Free chapter · Read without an account
15
_*SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
1️⃣5️⃣
A tsorace Hajiya Tanya tace " baka da hankali Nayan?
"Kasan abinda ka janyo mana kuwa?
Fuskar Nashwan d'auke da murmushi ya tako gabanta ta yadda suna iya jiyo numfashin juna ya jefa idonshi cikin nata,
yana fad'in karki damu babu wata matsala, ni abokin hark'alla ne yanzu, ba abokin adawa ba,
tafiyarmu d'aya ce, duk tsuntsu d'aya muke jifa, dole sai dani zaku cimma burinku, tunda tun kan a haifeni kike abu d'aya kin kasa kaiwa k'arshen abun
haka nima dole saida ku zan cimma buri na,
baya Hajiya Tanya taja had'i da fashewa da mahaukaciyar dariya tana tafa hannu tace " woooo shegiya naira, me raba uwa da d'anta,
me raba uba da d'anshi, me raba miji da mata, me shiga tsakanin rayuwa da numfashi, wato dai babu wata soyayya data wuce ta kud'i?
"Babu! ta bawa kanta amsa tana tsagaita dariyarta, tana kallansu tace " tam yanzu ta ina zamu fara?
Kafin Nayan yayi magana Nashwan yayi saurin cewa " ta rufe k'ofa idan zaku yi magana, ya k'arasa maganar yana kashewa Hajiya Tanya ido,
wanda yasa gaba d'aya tsikar jikinta da kashin jikinta mik'ewa, " zauna, Nashwan ya fad'a idonshi cikin nata,
saurin kawar da idonta tayi daga kanshi tana zama tace " meye abu na gaba?
"Yarda!, dole mu yarda mu aminta da junanmu, kada wani yayi abu ba tare da saninmu ba, Nayan ya fad'a yana kallan Nashwan,
a hankali Nashwan ya zauna had'i da hard'e k'afafuwanshi yana murmushi idonshi kan Nayan yace " yarda?
"Babu abu mafi illa a rayuwar d'an Adam kamar yarda da saurin amincewa mutane, yarda babban matsala ce ga mutum,
dan haka kada ka yarda da kowa ka zama naka kai kad'ai, kanshi ya karkata ga Hajiya Tanya ya d'age mata gira d'aya yace " ko!?
Yanayin yadda yayi mata maganar ya kashe mata jiki, gab'ob'in jikinta suka mutu, cikin sanyin jiki tace " tayaya zamu iya yarda dakai?
"Yarda! Yarda! Yarda! ina tunanin kamar yanzu nayi magana akan yardar nan ko?
"Ko nima bance ku yarda dani d'ari bisa d'ari ba, danni ma ban gama yarda daku ba, kallan juna Hajiya Tanya da Nayan sukayi kafin suka mayar da kallansu ga Nashwan,
ganin yadda suka tsura mishi ido yasa shi cewa " Barrister Khamal S Alk'ali yazo.....! "what?
Hajiya Tanya ta katse shi cikin tashin hankali, idonshi ya juya had'i da cewa " meyasa haka ne?
"Ai dai kya bari kiji k'arshen zancen ko?
Yawu ta had'iyi tana fad'in "ina jinka,
bai b'uyewa Hajiya Tanya komai ba, ya sanar da ita duk abinda ya faru, kana ya d'ora da cewa " dan bak'ar mugunta irin ta mutum da ganin kyashi,
duk irin halaccin da iyaye na sukayi mishi bai gani ba, shine zai ce tunda ya *RASA BASMAH* shikenan komai ya fita a ranshi,
baya san komai, babu sauran wani jin dad'in daya rage mishi, wai arabar da dukiyar, " bura uba, amma yaran nan anyi d'an iska,
mugu mai bak'ar zuciya wato duk abinda nayi ya tashi a banza kenan, bani da wata riba, to wallahi yayi ganganci dan yana wasa da wuta ne,
zan iya kashe duk ran dake neman tsayawa a gaba na akan duniyar nan, Hajiya Tanya ta fad'a tana huci, " babu babban munafuki sai Ya Mu'allim,
cewar Nayan, " ai ku kunga matsalar ku, baku yin abu da ilimi da tunani, saurin fushi illi ne ga lafiya, so ku rage saurin fushi, da nurmushi da dariya ake cimma ko a kawar da abinda kuka da b'acin rai suka kasa,
Ya Mu'allim yayi k'ok'ari wannan karon dan badan shi ba da tuni an rabar da dukiyar, ajiyar zuciya Hajiya Tanya ta sauke kafin tace " kuje ku barni nayi tunani nasan abin yi, Nayan zayyi musu ta d'ago jajayen idanuwanta ta zuba mishi, tana yi mishi alama da Nashwan,
bai kuma magana ba ya fita, Nashwan ma ya mik'e ya fita.
**********************************
Komai na duniya tsaya mata yayi cak, jinta da ganinta suka d'auke, hankalinta da nutsuwarta suyi tafiyar bargu, ta jima a haka kafin taja baya da sauri,
tana watsar da hotunan hannunta, ta shiga girgiza kanta kana fad'in " a'a no....! no....! ba haka bane, ba gaskiya na gani ba, ba gaskiya bane,
akwai dai wani abun amma hakan bazata tab'a kasancewa ba, ta k'arasa maganar hawaye na gangarowa daga idonta,
da gudu tayi parlour kamar wani abu zata d'auko, ta fad'a saman sofa tana mayar da numfashi,
tama rasa abinyi, ta rasa abin yarda, ta rasa ta inda zata fara tunani, ta rasa komai, komai ya kunce mata, jin an turo k'ofar parlour'n yasata saurin mik'ewa tana fad'in " waye kai Zaman?
Turus yayi yana binta da kallo kafin yace " ban gane waye ni ba, bata yi mishi magana ba, taja hannunshi zuwa bedroom, " meye wannan Zaman?
"Nace meye wannan?
"Meye alak'arka dasu, meya dangantaka da Bible da sark'ar cross?
"Meya kaika coci har kayi hoto?
Ta fad'a tana nuna mishi hotunan dake zube a k'asa, " hotuna a coci Zaman meye kai ka?
" Me kaje yi coci har kayi hotuna kana sanye da kayan ango rik'e da hannun amaryarka ku......! dakatar da maganar tayi dan sai a lokacin ta tuna wani abu,
da sauri jikinta na b'ari ta nufi hotunan ta d'auke su, " *AURE*
, hotunan aure ne Zaman, me hakan ke nufi?
" Meke faruwa ne Zaman, meke faruwa?
"Waye kai?
"Daga ina kake?
"Daga wacce duniya ka fito?
Ta jera mishi tambayoyin a lokaci d'aya tana durk'ushewa had'i da fasa kuka, tana cigaba da fad'in " waye kai dan Allah ka sanar dani gaskiya a kanka?
Zaman dake tsaye fuskarshi d'auke da murmushi, deep down zuciyarshi kamar zata fashe saboda tsoro da zallar kid'ima,
duk inda kake tunanin tashin hankali, hankalin zaman a mak'urar tashe yake, dakyar ya fara d'aukar step yana nufarta,
" no! Zaman karka sake ka k'araso inda nake, ka tsaya anan kayi min bayani, k'ara d'aukar step yayi yana k'ok'arin had'e tazarar dake tsakaninsu,
tayi saurin mik'ewa a mahaukace ta saka gaba d'aya k'arfinta ta hankad'ashi baya, ta d'auki glass jug dake kan bedside cike da ruwa ta jefa mishi tana cewa " baka ji abinda nace maka ba?
"Kada ka sake ka k'araso inda nake ka tsaya a nan ka fad'a min koma me zaka fad'a min, murmushi yayi yana bin glass jug d'in daya tarwatse da kallo,
wanda in banda Allah yasa yayi saurin matsawa da sayya illata shi, bai kuma k'ok'arin nufar inda take ba ya fice,
da k'arfi ta shiga kwala mishi kira " Zaman! Zaman ka dawo ka sanar dani komai in ba haka ba zan mutu, mutuwa zanyi idan baka sanar dani ba,
shirunka zai iya tarwatsa man zuciya, bai ko juyo ba ya fice harabar gidan ya shiga mota ya fige ta, a kwayar idonshi zaka fahimci tsantsar b'acin rai da tashin hankalin dayake ciki.
Tunda Zaman ya fice bai dawo gida ba, har wajen k'arfe biyu na dare, Basmah kam anan inda take zaune tana kuka bacci b'arawo yayi awon gaba da ita,
bata farka ba sai wajen k'arfe goma na safe, hasken rana ne ya haske mata ido wanda yasa dole ta bud'e idonta,
ganin haske ya sata saurin bud'e idonta tangaram, " subhanallahi tace tana mik'ewa da sauri, ban d'aki ta shiga ta d'auro alwala ta gabatar da sallah,
ta dad'e tana jera addu'o'i kafin ta mik'e ta koma parlour ta zauna saman kujera tayi jigum, har dare babu Zaman babu labarinshi,
jin yunwa na neman yi mata lahani yasata shiga kitchen ta had'a tea ta shanye cikin kitchen tana daga tsaye,
ta dawo parlour tana zaman jiran tsammani, batare data sani ba bacci yayi awon gaba da ita, shiru-shiru har kwanaki biyar babu Zaman,
har abun ya fara bata tsoro ta shiga tunanin kodai ba lafiya ba, hankalinta yayi mummunan tashi sosai, ta shiga tuhumar kanta akan duk abinda ya same shi itace sila,
a ranar kwana na shida tana kwance k'asa a parlour tana bacci sama-sama ta jiyo bugun k'ofa, da sauri ta mik'e dan a zatonta Zaman ne,
kasancewar da hijabin da tayi sallah a jikinta bacci ya d'auke ta yasa ta fita, fuskarta d'auke da murmushi cikin zumud'i dan ta manta da abinda yayi mata,
ta sawa ranta ko ya dawo bazata sake tada mishi maganar ba, yanayin fuskarta ne ya canja ganin bak'uwar fuska,
sama-sama suka gaisa da mutumin, saboda gabanta dake fad'uwa da fargabar ko wani abun ne ya sami Zaman, mutumin yace " ina me gidan?
"Baya nan, ta bashi amsa a nutse, d'an shiru yayi, " lafiya kuwa?
Ta tambaye shi, " lafiya lau, nine mai gida nan da kuke haya, da sauri tace " haya kuma?
Dan ita Zaman yace mata gidanshi ne, "eh haya, kud'in wata uku ya biya, kuma yanzu har kun shiga wata na shida, cikin rashin fahimta tace " haya wacce iri kuma Malam?
"Haya dai da kika sani, mutum ya fad'a yana gyara tsaiwarshi, ya d'ora da cewa " ko ke baki san haya ba?
Da ido kawai take binshi ta kasa furta koda kalma d'aya, ya cigaba da cewa " ni na bashi gidan haya, komai da kika gani a gidan haka kuka same shi, babu da abinda yazo, sai kayan sawarshi, amma dai-dai da cokali anan ya same shi,
kwat ta had'iye yawu tana zazzaro ido kamar mara gaskiya tace " baya nan idan ya dawo zan sanar dashi, fuska ya tsuke yana fad'in " gaskiya na gaji da wannan yawo da hankalin da ake min,
wallahi idan na sake dawowa ko yana nan ko baya nan sai kun bar min gida haba, na gaji ya fad'a had'i da jan tsaki yana barin wajen,
a hankali ta fara jan k'afafuwanta tana komawa cikin gidan, jiki ba kwari ta zube a k'asa tana tuna lokuta da dama da Zaman ya fad'a mata wannan gidanshi ne,
ya fad'a mata yafi a irga, kanta ta dafe dake juya mata tana fad'in " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un meke shirin faruwa da ni ne?
Jikinta ba kwari ta jawo wayarta ta latsa lambarshi a karo na ba adadi ta jita a kashe, ajiyar zuciya ta sauke ta jingina bayanta da jikin kujera,
tana d'orawa kanta lafin, gani take yi kamar itace ta jawo komai, wata k'ila data nutsu sunyi magana daya fiye mata, bayan kwana uku shiru dai ba Zaman,
a ranar me gidan ya dawo iya tijara da fallasa Basmah tasha wajen me gidan, yayi mata rantsuwa da Allah duk ranar daya k'ara dawowa saita fitar mishi daga gida,
ta yarda da hakan, yayi kwafa had'i da barin wajen yana tauna goro, dole tasa Basmah ta fara tunanin mafita, dan tasan yadda me gidan baida mutunci idan ya sake dawowar korarta zayyi,
hankalinta a tashe ta shiga d'aki ta hau binkice cikin kayanshi, ko zataga wani abu da zai sada ta da inda yake, har ta gama bincike ko'ina bata ga komai ba,
ta zauna bakin gado tana nishi da haki bak'in ciki yasata fashewa da matsanancin kuka mai cin rai, ta dad'e tana kuka kafin ta mik'e tana mayar da kayan,
ta d'ago rigarshi wani abu ya fad'o daga aljihun rigar, a hankali ta kalli abun, ganin d'an k'aramin kati yasa takai hannu ta d'auka,
get pass ta gani na Jaiz Guest House, jiki na rawa ta mik'e ta zumbula hijab ta zari jakarta ta fice, batare data san inda hotel d'in yake ba,
me adai-daita sahu ta tare ta nuna mishi katin tana fad'in " kasan wajen nan?
Wani iri kallo ya jefa mata kafin yace " eh na sani, k'asan ranshi yana mamakin abinda zai kai kamilar mace irin wannan dandalin mashaya,
ya manta da fad'in Annabi dayace " ko daga gidan karuwai kaga mutum ya fito kayi mishi uzurin akwai abinda ya kaishi, a kyautatawa mutane zato,
har suka isa zuciyarta na bugawa, ta fito ta biya mai adai-daita sahun kana ta tsaya tana k'arewa wajen kallo,
ganin yadda matan wajen suke kamar tsirara, ba k'aramin mamaki ya bata ba, wani ta gani tsaye a gefe ta matsa kusa dashi tayi mishi sallama,
bai amsa ba ya bita da ido, " am dan Allah tambaya nake, cikin maye yace mata " yi tambayarki ina jinki, "dan Allah kasan Zaman?
Fuska ya d'an turb'une alamar tunani, yayi wajen minti d'aya kafin yace " anya a wajen nan akwai wani me suna Zaman kuwa?
"Eh sunanshi Zaman, naga kuma yana zuwa nan, " inaga bada sunanshi na ainahi yazo nan ba, kin san idan za'a shigo bariki b'oye sunan gaskiya akeyi saboda tsaro,
d'an shiru tayi tana tunani muryarshi ta katse mata tunaninta " baki da hotanshi?
"Ina dashi ta fad'a tana zuge jaka ta ciro wayarta da sauri ta nuna mishi hotan Zaman, ido ya zaro a matuk'ar tsorace jikinshi ya d'auki kerrrma, " kai bura uba,
Ya fad'a cikin matsanancin tsoro jikinshi yana rawa, yadda kasan yaga mutuwarshi, yadda taga yanayinshi ya canja daga ganin hotan Zaman ya tabbatar mata ya sanshi,
" ka sanshi ne?
" Yarinya ina kika san *MUGU*?
"Meye alak'arki dashi?
"Na ganki a haka kamar mutuniyar kirki, da alama baki san waye shi ba ko?
" *MUGU...!* ta maimaita sunan a saman leb'enta, a hankali ta shiga tunanin kalaman mashayin..........!