ganin yanda suke nuna rashin damuwa akan shi, bai tab'a sanin dad'in iyaye ba, shiyasa yake son Granny domin ta kula dashi a lokacin da iyayen shi sukai abandoned d'in shi, a lokacin ne ya shiga Secondary School. Yana da tsafta tun yana yaro baya son kazanta.
*AYAAN* Kyakyawan saurayi mai tashen y'an mata kenan d'an shekaru ashirin da hud'u, saurayi mai farin jini, Fari ne amma ba sosai ba dan bai kai MAHEER ba, yana da kyau shima, iyayen shi su biyu suka haifa yana da Yaya sunan ta Naja'at. wacce take aure a Lagos da babyn ta d'aya, Alhaji nasir da Hajiya Batuul sune iyayen shi kasancewar ya taso shi kad'ai hakan yasa suka nuna mai gata duk abin da yake so shi yakeyi, yana da surutu kamar parrot, akwai shi da son jiki, dan ko bedroom d'in shi baya gyarawa, duk inda yaga dama nan yake watsar da kayan shi.
*Friendships*
Abokanen juna ne su uku, hakan ya samo asali ne daga lokacin da suka shiga Secondary School, duk da su SAMEER sun bashi shekara d'aya ama yana da kok'ari ajin su d'aya, tun lokacin suke tare koma burin su su ukun shine su karanci Building and Engineering, dan hk suna gama Secondary School suka had'a baki cewa zasu sama iyayen su dan su tafi OXFORD UNIVERSITY, ai ko hk akayi sukai musu magana kuma sun amince, suna jinjina yanda yaren su ke amintaka. Shi dai MAHEER Granny yayi ma magana itace tayi ma Baban shi magana, to dama shima yana son yayi karatun.
Rayuwar su a Oxford University na cike daban sha'awa domin sun had'e kan su sosai, ba tare da sanin iyayen suba suka fara zuwa School of Musicians, domin suna sha'awar hakan.
Kasancewar su masu hazak'a da maida hankali yasa dan danan suka fara iya wak'a, gasu da Zak'in murya, hk dai suka had'a karatun engineering da Musicians Wanda ba k'aramin wahala suke sha ba dan ko akwai wuya mutum ya had'a abu biyu, to da yake sun sa Kansu shiyasa suka iya.
Kyakyawan samaree ne guda uku cikin shigar su na kayan Graduation, don sunyi Graduating daga Oxford University inda suka fito a Engineers, sai dai saura musu shekara d'aya su gama School of music, lokacin da iyayen su suka gano hk sosai sukai musu fad'a yin hk, cewa bai dace ba, da k'yar da suka lalab'a iyayen suka barsu su cigaba, duk abin nan da akeyi fa ba ruwan Daddy'n MAHEER, shiyasa MAHEER yake k'ara jin zafin su saboda basu damu dashi ba.
Sunyi Graduating daga School of music, nan jirgi ya D'aga dasu zuwa k'asar su Nigeria, SAMEER da AYAAN gidan su na Kaduna suka wuce, shi kuma MAHEER yana tare da Granny a Abuja.
Iyayen su sun Samar masu aiki a Abuja a company's din Daddy'n MAHEER Wanda shine ya malaka musu company d'aya cewa su fara aiki anan.
Wani had'aden gida babba suka Gina domin yafi kusa da gurin aikin su, kowa da bedroom d'in shi, duk Friday suna kai ma Granny ziyara wacce ta zama kakar su, suna fara aiki suka had'u da wani shugaba na mawak'a a Abuja, nan suka nema shawarar iyayen su cewa suna son fara wak'a, sai da sukai masu nasiha sosai sannan suka amince sannan suka ce basu yarda suyi wak'ar da duniya zata zage su ba, komai za suyi suyi mai amfani.
Wak'ar su ba wai na Hausa bane, A'a na English ne da larabci, domin suna yin wak'a ne kamar irin na Al-Afasi, Harris j da Maheer Zain, irin su *Assalamu Alaikum, Muhammad (S.w.A) is my Hero, Eid Mubarak e.t.c, sai na Maheer Zain da Atif Aslam* ire iren su dai.
Superstars sunyi suna sosai dan ba inda ba'a San dasu ba.
SAMEER yana da sanyi bashi da yawan magana kuma ba ruwan shi da y'an mata, kullum yana cikin kewar iyayen shi, ko Yaushe yana jin shi incomplete, yana son samun macen da zata share mai damuwar shi, domin yana jin kad'aici.
MAHEER muskilanci ne dashi da wuya kiga dariyar shi sai dai murmushi idan yana tare da SAMEER da AYAAN, ko Granny kuma su kadai suka San halin shi, yana da tsafta sosai, baya son surutu shiyasa some times baya shiri da AYAAN, y'an mata tsoron tunkaro shi suke saboda ba fuska.
AYAAN sarkin son y'an mata kenan dan shi halin shi ya bambanta da nasu, SAMEER, shi har club yake zuwa ga neman mata, kuma yana d'an shan giya, duk da dai Su SAMEER na hana shi, holewar shi yake dan cewa yake ai lokacin shine.
*Cigaban labari*