Free chapter · Read without an account

Page 17

by Rahama muh'md Rufa'i Nalele · FITO NA FITO AKAN SOYAYYA TA

Fito na Fito

AKAN SOYAYYA TA

Labari da tsarawa RAHAMA MUH'MD RUFA'I NALELE

Wattpad @rahamanalele

Haske writer's association


Shafi na 17


Ban yarda wani ko wata ya d'ora min labari na akan shafinsa ba, ban amince ba, duk wanda yamin hakan ya d'ora toko ya d'ora haramun tunda babu amincewata, ina magana ne akan koma waye macece ko Namiji

Ina da hakk'in mallaka na copy right domin haka a kiyaye.




Direct part d'in SafiYYAH tayi, suna ganin juna ReeYAN ta rungumeta tana cewa, "Wallahi SafiYYAH Ya HaYdaR yaji dad'in girkin na jiya, yau me kike ganin zanyi please...


Dariya SafiYAN tayi bayan sun saki juna tace "barka da safiya an tashi lafiya

Dafe goshi ReeYAH tayi da cewa, "Ashe ko gaisawa bamuyi ba Nabi na hauki da zuba, yau nima na d'ana halinki, Lafiya Lau muka tashi da fatan kema haka.

SafiYAH tace "normal, ina ganin yau kiyi mana lafiyayyiyar jalof wacce kike gware basirarki tun a gida kin tuna..

ReeYAH tayi dariya, "tom jolof da Mene, tace "da farfesu Amma taji hanta naga bayan kifi Yana son hanta a fahimtata, tace "tabbas kinyi gaskiya, domin na tuna hakan tun a gida, tace "yauwa na tuna, ki had'a masa lemu koda Kala biyu ne, wallahi Yana so, idan yayi d'adi Kar kiso kiga yanda zaiji daɗin hakan

Tace "Amma Y'ar uwa nifa ba wani iya had'e had'en nan na iya ba, please zaki gwada min ko sau d'aya ne, na Miki alqawari daga Shi zan fara fasaha ta, Amma ina San ki fara gwadamin please.

 Tace "haba ba komai ai, zamu had'a kala biyu Amma kamar yanda kikace gobe da jibi ke dama ko yaushe ke zaki dinga yin abinki..

Dariya ReeYAH tayi da cewa "na yarda wallahi, nayi farin ciki sosai da kike kusa dani cikin rayuwar Aure na..

Tace "Nima haka..

Da haka suka d'an qara tab'a hira kana ReeYAN tayi shashinta Amma kafin ta Shiga sanda ta leqa RaHinAT Suka gaisa 


SafiYAH ma Kan ta kwanta baccinta na fama itama sanda ta leqa RaHinAT d'in, Amma ta fahimci kamar RaHinAT d'in bata ji dad'in zuwan nata ba, saboda yanda tayi mata Sam bata ji dad'in hakan ba




HaYdaR ya yaba duk abin da ReeYAN tamai, yaji dad'i sosai, sannan ya qara saka Mata albarka data basa had'in Kai daran suka fahimci juna, ya sameta a cikakkiyar mace itama yaji qarin qaunarta sosai akan hakan..


Aiko itama tun a daran ya dinga bata kulawa har washe gari, RaHinAT na Lura dasu ta fahimci gaskiya ne maganar SafiYAH ko waccensu zai bata kulawarsa, wannan shine Karo na farko dataji tsanar ReeYAH sosai aranta..


SafiYAH ko ko kusa bata maida hankalinta akan sai ta fahimci lamarin Shi da ReeYAN ba.



Haka a kwana bakwai din ReeYAH Gaskiya ne taji abin da SafiYAH taji, taji qaunar mijin nata over, tayi kuma addu'a akan ALLAH ya basu zaman Lafiya dukkansu da kwanciyar hankali..



Yau ya Shiga d'akin RaHinAT, gaskiya ne ya sameta a cikakkiyar mace itama, Amma fa RaHinAT ba girki, ya fahimci kowa cikin su, SafiYAH tafisu wayewa akan rayuwar aure, itace macen datayi masa ¹⁰⁰ yaji komai yayi masa, Amma ya a jin RaHinAT itace a burnin zuciyarsa, musamman daya kasance da ita daran jiya, gaskiya bazai manta da hakan ba, ya qara Santa da qaunarta sosai, Shi kansa ya kasa gane wacce yafi jinta aransa yanzu, tsakanin RaHinAT d'in da SafiYAN, Shi bayama ta ReeYAH domin ita komai nata a tsakiya yake irin kadaran Kadaham d'in nan..






A haka suka shafe wata uku, Saidai duk da RaHinAT bata qara wani motsin aikata mugunta ba, domin wani shiri da take San aikatawa Amma duk da hakan ReeYAH ta Fara fahimtarta..

SafiYYAH ko sai tayi kamar zata fahimci wani Abu daga garetan sai kuma ta watsar, Sam bata fiya San batama kanta da tunani da tunanin saita fahimci mutane ba, gabaki d'aya tunaninta akan mijinta yake shine Wanda take tsaida tunaninta wajen fahimtarsa

Gaskiya ne ko Shi kansa HaYdaR d'in yasan ba wacce ta fahimcesa kamar SafiYYAN, duk abin da zata mai ta da tabbacin Yana so ko zai soshi, kuma haka abin yake agunsa, wannan yasa yake qara Santa.


Ya fahimci RaHinAT tana da kishi, duk ta fisu kishi, ga shegen wayo, yanzu yanzu saita b'ata maka tunanin ka ta kauce, Yayin da ReeYAH take da wani irin hankali Wanda za'a iya kiransa da wayo, Amma tsantsan yarinta tana wajen SafiYYAH, yace da zuciyarsa duk sun fita wayo, zuciya d'aya take aikata abu Sam bata da wani manufa akai, da abin daya dace ta b'oye da Wanda bai dace ba kawai idan maganarta ta motsa nan take sakin layi..





Yau zai Shiga d'akin SafiYAN, Amma yanzu dai Yana d'akin RaHinAT breakfast yake 

Ta kallesa da cewa, "my love, bana Jin dad'in abin da SafiYAH takeyi, sai ta dinga nunawa kamar kafi Santa fiye da kowa a cikin mu, bazan manta maganar da tayi ba, wai kana jin dad'in ma'amala da ita tafi ReeYAH, shin Nima baka Jin daɗin hakan da ni, kallan ta yayi cike da mamaki, ganin Hakan sai taci gaba da  cewa, kodai nima maganin matan nan Zan Fara sha ne, wallahi duk zancen ya tsaya min arai ne, Bana San wata tafini awajen ka, kuma Dan Allah da gaske baka Samun farin ciki aguna fiye da ita... Takai qarshen zancen cikin damuwa Kamar gaske..

Cikin sauri HaYdaR d'in yace "Sam bamuyi haka da ita ba, ba gaskiya bane, sannan kidena biyema irin wannan zancen, ke ta musamman ce a gareni, ya kamata ki riqe wannan..

Ba haka taso yace ba, Amma sai ta qara cewa, "kasan kowace mace aka gaya mata haka dole hankalinta ya tashi...

  Tashi HaYdaR d'in yayi cikin rashin jin dad'in maganar ta SafiYYAN ya kalli RaHinAT d'in yana d'aukar agogonsa da wayarsa yace "Shin da mijinki zaki yarda ne ko da zancen SafiYYAN, nace ba haka bane miye yasa kike qara maimaita min..

 Tace "kayi hakuri, Nafi yarda dakai akan kowa, Amma miye dalilinta na fad'in hakan bayan tasan qarya ne..

Hanyar fitta ya nufa bayan ya ajiye Mata kud'i Yana cewa, "qila kawai ta fad'i hakan ne dan taji dad'i..

Cikin d'aga murya RaHinAT d'in tace, "kodai ta fad'i hakan ne danta b'ata min rai, domin Kalmar bame dad'i bace, yace "Wannan ne kuma ban sani ba, "kenan tana Jin kishi na ashe b'oyewa take bata Sona...

 Cak HaYdaR ya tsaya Wanda Saura kad'an ya fitta daga falan nata, ya juyo ya kalleta, sai yaga bashi take kallo ba kawai ta zubama abincin gabanta ido ne cikin damuwa, nan zuciyarsa ta Shiga tunani, Amma ya share da cewa, "Ni na tafi, Yana fad'in Mata hakan ya ficce zuwa shashin ReeYAH 

Murmushi ta sake 


Ya samu ReeYAH zaune Kan dinning cikin kwalliya, nan ya qare mata kallo Yana tuna duk cikinsu itace bata da yawan magana, Yana zuwa nan cikin tunaninsa yaji hankalinsa ya qara kwanciya da ita, nan ya sakar Mata murmushi da cewa, "barka da safiya, tace "barka dai honey an tashi lafiya, yace "lafiya Lau Amaryata, nayi latti Zan iya tafiya ko akwai wani Abun da kike buqata, murmushi tayi Mai da girgiza mai kanta, tana cewa "ALLAH ya kaika lafiya ya kuma dawo dakai lafiya..

  Yace "Amin nagode, daga haka ya ajiye mata kud'i sannan ya fitto dayin part din SafiYAH


Tana kitchen domin itakam bazata iya da breakfast d'in RaHinAT ba, Shi yasa ta shigo had'a wani..

 A falon nata ya tsaya Yana cewa "Gud morning luv, da sauqi ta fitto tana "Morning luv an tashi lafiya..

Kallan kwalliyarta yake tayi sosai, yace "lafiya, nayi latti bara naje,

Saurin qarasawa garesa tayi tana me Shan gabansa suka shaqi kamshin turaran juna ta karb'i agogon hannunsa tana cewa, "gaskiya ne kayi latti Amma bazai hanaka saka agogonka ka fitta tsaf ba, bara na saka maka na samu ladan.

Zubama fuskarta ido yayi sanda ta gama saka mai ta d'ago da fuskarta izuwa kallansa lokacin ya d'auke idansa daga kallanta zai fitta ta kama hunnunsa da sauri tana cigaba da cewa, Luv akwai damuwa ne, kallanta yayi da murmushin yaqe dama yasan ko yaya fuskarsa ta canja takan iya ganewa cikin sauri fiye da kawo, "Me kika gani..

Tace "Naga kamar ranka ya d'an b'aci haka, fuskarka ce ta nuna min hakan...

Shafan gefan fuskarta yayi da cewa, "Baby surutu yayi miki yawa, dan Allah badan ni ba, ki rage domin dukkan Ku ina jin dad'in ma'amala daku bake kad'ai bace nake jin ma'amala da ita dukkan Ku ne...

Gabanta ne ya fad'i, tace "me hakan yake nufi ban fahimci....

Saurin katseta yayi wajen saka Mata d'an yatsansa a bakinta alamar tayi shuru, kana yace "bana San naji kince komai, kawai ina San ki canja daga yau Dan Allah Dan Allah badan ni ba..


Sauke ajiyar ZUCIYA tayi da qara shigar da kwayar idanta cikin nasa, tace "shikenan Luv, Koma wane lefi na aikata maka Ka yafemin Dan Allah bazan sake ba, Amma Bana San fuskarka ta canja saboda ni, zanyi yanda kace, Dan Allah Kar kayi fushi dani, Ka b'ata min wannan ranar tawa dakai, Bana San ta Shafi gobe na, domin ina jin dad'i idan naga Ka dawo girki na, ta fad'i hakan cikin sanyi da damuwa..

Sauke ajiyar ZUCIYA yayi da cewa, "Komai ya koma normal yanzu, ina San ki manta, Allah ya baki ikon yin abin da nake so Baby..

Yanzu Zan tafi ina buqatar addu'arki, yakai qarshen zancen da sakin fuskarsa Yana sakar Mata murmushi, itama murmushin ta sakar Mai da cewa, "ALLAH ya dawo Kai lafiya ya baka abin da kake nema sannan yau ina San zanje na ziyarci wannan matar dasu Dady suke bata kulawa wacce nace maka tana da tab'in hankali, na samu labari agun Momy na cewa tana Samun lafiya ina San Ka barni naje na gani da Ido na, yace "Matsalar zanso na kaiki da kaina bansan kije ke kad'a, Saidai yau ina da aiki sosai Dan haka ki bar zuwan kawai, cikin sanyi, tace "Shikenan na fasa..

Kama hannunta yayi, cikin so da qaunarta yace, "kinji babu daɗi akan hakan, A hankali ta d'aga Mai Kai, "zuwa anjima zanyi farin ciki tunda hakan kake so, "shikenan toh Allah ya dawo dake lafiya, Zan miki message na abin da nake San ki girka min, idan banyi ba komai kimin domin nasan zai gamsar dani, tace "yayi luv ALLAH ya dawo dakai lafiya, nagode sosai.

 Kud'i ya bata itama, sanda ko ta sakar mai kiss kana ya fitta..



Yayi mamaki kwarai ganin RaHinAT a farfa jiyan gidan da alama tana San rakasa wajen motarsa ne,

Nan ta sakar Mai murmushi da cewa, "ban tab'a rakoka mota ba, saboda na barma SafiYAH da ReeYAH hakan, duk da nice na basu Idean hakan tun kan muyi Aure, yaudai nace bari na d'ana,

Jerawa sukayi Yana cewa, "kinko kyauta, na kuma nagode sosai..

Tsayawa tayi sanda ya Shiga motar tamai fatan alkairi, yay Mata godiya daga nan suka d'agama junansu hannu me gadi ya bud'e Mai get yayin da ita tayo part din SafiYAH..


SafiYAN Zama tayi Akan d'aya daga cikin kujerun falan nata me cin mutum d'aya, tana tunani da nazarin maganar HaYdaR d'in..

RaHinAT tasaki murmushi ganinta cikin tunani, nan ta dafata tana cewa, "keko tunanin me kike inata sallama baki amsa min ba, tace "wallahi luv ne, ya gayamin wata magana daban gane kanta ba... "Kai haba gayamin naji Allah dai yasa lafiya, tace "cewa yayi wai surutu na yayi yawa, dukkanmu Yana Sammu bani kad'ai bace wacce yake so acikin mu, dana tambayesa meya kawo wannan maganar Bai ban amsa ba, wannan Yana nuna kamar an gaya Mai wani Abu akaina, wanda banji ba ban kuma gani ba..


RaHinAT d'in tace "wai shikenan abin daya Gaya Miki.

"Wai da zancen yafi haka ne?, SafiYYAN ta tambayeta cikin sauri da kallanta..

 Cikin gyara kai RaHinAT d'in tayi murmushi da cewa, "bawai nasan wani Abu bane Akan hakan, kawai dai banga abin damuwa bane Akan hakan d'aya gaya miki, Amma fa ina ganin ReeYAH tasan wani abu, domin daya fitta daga part dina Yana dariya cikin farin ciki muka rabu da juna, Amma daya shiga part d'in ReeYAH ina Lura da fittowarsa Ransa a b'ace ya fitto, da qer ya iya control din kansa dazai shigo part d'inki, Wanda da bai d'an tsaya a kofar ki ya d'an saita nutsuwarsa ba, inaga da Yana shigowa marin ki zaiyi, saboda yanda ya fitto a fusace haushinki nagani a fuskarsa muraran ALLAH ne ya temakeki da baki San me zai faru ba..


Shuru SafiYYAN tayi tana San fad'awa tunani, ganin hakan sai RaHinAT din taci gaba da cewa, Ba mamaki itace ta gaya masa wata magana akan ki mara dad'i haka..


SafiYYAH tace "Anya ReeYAH zata aikata min haka kuwa, domin banyi Mata komai ba, kuma ba wata magana da mukayi da ita wacce zata b'ata masa rai har haka. 

  Tace "tab ai da kinga yanda ya nufo part d'inki da saikin tsorata..

  Shuru SafiYYAN tayi 

Can tace, ba komai ai tunda mun shirya dashi domin yace komai ya wucce, RaHinAT ta cije baki da cewa, "ai haka yace miki, tace "Yes..

Tashi tayi tana cewa, nikam bara naje sai anjima, SafiYAH tabita da kallo tana cewa mu jima lafiya..


Da sauri ReeYAH ta koma shashinta domin dukkan abin da suka tattauna taji komai, saboda itama ta fitto zuwa part din RaHinAT domin karb'ar naqurar busar dakai d'inta data ara, sai kuma ta ganta tayi part d'in SafiYAN hakan yasa tawo part d'in itama, Saidai bata kaiga qarasawa ba qafarta ta gurd'e, nan ta durqushe agun cikin Jin zafi, anan taji karkon maganar tasu zuwa qarshe, lokacin da taji RaHinAT d'in zata fitto hakan yasa tayi hanzarin tashi ta b'uya,..

Ran RaHinAT b'ace tazo ta wucce ta, jin SafiYYAH tace Mata sun shirya ita da HaYdaR wannan yasa ranta mugun b'acin, ita ta d'auka zaizo ya fittan Mata a giya ne, ashe bazai tsinana mata komai ba....


Itako ReeYAH hawaye ne ya zubo Mata, nan ta d'ingisa tayi part ɗinta, bayan ta zauna ne ta fad'a tunanin me yasa RaHinAT ta had'a Mata wannan abu..

Yanzu ya zatayi da SafiYYAH, me zatace Mata, nan tayi shuru cikin tunani..

SafiYYAH ma cikin tunanin take, can dai tatashi ta kintsa kanta, saboda da fittan da zatayi, nan ta kira direba tamai magana Kan ya shirya zai kaita unguwa, daga haka tayo shashin ReeYAN tana Anya kuwa lafiya ReeYAN take bata fitto sun gaisa ba..


Aiko ReeYA najin sallamarta sanda gabanta ya fad'i, a hankali ta d'ago kai ta kalleta, suna haɗa ido hawaye ya zubo mata, SafiYYAH ta qaraso da sauri ta zauna kusa da ita, "me nene ReeYA, me ya faru" cikin damuwa tace "ina cikin damuwa, bansan menzance miki ba.. tace "subhanallah, idan kin tsinci kanki a hali irin wanna cewa zakiyi la'ilaha'illallahul azimul halim, la'ilaha'illallahu rabbul arshil azim, la'ilaha'illallahu rabbul samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil Kareem, ita zakita maimaitawa ina tabbatar miki zaki samu mafitta..

Cikin sauri tahau fad'in hakan, yi take tana qara maimaitawa, SafiYYAH ta zuba Mata ido, cikin tunani iri iri, can ReeYA taji saukar nutsuwa agaretan, tabbas ya kamata ta b'ata Shirin RaHinAT ɗin, nan ta kalli SafiYYAN tace, "Y'ar uwa Ya HaYdaR ne daya shigo d'azu bansan waye ya kirasa a waya ba, ya shigo da farin ciki Amma Yana amsa Kiran da akayi masa a waya naga ransa ya b'aci, bud'ar bakinsa sai cemin yayi wai na rage surutu, dana tambayesa me nayi, Bai ban amsa ba Amma ya qara maimaita min na rage magana, Yana gayamin hakan ya fitta ranshi b'ace, SafiYYAH bansan mena aikata ba..

Wannan yasa tunda ya fitta nake hawaye fisabidillahi SafiYYAH ina da surutu dan Allah..

 Cikin Mamaki SafiYYAN tace "abin mamaki ai nima haka ya gaya min daya shigo, na faɗa tunani sosai akan hakan, bayan fitarsa da RaHinAT tazo shine nake gaya mata, anan take cemin lafiyarsa lau suka rabu ita dashi, Amma itama taga lokacin daya fitto daga part ɗinki ranshi b'ace, Ashe itama batasan ba kece silar hakan ba, to waye ya Kirasa Kenan...

Cikin damuwa ReeYAN tace "Nima tunanin da nake Kenan, Ashe kema yayi miki magana, ikon Allah, akan ni dake kenan akayi masa magana, tunda da yayi ma RaHinAT magana ai da zata gaya miki, dan ina zaune anan naga shigarsa mota kuma itace tamai rakiya..

 Jan numfashi SafiYYAN tayi cewa, "Tabbas in haka ne akan mu biyun aka mai magana, gashi yaqi cewa komai...


Share hawayen ta ReeYAN tayi, tana cewa, "kinga karmu damu da hakan, mu dage da addu'a Allah ya karemu daga sharrin dukkan me sharri...

SafiYYAH tace "shikenan kuwa, Allah ya shige mana gaba, "Amiin ReeYAN tace, daga nan suka canja hira, itama hirar batayi tsawo ba SafiYYAN tama ReeYA sallama akan fittan da zatayi, ta leqa tama RaHinAT sallama har zata tafi, sai kuma ta dawo tana gaya mata yanda sukayi da ReeYAN😂, ta qara da cewa, "Allah sarki RaHinAT har kina zargin ReeYAH, Ashe itama bata da sa'ni akan hakan, ai dama na gaya miki ReeYAH bazata min haka ba, ni bara naje saina dawo. tana fad'in mata hakan bata jirayi cewarta ba ta ficce ganinta tabar direba nata jiranta, aiko tana zuwa shiga motar tayi kawai direban ya jata...



Arewabooks

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.