Free chapter · Read without an account

6

by Hauwa A Usman · SAKI RESHE..

SAKI RESHE...!*_

*(CIGABAN GADAR ZARE)*

*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_

*LITTAFINA NA KUD'I NE IDAN KIN SAN BAKI BIYA KADA KI KARANTA DAN ZAKI BIYANI A GABAN ALLAH*

6️⃣

Tana gaf da ficewa daga get d'in makarantarsu taji ana kwala mata kira, cak ta tsaya had'i da runtse idonta,

" ina zaki haka kike ta sauri baki jira ni ba?

Safiyyah ta fad'a tana kallanta, d'an murmushin yak'e Basmah tayi batare datace komai ba, jerawa sukayi suna tafiya Safiyyah nata faman zuba while Basmah tayi shiru tana tunanin mafita cikin ranta,

" sannunku!, taji muryarshi ta dagi dodon kunnenta, da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi suka had'a ido,

lokaci d'aya suka sakarwa junansu murmushi, " an gaji ko?

"Murmushi ta kuma yi batare datayi magana ba, " ayi hak'uri a taimaka min a bani d'an lokaci kad'an na gabatar da kaina,

ya fad'a cikin alamar rok'o, ganin batayi magana ba yasa shi mayarda kallanshi ga Safiyyah yace " k'awarmu a taimaka a bani aronta minta biyu kawai,

ba musu Safiyyah ta juya da nufin barin wajen, cikin tsoro Basmah tayi saurin rik'e ta had'i da cewa " a'a ni dai ki tsaya dan Allah karki tafi,

Safiyyah na murmushi ta zame jikinta tana cewa " ba tafiya zanyi ba, d'an matsawa zanyi, ta fad'a tana barin wajen,

matsawa yayi kusa da ita yana murmushi yace " tsoro na kike ji?

Cikin nutsuwa ta girgiza kanta alamar a'a, yace " to meyasa kike tsoron kar'a barni daga ni saike?

"Haka nan kawai, ta fad'a kanta k'asa, d'an murmushi yayi kana yace " da farko dai ni sunana *ZAMAN* mahaifaffan garin Kaduna,

aiki ne ya kawo ni Zamfara, sai gashi Allah ya had'ani da matata uwar yarana a Zamfara, k'asa ta k'arayi da kanta cike da kunya, " Allah ya sani ina sanki Basmah so bana wasa ba, son gaske nake yi miki,

cikin sanyin muryar tace " nagode sosai da soyayya, sai dai gidanmu ba'a fara bari na zance ba, kaje ka samu Baba ko d'aya daga cikin yayyena kuyi magana,

"haka ne kam, in sha Allah zanje in same su, amma kafin naje ga manya sai na fara jin ta bakinki dan naji dad'in tunkararsu,

inda hali ma ina san mu fara sanin junanmu sosai kafin akai ga iyaye, sun d'an dad'e suna magana kafin sukayi sallama, tun daga ranar kullum sai Zaman da Basmah sun tsaya sunyi hira idan aka tashi daga makaranta,

tun Safiyyah nayi mata magana harta gaji ta kyale ta, danta lura tayi nisa, sannu a hankali so da k'aunar Zaman ta gama mamaye gaba d'aya zuciyar Basmah,

ya koyar da ita sonshi, ya shagwab'a ta da k'aunarshi, babu abinda kunnenta yake amsawa sai sautin muryarshi,

idanuwanta kam kullum cikin mararin ganinshi suke, cikin k'ank'anin lokaci duk wata gaba da magunar jikinta suka suka amshi sak'on son Zaman,

soyayyarshi ta zame mata abinci da abin sha, ya zama tana jinshi har cikin k'ahon zuciyarta, ta kamu da matsananciyar soyayyarshi,

yayinda Zaman ya zage yana nuna mata kulawa, so da k'auna, ya riga ririta ta yana tarairayarta,

yana k'ara cusa mata sanshi, abunka da ba'a samunba, macen kulle wacce bata saba mu'amula da maza ba, aiko ta haukace a sanshi, bata da aiki sai tunaninshi, duk abinda take yi yana ranta dai-dai da numfashinta yana fita ne da Zaman,

kullum addu'arta d'aya Allah ya cika musu burinsu su mallaki junansu,

a makaranta kam tuni Basmah ta dad'e da daina fahimtar durussan da ake koyar dasu, malamai nata faman b'ab'atu itako ta zurfa duniyar tunnin gwarzonta,

" ni fa gaskiya na gaji da abinda kuke yi ke da Zaman, ya kamata ku nemarwa kanku mafita, amma tsayawar nan da kuke yi a titi bai kamata ba,

Safiyyah ta fad'a fuskarta a d'an tsuke, "ayya kiyi hak'uri in sha Allah yau zan fad'a mishi yaje gida, ta fad'a cikin sanyinta,

" ya dai kamata gaskiya, dan nagaji da cin anamar iyayenmu da muke yi, Basmah zatayi magana taji yace " sannunku!, d'an tsoki Safiyyah taja yadda bamai ji, had'i da tsuke fuskarta,

" ayi hak'uri dai k'awarmu in sha Allah komai ya kusa zuwa k'arshe, banza tayi dashi, matsawa gefe Basmah da Zaman sukayi kana tace ,

" Safiyyah ta fara gajiya, kuma gaskiya ta fimu gaskiya dan hakan bai dace ba, bai kamata mu rink'a tsayawa a titi ba,

" yanzu ya kike son ayi?

"Ki fad'i duk abinda kike son ayi, " kaje gidan mu, dan ban san mu rink'a tsayawa a titin Allah, "to shikenan gobe zanzo, daga haka suka d'an tab'a hirar soyayya.

Yauma kamar kullum suna zaune a parlour gaba d'ayansu, suna hira, Ya Mu'allim ya fito daga bedroom d'inshi, " ina Mamana?

Ya fad'a yana zama, dan rabon Basmah da zama cikinsu harta manta kullum tana d'aki tana tunanin Zaman,

"Tana d'akinta, Umma ta bashi amsa, " Umma bata ci abinci ko?

Usman ya fad'a cikin sanyin murya, "Eh!, shiru Ya Mu'allim yayi yana sauraransu kafin yace " kira min ita, cikin nutsuwa Usman ya mik'e ya shiga bedroom d'inta,

kwance ya iske ta tana magana ita kad'ai while tana murmushi, " to! lafiyarki kuwa Auta?

Usman ya fad'a yana k'arasa shiga bedroom d'in, bata ji abinda yace ba balle tasan ya shigo, sosai Usman yayi mamaki dan yasan tunani ba halinta bane,

"Basmah! yace yana dafa ta, da k'arfi ta sauke ajiyar zuciya, ganin Usman tsaye a kanta yana binta da kallan tuhuma yasata saurin mik'ewa tana cewa " la! Yayana yaushe ka shigo?

Maimakon ya bata amsar tambayarta sai yace " meka damunki sister?

Murmushin yak'e tayi had'i da basarwa tace " babu komai Yaya, kamar zai k'ara tambayarta sai ya fasa yace " kije inji Abba, tare suka fito tana biye dashi, koda ya zauna ma kusa dashi ta zauna,

Usman da kanshi ya zuba abincin ya mik'a mata yana cewa " ci abinci autarmu, ta amsa had'i da cewa " nagode Yaya,

tana kai cokalin farko bakinta ta kware, a tare Umar da Aliyu suka mik'a mata cup d'in ruwa, " sha ruwa!, suka fad'a lokaci d'aya, tana murmushi ta sanya sannu ta karb'i cups d'in tace " nagode sosai,

Ya Mu'allim da Umma ko binsu sukayi da kallo cikin ransu suna godiya ga Allah daya had'e musu kan zuri'arsu, suke so da k'aunar junansu,

tunda Basmah tayi loma d'aya bata k'ara ba, sai juya cokali take ta kafe kwanan da ido, ta lula duniyar tunanin Zaman, " Mamana!,

Ya Mu'allim ya kira sunanta dan yana kula da ita, bata jiba balle ta amsa, dan haka gaba d'ayansu suka zuba mata ido, "Mamana! ya kuma kiranta a karo na biyu,

amma still bata ji ba, d'an tab'a ta Abubakar yayi had'i da cewa " Auta!, a firgice tace " *ZAMAN!*, kallan juna suka shigayi batare da d'aya daga cikinsu yace k'ala ba,

kula da tayi da tayi sab'ul da baka yasa ta saurin cewa " na'am Yaya Aliyu, a nutse Ya Mu'allim yace " bashi keyi miki magana ba nine nan,

yayi maganar idonshi kanta yana karantar yanayinta, cike da kunya ta sunyar da kanta, "meke damunki Mamana?

"Na lura kin canja a cikin 'yan kwanakin nan, gaba d'aya baki cikin hankali da nutsuwarki, lafiya?

"Bakomai Abba, ta fad'a tana wasa da hannunta, " mu iyayenki ne, dan harsu Abubakar tamkar iyaye suke a wajenki, dan haka baki da wad'anda suka fi mu,

mu muka fi cancanta da musan matsala da damuwarki, idan muna da hali muyi miki maganinta idan kuma tafi k'arfinmu sai mu fad'awa Allah,

k'asa ta k'ara yi da kanta tace " babu komai Abba, " kin tabbatar babu komai, "eh!, ta fad'a a hankali,

Cikin tsokana Usman yace " Kodai siriki aka samo mana, kafin tayi magana Ya Mu'allim ya daka mishi gigitacciyar tsawa,

" baka da hankali ne da kake irin wannan maganar?

"Bayan kasan nayi mata miji tun tana jaririya, salan ka bata k'ofar da zata samu dama, duk wanda ya kwana ya tashi a gidan nan yasan na dad'e dayiwa Basmah miji,

tun tana jaririya na bada ita, nayi alk'awarin bada aurenta ga *AMMAR*, kun fi kowa sanin bana magana biyu, bana yin alk'awari na sab'a koda za'a saka gaba na gabas,

dan haka ko bayan rai na Basmah bata da miji sai Ammar, wata irin razananniyar fad'uwa gaban Basmah yayi da k'arfi,

cikin tashin hankali ta d'ago kanta tana kallan Abbanta, yayinda gabanta ke cigaba da fad'uwa, zuciyarta ta shiga harbawa,

cikin k'ank'anin lokaci kamanninta suka sauya, firgici ya fito k'arara a fuskarta, sarai Ya Mu'allim ya lura da halin data shiga dan haka ya mayar da kallanshi gare ta,

yace " kwarai kuwa idan baki sani ba ki sani kina da miji dan na dad'e da bawa Ammar aurenki, kuma yana dawowa daga karatu zan d'aura aurenku,

cikin sanyin jiki ta sunyar da kanta k'asa, " kayi hak'uri, Usman ya fad'a cikin ladabi, "bakomai, Ya Mu'allim yace yana mik'ewa, gaba d'aya a wajen suka barta ta kasa kwakkwaran motsi,

tana jin zuciyarta kamar zata buga, ta dad'e zaune a wajen kafin ta tashi ta kwashe kayan ta wanke ta shige bedroom,

yadda Basmah taga rana haka taga dare burinta kawai gari ya waye taga abincin ruhinta ko ta samu sauk'in azalzalar da zuciyarta keyi,

a gaggauce Basmah ta gama shirin makaranta ta fice, kamar yadda tayi tsammani haka ta gani, sanye yake cikin k'ananan kaya kalar dark blue masu kyau da tsada, kalmi da agogon hannunshi black color, kwantaccen gashin ganshi yasha gyara yayi luf-luf, Zaman d'an gayu ne ajin farko ga kwalisa da kyau, gashi da tsafta da san k'amshi, koyaya ya rab'e saika ji k'amshinshi yana dukan hancinka,

kallo d'aya zakayi mishi kasan kud'i da ilimi da naira sun samu mahalli a tattare dashi, wani irin sanyin dad'i taji ya mamaye duk ilahirin jikinta,

tarin bak'i ciki da damuwarta suka yaye, ta tsinci kanta cikin annashuwa, shu'umin murmushi ya sakar mata wanda yake karyar mata da zuciya akoyaushe,

cikin salonshi ya kashe mata ido d'aya had'i motsa bakinshi yadda babu me jin abinda yace, yace " i love you, ta lumshe idonta gami da mayar mishi da maratarnin murmushinshi.

A b'angaren Ammar ko babu abinda ya ragu a mahaukaciyar soyayyar da yake yiwa Basmah, duk da bai san kamaninta bayan ta girma ba,

amma ya k'udurcewa ranshi duk muninta bazai tab'a k'inta ba koda ace nakashashshiya ce, kullum bashi da wata magana saita Basmah,

komai nashi Basmah, Nashwan har gajiya yake da hirar Basmah, Ammar na kishingid'e Nashwan ya fito daga toilet,

" yadai Na Basmah naga an had'a kai da gwiwa ko ana nan ana tunanin Basman?

Murmushi kawai Ammar yayi batare dayace mishi komai ba, kasancewar shi ba mai san yawan magana bane,

" Na Basmah ba gaba da gaba, Nashwan ya fad'a cikin tsokana, Ammar bai kula shi ba, dan idan da sabo ya saba da shak'iyancin Nashwan,

" please na tambaye ka?

Nashwan ya fad'a yana zama kusa da Ammar, "a'a karka tambaye ni dan nasan ba abun arziki bane, Ammar yayi maganar yana kwanciya saman sofa had'i da lumshe idonshi,

Nashwan ya tuntsure da dariya yana cewa " am serious Allah, inaso na tambaye ka Allah ba wasa a ciki, "uhun ina jinka, yace batare daya bud'e idonshi ba,

cikin nutsuwa Nashwan yace " please meyasa kake mugun san macen da baka san ainahin kamaninta ba, baka san yadda take a halin yanzu ba, wacce rabonka da ita yakai wajen 8yrs, dan inba mantawa nayi ba tun muna SS2 rabonka daka ga Basmah!?

A hankali Ammar ya bud'e idonshi had'i da mik'ewa zaune ya tattara gaba d'aya hankali da nutsuwarshi ga Nashwan yace,

" da farko ina santa ne saboda Allah, ban damu da kamanninta ko kyan halittarta ba, ban damu ba koda tafi kowa muni da munin halitta a duniya ba,

ban damu ba koda ace makauniya ce, kuturwa ce, gurhuwa ce, ma'ana bata ji bata gani bata magana wallahi zan iya auranta na zauna da ita danni ita d'in nake so bakomai nata ba,

tunda dama ban san komai nata ba bare na so shi, abu na biyu kuma shine farin cikin dana gani a fuskokin iyayenmu a ranar da aka bani ita tana jaririya,

duk da kasancewa ta yaro a ranar na fahimci ba k'aramin dad'i mahaifina da mahaifiyata suka ji ba, k"ara farin cikinsu ya bayyana,

sunyi matuk'ar farin ciki dan har muka isa Kano suna maganar, wannan farin cikin dana gani saman a fuskokinsu a ranar shine farin cikinsu da zan iya tunawa,

murmushinsu dana gani a lokaci shine murmushinsu dazan iya tunawa, haka babu wani farin ciki danaga sunyi har suka koma ga Allah dayafi na ranar da aka haifi Basmah,

ranar da mahaifinta yayi min alk'awarin aurenta, nasan babu abinda zanyi wanda zai faranta musu rai duk da basa raye kamar auren Basmah,

na aureta na rik'eta amana, nasan idan nayi hakan mahaifina zayyi alfahari dani,

sai abu na k'arshe daraja da k'imar mahaifinta Ya Mu'allim, wanda ba 'yar cikinsa ba,

ko wata ce a waje ya d'auko ya bani zan karb'a koyaya take wallahi, Ya Mu'allim mutum ne, yana da kyawawan halaye da d'abi'u, gaskiya, halacci, rik'on amana, hak'uri da juriya, irinsu Ya Mu'allim sunyi k'aranci a wannan zamanin badan karna zak'e ba,

da sai nace babu irinshi, ka duba kaga yadda yayi ta d'awainiya damu tun daga yarinta har girman mu, har kawowa yau bai daina ba,

shike yi mana komai na rayuwa, babu abinda bayyi mana ba, ya rik'e amanata, ya k'arasa maganar hawaye na gangaro mishi,

a hankali Nashwan ya mik'e daga inda yake zaune ya koma kusa da Ammar ya rungume shi, yana cewa " kayi hak'uri Brother bakai kad'ai kayi rashin Daddy ba,

hak'ik'a Ya Mu'allim ya cika cikekken d'an halak mutumin kwarai, bamu da abinda zamu saka mishi sai addu'a, muryar Ammar na sark'ewa yace " badan Ya Mu'allim ba Allah kad'ai yasan inda nake, da halin dana ciki a yanzu,

Allah kad'ai yasan a wacce duniyar muke, wata k'ila muna can muna talla, dan neman na abinci,

bani da abinda zan biya mutum hud'u a rayuwata Baba da Umma (Hajara da Madu) da Ya Mu'allim da Umma, sunyi min komai a rayuwata sai dai addu'ar Allah ya biyasu,

dakyar Nashwan ya daure ya danne abinda yake ji, ya shiga gugewa Ammar hawaye danya kawar da maganar yace " to yanzu dai bani labarin Basmah,

Ammar yayi murmushi danya gane nufin Nashwan yace " dai-dai da sunta fa ni na zab'a mata,

ni nace a rink'a kiranta da Basmah, " uhmmm wato kace kaika zab'awa matar taka suna?

Banza yayi dashi dan yasan so yake ya tsokane shi, Nashwan yace " to yanzu yaushe zaka sanar da su mun kusa komawa?

"A'a bazan sanar dasu ba, so nake nayi musu zuwan unexpected, sai dai su ganni kawai, " an kusa zuwa aga Basmah, aka yadda ta koma, kafin musha biki, simple smile Ammar yayi batare data furta komai ba,

kamar yadda Zaman yayiwa Basmah alk'awarin zuwa gidansu hakance ta kasance, yayi parking motarshi a k'ofar gidansu,

ya fito daga motar ya taka zuwa k'ofar gidansu cikin takunshi na isa da tak'ama, ya d'au wanka yasha gayu sai zuba k'amshi yake,

Basmah na zaune kusa da Ummanta, Ya Mu'allim da Ababukar da Umar na zaune gefenshi, while Aliyu da Usman na gefe,

dan duk da kasancewarsu maza basa fita indai basa makaranta ko islamiyya to suna gida, inbanda dukan uku-uku babu abinda gaban Basmah keyi,

ta kasa zaune ko tsaye, duk bayan minti d'aya saita saci kallan agogo, ta yunk'ura zata mik'e taji sallar yaro " Salamu Alaikum wai ana sallama da Basmah, tsayawa tayi cak a yadda take ta gabanta na cigaba da fad'uwa,

da sauri gaba d'ayansu suka kalli Basmah dake duk'e kamar an dasa ta, Umar zayyi magana Abubakar yayi saurin cewa " je ka ce anyi mata miji,

dab'as Basmah ta koma ta zauna k'irjinta ya shiga bugawa da tsananin k'arfi,

zuciyarta ta shiga suya tana d'aci, ji take tamkar ta fasa ihuu, dawowa yaron yayi yace " wai yace dan Allah minti biyu kawai, " kaje kace tana da mijinta da zata aura,

dakyar Basmah ta iya mik'ewa tana dafa bango ta shige bedroom d'inta, ta shiga lek'enshi ta windo, sai da yayi wajen awa biyu kafin yabar k'ofar gidansu,

jiki a sanyaye ta zube saman bed rigingine idonta yana kallan pop, " me Abba yake nufi da anyi min miji?

"Waye mijin?

"A ina yake?

"Waye Ammar d'in da Abba yake irin wannan abun akanshi meye alak'arshi da Abba?

"Ya akayi bata sanshi ba, bata kuma tab'a ganinshi ba?

Ta jerawa kanta tambayoyi, a hankali ta lumshe idonta tana tunano kalaman Zaman da hoton kyakkyar fuskarshi,

" ina sanka Zaman! kai kad'ai nake so, akanka na fara sanin meye so, meye soyayya, akanka na fara sanin zak'i da dad'in so, bazan iya rabuwa dakai ba,

ta fad'a hawaye na gangowa saman fuskarta, washe gari bayan sun taso daga makaranta,

ta ganshi tsaye hard'e da hannuwanshi a kirjinshi, kallo d'aya zakayi mishi kasan yana cikin damuwa, " sannunku, ya fad'a cikin sanyin murya,

cike da tausayin kansu tace " yauwa, ina yini?

"Ba lafiya ba Basmah, wallahi jiya ban runtsa ba ina cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, yayi maganar hawaye na neman zubowa daga idonshi,

" kayi hak'uri please, nima ban san abinda ke faruwa ba, hawayen dayake k'ok'arin dannewa suka shiga zubowa daga idanuwanshi,

" ina sanki Basmah, wallahi bazan iya jure rashinki ba, dan Allah ki taimaka min, kada ki bari a raba mu please, mutuwa zanyi idan aka raba mu,

kece rayuwata Basmah, ya fad'a cikin wata irin murya dabata tab'a jinshi da irin taba, take zuciyarta ta karye wutar sonshi ta shiga ruruwa, zuciyarta ta shiga tsalle kamar zata fasa k'irjinta ta fito, jikinta ya d'auki rawa da kerrrma, cikin sanyin murya tace " nima ina sanka kai ne rayuwata,

bazan iya rayuwa da waninka ba, dan kai kad'ai aka halicce ni, da kai kad'ai zanyi rayuwa, ina sanka in sha Allahu baza'a raba mu ba,

bama zamu tab'a rabuwa ba, tare zamuyi rayuwa a duniyarmu har rai da mutuwa, da sauri yace " kinyi alk'awari Basmah?

Kai tsaye ta biyewa umarnin zuciyarta tace " eh! nayi maka alk'awarin tare zamu rayu, "ke! Malama ce Basmah kin san muhimmancin alk'awari,

"in sha Allah kai ne uban 'ya'yana ,ta fad'a cikin sanyi, murmushi ya saki wanda kallo d'aya zakayi mishi kasan bana nishad'i bane, " nagode Allah yasaka miki da alkhairi,

ta amsa da " amin ya Allah, amma dan Allah ka daina min kuka ka share hawayenka, da sauri ya goge hawaye yana cewa " na daina my everything, yanzu meye mafita?

D'an shiru tayi kafin tace " idan kaje gobe kada kace ni kake nema, kayi magana da Abba, nasan zaiji nauyin yace maka bazai baka ni ba, "a'a ba sai gobe ba, yau zanje wajenshi muyi magana,

yanayin yadda yayi maganar ya bata dariya, sai da suka sha hirar soyayya kana sukayi sallama,

k'arfe 7:00 na dare a k'ofar gidan Ya Mu'allim tayiwa Zaman, Usman ya fito daga masallacin dake manne da gidansu zai shiga gida,

da sauri Zaman yace " sannu!, cikin nutsuwa Usman ya amsa mishi da " assalamu alaikum ya fad'a yana mik'a mishi hannu suka gaisa,

" dan Allah idan ka shiga kayi min magana da Ya Mu'allim, " to!, Basmah na zaune Usman ya shigo, yace " Umma ina Abba?

"Yana ciki, lafiya?

"Eh! wani ne yake son ganinshi a waje, da sauri Basmah ta kalleshi deep down tana addu'ar Allah yasa Zaman yayi nasara akan Ya Mu'allim,

Umma ta shiga ta sanar dashi yayi bak'o, bai dad'e ba ya fita, bayan sun gaisa da Zaman Ya Mu'allim yace " ban gane ka ba,

cikin jin kunya Zaman ya shafa kanshi kana ya shiga yiwa Ya Mu'allim bayanin dalilin zuwanshi,

d'an jimmm Ya Mu'allim yayi kafin ya nisa yace " kayi hak'uri Basmah nada miji na dad'e da bada ita, dan tun tana zanin goyo na bada ita, kuma a addinance haramunne nema cikin nema,

tunda Ya Mu'allim ya fara bayani Zaman ya shiga girgiza kanshi gumi ya jik'a shi sharkaf, jikinshi ya d'auki rawa kamar mazari, "dan Allah Abba ka tauyawa mana, wallahi ina santa,

" kayi hak'uri yaro shima wanda na bawa ita yana santa, koma ince ya fika santa, jikin zaman a sanyaye sukayi sallama da Ya Mu'allim yabar wajen,

a tsakar gida ya taradda Umma da Basmah wacce zaune kawai take kamar mutum mutumi, Allah kad'ai yasan me take ji a ranta da zuciyarta,

" na gaji da masu zuwa neman auren Basmah idan Ammar ya dawo koya gama karatu kobai gama ba zan d'aura musu aure na hutu da sallamar mutane,

dammmm! k'irjinta ya buga da tsananin k'arfi, Umma tace " yauma wani ne yazo?

"Eh wai sunanshi ko Zaman, jin an kira sunan Zaman yasata jin tamkar an d'auketa anyi jefa da ita, Ya Mu'allim ya cigaba da cewa " na dayyi mishi bayanin na riga na bada ita, kwat! yawo ya wuce mata ba shiri wanda ya sakata kwarewa ta fara tari sosai,

ido Ya Mu'allim ya kafe ta dashi batare dayace komai ba, jikin Abubakar na rawa ya d'auko ruwa a fridge ya bata tasha,

tarin ya lafa mata, amma har lokacin jikinta bai bar rawa ba, har zuwa lokacin idon Ya Mu'allim na kanta yana karantar yanayinta,

jikinta a sanyaye ta kwanta saman bed tana mayar da numfashi, ta sanya hannunta d'aya ta dafe k'irjinta saitin zuciyarta,

dake mata zafi tamkar zata kama da wuta, mak'ogwaranta ya bushe, cikin takaici tayi kwafa had'i da gyara kwanciyarta, tace " me Abba yake nufi ne?

Ta fad'a tana lumshe idonta, bacci b'arawo ya sace ta, tun daga nesa ta hangoshi a hargitse, gaba d'aya yanayi da kamanninshi sun sauya,

da k'arfi k'irjinta ya shiga bugawa yana dukan uku-uku, jikinta na rawa ta damk'e hannun Safiyyah cikin nata, suna cigaba da tafiya, a hargitse Zaman ya isa gabanta ya tsaya,

yana fidda wani irin mawuyawacin numfashi idanuwanshi sunyi jajir kamar gauta, " dama anyi miki miji Basmah?

"Kin san anyi miki miji amma kika jefa rayuwata a had'ari, kikasa na sakankance na fara sanki, kina sane da kina da wanda zaki aura amma shine kika yi min rik'on talala?

"Why Basmah!?

"Meyasa kike neman kashe ni, meyasa kike san tarwatsa min zuciya?

Yayi maganar muryarshi na sark'ewa, " wallahi ban san da maganar ba, sai ranar nake jinta, ta fad'a kanta a sunkuye,

" d'ago ki kalle ni Basmah, ya fad'a kuka na neman kufce mishi, a sanyaye ta d'ago kanta, karaf idonta ya sark'e cikin rinannun idanuwanshi,

" me kika gani a cikin kwayar ido na?

" Nasan babu abinda zaki gani daya wuce so da wahalalliyar soyayyarki, idan aka raba mu mutuwa zanyi, wallahi bazan iya jure ganinki da wani na ba,

zuciyata tarwatsewa zatayi, ina gaf da mutuwa Basmah, ina gaf da rasa rayuwata, numfashi da bugun zuciyata na gaf da tsayawa,

dan Allah ki taimake ni Basmah , ya k'arasa maganar yana fashewa da kiritaccen kuka, " kayi hak'uri nima ban san da maganarshi ba,

" me kike nufi da nayi hak'uri, kina nufin shikenan mu hak'ura da juna?

Bata bashi amsa ba, illa hawaye da suka shiga gangarowa daga idanuwanta, a kid'ime ya shiga girgiza kanshi yana ja baya had'i da cewa " no! no! Basmah,

karkiyi min haka dan girman Allah, ki ceci rayuwa ta, ban cancanci haka daga gareki ba, ina sanki Basmah, ina sanki da duka zuciyata,

na dad'e da mallaka miki rai da rayuwata, dan Allah don't live me please, i loves you so much, ya fad'a cikin matsanancin kuka yana zubewa bisa gwiwowinshi a gabanta,

" ka tashi dan Allah, bai kula ta ba, ya matsa ya rik'e k'afafuwanta had'i da rushewa da kuka tamkar wanda aka ce uwarshi ta mutu,

" please....! please...! Basmah kece rayuwata, kece duniyata, kece ji da gani na, please karki barni ina sanki, " ka sake ni please, " bazan sake ki ba har sai kinyi min alk'awarin bazaki tab'a rabuwa dani ba,

yadda yayi maganar tamkar k'aramin yaro ya karya zuciyar Basmah, ta fashe da kuka tana cewa " ina sanka nima, wallahi ina mugun sanka, dan kai kad'ai zuciyata ke bugawa,

" idan haka ne meyesa bazaki fad'awa Ya Mu'allim ni kike ba?

"Meyasa bazaki fahimtar dashi kina da wanda kike so ba?

" Tsoro nake ji, ta bashi amsa cikin kuka, " bakya so na Basmah dan inda kina so na da bakiji tsoran tunkarar komai a kaina ba,

da bakiji shayin bayyanar da soyayyata a gaban kowaye ba, ni kad'ai nake ta haukan banza akanki, " ba haka bane Allah nima ina sanka,

" to ki sanar da iyayenki ni kike so ba wanda suke zab'a miki ba, ki fad'a musu kina da zab'in ranki, why bazaki cece mu ba?

"Komai yana hannunki ke kike da damar da zaki cika mana burinmu na mallakar junanmu, ki fito ki fad'a musu gaskiyar abinda yake ranki,

karki cutar da mu da zuciyoyinmu please, a hankali ta sauke ajiyar zuciya had'i da cewa" Bazan iya ba, ta fad'a tana runtse idonta da tsanin k'arfi,

wani irin mahaukacin kuka ya fashe dashi yana dafe da k'irjinshi yace " wayyo mutuwa zanyi, rayuwata ta zo k'arshe, da sauri ta durk'usa a gabanshi tare da fashewa da kukan itama, cikin raunananniyar murya yace " please Basmah ki taimake mu, zatayi magana yayi saurin cewa " kina so na?

A hankali ta d'aga mishi kanta, " to indai soyayyar da kike min gaskiya ce kiyi min alk'awarin duk wuya duk runtsi muna tare,

bazaki tab'a bari a raba mu ba, bazaki tab'a bari wani ya shigo tsakiyarmu yaci nasarar shiga tsakaninmu ba,

kiyi min alk'awarin zaki kasance dani, zaki kasance mai bin umarni na, kiyi min alk'awarin ke tawa ce ni kad'ai, dani kad'ai zaki kasance, ni kad'ai zaki mallakawa zuciyarki, yayi maganar yana k'ara damk'e k'afafuwanta,

take giyar soyayyarshi ta ranjayi duk wani sassan jikinshi, zuciyarta ta amince da kalamanshi, harta rink'a jin idan duniya da abinda ke cikinta zasu taru basu isa su rabata da hasken ranta ba, koda za'a kashe ta, bazata tab'a barin a rabata da Zaman ba, dan shine farin cikinta da annurin rayuwarta,

bazato ba tsammani Safiyyah taji Bsmah na furta " nayi maka alk'awarin duk wuya duk runtsi muna tare, bazan tab'a juya maka baya ba,

zan kasance a tare dakai cikin kowanne irin hali, nayi maka alk'awarin bazan tab'a barin wani ya shiga tsakaninmu ba balle harya samu ikon raba mu.........!

*KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE IYA KUD'INKU IYA SHAGALINKU.....*

MOMYN ZARAH. 'YARBAIWA!

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol