Free chapter · Read without an account

9

by Khadeeja Candy · CIWON SO

Yana dawowa daga cefane, Yaya Maryam ta karba ta girma mana shimkafa da miya da dan kifin daya siyo mana. 

Muna tsakar gidan ni da Yaya Maryam Baba ya sallamo ya shigo fuskarsa dauke da damuwa, ni da Yaya Maryam muka gaishe shi ya amsa mana yana kara tambayar bayanin abun da likitocin suka ce, Deen na jin haka ya fito ya tarbi mahaifinsa da far'ar suka shiga cikin falo, be wuce awa daya da yan mintuna ba ya fito cikin yanayin damuwa yayi mana sallama ya fice, duk yadda na so ya tsaya har Yaya Maryam ta karasa girkin ya ci be tsaya ba, sai addu'a yake ta mana yana saka mana albarka. 


Bayan Yaya Maryam ta gama ta zubo mana ni da Deen ita kuma ta zuba a plate dabam ta ci, ni kam kasa ci na yi ga mamakina shi kam sai ya ci abincin sosai kamar ma be taba ci abinci mai yawa irin na ranar ba, aka'ida idan ban ci abinci ba baya ci amman a yau sai ya manta da duk wannan ya zauna ya ci abincin sosai kamar shi ne abincinsa na karshe. 


“Bari na fita na samo miki wani abu da zaki ci”


Ya fada bayan ya kwashe kayan da muka ci abincin, yana fitowa waje Yaya Maryam ta tsayar da shi ta kira ni. 


“Zahra...”


“Na'am”


Na amsa ina yunkuwa da cikin na tashi abu ga mai son jiki. Daker na karaso falon na zauna kusa da mijina, sai ta kalleni ta ce. 


“Kamata yayi ku koma asibiti abaku takardun da ake bukata so that ko zamu nunawa wani muna da hujja amman idan babu takardun aikin da kudin aikin yake rubuce rubuce wani zai yi zaton kamar karya ne, abu na biyu kuma Deen ka yi magana da Hajiya idan tana da wata hanya can da zamu iya samun taimako sai a kara, nima kuma zan yi duk abun da ya dace da yardar Allah”


Shiru Deen yayi kamar ba zai ce komai ba, har sai da na kai hannu na taba shi. 


“Deen”


Ya juyo ya kalleni da murmushi a fuskarsa. 


“Da dai mun dan jira mu ga abun da Allah zai yi, akwai wani magani na sauka da nake son na gwada, kuma idan muka dage da addu'a wata kila komai zai zo da sauki”


Daga ni har Yaya Maryam mamaki muke masa. 


“Wane irin maganin hausa kuma? A garin neman gira a sai a rasa ido, abun da aka ce ya kai stage din da ba a so sai kuma ka ce zaka sha wani maganin hausa?”


Yaya Maryam ta fada, sai yayi murmushi.


“Miliyan bakwai? Haba samunsu ai ba mai yiyuwa ba ga talaka, da ma ace ina da wata kaddarar ne da na aje shago ne nake tsoro fa shagon ma kuma ba nawa ba, Hajiya kuma bata da komai Wallahi yan'uwanta kuma ba wasu masu son zumunci bane balle mu saka ran su taimaka mana, mai son Zumunci yayanta ne kuma Allah ya karbi abun sa, Baba Kuma danginsa ba wasu masu karfi ba ne daga shi har su babu mai tada wani”


“Allah zai ba mu Deen”


Na fada a sanyaye.


“Toh Allah ya kawo mana mafita”


Duk muka amsa da Ameen sannan ya tashi ya fice, be dade da fita ba Yaya Maryam ta saka hijab dinta ta fice bayan ta yi min nasiha ta kwantar da hankali, be dade ba ya dawo da lemun kwalba marar gas da gasashen naman ragon da nake kyautata zaton zai kai dubu uku a yadda rayuwar nan take da tsada. Sai da ya zauna ya bude naman sannan ya riko hannuna na dawo kasa na zauna. 


“Allah yasa ba kudin da kace kana ajiya ka taba ba”


“Toh idan ban taba na siya miki abun da kike so ba, mi zan yi da su”


“Amman kasan abun da yake gabanmu”


“Wannan dabam yanzu kika gama fadin Allah zai kawo mana mafita ai, so kawai ki yi shiru da bakinki ki ci kawai”


Murmushi na yi na kai hannu na taba fuskarsa, sai ya saka hannunsa yana daukar naman yana saka min a baki. 


Washe garin ranar muka koma asibiti duk wani abu daya kamata mu yi sai da muka yi suka hada mu da likita da ya kamata ya duba shi aka kara ba mu wasu gwajen gwajen da zai kai dubu dari biyu da ashiri har da yan canji sama, sannan kuma suka ba mu takardar aikin dabam dake dauke da kudi kusan miliyan shida da dubu dari da sittin, a lokacin ne hankalina da na Hajiya ya kara tashi sai dai shi kadan ban ga wata damuwa a tare da shi ba, har kara ma jiya da aka fada mana yanayin ciwonsa ya nuna damuwa a tare da shi tsabanin yau da kamar ma murna yake da abun. 

Nikam gaba daya na gama tsinkewa duk kuwa da irin kokarin da yake na kwantar min da hankali, Mama ma ko wane dare sai ta kira ta ji lafiyata sannan take iya bachi, sa safe kuma Mijinta zai kira wato mahaifin Deen ya tambayi lafiyar dansa da kuma ni. Ina cin abinci amman hakan be hana rama samun muhallin a jikina ba, daman ance kwanciyar hankali ke kawo kiba ba yawan cin abinci ba, wata kila kuma har da cikin nan dake kara girma kamar yana zanje ni, daman can ni ba wata mai kibar bace, balle kuma yanzu da abubuwa biyu suka hade min gurin daya.

  Ina ganin tausayin mijina a idona, nima kuma zuciyata cike take da tausayinsa ga wata kalar shakuwa da soyayyarsa dake kara rabata wacce ta dara ta da. Ba a dauki lokaci ba aka saka gidanmu na gado kasuwa, duk wanda ya zo ya duba sai yayi masa tayin wulakancin abun da muke zaton zai kai miliyan biyu da wani abu sai ayi masa tayin miliyan daya da yan kai, sai dau daga karshe aka fada mana cewar dilali ake kira yayi masa kudi gida uku sai a dauki na tsakiya. Haka kuwa aka yi sai muka kira dilallin unguwarmu ya duba gidan yayi masa kudi miliyan daya da budu dari takwas sai kuma miliyan biyu da rabi sai kuma miliyan biyu da dubu dari tara. Wasa wasa aka kwashe sati biyu ba siye gida ba wasu idan suka zo suka yi ciniki ba abari ba ba za su dawo ba, wasu kuma idan suka siya sai suce zabi zasu bada mu kuma sai mu ki aminta da hakan saboda muna bukatar kudin ne, sai dai na lura da wani abu daya kwanaki suna ja, lafiyar Deen tana karuwa har wani fresh yake kumatunsa na tasowa kamar wanda lafiya tayi masa yawa. Duk lokacin da yake na ya kwantar min da hankali ne, idan ya dawo daga aikin tsaron shagon da yake sai ya fito da ni tsakar gidan mu zauna mu yi ta hira, daman kuma ya saba baya shigo min hannu rabbana sai ya riko min wani abu ko da minti ne domin ya san ni sarkin kwadayi. 

Yau ma bayan mun magana cin abinci muna zaune waje muna hirar gidan da har yanzu ba a samu mai siya ba, ya kwaso kayan wankina ya fita ya siyo sabulu da omo da zimmar zai wanke min tufafin kamar yadda ya saba idan kayana suka yi datti shi yake wanke min ya goge ya jera min a wardrobe. Sai yau wannan karon bana jin zan iya barinsa na saka hannunsa cikin ruwan ma balle har ya wanke, sanin ciwon dake damunsa ko a da da ace na san ba lafiya yake ba ba zan taba yarda yayi min wanki ba, girki dan kam zan bari domin ban iya girka komai ba ban da ruwan zafi, indomie ma idan aka yi wasa koneta nake, domin na girma da kiriniyar da bata bar ni na iya komai ba. Ina ganin ya dauko bokiti na tashi na fara kwashe kayana


“Me zaka yi wanki saboda na maida ni mahaukaci”


Tsayawa yayi yana kallona kamin ya kyalkyale da dariya.


“Shikenan zauna ki wanke daga yau ba zan sake saka hannuna na wanke ba”


Ya fada saboda ya san babu abun da na tsana a duniyar nan sama da wanki.


“Ai ban ce zan yi ba, amman kai ma ba zaka yi ba”


Kayan ya mika hannu zai karba sai na juya muka fara kokuwa da shi har ya fisge kayan ni kuwa sai haki nake kamar wanda ta yi gudun fanfalaki. Yayi saurin rika ni ya zauna ya rumgume kamar ya san abun da nake bukata kenan rumguma, kamar kar na san da ciwon nan nasa sai na ji babu abun da nake bukata a gurinsa irin ya rumgume ni, sai na ji wani irin sanyi da dadi kamar daman can be saba min da haka ba. 


“Ki daina cewa zaki wahalar da kanki, yanzu fa kin shiga wata na bakwai, cikin nan kara nauyi yake miki”


“Ai ana son a rika motsawa saboda a samu saukin haihuwa”


“Karki damu idan kin je haihuwa ni zan miki nakuda”


Na saka dariya sai ya kama hannuna ya sumbanta.


“I can't wait na ga abun da zaki haifa min Zahra, mace ko namiji duka ina so, ina son na ganki rungume da dana ko yata, and ina fatar wata rana zaki girka min delicious food da hannunnan naki na ci even for once i love you love”


Na yi murmushi ina shafa cikina da yana hannuna, kamin na dago na hade bakina da na shi, da haka na kashe masa jiki zancen wanki tufafi sai ya bi ruwa, daman dai inda ta wannan bangaren ne Deen ba shi da karfin hali, domin ko kwalliya na yi na yi kyau sai yawunsa sun tsinke balle kuma ace na kai ga jikinsa, musamman ma kwana kin nan yana son shige min sosai wani lokacin har da rana baya bari na huta. Ni ko gani gwanar son jiki abu kadan na gaji sai raki haka dai nake hakuri ina bashi hakkinsa domin ko kadan bana son na gasa ta wannan fannin, shi kadai ne hakkinsa da nake jin ina saukewa yadda ya kamata, tun da shi yake dawaniya da ni ta ko wane fanni. 

 Sai daf da sallah La'asar muka yi wanka shi ya fita zuwa masallaci ni kuma na yi tawa Sallar a gida, babu komai a cikin addu'a sai sai namawa mahaifina gafara da kuma rokon Allah ya ba mijina lafiya ya bude mana hanyar da zamu samu kudin magani, daman ita ce addu'a tun daga lokacin da muka shiga wannan matsalar. Baya na gama na dauki carbi ya fara addu'ar da Mama ta sha fada min cewar tana maganin ko wane kalar damuwa kuma tana yaye bakinciki ta kawo haske cikin al'amurra wato La'ilaha illa anta subhanaka inni kuttu minal zalimin.

 Ban aje carbin ba sai da aka kira sallah magariba, abun ka da mai ciki sai da na sake dauko wata alwalar sannan na gabatar da sallah, ina sallamewa na ji muryar mijina ya shigo sai dai addu'ar da nake bata bani damar amsa masa ba, ina kokarin na juyo na kalleshi sai na ji ya rumgume me. 


“Maman Zahra i love you di you know that”


Na daga masa kai sai ya dawo gabana ya zauna yana min murmushi. 


“Allah ya sauke ki lafiya, i can't wait na ga abun da zaki haifa min ina son Allah ya muna wannan ranar”


Ya fada da irin sigar dake bani kamar mijina ba zai ga abun da zan haifa ba.


“Zan haihu Deen kuma zaka ga abun da na haifa da yardar Allah”


Na fada ina kai hannu na taba fuskarsa ga mamakina sai hawaye suka sauko masa fuskarsa kuma dauke da murmushi. 


“Fada min Deen wani ciwon kake ji?”


“No bana jin komai”


Ya fada min yana girgiza kai, a take hankalina ya tashi domin ganin hawaye a idon mijina abu mai matukar wahala, ba kasai abu ke kasa Deen zubda hawaye ba. Wata kila kuma yana cin ciwon ne boye min yake ko kuma wani yanayi yake ji na dabam sai na rasa gane ko daya. 


“Dan Allah ka fada min idan wani abu kake ji”


“Dazun dai ina ji, amman yanzu bana jin komai amman wannan ciwon Zahra bana tashi ba ne na sani, kuma ban san a wane hali zan barku ba, ke da abun da zaki haifa”


Cikin dakiku hawaye suka hadu a idona suka taru suka zubo a fuskata. 


“Tashi muje asibiti”


“Likita ba shi ne Allah ba, ba zai iya canja abun da Allah ya tsara zai faru ba”


“Why are you telling me this Deen? Why?”


“Saboda ina son ki zama mai karfin hali, and ina son ki rika neman min gafarar Allah bayan mutuwa”


Gaba daya sai na ji kamar mafarki nake, domin Deen be taba fada min wata magana da zata tashi hankalina ba irin wannan, wata kila wani yanayin yake ji na dabam. Fashewa na yi da kuka sai ya matso kusa da ni ya rumgume ni ya dora hannunsa saman cikina, a take cikin nawa ya fara motsi kamar zai fasa fatar cikin ya fito ni kaina sai da na yi mamaki domin be taba min haka ba hasalima cikina ba mai motsi ba ne sai idan ina jin yunwa ko kuma can ba a rasa ba, murmushi yayi mai sauti ya daga hijabi ya sumbanci cikin ya dora kansa a sama ya lumshe ido. Haka muka zauna tsit na kasa cewa komai shi ma kuma be dago ba har aka kira sallah Isha'i, sannan ya daga ya mike tsaye sai na bishi da kallo har ya fice. Juyowa na yi na fuskanci alkibla na daga hannuna sama. 


“Ya Allah ni baiwarka ce mai yawan zunubi mai yawan aikaa kuskure, Allah ga baiwar Zahra, Allah makaskanciya a cikin bayinka, Allah ba ni da gata sai naka, ba ni da kowa sai kai Allah, ya Allah dan mijina zai yi rayuwa mai tsawo da wannan ciwon ka sani, idan kuma ba zai yi ba Allah ka sani, Allah ka dauki rayuwata kamin ta mijina, Allah karka bari na dandani dacin rashin mijina a kusa da ni...”


Na fada addu'ar da wasu irin hawaye da ban san adadinsu ba, sannan na kwanta a gurin ina kuka kamar raina zai fita, daker na samu kukuna ya kwanta min har na samu na yi sallah Isha'i, sai na kasa tashi sai rarrafe na yi na isa kusa da gadona na janyo filo na dora na kwanta ina yadda kaina yake sara kamar zai fashe. 

 Ban kwanta dan bachi ba sai dan na samu salama a zuciyata da kuma ruhina, sai kuma bachin ya bani hadin kai yace fir ba sai idonki ba Zahra, har tara da rabi ido na rufe amman babu alamar bachi a kusa ni, sai kusan goma na ji shigowarsa cikin falon bayan ya rufe gidan ya karaso cikin dakin rike da ledar, da gangan na ki na bude ido har ya karaso kusa da ni ya leki fuskata. 


“Zahraty...”


Ban amsa ba, ban kuma motsa ba, hakan yasa shi aje ledar hannunsa ya saka hannunsa biyu ya dauke ni ya dora saman gado ya cire min hijab ya gyara min kwanciyata yadda zata min dadi, sannan ya warware net din dake nade ya rabe iskar fankar dake aiki, ya nufo wayata dake ringing ya dauka. 


“Hello Mama”


Ban ji abun da Mama tace masa ba, sai bayan sun gaisa na ji yana fadin. 


“Ta yi Bachi da safe zan fada mata kin kira Inshallah mun gode”


Sannan ya aje wayar tare da sauke ajiyar zuciya, ya tashi ya nufi bandaki ina jin motsin ruwa sannan ya fito ya nufo ni ya taba ni. 


“Babe na tashi ki yi wanka kar dare yayi jiki jikinki ba dade, kin san ba ki saba bachi ba ki yi wankan dare ba”


“Bana son wanka ni dai hau gadon ka rumgume ni”


Na fada ba tare da na bude idon ba.


“Daman ba bachi kike ba? Toh Bari na yi wankan sai na zo na rumgume ki”


“Yanzu fa”


Sai ya dawo da sauri ya sauro saman gadon ya rumgume ni, wanka da ba mu yi ba kenan daga ni har shi kuma muka kasa bachi dare sai ya zame mana rana. Akan idona aka kira sallah azuba ina kokarin barin jikinsa sai ya rigani tashi ya rika ni muka shiga bandakin da taimakonsa muka yi alwala bayan mun fito ya shimfida min abun sallah shi kuma ya fita zuwa masallaci daman sallahr jam'i bata wuce shi tun da na sani har yanzu da muke tare. 

 Ina lazimi ya shigo, ya juyo na gaishe shi muryar cike da damuwa sai ya amsa cikin far'a da karfin hali irin nasa.


“Ki kwanta ki yi bachi zan hada miki breakfast”


“Mu kwanta tare idan na tashi sai mu sha tea”


“Toh”


Ya amsa min, sai na tashi muka sake komawa saman gadon da niyar bachi sai dai shi a gurinsa ba bachin ne a ransa ba, a take ya sauya salon bachi zuwa biyan bukatarsa. Sai kusan takwas na samu bachi yayi gaba da ni, guraren goma da yan mintuna na farko babu kowa a bayana sai filo ga breakfast dina saman bedside drawer, ina yunkurawa na tashi na ji kaina na sara irin tsararwa da be taba yi ba, yayi min wani irin nauyi kamar ya hadu gaba da yamma an dora min a saman kam. 


“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”


Shi ne abun da na furta sannan na samu sukunin tashi. Ya gyara dakin kamar yadda ya saba, falon ma tsab ya goge ko'ina tsakar gidan tass kamar ni na gyara ya share ko'ina ya wanke komai da muka bata. Komawa na yi daki na samu dankwali na saka a kaina sannan na shiga na hada ruwan wanka na watsa a jikina na fito na saka kokon a gaba na kasa sha, sai hawaye daman idan ban yi kuka ba me zan yi? Haka na wuni cikin damuwa da tunani har wani abu nake jin yana min yawo a zuciyata gashi an ce ba a son mai ciki tana yawan tunani saboda zai iya haifar mata da matsala. Bayan na yi sallah azahar na dawo falo na kunna kallo wai ko zan samu sukunin zuciyata wata kila na iya saka wani abu a cikina, amman sai kallo ya ki burge ni, babu dadi sai kawai na ji ina hawaye. Sai da na yi da gasken gaske na yi ta ambaton Allah sannan na samu hawayen suka tsaya min. Misalin karfe uku na rana na ji ana kwankwasa kofar gidan a take gabana ya fadi for now reason, ba tare da tunanin komai ba na nufi kofar na leka sai na abokan aikinsa Usman da Sani suna rike da Deen idonsa a lumshe yana numfashi a wahale. Da sauri na bude kofar hawaye har sun gama wanke min fuska. 


“Ina ganin Maleria ce ta yi masa mugun kamu, muna aiki kawai muka ga ya fadi jikinsa yayi zafi sosai, amman dai mun kai shi chemist an amsa allura”


Usman ya fada, sai na kasa ce musu komai kuma na kasa janyewa jikin kofar su shigo da shi sai kallon fuskar mijina nake, kamar ya san ina kallonsa sai ya dan dago idonsa ya kalleni, gaba daya kalar idonsa ta canja ta zama rawaya kamar mai yellow fever, baya baya na yi na rufe baki ina fadin. 


“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.