Free chapter · Read without an account

3

by Hauwa A Usman · SAKI RESHE..

SAKI RESHE...!*_

*(CIGABAN GADAR ZARE)*


*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_


_Masu buk'atar complete littafin *SAKI RESHE...!* zasu biya 300 ta account number Hauwa Auwal Usman GT Bank 0153259310 idan aka turo kud'in sai ayi screenshot (shaidar biya alert sms) a turo ta WhatsApp number ***, ko a turo katin waya na 300 ta WhatsApp number *** banda kira please WhatsApp chart kawai_


Free page


3️⃣


A kid'ime Ya Mu'allim ya d'auki Ammar da nufin kaishi asibiti, yana gaf da isa motarshi ya jiyo muryar Hajiya Tanya na cewa, 

" dawo dashi annamimi bak'in munafuki, gidan uban wa zaka kaishi? 


Tsohon banza tsohon wofi, yadda ka raba ni da ubanshi haka zaka raba ni dashi shima? 


"To yanzu babu Yaseer daka shanye ka mayar dashi lusari sai abinda kace mishi yake yi, 

Hajiya Tanya macece me kamar maza ce gidan, ita ke da iko akan kowa da komai na gidan, 

sai abinda tace za'ayi dan haka dawo dashi asararran banza, a haka sumi-sumi dakai kamar na Allah, 

kana Malami dakai amma baka amfani da Malantarka babu abinda ka sani sai bak'in munafurci, makirci da annamimanci, 

sai bin gidan mutune kana tsegumi kana raba aure, shege sai fama da uban rawani kana yawan bin gidajen TV da radio kana Allah yace Annabi yace, 

kana bin masallatai k'asa-k'asa kana abar kaza babu kyau, ayi kaza, 

idan kana wa'azi ko hud'uba kamar kayi zamani da Annabi, har Hajiya Tanya ta gama tijararta Ya Mu'allim baice mata ko kanzil ba, 

illa ido daya kafe ta dashi, sai da yaji tayi shiru kana yace " duk zagi da cin mutuncin da zakiyi min kiyi bakomai, 

amma dan Allah ki bari a ceci rayuwar yaron nan, ki barni na kaishi asibiti, salati Hajiya Tanya ta saki tana tafa hannu tace " oh! ni yau naga munafurci k'iri-k'iri ashe haka ka iya makirci Iro? 


"Ah! lalle ba mamaki danka shanye Yaseer irin wannan tugga haka kamar mace, to bari kaji kurwata kur nafi k'arfinka, 

ni Tanya sunana ba Yaseer ba, naci dubu sai ceto, dan haka ka aje shi nan inda kazo ka same shi tun kafin na tara maka jama'a, 

hawaye na zubowa saman kuncin Ya Mu'allim yace " dan girman Allah ki bari a cece bawan Allah nan, 

" kowa ma ai bawan Allah ne, ko akwai bawanka cikin mutane? 


"Muma nan duk bayin Allah ne ba bawan k'aton banza ba, " Tanya ki bari na kaishi asibiti kar yaron nan ya mutu, 

" halan ka manta kune masu cewa rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke, shike rayawa shike kashewa? 


A sanyaye yace " haka ne, "to kuma tunda kasan haka ne ka barshi Allah zai raya shi, idan kuma ya mutu kwananshi ne ya k'are, 

wata k'illa ma a rage mugun iri, ta fad'a idonta tar cikin na Ya Mu'allim, zayyi magana tayi saurin cewa " ka fita Iro dan akwai d'an saurin mutuncinka daya rage a ido na, 

bana san abun ya kai mu ga dambe dan bazan ji kunyar tub'ewa zindir nayi dambe dakai ba, 

ganin bai motsa daga inda yake tsaye ba, yasa ta cewa " kana ganin kamar k'arya nake bazan iya ba ko? 


K'ara rungume Ammar yayi yana cewa " please Tanya, " bari dai ka gani danna lura abun sayya kaimu ga dambe, 

ta fad'a tana cin d'ammara da d'ankwallinta while tana nufarshi gadan-gadan, ganin yadda ta nufoshi yasa Ya Mu'allim kwantar da Ammar a k'asa, 

had'i juyawa ya shiga motarshi yaja ya fita, direct hanyar Zamfara ya nufa bai biya ko'ina ba, har ya isa Zamfara yana matse hawaye, 

dan gani yake tamkar Ammar ya riga ya mutu an gama, daya isa gida bai sanarwa Saratu inda yaje ba, balle ya fad'a mata abinda ya faru gudun kar itama ta shiga damuwa, 

Tanya ko shigewarta gida tayi tabar Ammar nan inda Ya Mu'allim ya barshi, 

Madu na ganin ta shige gidan ya fito da gudu ya d'auki Ammar ya kaiwa Hajara matarshi, 

yace " fito maza ki kaishi asibiti karki bari a kwantar daku, idan likita ya duba ku ya rubuta magunguna ki dawo, 

sai naje na siyo masa maganin, ya fad'a yana nufar inda ya yaje kud'in da Ya Mu'allim ya bashi, dan bai tab'a su ba sai yau, ya zari duba goma ya mik'awa Hajara yace " karki dad'e kiyi maza ki kaishi ki dawo, 

mik'ewa NASHWAN yayi d'an Madu da Hajara wanda sa'anni ne da Ammar, yace " dani za'a tafi? 


"A'a muna tare dakai kaji, Madu ya fad'a yana kwantar dashi, kasancewar Nashwan me hak'uri ne yasa yayi lamo, 

jikinta na rawa ta sab'a Ammar a baya ta goya ta zumbula hijabi ta fice, har sha biyun dare Hajara bata dawo ba, 

tsoro ya kama Madu duk bayan minti d'aya sayya lek'a get, gata bata da waya balle ya kira ta, 

Hajara kuwa asibitin kud'i takai Ammar, bayan Doctor ya duba shi yace " dole sai an kwatar dasu, 

hankalin Hajara a tashe tayiwa likitan bayanin komai, ya fahimce ta amma duk da haka yace sai an k'ara mishi ruwa dole, 

badan taso ba ta hak'ura aka saka mishi k'arin ruwa leda biyu aka k'arawa Ammar, 

kana ya farfad'o, likita ya rubuta musu maganguna ya basu, gaf da asuba Hajara ta dawo gidan, cikin ikon Allah ko sau d'aya Hajiya Tanya bata lek'o ba,

bare tabi takan Ammar, jikin Madu na rawa ya tare su, suka shige BQ Hajara tayi mishi bayanin yadda sukayi da likita, 

Madu ya sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " dole na sai miki waya saboda irin haka, 

zatayi magana Ammar ya farka daga bacci, da sauri Hajara ta d'auke shi, Madu ya shiga kitchen d'in su ya d'auko mishi abinci, 

hannu bibbiyu Ammar ya rink'a cin abinci da gani yana jin matsananciyar yunwa, sai da cinye abincin tas!, 

kana yace " ruwa! da sauri Madu ya fasa pure water ya bashi, sai da yasha kusan rabi sannan ya kauda kanshi gefe, 

yace " bacci zanyi, kusa da Nashwan Hajara ta kwantar dashi, bai jima ba bacci ya d'auke shi, 

Hajara da Madu suka sauke ajiyar zuciya a tare suna bin Ammar da Nashwan da kallo batare da sunce komai ba, 

washe gari Madu ya kira Ya Mu'allim ya sanar dashi dan hankalinshi ya kwanta, 

sosai Ya Mu'allim yayi mishi godiya, ya kuma samu nutsuwa.


Washe gari da safe bayan Ammar ya karya Hajara tayi musu wanka shi da Nashwan, ta shirya su tsaf kana ta rik'e hannun Ammar suka shiga gidan, 

Tanya na zaune a parlour tana busa hayak'in sigari sama, yayinda Nayan ke zauna kusa da ita yana cin fruit, 

a d'arare Ammar ya shiga ya zauna k'asa saman tiles, ya rakub'e yana bin kwanan da Nayan ke shan fruits da kallo, 

mangari Hajiya Tanya ta kai mishi da k'afa ta hanakad'e shi, tana cewa " shege me mugun hali wanda ya gaji mugun abu wajen uwa da uba, kazo ka tsare ni da ido baka iya gaisuwa bane dan ubanka? 


"D'an iska ba, ji yadda ya tsare ni da ido, kamar tsohon maye ni karma ya sani na kware, Nayan ya fad'a had'i da kwad'a mishi kwano aka, 

" dalla tashi ka bani waje jarababbe, a tsorace Ammar ya mik'e ya nufi bedroom d'inshi, Hajiya Tanya ta daka mishi gigitacciyar tsawar data razanar dashi da Leenah, 

suka saka kuka a tare, " gidan ubanka zaka je dakayi nan? 


Cikin kuka yace " d'aki na zani, " bani da wajen ajeka a cikin nan, dan babu spare room ka kwashe kayanka ka koma Boys Quarter, 

kallanta ta mayar k'ofar kitchen had'i kiran Hajara "ke!, dan haka take ce mata da wuya ta fad'i sunanta, 

Haraja da duk abinda ake tana ji, ta fito da sauri ta zube gaban Tanya, tace " Hajiya gani, sai da ta d'auki lokaci kafin tace " d'auko buhu ki shiga d'akin can ki kwaso kayan Ammar, 

ki tafi can wajenki BQ ya zauna acan, sosai Hajara taji dad'in hakan dan sun samu damar kula da Ammar yadda ya kamata, 

batare da b'ata lokaci ba Hajara tayi kamar yadda aka umarce ta, ta kama hannun Ammar suka fita, 

bayan ta kai Ammar ta shirya mishi kayanshi kusa dana Nashwan sannan taje bakin get yayiwa Madu bayani, 

shima yayi farin ciki sosai jin Ammar ya dawo hannunsu, " ki koma kada ta neme ki, 

bari na kira Ya Mu'allim na sanar dashi, ya fad'a yana ciro wayarshi daga aljihu, Hajara ta shige gidan, 

bugu d'aya Ya Mu'allim ya d'aga wayar dan yasan akwai wani abu, bayan Madu yayi mishi bayanin komai Ya Mu'allim ya sauke numfashi,

yace " dan Allah ku dubi girman Allah ku rik'e Ammar bisa gaskiya da amana, tunda kukaga Allah yayi haka, 

akwai manufarshi tayi hakan, dan Allah ku tausayawa yaran nan, bashi da kowa a duniya daya wuce ni da ku, 

a sanyaye Madu yace " karka damu in sha Allah zamuyi mishi fiye da abinda zamuyiwa d'an mu, 

Ya Mu'allim yace " nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, in sha Allah duk wata zan rink'a zuwa ina duba shi, 

ina kawo muku kayan abinci, da abubuwan buk'ata, amma ka finnan zan zo a cikin satin nan, ka rubuto min abinda baku dashi sai na taho muku dashi, 

" bama buk'atar komai Ya Mu'allim, Allah ya kawo ka lafiya, Ya Mu'allim ya amsa da "amin ya Allah, 

bayan kwana uku Ya Mu'allim da Saratu suka shirin zuwa Kano, sai da suka biya kasuwa sukayi siyayyar kayan abinci komai da komai, nama, kifi kaji, kayan sawa, da kayan gida, irinsu Tv, dvd, katifa, bargo, pillows, kayan sawa, kayan sanyi da phones, 

kana suka nufo gidan, wannan karon bayyi gigin shiga da motarshi cikin gidan ba, saboda tsoron abinda zai biyo baya, 

sukayi sa'a har aka gama sauke kayan kaf suka shigar dasu BQ babu wanda ya gansu, Ya Mu'allim yana rungume da Ammar, 

ya mik'awa Madu sababbin wayoyin daya soyo musu shida Hajara, ya mik'a musu ya had'a da 100k, 

Madu nata godiya, while Hajara na biye dasu, ganin Ya Mu'allim na shirin tafiya yasa Ammar fashewa da matsanancin kuka, 

yana cewa " sai na bika, dan Allah ka tafi da ni, d'aga kan da Ya Mu'allim zayyi idonshi ya sauka kan Hajiya Tanya, 

bakinta d'auke da karan sigari tana busa hayak'in sama kanta babu ko d'ankwalli ta nufo shi, gaf dashi tazo ta tsaya, 

ta zuk'i sigarin ta busa masa hayak'in a fuska, murmushi Ya Mu'allim yayi had'i da ja baya, yace " ina wuni? 


"Da ban wuni ba ka ganni tsohon makiri?


" Wato baka ji abinda na fad'a maka ba ko? 


Ta fad'a tana k'ara busa masa hayak'in sigarin, zayyi magana tace " fita daga gidan nan tunda ba gidan tsohonka bane, 

fuskarshi d'auke da murmushi yace " hala kin manta nan gidan Ammar ne ba gidanki bane ba, shewa Hajiya Tanya ta saka had'i da tafa hannu tace " ikon najabu tsoho yak'i fad'ar Allah, 

kai ka san haka uban kinibibi, hala kaima ka manta kai da k'afa duk mallakin wuya ne? 


"Ka manta cewar Yaseer da Sumayya basa raye, kuma koda suna rayen ma me akayi? 


"Me jiya tayi ballantana yau? 


Tayi maganar kamar zata bangaje Ya Mu'allim, baya ya kuma ja fuskarshi d'auke da murmushi yace " ko kink'i ko kin so nan gidan Ammar ne saboda gidan Sumayya ne dan haka har abada ba'a canjawa tuna suna, 

" me ubanshi da uwarshi ma sukayi balle wannan d'an k'aramin alhakin? 


Ta fad'a tana nuna Ammar, ta cigaba da cewa " ko kana tunanin kokawar da manyan maza da mata suka kasa wannan abun zai iya yinta? 


Ta k'arasa maganar tana zubawa Ammar rankwashi a ka, kuka Ammar ya sanya had'i da sanya hannu yana shafa kanshi, 

ta watsa mishi uwar harara tace " maida kukan nan ka had'iye shi tun kafin na hau ruwan cikinka nayi lugude, 

tsit yayi cike da tsoro, ta mayar da kallanta kan Ya Mu'allim tace " kaga tun muna shaida juna dakai ka fita daga gidan nan, 

kuma karka k'ara gigin zuwa har abada, ido ya zubawa Tanya yana yi mata kallan tsanaki, 

yace " kiji tsoron Allah Tanya, ki dubi zaman mutunci da amanar da kikayi da iyayen yaron nan, 

ki tuna irin alkhairan da suka yi miki a rayuwa, hannu ta d'aga mishi had'i da cewa " kai ka san wannan, 

zayyi magana tayi saurin cewa " zaka fita ko bazaka fita ba? 


"Zan fita yace yana juyawa, Ammar ya fasa gigitaccen kuka had'i da k'ank'ame shi yana cewa " dan Allah ka tafi dani,

Hajiya Tanya ta kalli Ammar kana ta mayar da kallanta ga Ya Mu'allim tace " idan baka so na b'ata maka suna, 

na zubar maka da mutunci a idon duniya na k'ulla maka bak'in sharri ka fita, 

idan ba haka ba wallahi yanzu zan tara maka mutane nayi maka mummunan kaidi, ta fad'a tana huci had'i da take mishi k'afa, 

jiki a sanyaye ya saki hannun Ammar had'i da nufar get zai fita, ta d'aga murya tace " kuma daga yau duk ranar daka k'ara zuwa gidan nan sai nayi maka sharri, 

ya jita sarai amma bai ko juyo ba, while Ammar na kwala mishi kira "Baba Malam! Baba Malam, 

cikin zafin rai Tanya ta damk'o Ammar ta shiga dukanshi hannu da k'afa yadda kasan ta samu garjejen k'ato, 

tana surfa mishi ashar, bata daina dukanshi ba sai da taga baya motsi kana ta tsallake ta barshi nan, 

Madu da Hajara suna ganin ta shige sukayi saurin nufarshi, dukkansu suna zubar da hawayen tausayi, ruwa Hajara ta d'umama ta gasa mishi jikinshi, 

ta bashi abinci ya ci kana ta bashi magani, bai dad'e ba bacci ya kwashe shi,

washe gari Monday da wuri Hajara ta shirya dan tafiya makaranta, tare suka fita tana rik'e da hannunshi, ta kaishi jikin motar da aka saba kaisu makaranta, 

tace " ka tsaya anan idan Nayan ya fito driver ya kai ku, cikin sanyi ya amsa mata da to, 

Hajara na k'ok'arin shiga gidan dan fara aiki Hajiya Tanya ta fito rik'e da jakar makarantar Nayan da lunch box d'inshi, 

tana lallab'a shi kamar kwai, yayinda shi kuma yake kukan shagwab'ar bazaije makaranta ba, dakyar ta saka shi a mota, Ammar na k'ok'arin shiga motar ta finciko shi tayi wurgi dashi gefe, tana huci tace " gidan ubanka zaka? 


"Ma... Makaranta zani, ya fad'a muryarshi na rawa cike da tsoro, " badai a wannan motar ba, 

dan ta zama ta d'a na shi kad'ai, idan zaka karci k'asa gwara ma tun wuri dab'a, idan kuma bazaka ba, 

dama karatu bai dace dakai ba, kallanta ta mayar ga driver had'i da watsa mishi uwar harara, tace " kai kuma tsayuwar uban me kake yi da bazaka shiga ka kaishi ba? 


Jiki na rawa driver ya shiga motar ya ja, batare databi takan Ammar ba tayi shigewarta gida, 

da gudu Madu ya d'auki Ammar yayi waje, yaci sa'a yana fita ya had'u da Bala me adai-daita sahu, 

Bala mak'ocin Madu ne a tsohuwar unguwarsu kafin ya dawo BQ, da sauri Madu ya tsayar da Bala, bayan sun gama gaisawa Madu yace " dan Allah wannan yaron nake san ka rink'a kaiwa makaranta kullum kana d'auko shi, 

cikin fara'a Bala yace " ba damuwa, k'arfe nawa suke tafiya, k'arfe nawa suke tashi? 


"Ka rink'a zuwa k'arfe bakwai na safe kana d'aukarshi, ka rink'a d'auko shi sha biyu na rana, 

" to in sha Allah zan rink'a zuwa, Madu yace " me za'a rink'a baka a wata? 


"Ka bada kawai ba damuwa, d'an shiru Madu yayi kafin yace " dubi ashirin yayi? 


"Ido Madu ya zaro a d'an tsorace yace " dubu ashirin fa kace? 


"Eh ko yayi kad'an ne, cike da mamaki Bala yace " nan nan ne fa makarantarta su ba nisa, Madu yace " ba damuwa za'a baka hakan amma dan Allah ka rink'a kula dashi, bakin Bala a washe yace " karka damu, Madu yace " yanzu ba kud'i a hannu na amma idan ka dawo dashi zan baka na wata ka rik'e a hannunka, 

cikin jin dad'i Bala yace " madalla nagode sosai, haka kuwa akayi bayan Bala ya d'auko Ammar Madu ya cike masa dubu ashirin ya bashi, tun daga ranar Bala ya zama me kai Ammar makaranta, cikin aminci da amana, 

yana bashi kulawa sosai kamar d'anshi, dan wani lokacin idan Ammar yaga abu yana so a aljihunshi yake siya mishi, 

har ma ya basa duk lokacin dayakai Ammar makaranta sayya bashi naira ashirin, haka daga b'angaren Ya Mu'allim ya d'auke musu komai, duk wata dubu d'ari yake bawa Madu ya rik'e a hannunshi, 

saboda buk'atun Ammar, har fridge da cooker gas ya sai musu, haka duk watan duniya sayya zo ganin Ammar,

sai dai ba gidan yake zuwa ba makaranta yake zuwa ganinshi, tun daga ranar da Hajiya Tanya tace zatayi mishi sharri bai k'ara zuwa gidan ba, 

a makarantar su Ammar kuwa kunya ce ta hana su korar Ammar saboda rashin biyan school fees, 

suna jin kunyar korarshi ne saboda haliccin mahaifinshin Yaseer dan ya taimakawa makarantar sosai, 

saboda ya d'auki nauyin d'alibai sama da 20 yana biya musu kud'in maranta, dama su kansu Malaman suna shan alkhairi daga wajenshi, 

ganin shekara guda ta wuce cur ba'a biyawa Ammar kud'in makaranta ba, yasa suka sallameshi, 

shugaban makarantar da kanshi ya fad'awa Ammar cewa idan yaje gidan ya fad'a azo a biya mishi kud'in makaranta, 

idan ba'a biya mishi ba karya k'ara zuwa, a harabar gidan ya iske Hajiya Tanya, tana shirin mota, 

da sauri ya k'asa inda take, cike da tsoro yace " a makaranta ance karna k'ara zuwa idan ba'a biya min kud'in makaranta ba, 

tana kallanshi shek'ek'e tace " yanzu da kazo ka gaya min uban me kake so nayi maka? 


Abinka da k'uciya yace " biya min zakiyi, a hasale ta kifa mishi mari had'i da hankad'e shi tace " da kud'in ubanka zan biya maka makarantar? 


" Ka bud'e kunnenka dakyau kaji ni, bani da kud'in da zan iya biya maka kud'in makaranta, 

kona d'auki nauyinka, idan kaga dama kana iya shiga duniya, tayi mafanar tana murd'e mishi kunne da k'arfi, 

had'i da kwara kanshi da bango, harta shiga mota ta fito, ta kwalawa su, Madu da Iro me wanki da guga da Idi me bawa flowers da sharar harabar gidan kira, 

jikinsu na rawa suka zube gabanta, ta kalle su cike da k'ank'ami kamar taga kashi, kana ta mayar da kallanta ga Ammar tace " dama baka dace ka karatu ba, 

dan haka daga yau ka shiga cikinsu ku rink'a aiki tare, ta kalli Idi tace " daga yau duk wanda zayyi aiki cikinku ya tabbatar tare yayi dashi,

suka amsa da to, haka aikin cikin gida tare zaku rink'a yi da Hajara, wanke-wanke da gyaran d'akin na dana Nashwan da wankin band'aki ya dawo kanka daga yau, 

jin bai amsa ba yasata daka mishi tsawa " ko baka ji abinda nace ba?


Ba Ammar ba har su Madu sai da jikinsu ya d'auki rawa saboda tsoro, muryarshi na rawa yace " naji, 

bata k'ara bi ta kanshi ba ta shige mota fuce abinta, a fili su Idi suka sauke ajiyar zuciya, Madu ya kalle su a kasalance, 

yace " kudubi girman Allah kada ku azabtar da d'an marayan Allah, ku tuna irin alkhairan da iyayenshi suka yi muku, 

Idi da Iro suka had'a baki wajen cewa " haba Madu kana tunanin zamu iya cutar da Ammar? 


" A'a kawai na fad'a ne, Madu ya fad'a yana jawo Ammar jikinshi, Iro yace " wallahi ko mutuwa ce ta doso Ammar zamu tare shi mishi ita, 

sosai Madu yaji dad'in kalamansu, yayi godiya had'i da mik'ewa ya shige BQ da Ammar, bayanin abinda ya faru Madu yayiwa Hajara, 

iska Hajara ta furzar kana tace " anya Malam bazamu d'auke Ammar mu gudu dashi ba? 


"Wannan azabar ta isa haka, ace yaro d'an shekara tara 8 ake azabtarwa haka? 


"Humm wallahi nima na fara tunanin d'auke Ammar, Madu yayi maganar yana rafka tagumi, 

jikin Ammar a sanyaye yace " babu inda zamu, anan aka haife ni, anan zan rayu, nan ne gidan uba na, dama ai burinta kenan na tafi na bar mata gidan, 

kunga idan muka tafi burinta ya cika, wuya bata kisa sai dai idan kwana ya k'are, sosai kalamanshi suka bawa Hajara da Madu mamaki, 

Hajara tace " Ammar ina kaji wad'annan maganganun dan nasan sunfi k'arfin kwakwalwarka? 


"Baba Malam ne yake fad'a min duk sanda yazo gani a makaranta, yace " duk irin wuya da azabar da za'abani karna sake na karaya, 

ko inbari zuciyata ta mutu, yace na jajirce na rink'a tunawa ni namiji ne kuma jinin Yaseer ne, Yaseer kuma ba rago bane, 

dan baya tab'a sadaukarwa akan komai, yace nayi hak'uri komai lokaci ne wata rana sai labari, 

yace na dage nayi karatu danshi kad'ai ne zai iya tayani kwatar 'yanci na, gashi yanzu kuma an cire ni daga makarantar, 

ya k'arasa maganar hawaye na gangaro mishi, tsananin tausayinshi ne ya hana Madu da Hajara magana, 

" karkayi kuka, zamu rink'a tafiya makarantar mu dakai, Nashwan ya fad'a yana goge mishi hawaye, 

da sauri Ammar ya kalli Nashwan yace " da gaske kake Nashwan? 


"Eh! gobe ma ka shirya zamu je, jin abinda Nashwan yace yasa Hajara da Madu suka kalli juna, dan sai lokacin shawara ta fad'o musu, 

cikin zumud'i Ammar ya kalli Hajara da Madu yace " Mama bazatayi muku fad'a ba? 


Fuskar Madu d'auke da murmushin yak'e ya shafa kan Ammar yace " sai dai kayi hak'uri, dan maranatar su Nashwan ta gwamnati ce, 

kai kuma ka saba da makarantun kud'i boko da islamiyya, 

" ni dai zanje Baba (sunan da suke kiran Madu dashi Hajara kuma Umma) tunda can Brother yake zuwa, 

" to shikenan in sha Allah, gobe zan kaika kaji, har da islamiyyarsu, cike da murna Ammar ya fad'a jikin Madu da Hajara yana cewa " nagode sosai Umma da Baba na, 

washe gari kamar yadda Madu ya fad'a hakance ta kasance da kanshi ya kai Ammar Yaseer makarantar, aka sakashi ajinsu Nashwan, 

kullum kafin Ammar ya tafi makaranta sayya fara zuwa ya gyara d'akin Tanya da Nayan ya wanke band'aki kana yake tafiya makaranta, 

bayan Hajara ta gama aikinta tazo ta durk'usa gaban Tanya tace " Hajiya na gama zan tafi, da hannu Tanya tayi mata alama data je, 

adak'ile Nayan yace " idan kinji ki turo min shi, ta amsa da to, bata jima da fita ba Ammar ya shigo, 

ya durk'usa har k'asa ya gaida Hajiya Tanya da Nayan amma cikinsu babu wanda ya amsa,

ya kai minti 15 a durk'ushe babu wanda ya kalle shi bare yayi mishi magana, jiki a sanyaye yace " gani Yaya, 

batare daya kalle shi ba yace " na ganka ai, sai da aka d'auki lokaci kana Nayan yace " gyara min d'aki na, 

Ammar yace " d'azu na gyara, kofin tea dake hannun Nayan ya jefi Ammar dashi shayin ya fallatsarwa Ammar a jiki, 

" dan uwarka ni nake fad'a kana fad'a? 


"A'a Yaya ba musu nayi dakai ba, "wato k'arya nayi maka ko? 


Nayan ya fad'a yana nufar Ammar a hasale, ja da baya Ammar ya farayi yana cewa " kayi hak'uri ban k'arawa, 

ido rufe Nayan ya rufe Ammar da duka ta ko'ina ya zage iya k'arfinshi ya nad'a mishi dukan tsiya, wuya ta saka Ammar fashewa da kuka, 

Tanya na zaune tana busa sigari bata kalli inda Nayan yake ba balle ta hana shi, sai da ya gaji dan kanshi sannan ya kyale shi, 

Hajiya ta kalle shi a wulak'anci tace " kai dan kan uwanka had'iye kukan nan karka tasar min 'ya tana bacci, 

hannu Ammar ya saka ya tushe bakinshi saboda kukan bazai iya tsaida kukan ba, da k'arfi Hajiya Tanya tasa k'afa ta hankad'e shi, 

had'i da cewa " dan bura ubanka bazaka had'iye kukan ba? 


Jikinshi na kerrrma yayi tsit saboda tsabar razana, Nayan na huci yace " wuce kaje ka gyara min d'aki na, Ammar na tallafe da kanshi daya fashe ya wuce da sauri ya shiga d'akin, 

ganin d'akin yayi tsaf babu abinda ya same shi, amma saboda tsoro dole ya k'ara gyarawa, 

ya fito ya durk'usa gaban Nayan yace " na gama Yaya, batare da Nayan ya kalle shi ba ya nuna mishi k'ofa, 

ya mik'e zai fita jikinshi duk jini, Hajiya Tanya tace " kai!, jiki na rawa ya dawo ya zube gabanta, 

d'auketa ka rarrashe ta, ta fad'a tana nuna mishi Leenah dake kuka, jiki na tsuma ya d'auke ta, 

ya shiga jijjigata, Hajiya Tanya ta mik'e ta shige bedroom d'inta tabarsu anan, Nayan ma ya shige nashi bedroom d'inshi, 

Ammar bai samu Leenah tayi bacci ba sai k'arfe biyu na dare, 

ya lallab'a ya kwantar da ita saman sofa, ya zauna k'asan tiles, yana ta rawar sanyi kasancewar lokacin muku-mukun sanyi ne, 

yadda kasan ana ruwan k'ank'ara haka Ammar yake ji, ga jikinshi duk afashe saboda duka, ga yunwa da bacci da yake ji, 

yana nan zaune bacci ya d'auke shi, Hajara da Madu na can sun kasa zaune ko tsaye dan sun tabbatar akwai abinda ke faruwa,

k'arfe biyar saura na asuba Nayan ya fito d'aukar caja a parlour ya tarar da Ammar kwance kan tiles ya k'udundune, 

yana baccin wahala, sai sauke ajiyar zuciya yake cikin baccin, har Nayan ya juya zai shige bedroom d'inshi wani tunani ya fad'o mishi, 

dan haka ya fasa shiga d'akin ya komo da baya cikin sand'a ya shiga kitchen yana dariyar mugunta ciki-ciki dan shi kad'ai yasan meya shiryawa Ammar...........! 


*KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE, IYA KUD'INKI IYA SHAGALINKI....!*


MOMYN ZARAH. 'YARBAIWA


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol