Free chapter 路 Read without an account

CHAPTER ELEVEN

by Ummubasheer 路 KE HASKE CE

Sannu* a hankali lokaci sai gabatowa yake gashi yanzu biki saura sati uku. LAILAH adaidai lokacin ne LAILAH ta gama exam's d'in ta. Kawu yace ta dawo k'auye dan haka shiri ta fara babu yanda ta iya. Aunty Fateema ta dage fa kullum cikin gyara K'anwar ta take har shopping suka je ta siya mata English wears masu daukar hankali ita dai LAILAH kallon ta kawai take. Ga girki ta k'ara koya. Yawan ci y'an school d'in su da k'yar ta sanar musu shima sai da Aunty Fateema tasa ta. Akwai y'an seat mate d'in ta Aysha da Rukayya suna shiri sosai ko ranar da take shirin tafiya sunzo sunyi mata sallama Aysha Nada aure sai Rukayya da aka sa mata rana .taji dad'in zuwan su nan sukayi mata sallama washegari MAHEER ya tura driver ya kai ta k'auye.




Tun dawowan ta tana jin dad'in zaman gidan damuwar ta kawai shine auren nan da tunanin yanda SAMEER yanzu bai yarda da ita ba. Abin mamaki wai kawu na ji da ita yanzu koda yake tasan MAHEER ya siye shi da kud'i.


Matar kawu Inna Jumai mace ce mai kirki kwatata bata da halin Kawu. Tana son LAILAH Shiyasa yanzu da bikin ta ya gabato ta dage da gyara ta kamar y'ar da ta Haifa. Ko yaushe cikin mata nasihar zaman aure take haka ma su Kaka da Hajaju yanzu Hajaju ta warware jiki yayi kyau kamar ba tayi ciwo ba sai dai kuma abin da ba'a rasa ba. Gashi kuma jikin tsufa.



Biki saura sati biyu aka kawo akwati set biyu na gani na bugawa a jarida馃槀 shake suke da kaya wanda Daddy yasa da k'yar mommy ta had'a ita da kawar ta duk da bata son auren hakan bai hana ta Zuba kaya masu kyau ba dan bata son a raina mata d'an ta. MAHEER cewa yayi ba sai yaga kayan ba da Daddyn shi yake cemai yazo ya gani.



Kowa a k'auyen sai labarin kayan auren LAILAH suke dan a k'auyen ba'a tab'a ma wata irin shi ba. LAILAH ma taji mamakin kayan da aka Zuba koda yake tasan Iyayen MAHEER akwai kud'i sosai.



MAHEER wasu abokanen shi su biyu yasa suka je gurin LAILAH suka kai mata Invitation cards. wanda da k'yar Kawu yasa ta fita dan haushin da take ji.



Invitation cards d'in sun had'u fa sosai LAILAH ko ta Kansu bata biba da suka ce akwai abinda za'ayi cewa tayi babu komai sunyi mamaki dan sun MAHEER dai d'an qayu ne. Sai dai sun rok'e ta ta basu number'n wata kawar ta saboda sauran shiryayen da k'yar ta basu number'n Rukayya Shima sai da ta kira Rukayya d'in.


Shiri ake sosai na biki. Kawu sai washe hakora yake dan MAHEER ya bashi kud'in hidimar aure.


AYAAN yayi matukar mamaki bai tab'a tunanin MAHEER zai auri LAILAH ba sai dai shi kanshi ta tabatar ya rasa LAILAH rasawa ta har abada. Sai dai yayi ma d'an uwan shi fatan alkhairi.



SAMEER ya d'auki kusan wata yana jinyar son LAILAH tabbas tayi mai babbar illa a zuciyar shi sai dai yanzu ya sama kanshi hakuri bai nuna ma MAHEER komai ba duk da yana jin zafi sai dai yafi jin zafin LAILAH saboda yasan laifin ta ne da bata amince ma MAHEER ba da hakan bata faru ba.




Sati d'aya aka d'auka ana ma LAILAH dilka. Ranar Wednesday Akayi mata lalle Thursday Akayi saloon. Amarya LAILAH fa ta fito sak a amarya sai dai MAHEER bai zo ba. Dan yasan had'uwar shi da LAILAH sai ahankali dan tana ganin shi zata ce ta fasa auren shiyasa yake lalab'a ta amma ko yaushe cikin mai text messages na bakar magana shi dai shiru yake mata.




Babu wani abu da za'ayi a k'auyen sai dai Walima ranar Friday.


Aunty Fateema tun Wednesday tazo aka fara shirin bikin da ita dan ta tsaya ma Amarya gidan tane ita da y'an uwan ta. Dan MAHEER ya Gina wani hadad'an gida. Gidan ya tsaru kamar a birni. Komai na kayan gida shi yayi sai dai su Aunty Fateema da sukayi wasu gyaran. Gidan ya had'u babban flat ne mai d'auke da 3 bedrooms.


Komai na parlour'n Arsh da bak'i ne har dining area. Kitchen kuma Orange and lemon green an Zuba mata kayan kitchen sai bedroom d'in ta light purple and white. Toilet kuma pink and purple. Bedroom d'in MAHEER kuma Blue and white ne sai D'akin bak'i shi kuma milk and brown colour ne. A parlour'n ta Kujeru set biyu aka Zuba mata dan yana da girma sosai. Akwai wani d'aki na mussaman wanda yake kamar library da office ne sai gurin wak'a ta gefe anyi decoration d'in shi gidan ya had'u sosai gaskiya har wata K'anwar Fateema Maimuna tana fesa ma LAILAH gulmar gidan ya had'u sosai. Ita dai murmushi tayi amma a zuciyar ta haushi ne cike.




Ranar Friday aka gayato wata malama tazo tayi wa'azi da nasiha game da zaman aure. Jikin LAILAH yayi sanyi dan tasha kuka sosai. 



A ranar da daddare MAHEER yazo shida AYAAN dan sun rasa SAMEER wai akwai wani aiki da zaije yi a Kano. Alhalin dai ba zai iya Tsayawa ganin daurin auren bane dan wata irin zafi yake ji bazai iya jure ganin LAILAH da MAHEER ba a matsayin ma'aurata. Ni ko nace gara SAMEER Allah ya baka wata,





Da k'yar Fateema tasa LAILAH ta shirya ta feshe mata jiki da turare. A shagon zaure ta same su suna Zaune kan kujera da yake an gyara gurin sosai saboda juma'a.



MAHEER na rik'e da waya ya d'aura kafa d'aya kan d'aya. AYAAN ne yaga shigowar ta nan ya cire space d'in shi. Yana tsokanar ta.



". Amarya kinsha k'amshi"


Murmushi kawai tayi tana sunkuyar da kanta cikin kunya sai k'amshi ke tashi. MAHEER ko dago kai baiyi ba. Haka dai AYAAN yayi ta Zuba daga karshe dai ya basu guri.



Bayan ya fita babu wanda yace komai har tsawon 15mimutes sai lokacin MAHEER ya dago ya kalle ta. Kamar ya rungume ta yake ji domin tayi mai massifar kyau duk da fuskar ta a rufe yake. Mik'ewa yayi yana cewa"gargad'i d'aya zanyi miki shine kar ki tab'a bari a zargi wani abu game da auren nan ina son mu dinga nuna ma juna soyaya a gaban jama'a"


Ko kallon shi ba tayi ba Shima bai damu ba ya fita.


Komawa d'aki tayi tana share hawaye dan bakin ciki.





Ranar Saturday da missalin k'arfe 2:00pm


A lokacin dubanin mutane suka shaida daurin auren *MAHEER & LAILAH* a bisa sadaki mafi daraja dubu hamsin. MAHEER na hango cikin farar Riga sai murmushi yake yayi bala'in kyau bai tab'a Samun kanshi a cikin farin cikin rayuwa ba irin na yau. Ji yake yafi kowa sa'a da Allah ya bashi masoyiyar shi LAILAH a matsayin matar shi ta aure.




Cire hular kanshi yayi yana Mik'a ma AYAAN wai shi zufa ya ishe shi bai saba ba. AYAAN sai dariya yake abokanen su suna tsokanar shi.



Shiga gidan sukayi domin gaishe da iyaye. MAHEER dai sai bata fuska yake ganin yanda y'an k'auye suka cika gidan sai kud'a akeyi daya shigo wanda sai da yaji kanshi na Sara mai.



A wannan lokacin ko LAILAH tana kunshe kan gado sai kuka take ana faman bata hakuri da k'yar mata shirya cikin wani swiss lace na green and black.



Duk MAHEER ya kosa su fita koda suka fita kuma marok'a Na aikin nasu gurin sai ya cika da hayyaniya sosai sa k'yar ya Shiga mota yasha drinks. Abokai na mai dariya.





Around 6:00pm


Aka shirya amarya domin kai ta gidan mijin ta. LAILAH tasha kuka sosai. Hajaju tayi mata nasiha da k'yar aka raba ta da ita dan Hajaju d'in ma kuka takeyi.



Kaka da Inna Jumai ma duk nasihar sukayi mata. Kawu ma yayi mata ya bata Carbi. Qur'an da abin sallah. Tana kuka aka sa ta a mota. Sai cikin garin Abuja.





Sun iso ana kiraye kirayen sallar magriba. Garin ya fara duhu. Fito da ita akayi akace tayi bissimillah ta Shiga da kafar dama haka Akayi kuwa.


Har kan gadon ta aka kai ta wanda yasha decorations. Ko awa ba suyi ba aka fara shirin tafiya dinner wanda abokanen su MAHEER suka d'auki d'auyin yinshi.



LAILAH kuka tasa ita wallahi baza taje ba sai da Fateema ta had'a ta da Hafiz to dama tana ganin girman shi shine aka shirya ta cikin doguwar Riga na material white. Necklace da earrings duk silver ne. Har takalmi da jaka. 


Kawayen ta kuma blue d'in doguwar Riga sai yellow d'in veil da suka d'aura.



Fitowa da ita su Aysha da Rukayya sukayi. Suka Shigar da ita wata hadad'an mota.


Ashe MAHEER na ciki sai da aka fara tafiya taji mutum ya d'aura hannun shi a saman nata a tsorace ta kalle shi. Murmushi ya sakar mata.


Hararran shi tayi taja hannun ta. K'ara matsuwa kusa da ita yayi yana mata rad'a a kunne wanda nima banji ba sai naga LAILAH ta fashe da kuka. Handkerchief ya Mik'a mata yana cewa"come on baby kar ki bata min kwaliyar ki mana"


Banza dashi tayi har suka isa gurin.


Masha Allah gurin ya had'u tunda inda motar tayi parking Akayi decoration da flowers. Suna fitowa ya rik'e mata hannu suka taka grass carpet d'in sai Jim zubowar flowers sukayi akan su nan kawayen wasu kyakyawar yara biyu suka Shiga gaba suma cikin wedding gown amma pink sun rik'e flowers.


Nan aka saki wata kida wanda SAMEER. AYAAN da MAHEER sukayi. Mai taken *I can't live without you*. Sosai gurin suka mik'e suka dau tafi dan ganin shigowar Ango da Amarya.


Y'an *KE HASKE CE* fans na gani sunsha anko Wato su馃憞馃徎



Queen .zarah lb. princess .Maimuna Muhammad

.Nabeela.Hafsat

.Nafisat Umar.maman Adnan.Meenat.Khadiy pinky.Mariam Tijjani.Sainah(Ummu Meenal)

.Rukkaya Khadija.mom Sayeed.precious.Yar yola.maryam Ibarahim.mommyn Anas.zahra

.Rukkaya. Mommyn Ilham.Ummu Rahma.Rahmat Nalele.Mammyn Abdul.Ummu Hanan.Aisha

.Rahma sambo.Mme Boukar Fatime.Ummu Hanan.Aisha馃尮

Maman ishaq馃尮.Maman Samha

Mamansadiq馃挆.Ummu Saif

Haleemahn sameer馃槄

Beauty.

Surayya馃尮. Ramla(Ummu Ihsan) 

.Xeemah( zainab abdullah

.zainab umar musa. zainab Aliyu

41 Maryam Abdullahi. Ummul masakin.khadyjah(ummu Adnaan)

.Zarah Madikko .Abubakar Ayuba.Ummi ajmal. sumayya yarima . jedda Muh'd. Sumayya yarima.momy hanan

Faeexa Fakai sa'adatu lawal kura


deejama hussain

 Murjanatu. MRS ADAM. Husaina Ahmad dikko(mmn Abdul).



*MAMAN KHALID* 

 *Hindu*

. *Mimi*

. *leemart*

. *juwairiya*

. *momyn Irfan*

 *maman Afra*

. *Umman Annur*

. *maryam*

. *fatima*

. *Bilkisu Muhammad*

. *fatima s noma*

. *aisha kalgima*

 *jamila usman*. *Radiya yahya lawan*. *_~Rukaiya abubakar~_* . *zaynab sarina*

. *ummy*. *mareeyah*. *samira bishir*. *Hauwa Magaji (ummin xee )*. *Hauwa'u mohammad*

. *princess*. *Amal (ummu mis'ar)*. *maman ahmad*. *maman sadiq*. *sumayya yarima*. *Maman muhammad*

. *maman waleed*. *Zainab Muhammad. famcy Abdhul. *_sumayya bashir_Hassana Umar .Muhmelat .maman samha. Yar pot.



Gaba dayan su sunsha anko har y'an team d'in SAMEER.


MAHEER dan dole yasa LAILAH ta saki fara'a tana d'an murmushi duk da zafin da take ji. Har aka umarce su da su yanka cake. Ai ko MAHEER ya nuna ma LAILAH soyaya ita ma haka zaku rantse massoyan juna ne da suke matukar soyaya. 

AYAAN ne ya fito ya fara wakar *KE HASKE CE*馃挕


Habawa nan gurin ya d'auki tafi domin dama kowa cikin su na mata kirarin ita Hasken su ce.


Su Habiba. Beauty. Maman sadiq sai lomar fried rice suke. Yayin da Su Queen. fati s noma. Umman Annur da juwairiya sai lika ma Amarya da ango kud'i suke. Wai nikam kunga min Summaya. Faeexa. Ummu Adnan. Nabeela. Ummu saif. Kuwa inajin dai suna can ana gaisawa da mutane.


Niko Ummu Basheer da sis Maimonath tare da Kawas Badeeyerh sai fama muke da bak'i. Mamyn Abdul ce muka Gani sai yanzu ta iso.


Surukai na su Ummu Rahma da Mommyn Ilham. Maman ishaq na gani nan na K'arasa muka gaisa.


Y'an Haske writers ma ba'a barsu a baya ba dan suma sunci anko sunzo.



Ba abin da ya k'ara sani farin ciki sai dana ba Aunty Rahmat Nalele. Aysha Garkuwa tare da Billyn Abdul. Meneert ce nasa ta kawo musu drinks.



Kai a gaskiya taro yayi taro fa an watse dinner lafiya.


A Daren sai da LAILAH tayi ciwon kai washegari ma da Safe wani taron Akayi dan Mommy ce ta iso da tawagar ta a filin gidan Akayi wani event d'in kuma wanda shigar India Akayi ma LAILAH da MAHEER suka zauna a kujer Shima taron yayi. Dan mommy bata nuna bata son LAILAH ba. Abin mamaki iyayen SAMEER da AYAAN suma sunzo. Har da INDO aka zo sai dai tayi kyau cikin doguwar rigar ta peach colour. AYAAN yaji haushin zuwa da ita da Akayi dan yanzu ma sai da sukayi fad'a dan yace mata y'ar k'auye a abuja. Da k'yar mom ta rarrashe ta.


LAILAH da INDO sun gaisa da juna yayin da jinin su ya had'u sai hira INDO take mata.





Around 6:30pm


Kowa duk sun watse kamar ma ba'ayi taro ba daga Amarya sai Aunty Fateema da Rukayya suna ta mata nasiha suka k'ara gyara ta.da nuna mata ko'ina na gidan. K'arfe9:00pm mazajen su suka zo daukar su LAILAH tasha kuka.


Abokanen Ango ne suka rako shi. Sai dai shi ya hana su Shiga wai baza su takura mai mata da surutun su ba dolle yasa suka tafi shi kuma ya shige ciki rik'e da gasashiyar kaza da fresh milk.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol