Free chapter · Read without an account

Part 2

by Amina Abubakar Yandoma · KULLALLIYA

*ƘULLALLIYA!*

[ _Littafin kuɗi N300_]



    Labari/Rubutawa

*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*

[ _Meenat A Yandoma_]




```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` 📚🖊️

     *M.W.A*


 *Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*🥰

***

____________________________

*LITTAFIN ƘULLALLIYA NA KUƊI NE AKAN FARASHE MAI KAMA DA KYAUTA N300 KACAL! ZAKU TURO KUƊIN KU TA WANNAN ACCOUNT ƊIN AISHA ABUBAKAR 2151366600 UBA BANK, KO KUMA KATIN MTN NA 300 TA WANNAN NUBER *** KADA KI BARI AYI WANNAN TAFIYAR BABU KE.*



*PAGE 3️⃣__4️⃣*

...Innalillahi wa'inna ilaihirajiun, Aishatu! Aishatu!"

Inna Yalwa ta ƙarasa maganar tare da bubbuga Aisha dake faman barci abun ta.


Ganin Aisha bata da niyyar farkawa yasa Inna Yalwa zabga mata tafi a gadon baya, a matuƙar gigice Aisha ta buɗe ido.


"Ungo nan Aishatu, yanzu Aishatu dan bani na haifi Uwarki ba shine zaki bari a sabautani, ana neman kasheni ke kuma kina nan kina barcin asara."

Inna Yalwa ta ƙarasa maganar tare dayin tsalle ɗaya ta koma bayan Aisha.


Cike da rashin fahimtar maganar Inna Yalwa Aisha ta diro daga saman gadon ta hau dube_dube amma bata ga komi ba.


"Inna Yalwa babu komi sai dai in firgita kikayi."

Aisha ta ƙarasa maganar tare da zama bisa gefen gadon.


"Ƙarya kike Aishatu! Wayyo ni Yalwa ya zani ga abu yana neman shaƙeni sannan kice mani babu komi, yanzu duk ihun dana kurma kice baki ji ba, ki tattara kayanki cikin daren nan dole ne gobe in ɗauke ki mu nihi zazzau, wannan gida ana tsorata mutane wama ya sani ko shine sanadin daya hana abinda ke cikin ki fitowa, Allah ya kai mu gari ya waye ko Auwalu bai yarda ba dole ki bini mu tafi."

Inna Yalwa ta ƙarasa maganar tare da sanya Fulo ta danne kanta gudun kada ta sake ganin abinda ya tsorata ta.


Shuru Aisha tayi ganin yadda waɗan nan tsoffi ke buga Auwalu tamkar kwallo in wannan ya taro tanan sai wancan ya taro ta nan.


Tunda asuba Auwalu ya shigo ɗakin domin duba lafiyar Aisha, Inna Yalwa ya fara gaidawa tare da tambayar ta ya mai jiki.


"Jiki da Sauƙi ɗan anace, yanzu tunda asuba bazaka barmu mu runtsaba shine zakayi safkon shigo mana ɗaki, to ka buɗe kunnuwanka da kyau Auwalu yau nida Aishatu Zazzau muka nufa kuma ba zaka sake ganinta ba sai ta sauka."

Inna Yalwa ta ƙarasa maganar tare da gyara ɗaurin kallabi.


Wata faɗuwar gaba ce ta ziyarce shi.

"Inna Yalwa dan Allah kada ki fita da Aisha konan da zaure ne, kiji tausayinmu kibar Aisha ta haihu a gidan ta."

Ya ƙarasa maganar kanshi a ƙasa.


"Yo Auwalu miye na duƙar dakai ƙasa, ai kan ka zaka tayar in san ka renani baka ɗaukeni sirikar ka ba, to nidai na gama magana babu wanda ya isa ya canza ta."


Ganin da gaske take bazata yarda ba yasa Auwalu miƙewa jiki ba kwari ya nufi ɗakin mahaifiyarshi.


Bayan sun gaisa yake sanar da ita yau su Aisha zasu Zariya, a gigice Ladiyo ta miƙe.


"Wani irin mummunan zance ne nike ji haka ni Ladiyo! Jikallen nawa ne za'a haifa a Zariya, wannan magana bata taso ba dole a barni da sirikata nan har ta sauka in yaso in Jikana yazo duniya yayi kwari sai aje Zazzau ɗin, kai tashi muje in gana da tsohuwar nan dan dai_dai nike da ita."

Ladiyo ta karasa maganar tare da ficewa daga ɗakin.


Ranar an sha rigima a tsakanin Ladiyo da Yalwa, Auwalu kuwa kamar ya zabga ihu haka ya riƙa ji, Aisha kam baiwar Allah ga Tsohun ciki daya gawurta bai zo duniya ba ga kuma rigimar wannan tsoffi kuka ta rikayi tana ƙara tausaya ma mijinta.


Ladiyo da maƙoshinta ya bushe goro taje ta ɗauko masu ita da yalwa suka hau ci kuma hira, da dai Auwalu yaga sun sauki sulalewa yayi yabar gidan.


Ganin Inna Yalwa ta amince ba zata tafi da zazzau ba nan fa suka ƙulle da Ladiyo suka hau maida yadda akai.


"Ni ko Ladiyo tunda kika zo garin nan yaran nan sun barki kin fita kinga gari kin san ance zama wuri ɗaya tsautsayi."

Inna Yalwa ta jefama Ladiyo tambayar.


"Wa! Ai kullum ina kulle cikin gidan nan nida su babu inda nike fita, amma yau tunda gaki ƴar Uwa ya kamata mu fita muga gari."

Ladiyo ta faɗa.


"Yanzu kinga rana ta fara mu bari ayi la'asar tukun, Aisha kema ki shirya sai mu fice tare mai ciki anfiso tana fita tana wasa ƙafarta."

Jin abinda Inna Yalwa ta faɗa sai da gaban Aisha ya faɗi domin yau sam bata jin daɗi, tun ɗazu takeji abinda ke cikin ta yana motsi, ji take tamkar ana cizon ta ga abinci da taci zai zurare taji tamkar bataci komi ba.


Mai aiki na gama abincin rana Aisha ta zubama su Inna Yalwa a tare tunda taga yau ƴan mutumcin suke ji kafin su fara halin nasu.


Tamkar masu shirin zuwa unguwa haka suka shirya suna fitowa harabar gidan driver ya taso da sauri domin a tunanin shi unguwa zasu amma sai yaji abinda ya kusa sashi fashewa da dariya amma babu dama.


Da kyar Aisha ke jefa ƙafa domin tun fitowar su kasancewar Unguwace ta masu hannu da Shuni babu wata hayaniya sai kukan karunuka.


"Yalwa kinji wani iskan ƴanci dana shaƙa, kai yawo yayi Yalwa."

Ladiyo dake gaba ita da Yalwa ta karasa maganar.


"Ai ni naga laifinki, ace tunda kika zo gidan nan baki fito yawon miƙe ƙafa ba ina dalili kamar dai kina gidan kurkuku."

Inna Yalwa ta faɗa.


"Ai kam nima na koya daga yanzu sai mu riƙa fitowa nida ke tunda kin fini sanin gari, yo ina amfanin zama wuri ɗaya."

Inna ladiyo ta karasa maganar tare da shigewa wata doguwar hanya.


Ganin zasu bar Area ɗin unguwar yasa Aisha buɗe baki da kyar ta fara magana.

"Inna dan Allah mu koma gida kada mu bace domin koni dana shekara ban taba zuwa wurin nan ba."

Aisha ta karasa maganar tare da cije lips domin ji take mararta ta ƙulle ga wani azababben ciwo da take mata.


"La'ilaha illallahu, Muhammadu ɗan Abdullahi! Aishatu muda muke tsohon jini har mu fiki dauriya da ƙarfin hali, kai yaran zamani kun lalace da shegen son jiki "

Inna Yalwa ta ƙarasa maganar tana riƙe ha6a.


 "Yalwa ki taho muje, dan ni yadda naji daɗin yawon nan ko tsayawa bani so munayi."

Ladiyo ta karasa maganar tana mai kamo hannun Inna Yalwa.


Aisha mace ce mai kawaici da kauda kai Uwa Uba ga hakuri, dan haka duk ciwon dake cinta kasa magana tayi domin tasan yau kam sai ta Allah tunda har suka fito.


Wata babbar santan suka karaso inda wata mabaraciya ke zaune da ƴar robar bararta tana bara.


Tunda suka shawo kwanar Aisha ta buɗe jikka ta ciro kuɗi tana jira su ƙarasa ta miƙama Mabaraciyar, a cikin robar barar Aisha ta saka mata kuɗin, ɗago kanda mabaraciyar zatayi suka haɗa ido da Aisha, ji tayi cikin ta ya murɗa lokaci ɗaya, ba shiri ta dafe cikin ta tare da ambatar sunan Allah.


Cira kafa Aisha tayi tare da bin bayan su Inna Yalwa da har sun tsallaka titin, hawaye mabaraciyar ta share tare da bin bayan Aisha domin ta sanar da ita wani abu da ta hango yana gaf da faruwa da ita wanda ya kasance wata ƘULLALLIYA CE mai wuyar warwaruwa , da gudu mabaraciyar ta bi bayan Aisha da itama har ta tsallake titin.


Ƙuuuw! Ita ce ƙarar data yima kunnen jama'ar wurin dirar mikiya, a gigice kowa ya maido hankalinshi ga Matar da tazo tsallake titi wata mota da ta taho a guje tamkar walƙiya tabi ta samanta ta wuce.


A gigice jama'ar wurin suka yo kan Mabaraciyar dake yashe a ƙasa rai yayi halinshi, nan fa jama'ar wurin hankalin su ya dugunzuma domin sun ga Lokacin da matar ke tsallake titi babu motoci to daga ina wannan motar ta fito?


Jami'an tsaro suka kira domin Accident ɗin ya haɗa da mutuwa, Inna Yalwa da Ladiyo kuwa ido ne ya raina fata domin yau ne rana ta farko da akayi banka a gaban idanunsu kuma har aka rasa rai.


Aisha Kuwa wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta domin yanzu taba matar sadaka kuma ace itace mota ta bige, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.


 "Munga idi Yalwa, kizo mu tattara ƙafafunmu mu shiga mota mu koma gida tun kafin muma a samu wata mota tayi awon gaba damu duk ta ragargajemu anan."

Inna Ladiyo ta karasa maganar a tsorace.


"Muna zaman mu lafiya rabon mu fito muyi mugun gani ya fiddo mu, Ladiyo wata gudawa nike ji ƙafafuwana da ƙyar suke ɗauka ta, Aishatu dan iyayenki ki taho mu wuce gida."

Inna Yalwa ta karasa maganar jiki na ciri.


Tamkar butum-butumi haka su Yalwa suka ja Aisha suka ɗauki hanyar gida, sun sha tafiya ba kaɗan ba amma babu abun hawa ko machine basu ga ya giftaba bare kuma mota.


"Yawo, yawo bai yi ba, Auwalu kana ina gamu nan a titi munata Gantalewa Allah ka taimake mu gano hanyar gida."

Inna Ladingo ta karasa maganar tana gugu_gudu.


Wasa_wasa sai ga magriba ta ƙarato amma babu mai abun hawa bare susa ran zasu isa gida kafin dare.


Aisha kam ta galabaita ba kadan ba, babban abinda ke ƙara tayar mata da hankali shine wani baƙin hadari da kallo ɗaya zakai mashi gaban ka ya fadi ne yayi ma sararin samaniya rumfa, wani iska ne ya fara kaɗawa alamun ruwa na gaf da sauka.



Kuka Aisha ta fara tana tunanin mijinta da irin baƙar wahalar dasu Inna suka bata.


Wata walkiyace aka haska saboda tsananin haskenta tilas mutum ya rufe idonshi, babban abinda keba su Yalwa mamaki shine yadda mutane keta gudanar da hidindimonsu cikin lubana tamkar basu ganin wannan hadari


 "Ladiyo! Ladiyo inaga tashin ƙiyama ne yazo kinga wata walkiya da aka falla."

Inna Yalwa ta faɗa.


"Yalwa a kiɗime nike domin ni kunnuwa na sun fara jiyo kamar sautin ƙahon nan da akace za'a hura a ƙarshen duniya, Allah dai yasa ba tashin duniya bane ya riskemu a waje a gantale."


Wata bakar mota ce ta yi parking gaban su.

"Ku shigo!"

Suka ji an faɗa daga cikin motar.


"Yawwa Allah mungode, ga Auwalu nan yazo jama'a ku shigo mu wuce nidai na shige."

Inna Ladiyo ta fada tare da shigewa Motar.


Basu da yadda zasu yi haka suka fada cikin motar sai dai ji sukayi anja motar da mugun gudu.


"Auwalu buɗe mani gilashin motar nan insha iska naga an fara sheka ruwan sama."


Shuru direban yayi tamjar bai ji mi aka ce ba,

"Auwalu dan iyayenka ka buɗe mani gilashin nan ko sai na sulalo da hannu na na lafta maka mari tukun."

Inna Ladiyo ta faɗa.


"Wa zaki mara? Tsohuwa shiga taitayinki, arzikin mai daraja kukaci Umarni aka bani in ɗauki mai daraja kada ruwan sama ya doketa, badan haka ba tsohuwa barinki zanyi ruwan nan yayi maki shegen duka."

Mutumin ya karasa maganar ba tare daya juyo ba.


"Mun shiga ukku mun shigo motar Aljanu."

Su Ladiyo suka fara ihu.


"Ku haɗiye kukan ku ko kuma bakunan ku su koma saman ƙeya."

Mai tuka motar ya fada ba tare daya kalle su ba.


"Salamun ƙaulin min rabbi rahim, Ladiyo haɗiye kukan ki nidai na haɗiye nawa."

Inna Yalwa ta faɗa tana mai sanya hannuwan ta tana toshe baki.


Aisha kuwa addu'a kawai take domin tun tsayuwar motar taji cikin ta ya katsa.


Tsayawar da motar zatayi su Inna Yelwa duk watso su aka banda Aisha da aka buɗema mota ta fito.


A guje suka faɗa gidan suna salati da sallallami.


Auwalu kuwa da tun da jimawa ya dawo gida bai gansu ba ya shiga tashin hankali, ganin sun shigo afujajan yasa shi miƙewa da sauri.


"Ina kuka je, Inna Yalwa hada Aisha da tsohon cikin nan haka kika fita."



"Kai ar! Yau mune da shiga motar Aljanu."

Nan suka kwashe kaf abinda ya faru suka sanar dashi.


Kasa kwakkwaran motsi yayi tausayin Aisha ya kama shi tabbas Aisha mace ta gari ce mai matuƙar biyayya.


Ranar Inna Yalwa da Ladiyo da yake mutumci suke ji ranar a ɗaki ɗaya suka kwana.


Aisha da mijinta suma suna ɗakin su, sam Auwalu ya kasa bacci musamman da yaga Aisha tayi bacci, kallon ta yake yana jin ƙaunarta na ratsa jinin jikinshi.


Tana cikin barci taji muryar Jariri na magana.

"Umma ki farka yau zani iso duniya."

Firgigit! Aisha ta miƙe lokaci daya ciwon baya da mara yayi mata dirar mikiya, Duk irin ƙarfin hali da dauriya irin na Aisha sai da ta ƙwalla wata mahaukaciyar ƙara data yi sanadin farkawar su Inna Yalwa daga barcin da suke, a gigice suka nuho ɗakin Aisha...........








*MEEN@RT.........✍🏻*

***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol