Free chapter · Read without an account
Chapter 9
♠️♠️ *HUSNA KO HUZNA* ♠️♠️
*MALLAKAR*
*Maryam Umar Abdullah (mmn Yusuf)*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*____________________________________*
*Littafin na kudi ne 200 maiso ta turo kudinta ta wannan account number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Account no 1647784887
Account name Access bank
Name Maryam Umar
Ko katin waya ta wannan number 👉🏻***
🅿️ -9
"Saketa Mu'azzam , cewar Mamah cikin d'aure fuska , don tasan inba haka tamashi ba zai iya dukan 'yar mutane daga zuwanshi ,
Kallon Mamah yayi yace Mamah bani abincin zamu tafi tare ne in na saketa zata tafi ta barni ne , jin hakan yasa Mamah sassauta yanayin fuskarta kamun tace yakamata dai ka rink'a Jan 'yan uwanka ajiki ba karink'a hantararsu , kaga dai Kaine baba lallabasu yakamata karinkayi tare da sasu a hanya ,
juyawa tayi ta dauko mashi k'atuwar Kular data had'a masu komai , gefe daya sai kuma kwalin Holondiya dana lemu duk ta d'auko ta kawo gabanshi ,
Kallon Jamil yayi yace kai zo nan , da sauri Jamil ya k'araso yace gani Yaya ,
Yawwa d'auki kayan nan kazo muje Gidan Abba , da sauri Yaya Aliyu ya k'araso yace nima zanje , jin hakan yasa Yaya Mu'azzam juyawa yafara tafiya wanda har yanzu hannunshi na rik'e da hannun Huzna ,
Yaya Aliyu ne da Jamil suka dauko kayan suka biyo bayansu ,
Huzna in ranta yayi Dubu to ya 'baci akan mi zai dinga janta haka kamar wata 'barauniya , shikuwa da gangan yake Jan hannunta da k'arfi don wallahi yau banda Mamah da sai yamata lilis son yakula yarinyar sam batada tarbiya
Turo baki tayi Cikin siririyar muryar ta tace ....."nika sakemun hannu nayi sauri naje na duba kazata , nasan wannan mguwar kazar ta Husna ce taci zalinta to wallahi saina rama mata ,ta yi maganar tana wani murgud'a baki kamar wadda takeyi da ita tana gabanta , daga Yaya Aliyu har Jamil basu San sanda suka fashe da dariya ba , don wannan yarinyar dariya take basu sosai , sukam yanzu ko ba TV basuda matsalar kallon dirama😂 Yaya Aliyu yace nidai na matsu naga wannan Husnar Allah itama kamar kece don inason wannan diramar taki gaskiya naji dadin tafiyar da zamuyi daku ,
Kallon shi ta yi a d'age tace suwa zaku tafi dasu ? Allah ni ba inda zanbiku saidai kuje da Husna, Aikuwa yarinya ko bakiso sai mun tafi dake , murgud'a baki tayi tace wallahi ba inda zani ,
Yaya Mu'azzam dai na jinsu baice komai ba har suka k'arasa inda yayi parking mota , bud'ewa yayi yashiga inda Aliyu ya bude bayan motar ya sanya kayan aciki sannan ya zagayo yashiga gaban motar ,Jamil kuwa bud'e bayan motar yayi ya shiga kamun ya juyo ya kalli Huzna wadda tayi tsaye k'erere takama k'ugu tana girgiza jiki irin na alo tsiya alo danjan nan 😂
Jamal ya kalleta yace to uwar fitsara zo mutafi ko mu barki a nan ,
Wall tayi ta da fararen idanunta kamun ta dubeshi tace dama kunsan gidan ne ?
"Ta ina zamu Sani muda ba zuwa mukeba kawai kishigo muje kina 'bata mana lokaci ,
Wani miskilin murmushi tayi kamun ta kama hanya tafara tafiya hankalinta kwance ,
Duk abunda suke Yaya Mu'azzam na jinsu yayi masu banza , dukda ranshi yafara 'baci ganin tak'i shiga motar don yak'agara yaganshi agidan Abbanshi , ganin ta juya tayi tafiyarta ne yasa shi fitowa da sauri , shan gabanta yayi yace waike wace irin dak'ik'iyar yarinya ce wallahi da badon Mamah tace karna dake ki ba wallahi yau da sai na k'aryamaki wad'an nan shegun kafafun masu kama da kara , oya Don Allah maza kishiga kina 'bata mana time yayi maganar yana zabga mata wata uwar harara ,
Dukda ta tsorata hakan baisata yin abunda yace ba , saima gyara tsayuwarta da ta yi tareda turo dan k'aramun bakinta gaba tace " nifa indai ni zan kaiku tofa saidai kuzo muje a k'afa Donni bazan shiga wannan motar ba , tayi maganar tana hararar motar ,
Daga Yaya Aliyu har Jamil dariya suka sanya Don su harga Allah dariyar diramar yarinyar ke basu ,
Yaya Mu'azzam kuwa runtse idonshi yayi gam yanaji kamar ya shak'e yarinyar Don yakula wannan aljanar yarinyar sam batada tsoro duk yadda ake tsoronshi amma ita ko a jikinta , tabbas badon Mamah tace karya daketa ba wlh yau da baisan Abunda zai mata ba Don ya tsani raini sosai matsalar kawai shine sam baya iya tsallake umurnin mahaifiyarshi wannan kawai yasa zai k'yaleta ,
Janyo hannunta yayi da nufin sanyata mota ta k'arfi , ganin haka yasa tafara k'ok'arin k'watar kanta cikin tsiwa tace wallahi bazan shiga motar nan ba akan wannan motar har wad'an can k'attin ke zagin Abbanah suna cemana k'auyawa itafa wannan mai kama da k'warank'al har cewa Abba tayi wai k'azami tayi maganar kamar zatayi kuka ,
Cak Yaya Mu'azzam ya tsaya yana kallonta tsaf ya fahimci inda zancenta ya nufa tabbas wannan rashin mutuncin nasu Harira ne ,
Kallonta yayi yace suwaye suka cewa Abba k'azami ,? Ganin ya sassauta fuskarshi ne ta gaya mashi duk abunda yafaru
Ranshine ya 'baci sosai amma doli ya danne 'bacin ranshi ya kalleta yace kinga shiga mota muje zan ja masu kunne bazasu sake ba ,
Mak'ale kafada tayi tace bafa zan shiga ba kawai kuzo muje a k'afa Don ni sauri nakeyi zanje naga kazata ,
🤦🏻♀️Dafe kai Yaya Mu'azzam yayi kamun ya kalli su Yaya Aliyu yace ku kwaso kayan nan muje tun kamun na lahanta yarinyar nan ,
Dukkansu danne dariyarsu sukayi ganin yau Yaya Mu'azzam ya had'u da gamonshi ,fitowa sukayi suka fito da Kayan sannan suka kama hanya sai dariya suke ciki-ciki ,
Huzna ce a gaba tana rik'e da wani dan siririn icce tana tafe tana 'yan wak'ok'insu na k'auye yayinda take d'an cilla iccen tana wata rausaya , har sun fara nisa da yake tanajin mugunta sai cewa tayi sai kawai ta saki hanya takama wata hanyar daban , tun suna tafiyar cikin annashuwa har ransu yafara sosuwa ,ganin tafiyar bata k'are bace Yaya Aliyu ne ya dubeta yace ke wai yar rigima har yanzu bamu k'araso bane naga sai tafiya mukeyi ,
Dan marairaice fuska tayi kamar gaske tace wallahi na manta hanyar ne nima naga har yanzu bamu kawo ba 😢
What Yaya Aliyu da jamil suka had'a baki wajan fad'a , Aliyu yace amma lallai yarinyar nan bakida mutunci wallahi , yanzu ak'alla mun shafe minti 30 muna tafiya baki tashi cewa baki gane hanya ba sai yanzu , yanzu ma saida muka tambaya ?
Turo baki ta yi tace to nima ba nagaji ba tun d'azu nake nekan hanyar bangani ba kilama da a mota ne da zan gane wallahi ko zamu koma kawai sai mu shiga motar ,ta yi maganar tana kallon Yaya Mu'azzam,
Tunda tace wai ta manta hanyar ranshi yayi bala'in 'baci ,yanzu kuwa jin wannan rainin wayo nata yasa baisan sanda ya d'aga hannu ya wanka mata mari ba saida taga taurari ,
D'ago kanta ta yi da sauri ta tsura mashi ido , wani irin kallo take mashi wanda shi kanshi saida yasha jinin jikin shi , nan take idon ta yakad'a yayi jajir d'aga hannu ta yi ta nunashi dashi zatayi magana kenan kamar daga Sama sukaji magana a bayansu ,
Kai Mu'azzam lafiya ? Miyakawo nan kuma ina zakuje ? Abba ne ke masu wannan tambayoyin , dawowarshi kenan daga kasuwa tun a nesa yake kallonsu har lokacin da Mu'azzam ya mari Huzna ya gani , mamkinshi shine ina zasuje haka ??
Alhamdulillah Abba tun d'azu muka fito zamuje Gidan ka wannan yarinyar sai yawo take mana da hankali mushiga nan mu fita nan wai sai yanzu kuma zatace wai ta manta hanyar Gidan shinefa tabani haushi na mareta ,
Kamun dai-dai wallahi iskanci ne kawai gaba daya ba hanyar Gidan ta dauko ba doli sai mun koma baya sosai nima yanzu daga kasuwa nake Allah NE yayi zan ganku da bansan iya inda wannan sarkin rashin jin zata kaiku ba , wallahi har narasa yadda zanyi da yaran nan yanzu 'yar uwar ta ma saida na zaneta wai akan kawai na yanka kaza shine tafara mun bore saida na zaneta sannan to wallahi inaga saura ke shashasha kawai ............
😨Kaza , kazarwa aka yanka Abba?? ...kamun ma yabata amsa ta juya aguje ta koma hanyar da suka fito kamun kace mi har ta lashe kwanar ,
( _ko ya akayi ta gane hanyar yanzu oho_😂😂)
Tsaki Abba yayi yace kuyi hakuri kuzo muje haka suka kamo hanyar suka dawo da baya , Abunda yabasu mamaki shine har ta gaban Gidan sukabi suka wuce tun d'azu amma wannan hatsabibiyar yarinyar ta wuce dasu sai saran hanya suke duk sun gaji abunka da wanda bai saba ba , Don Jamil sai tsaki yakeyi tun dazu
Ke lafiya kika shigomun haka kamar wadda aka koro ? Wai kukam yaushe zakuyi hankali ne ko kuma kin janyo mana rigimar ne kamar yadda kuka saba ,
Ko kallon mama Huzna batayi ba sai Allah-Allah take ta k'arasa inda ta d'aure kazarta ,
Ganin wayam ba kaza ba alamarta ne yasa ta d'ago da sauri tafara dube-dube , can idonta ya hango mata robar da aka sanya kajin , jikinsu duk jini alamar dai da gaske an yanka su ,
Cikin wani irin sauti tace "yanzu mama saida kika yankamun kaza , to wallahi sai an tayar da kazar nan ba wanda zaicita tayi maganar tana fashewa da wani irin kuma kamun ta fadi k'asa ta fara shure-shure da kafafu tana fadin it's wallahi sai an tayar mata da kazarta , tsaki kawai mama ta yi taje ta duba ruwan zafinta ,ganin sun tafasa ne yasa ta dauko ta zubama kajin ta shiga figa, sai 'yan wak'e-wak'enta take tana ganin yau lafiya lau suke zasu maida yawu ,
Suna haka Abba ya shigo dasu Mu'azzam ,ko bai tambaya ba yasan kukan da huzna keyi shiyasa ma bai kulata ba ya ajiye kayan sannan ya dauki buta yadan zagaya,
Su Mu'azzam kuwa zubewa sukayi suna gaisa mama yayinda take amsawa cike da farinciki , nan suka fara firar yaushe gamo da mu'azzam batare da sun koma bi takan Huzna ba Don dukkansu ba karamun haunshinta sukeji ba ganin ba wanda ya kulata yasa ta tashi ta koma can kusa da Husna suka tsurama juna ido Baku k'yaftawa ,
Murna sosai mama ta yi da ganin irin garar da aka kawo masu nan fa tashiga godiya dasa albarka, ahaka Abba ya fito shima godiya yayi masu sosai nan yasa aka baza mashi k'atuwar tabarma ya zauna taredasu Mu'azzam din ,abincin Mama ta sanya masu a babban tire da yake Abba yace tare zaici da yaranshi nan fa ta zuba masu hadaddiyar shinkafa da miya wadda taji naman kaji zuk'u-zuk'u , bayan ta kai masu komai ne tazo ta dibawa su Husna ta kai masu tace gashinan in kunga dama kuci kaji ne dai nagaji da zamansu da fitinarku da bata karewa kullum akan kajin.