Free chapter · Read without an account
23
_*SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
2️⃣3️⃣
Dariyar mugunta ya saka harda dafe ciki yana fad'in " shegiya waya fad'a miki lahira ana d'anwake, yana dariyar ya gyara tsaiwarshi,
ya wara k'afa ya ciro cillarshi ya sakar mata fitsari, a hankali ta fara bud'e idonta dake rufe sakamakon ruwan dataji an zuba mata a fuskarta zuwa jikinta,
fuskarshi data tsana fiye da komai a rayuwarta ta fara yin arba, wacce take ganinta tamkar ta gwaggwan biri, ada ganin fuskar take tafi ta kowa kyau da annuri,
sai da ta k'arasa wartsakewa ta fahimci fitsari yayi mata a jikinta ba ruwan datake zaton ya zuba mata bane, kasancewar har lokacin yana rik'e da cillarshi, da sauri ta mik'e tana fad'in " na shiga uku, me nayi maka Zaman?
" Wanne irin mugun abun nayi maka da kake wulak'anta ni kake tagayyara min rayuwa?
"Ban canci haka daga gareka ba Zaman, dariya ya sanya yana fad'in " taurin kanki ne yaja miki, " wanne taurin kai nayi maka?
"Danna biyewa zuciyata naso abinda nake so laifi ne?
" Ko kuwa zab'in rai na danabi shine taurin kai?
"Ka tuna akanka nabar uwa har uba na, nabar dangi da 'yan uwana, na zab'e ka akan kowa, nayiwa kaina *SAKI RESHE...!*,
amma memakon na samu sassauci da sauk'i daga gareka sayya kasance kaike bani wuya Zaman, why! meyasa?
Ganin bashi da niyyar yin magana, saima ido daya tsareta dashi, yasata bawa kanta amsa sa cewa,
" na sani! Zaman na san amsata, bijirewa umarnin iyaye, k'in bin umarninsu, da saka iyaye zubar hawaye, dama Umma ta fad'a min cewar,
koda basuyi min baki ba, hakk'insu da hawayen da suka zubar akaina bazai tab'a bari na na samu salama a rayuwata ba,
na biyewa rud'in duniya dana shaidan, na afka tarkon zuciya nayiwa kaina illa, na sabauta rayuwata,
na cuci kaina nayi *SAKI RESHE...!* nak'ibin shawarar 'yan uwana, ta k'arashe maganar cikin kuka, kafad'a ya d'age had'i da tab'e irin ko'a jina,
kafin yace " ni dai ba igiya na saka na jawo ki ba, ba dole nayi miki ba, da kanki da k'afafuwanki kika biyoni,
zab'i ma aka baki kikaga nafi cancanta dana zauna dake, na cancanta daki mallakamin ragamar tayuwarki, kikaga zanfi kowa baki kulawa da farin ciki d'orarre har k'arshe rayuwarki,
kikaga nafi iyayenki, danginki da kowa naki cancanta da......! " ya isa Zaman ya isa haka, ta fad'a tana d'aga mishi hannu, a wahalce ta fitar da numshi tace,
" duk naji haka ne, amma kaika hure min kunne, ka nuna min kai mutumin kirki ne, mai dattako da tsoran Allah,
ashe kura ce da fatar akuya, lumbu-lumbu wutar k'aik'ayi, macijin sari ka nok'e, ka sani idan babu duniya akwai lahira,
kuma Allah yana ji yana ganinka, duk abinda kake min bazan tab'a yafe maka ba,
bakin Zaman a sake kamar dole yana kallan Basmah harta dasa aya kafin ya tafa hannu yace " Allah ko?
"Ashe bazaki yafe min ba, to kin dad'e baki yafe min ba, harya juya zai shiga d'aki ya juyo yace " ki san yadda zakiyi da kan wannan la'anannan,
" kaga nan la'anannan Allah banza kawai, duk abinda Allah ya hana su kake aikatawa, Basmah ta fad'a cikin ranta,
mik'ewa tayi a tsorace tana ja baya had'i da girgiza kanta tace " no! Zaman kaima kasan ko mutuwa ce tsaye a kaina bazan iya ko kusatar kan nan ba,
ta fad'a tana k'ara kallan kan a karo na biyu da tunda ta kalleshi sau d'aya bata kuma gigin k'ara kallanshi ba,
ya datse harshenshi da hak'oranshi da alama yasha bak'ar wuya kafin fitar ranshi,
kafad'a ya d'age yana fad'in " ruwanki, saurin bin bayanshi tayi har tana kifawa, ta k'ara sautin kukanta " wallahi bazan iyaba,
dan Allah ka taimake ni ka raba ni dashi, dariya ya saka yana hankad'ata wajen kan yace " idan kinga dama ki barshi anan,
ya fad'a yana shigewa d'aki, bata damu da muguwar buguwar datayi ba, ta mik'e zumbar tabi bayanshi,
can k'uryar d'aki ta rab'e k'irjinta na dukan uku-uku da sun tsaida da hayaniyar da sukeyi da sun jiyo sautin dokawar da k'irjinta yake yi.
*******************************
" Gashi can ya fito, Shakira ta fad'a tana l'eka window, tana daga inda take tana iya hango ko'ina na gidan ciki kuwa harda Ammar dake fitowa daga BQ,
ganin ya nufi get yasa Shakira cewa " zai fita fa, jiki na rawa Hajiya Tanya ta mik'e tana fad'in " karki manta point d'inki,
juya ido Shakira tayi irin na gogaggun 'yan duniya tace " idan ni ban manta ba ke ai gashi can zai fita ya barki da naki point d'in,
bata tsaya bawa Shakira amsa ba ta fita, " d'an albarka, Hajiya Tanya ta fad'a tana gyara d'aurin zaninta fuskarta d'auke da annuri,
murmushin dole ya k'ak'aro ya sanyawa fuskarshi yace " ina kwana Hajiya?
Bata amsa gaisuwarshi ba tace " wato tunda nayi maka maganar aure ka shiga wasan b'uya dani ko?
Kanshi ya shafa yana sadda kai k'asa yace " a'a ba haka bane, " to yaya ne?
Murmushi yayi batare dayace komai ba, matsawa tayi kusa dashi ta dafa shi had'i dayin k'asa da sosai da murya tace " abinda yasa nayi maka maganar aure,
saboda ina san na samu nutsuwa da hutu, idan kayi auren koyayane zan samu sauk'in wani abu, matarka zata rage min nauye-nauye da dama, ciki kuwa harda kulawar danake yi maka, kallan dayayi mata ne yasata saurin gyara maganarta "ina nufin ka samu me kular min da kai,
tunda ka rasa kulawar farkon rayuwarka, gefen zaninta ta kunce tana matse hawayen munafurci,
" Allah sarki rayuwa, nayi nadama Ammar, nayi nadamar abubuwan danayi maka a rayuwa, shiyasa nake san gyara laifi na na baya,
cikin nutsuwa da shigar 'ya'yan mutunci Shakira ta fito zata wuce ta gabansu, yi tayi kamar bata san suna wajen ba, saida ta isa gaf dasu,
ta d'age nik'af d'in fuskarta, ta tattare zumbulalen hijabinta dake jan k'asa, ta durk'usa har k'asa tana murmushi tace " ina kwana Yaya?
Ta fad'a kanta k'asa batare data kalle shi, a tak'aice ya amsa da " lafiya, satar kallan juna sukayi ita da Hajiya Tanya, suka kashewa juna ido,
kafin cikin nutsuwa Shakira tace " zan tafi Hajiya, kina da sak'o wajen Mama?
"A'a bani da sak'on komai, ta cikin zanin datake matse ido, ta kyallara ido ta kalli Ammar, ganin ko gezau bayyi ba,
yasata fara dukan k'irjinta tana fad'in " wayyo ni Allah, wayyo rayuwata, kaico na, kaicon duniyata, na cuci kaina Ammar yak'i yarda dani,
mutuwa me tonan asiri da ace Yaseer da Sumayya suna raye da haka bata faru na, na biyewa san zuciya da kyale-kyalen duniya, na cutar da marayan Allah,
k'irjinta ta dafe ta fara hakki had'i da yin luuuu zata zube, da sauri ya tareta suka zube k'asa, bisa gwiwowinshi, jijjigata ya fara yi yana kiran sunanta,
far far Hajiya Tanya take yi kamar me farfad'iyar mutuwa, tana shure-shuren k'afafu,
bak'in cikin idonta ya d'auke sai fari fat, sosai tsoro yayi mugun kama Shakira dan basu shirya haka a plan d'insu ba,
jikinta ya d'auki rawa, ta tallafe Hajiya Tanya tana girgiza ta, Hajiya Tanya ta gane tsoratar da Shakira tayi,
dan haka ta fakaici idon Ammar ta kashe mata ido, baki Shakira ta bud'e had'i da sauke ajiyar zuciya, cikin ranta tana mamaki da al'ajabin Hajiya Tanya,
dan tunda take a duniya da yawon barikinta kaf bata tab'a ganin irinta ba, mitsinin Shakira Hajiya Tanya tayi, wanda yasa Shakira saurin kallanta,
da ido tayi mata alamar da koni jiddarh ban gane abinda take nufi ba, Shakiran ma saida ta d'anyi jimm kafin ta fahimci abinda Hajiya Tanya ke nufi,
kuka ta saka had'i da kifa kanta a jikin Hajiya Tanya tana fad'in " saida Mama tace kibar maganar nan tunda baya so, kinga ke ba lafiya ce ta isheki ba,
ko jiya saida likita yayi miki gargad'i akan d'aga hankalinki da shiga damuwa, tari Hajiya Tanya tayi a galabaice tace,
" dole na shiga damuwa Shakir..., zungurin da Shakira tayi mata ne yasata gane ta kusa b'allo ruwa,
ta gyara maganarta da cewa " dole na damu Basmah...! a razane Ammar ya d'ago kanshi ya kalli Hajiya Tanya, kallanshi ya mayar ga Shakira dake kuka wiwi kamar gaske,
tari ta kumayi a karo na biyu tace " ban sauk'e nauyinshi da Allah ya d'ora min ba, ban fita hakk'inshi ba, ban sauke amanar Yaseer da Sumayya ba,
dan in kyautata mishi na nemo mishi ke, ganin sunanku d'aya da masoyiyarshi *BASMAH*,
haka halayyarku tazo d'aya da Basmanshi dayake so shiyasa nayi mishi sha'awarki amma ya watsa min k'asa a ido saboda bani na haife shi ba,
ta k'arasa maganar tana k'ara sautin kukanta, ta saka gefen zanenta ta face gajina, ba zato Shakira da Hajiya Tanya suka ji Ammar yace " *NA AMINCE ZAN AURE TA* ,
zumbur Shakira ta mik'e dan tun ranar data fara d'ora idonta akan Ammar Allah ya jarrabeta da masifaffiyar sha'awarshi,
haka nan take lab'ewa tana kallanshi, ba wai shi d'in take kallo ba, hantsarshi take kallo, dan duk lokacin da Shakira take kallan Ammar,
idan kabi idonta zakaga babu inda take kallo sai tsakiyar wandonshi, yadda jikinshi yake a murmurd'e yayi gyming jikinshi, gashi bari tas har wani yalo-yalo yake, kun san mahaifiyarshi baturiya ce,
kalar gashin kanshi ja-ja me kamar golden color irin na asalin turawan England, fararen idanuwanshi manya wanda ake kira da sexy lulu eyes su suka k'arawa fuskarshi kyau,
siririn dogon hancin dake tsaye car kamar biri ya k'ara fito da kyanshi, ga madaidaicin bakinshi mai d'auke da jerarrun hak'ora farare tas kamar takarda,
cutie pink lips d'inshi kuwa ba'a magana, "masha Allah Shakira tace a zahiri wanda yasa Ammar kallanta,
saurin jan hannunta Hajiya Tanya tayi da k'arfi ta zaunar da ita, tana yak'e, sai lokacin hankalin Shakira ya dawo jikinta, harara Hajiya Tanya ta watsa mata,
cikin ranta tana fad'in " mayya jarababbiya, a zahiri kuma tayi d'an tari tace " ka yarda da auren Basmah Ammar?
Saida yaji sunan ya ratsa k'irjinshi ya shiga zuciyarshi, ido ya lumshe had'i da d'aga mata kai alamar eh, hannu Hajiya Tanya ta saka ta dafe k'irjinta,
tana fad'in " un un ga abin gudu amma ba wajen zuwa, da sumul nake da nayi rawa da gud'a dan murna,
amma bakomai an biyo ni bashi, nayi ranar bikin, ta k'arasa maganar tana zungurin Shakira, da ido tayi mata alamar tabar wajen,
harara ta zubawa Hajiya Tanya kafin ta mik'e tabar wajen cikin alamun jin kunya, Hajiya Tanya tabi bayanta da kallo tana fad'in " Hmmm Basmah badai kunya ba,
a hankali ta mik'e tana cewa " jeka inda zaka bari na shiga na sanar da iyayenta da Ya Mu'allim, bayyi magana ba yabar wajen,
tabi bayanshi da harara cike da tsana tana fad'in " wallahi badan dukiyar nan ba da tuni nasa an kashe ka, dan duk sanda na kalleka ji nake kamar an watsa min wuta,
da sauri Shakira ta tareta fal da farin ciki tana kod'a Hajiya Tanya " jinjinar ban girma uwar d'akina, dole na sara miki irin wanna tuggu haka?
"Ke kinga yadda kikayi acting kuwa?
"Da a film ne da banga abinda zai hana a baki kyauta ta musamman ba, i salute you uwar makiran dukiya, Shakira ta fad'a tana sara mata,
tureta Hajiya Tanya tayi ta zauna tana fad'in " 'yar duniya ni zakiyiwa dad'in baki?
"Wallahi da gaske nakeyi ba dad'in baki nake yi ba, da kika fad'i ko nayi masifar razana, " kin d'auka mutuwa zanyi?
"Hmmm kedai bari kawai, amma hantar ciki na ta kad'a da gaske, dariya Hajiya Tanya ta saka tana fad'in " mutuwa ba yanzu ba dan ubanki,
sai anci ancinye dani, duniyar nan me dad'i idan na mutu yanzu ai akwai matsala, dariya Shakira ta sanya tace " wato ke kanki kin san k'afarki k'afar shaidan a wuta, dan kafad'a da kafad'a zaki shiga wuta da ibilis,
shigowar Nashwan da Nayan ce ta katse abinda Hajiya Tanya daga fad'ar abinda tayi niyya, cike da d'oki Shakira tace " ya amince,
" to sai me dan ya amince?
Cewar Nayan yana watsa mata uwar harara, basar da maganar tayi dan tasan kishi Nayan yakeyi, numfashi Nashwan ya fitar kafin yace "meye next?
"Fad'awa Ya Mu'allim, muji me zaice uban kinibibi, " ki fad'a mishi mana, baki ta kama tana fad'in " ni Tanya, ai kaine zaka fad'a mishi,
bayyi magana ba ya zaro waya daga aljihu yayi dialing number Ya Mu'allim had'i da saka wayar a hand free yadda kowa zaiji,
da sallama ya amsa wayar, Nashwan ya haida shi cikin ladabi, d'an shiru sukayi kafin Nashwan yace " dama Ammar ne ya samu matar aure,
" Alhamdulillah masha Allah, amma nayi farin ciki, a ina take?
"Anan Kano take, muryar Ya Mu'allim kad'ai zata sanar dake farin cikin dayake ciki, cikin jin dad'in yace " masha Allah, a Kano a ina?
"Ai kusan a kusane ma 'yar k'awar Hajiya Tanya ce, d'an shiru Ya Mu'allim yayi dayasa Hajiya Tanya da Shakira kallan juna,
uwar harara suka zubawa wayar kamar shi d'inne, ya d'an jima baice komai ba, kafin ya nisa yace " kasan bana san abinda zai haifar da matsala,
koya kawo rugujewar d'an sauran zumuncin daya rage, saida Nashwan ya kalli su Hajiya Tanya kafin yace,
" babu komai Abba, dan saida mukayi bincike da nazari sosai akai, yarinyar tana da hankali da nutsuwa sosai,
kuma gidansu akwai tarbiya da dattako, cikin sanyi murya wanda zai tabbatar maka da hankalin Ya Mu'allim bai kwanta da abun ba,
yace " Allah ya tabbatar da alkhairi, idan na bincika sai asaka bikin tare danasu Umar, Nashwan ya amsa cikin ladabi, " oh ni Tanya! na uku a wajen wannan shegen, me nayi mishi haka da zafi daya tsane ni ya sako ni a gaba ya hanani sakat?
"To wallahi sayya gane kuranshi, sayya gane fad'a da aljani ba riba, badai yace dani zayyi takun sak'a ba, idan bai kiyaye ni ba,
fitowa k'ofar gidanshi ma saita gagareshi, idan na k'ulla mishi kitumurmurata zai gane shayi ruwa ne, barni dashi, ta k'arasa maganar tana kwafa,
" ki tsaya asan abinyi ba surutan banza ba, dukda taji haushin maganar da Shakiran ta fad'a mata, bata nuna komai ba tayi murmushi had'i da cinnawa sigari wuta,
ta zuk'a ta busar da iskar, tabisu da kallo d'aya bayan d'aya ta nisa tace " nasan za'ayi haka shiyasa na shiryawa komai,
na riga da na nemi iyayen bogi tuni, wanda wajensu Ya Mu'allim zaije neman auren Shakira, acan kuma zayyi bincikenshi na banza,
inda bazai samu komai ba, sai abinda muka so ya sani, " ban gane ba?
Cewar Shakira tana zare sigarin daga bakin Hajiya Tanya, harga Allah bata san abinda Shakira keyi mata, amma zata shanye harsu cimma burinsu da ita,
su yarda kwallan mangwaro su huta da k'uda, murmushi tayi me d'auke da fassarori da dama tana kallan Shakira tace,
" haya na d'auke su, zasu amsa sunan sune iyayenki, idan yaje wajensu sune zasu bashi aurenki, haka idan yayi bincike za'a sanar dashi abinda muke san ya sani, " idan kuma aka samu matsala daga wajensu daga baya fa?
" Kin tab'a gani na taka waje anga sawon k'afata wajen?
" Jahili, bak'on makirci, wanda bai iya had'a tuggu ba shine zayyi abu yabar shaida a wajen, amma wanda yasan me yake yi, idan yayi abu ko aljani k'arya yake ya iya ganowa,
ni idan nayi kashi waje, nasan kuma na b'ata wajen da kashi bana sake waiwayar wajen har abada, dan haka na gama tsara komai,
da nan nake aiki ta fad'a tana nuna kanta, " ina da lissafi, bazan b'ata abinda na shafe shekaru fiye da talatin ya tafi a banza ba, tun kan a haifi Ammar nake shirya komai..........!
*Kuyi hak'uri a daddafe nake typing bana jin dad'i, nasan akwai typing erros sosai so please manage*