Free chapter · Read without an account

26

by Hauwa A Usman · SAKI RESHE..

26


"Aiki?


Ya fad'a cike da mamaki, " wanne irin aiki?


Bakinta na rawa ta fad'a mishi irin aiyukan da take yi, ashar ya danna had'i da shak'arta ya mak'ureta yana fad'in " a gidana Basmah?


"A gidana kikeyi min wannan iskancin, kakari da k'ok'arin kwace kanta ta shigayi, ta rik'e hannunshi dake wuyanta gam, amma yak'i sakinta, sai da ya tabbatar ta jigata kana ya warb'ar da ita gefe ya furzar da iska me zafi daga bakinshi,

" tunda ke 'yar wahala ce, aiki kike so ki bari zan baki aikinyi, ya fad'a had'i da fincikota ya tura ta d'aki, 

da daddare da zasu fita yawon sharholiyarsu yace " ke shirya dake zamu fita, cikin rashin fahimta tace " ina zamu?


Batare daya kalli inda take ba yace " aikinyi zan baki, muguwar fad'uwa gabanta yayi da k'arfi, ta tsorata sosai amma ta dake tace " bance maka ina neman aikiyi ba, dan haka kuyi tafiyarku ba inda zani,

bayyi mata magana ba, ya fiageta da k'arfi kamar zai b'allata ya nufi waje da ita, turjewa ta farayi had'i da fasa kuka tana fad'in " bazani ba,

bazan biku yawan iskancinku ba, ka kyaleni, bashi da niyyar yin magana saima dannata mota da yayi, ya zagaya ya shiga, 

dukan murfin motar ta farayi da iyakacin k'arfinta tana ihuuun " ka rabu dani nace maka bazani ba, a hasale ya d'auketa da mari,

yana cewa " karki soma, wallahi karki sake ki soma cewa zakiyi min iskanci da taurin kai Basmah, dan wuya zaki sha, dafe kuncinta tayi,

tana jin wani abu na gifta mata saboda zafin mari, a k'ofar Fulbe Villa yayi parking, ya fito ya zagaya ya fisgota daga cikin motar,

d'an kwallinta daya fad'i take k'ok'arin d'auka amma yak'i tsayawa, har ciki ya shigar da ita ya, sai a lokacin ta gane Club ya kawo ta,

sai kad'e-kad'e da raye-raye akeyi, maza da matan wajen kamar tsirara wasu ma a tsiraran suke, wasu nashan shisha, wiwi, sigari, roci, syrub,

yayinda wasu ke kwankwad'ar giya, wasu gam anan cikin mutanen suke neman junansu,

" wa'iyazubillah, ta furta had'i da runtse idonta da k'arfi, maganar Zaman data dira a kunnenta ce tasata saurin bud'e idonta,

tana kallanshi a kid'ime cike da firgice, " ga aikin yi nan tunda wahalar kike so, daga yau anan zaki rink'a yin aiki, aikinki kuwa shine kwashe kwalaben giyar da muka sha,

da kwashe condoms, goge-goge da shawara, ya k'arasa maganar yana hankad'ata, wani irin wulak'antacce kallan tsana take jefa mishi,

zuciyarta ta gama bushewa rak'ayau, kwata-kwata babu d'igon tsoranshi cikin ranta, sai tsantsar tsanarshi dake ingizata data d'auki kwalba d'aya ta kwad'a mishi aka,

" tuf! ta tofa mishi yawo a fuskarshi had'i da nuna mishi yatsa har tana lakuce mishi hanci, idanuwanta da sukayi jajir sun firfito waje,

kamar zaro fad'o saboda bala'i, jikinta sai rawa yake yana b'ari, cike da rashin tsoro da k'ek'ashewar zuciya tace " kaiconka wulak'antacce,

tab'abb'e mushiri, mak'iyin Allah, kayi asara, tunda baka da aiki sai ja da Allah, sai yad'a fasadi da b'arna a doran k'asa, ni dana sha tarbiyya da ilimin addini zaka kalla kace nayi aiki anan?


"Na rasa wad'anda zanyiwa aiki a duniya sai tsinannun Allah, tur dakai da rayuwarka, ina jiye maka tsoron k'arshenka, dan wallahi muddin baka tuba ba,

sai Allah ya wulak'anta ya d'aid'aitaka kafin kabar duniya, wad'anda sukayi iskanci tun iskanci yana iskanci ma ina suke yanzu?


"Duk irin abinda zakayi a duniya daga baya ne dan kafin kai anyi kakanninka a fagen wad'anda sukayi dangaske bakai da kakeyi yinshi da wasa ba, wanne iskanci ne ya rage yanzu a duniya?


"Wanne kalar islanci ne ba'ayi shi ba?


"Babu Zaman, kuda kuke yinshi yanzu kale aka bar muku, tsinta kukeyi, dan an gama iskanci tun a baya, manyan kafiran duniya da suka kafa tarihi,

sunyi abinda zasuyi sunyi sun shud'e, duk abinda zakayi bazaka kai Fir'auna ba, bazaka kai Abhu Jahil ba, bazakai d'an k'aruna ba, duk ina suke yanzu?


"A cikinsu harda wanda yayi da'awar shine Ubangiji, balle kai k'aramin mara kunya, me yawo da guntun iskanci, duk abinda zakayi kayi Allah yana madakata yana jiranka,

ba zato taji ya damk'i kanta ya buga da teburin glass d'in dake gabansu, kanta da teburin suka fashe, jini ya b'alle ta goshinta, taji sosai,

taji buguwar sosai dan saida numfashinta ya d'auke, ta suma a tsaye, azaba tasata yin shiru dole, ya nunata da yatsa yana fad'in " nafi k'arfinki Basmah,

nafi k'arfin 'yar k'aramar rashin kunyarki, na wuce ki tsaya a gabana kina yi min fitsara, kasheki ba wahala zai bani ba,

dan haka ki kama kanki, inba haka ba na baki mamaki, " mamaki?


" Har akwai mamakin daya rage ka bani Zaman bayan gidauniyar mamakin daka shayar dani?


Tayi maganar tana tallafe da kanta, " idan bakyason na b'allaki ki tashi ki fara aikin dana saki, guntun murmushi tayi tana goge jinin dake neman rufe mata ido,

tace " na riga na gama magana kasan mutumin kwarai baya magana biyu, dan haka d'auki duk matakin da kake ganin ya dace,

dan wallahil azim ko zaka kashe ni bazanyiwa 'yan caca da mashayan giya aiki ba, " caca...! caca... Zaman ya fad'a, idonshi kanta, kafin ya d'ora da cewa da kud'in caca nabiya sadakinki,

kallanshi tayi ido cikin ido tana murmushi tace " koda kud'in luwad'i ka biya sadaki na bani da matsala da hakan, tunda na riga nasan kai me matacciyar zuciya ne,

baka iya neman na halak ba, sai dai na Allah ya isa, kuma idan baka sani ba ka sani, babu aure tsakaninmu, ko'a sake ni, ko baka sake ni,

Addinina ya haramta aure tsakanin mace mumina da namiji kafiri, "Basmah ki tashi kiyi aikin dana sakaki, yayi maganar idonshi a rufe,

zuciyarshi ta gama b'aci tuni ranshi ya bashi ya kashe ta, k'ok'arin saita kanshi kawai yake yi, amma Basmah ta kaishi bango, 

" bazan yi, wallahi bazanbi umarninka ba, dan babu biyaya ga abokin halitta wajen sab'awa Ubangiji, dan haka ko zaka bani rayuwata a hannuna bazanyi b...... 

bata k'arasaba ya d'auki d'aya daga cikin kwalaban giyar dake gefenshi ya kwad'a mata aka, ya damk'eta ya jefa saman teburan giya,

ya bita ya d'agota ya shiga dukanta da iya k'arfinshi, idonshi ya rufe saboda b'acin rai ta kunyata shi a idon 'yan barkin dake mugun tsoranshi,

yana dukanta yana zaginta, harta daina motsi jini ya b'alle mata, a k'asa yajata har bolar unguwarsu ya jefata tsakiyar bolar,

ya tsaya kanta yana fad'in " dama albarkacin cikin jikinki kike ci nake zaune dake, tunda ya zube shikenan, amma duk da haka ki sani, matsawar ina raye babu namiji daya isa ya rab'e ki,

balle ya mallakeki, duk namijin da yayi gangancin yin haka saida uwarshi ta haifi wani, harya juya zai tafi ya juya yace " then ki sani sharri nayiwa Safiyyah,

danna rabaku, nemanta nayi tak'i baki had'in kai, shiyasa nayi mata sharrin danasan dole sai kun rabu, duk da bata cikin hayyacinta taji maganganunshi,

a hankali siraran hawaye suka gangaro ta gefen idanuwanta dake lumshe, daga nan bata k'ara sanin inda kanta yake ba.....


Cigaba.....


Asibiti mafi kusa dasu suka kai Basmah, tun daga harabar asibitin suke kwalawa Doctor kira, da sauri Nurse's da Doctor suka nufo su,

basu tsaya tambayar komai ba suka amshi Basmah suka shgar da ita Emergency room, Ammar yabi bayansu yana fad'in " please ku taimaka ni ku ceto rayuwarta,

dan Allah kada ku bari na rasata, ya fad'a kamar wani zararre, murmushi likitan yayi had'i da cewa " in sha Allahu zamuyi iya yinmu, kudai tayamu da addu'a,

sintiri Ammar ya farayi a k'ofar Emergency room d'in hannayenshi duka cikin sumar gashin kanshi, kallo d'aya zakayi mishi kasan yana cikin matsanancin tashin hankali,

ya kasa zaune ko tsaye, bakinshi dake motsi ne zai tabbakar maka da add'a yake, duk wata dak'ik'a dake gotawa tana wucewa ne da nutsuwar Ammar, 

in banda rawa babu abinda jikinshi yake yi, tsoro yayi masifar kamashi, an d'auki lokaci me tsayi a haka, mintina da awowi sun wuce,

wanda idan za'a kashe Ammar bazai ce maka ga iya dad'ewar da akayi ba, hannuwanshi ya dunk'ule ya daki iska, idanuwanshi sunyi jajir kamar gauta,

jijiyoyin kanshi sunyi rad'o-rad'o, kamar zanasu akayi, a hankali likita ya fito yana goge gumi, a kid'ime Ammar ya nufeshi,

har yana tunb'e, "ya jikin nata?


Ajiyar zuciya likita ya sauke wacce tasa gaban Ammar mahaukaciyar fad'uwa, yayi baya dafe da kanshi yana fad'in " no...! no...! please,

a zabure kamar wanda aka tsikara yayi kan likita yaci kwalarshi cikin tsawa yace " kayi min magana, ka fad'a min a wanne hali take?


Jiki a sanyaye su Usman suka dafa kafad'ar Ammar ta baya batare da sun iya surta komai ba, jin sun dafa shi yasashi runtse idonshi da k'arfi,

" muna fatan tana lafiya, sai dai munyi iya yinmu dan ganin mun ceto rayuwarta abun ya gagara......!, kanshi ya soma girgizawa yana ja baya cikin wani irin yanayi,

tamkar wanda ya shekara cikin hauka, ganin yanayin dayake ciki yasa Usman saurin rik'e shi ya zaunar a d'aya daga cikin kujerun dake reception d'in,

kanshi dake barazanar tauwatsewa ya dafe yana fad'in " shikenan na kuma rasata a karo na biyu, na rasata rasawa ta har abada, yayi maganar hawaye na gangaro mishi,

" bafa ina nufin mutuwa tayi ba, baka bari na k'arasa bayanin ba ka datseni, cikin jikinta bai k'arasa fita ba, muddin ana san ceto rayuwarta,

dole a k'arasa cire cikin ayi mata wankin ciki...... bai bari likitan ya k'arasa ba, ya mik'i yana huci kamar zaki yace " to wacce uwar ka tsaya yi?


"Kaje koma meye kayi muddin za'a ceci rayuwarta, murmushi likitan yayi dan yayiwa Ammar uzuri, yace " dole sai mijinta ko mahaifinta sun saka hannu, 

ya fad'a yana mik'a musu takarda, wartar tadarkar Ammar yayi ya saka hannu jikinshi na rawa ya mik'a mishi yace " kuje kuyi koma meye, 

batare da likitan yayi magana ba ya juya.


Shakira tsaye tsakiyar parlour tana ta faman sintiri tana cika tana batsewa sai huci take kamar kububuwa, " wai yau ni Shakira ake wulak'antawa akan wata 'ya mace,

ranar aure na, ranar data kasance ranar daren farko na amma ace mijina yana can asibiti da wata, lalle wannan ko wacece ta taro yak'in hitila na biyu,

ta d'auko dala da gwauran dutse ba gammo, dan wallahi Allah bai yiwa ina ji ina gani a mayar dani bora ba, in my wedding day, my first night, aka wulak'anta ni haka?


Ta fad'a kamar zata tashi sama, baki Hajiya Tanya ta tab'e tana cigaba da gyara farcenta, bakinta d'auke dankaran sigari tace " haka dai, Nayan da Nashwan suka kalli juna, 

a d'an hasale Nayan yace " to ke ina ruwanki?


"Yaje can ya k'arata da bazawararshi me zai dameki?


"Ina tunanin ta kud'i kike yi bata wani wedding day da first night ba, indai burinmu ya cika babu abinda ya shafemu da duk abinda zayyi, ya tattara kayanshi ma ya koma asibiti kacokan da zama gaba d'aya so fucking what?


Itama a d'an hasale tace " amma dai mijina ko?


"Kuma daren farko na ne, dan haka babu abinda ya shafeka aciki, cikin masifa yace " wanne dare ne jemage bai gani ba?


"Saina mutuwarshi, idanko ya kuskura yaga wannan daren daga shi bazai k'ara ganin wani daren ba, cewar Shakira tana watsa mishi kallan banza,

" wanne darere ne baki gani ba Shakira ina zaton ke har daren mutuwar taki ma kin gani? 


" Da kike zumud'in daren farko meye saura da zaki bashi?


"Ke da harta duburarki ake saduwa dake, a razane Shakira ta zaro idanuwa waje cike da tsoro, cikin rawar baki tace " me...me?


"Eh ko karya nayi dadironki baya saduwa dake ta takashinki?


Shiru Shakira tayi cikin ranta tana mamakin yadda akayi Nayan yasan haka, ta tabbatarwa kanta akwai abinda suke shiryawa shida uwarsu abayan fage,

dan haka dole saitabi a hankali ta iya takunta ta kuma saka musu ido, inba haka ba k'ilu zata ja bau, " hmmmm a banza man kare ko yayi tifa d'aya saidai a tsiyayar dashi,

Hajiya tanya ta fad'a cike da rashin kulawa, harara Shakira ta watsa mata tana fad'in " sai dai indan baije hannun hannun arna ko gwari da maguzawa ba,

ba man karen ba, ko karen dan ubanshi dafa za'ayi cinye a shanye romanshi, "ya isa haka please, ba shirmen banza da habaice-habaice ya kamata mu tsayayi ba,

cewar Nashwan kafin ya d'ora da cewa " godiya ya kamata muyiwa Allah daya kawo mana komai cikin sauk'i, " kamar ya?


Suka fad'a a tare, " da Basmah ta dawo mana, kallanshi suke cike da rashin fahimta, idonshi ya juya cike da k'osawa, kana yace " da ba saboda ya rasata ne yak'i karb'ar dukiyarshi ba?


Da ido suke binshi batare dasun amsa ba, " yanzu tunda ta dawo gareshi nasan da gudu zai karb'i dukiyar kodan yajiyar da ita dad'in duniya,

kunga a cikin kaso 100 na aikin da Shakira zatayi an rage 70 dan karb'ar dukiyar a hannunshi bazayyi wuya sosai, akan a shawo kanshi ya karb'a, 

baki Hajiya Tanya ta washe cike da farin ciki da mamaki tace " haka ne kuma fa, yaya akayi banyi wannan tunanin tun farko ba?


Shakira ta watsa mata kallan banza, cikin ranta tace " da kwakwalwar kifin zakiyi tunanin abin arziki?


Kallan da Hajiya Tanya tayi mana ne ya tabbatar mata taji abinda tace, murmushin yak'e tayi had'i da basarwa, " zaki gane baki da yawo Shakira, cewar Hajiya Tanya cikin ranta.


Tunda Ya Mu'allim ya shiga d'aki yake rusgar kuka dan sosai maganganun Ammar sukayi tasiri a zuciya da ranshi, yasan shima yayi kuskure,

" me yasa na kasa cin jarabawata?


"Me yasa ban yarda da k'addarar da Allah ya saukar min ba?


"Meyasa nayi haka bayan nima mutum ne kamar kowa, ban kai wani ba, balle nafi wani?


"Astagfirullah Astagfirullah Allah na tuba ka yafe min, d'an bubbuga k'ofar Umma tayi tana fad'in " Malam lafiya?


Saurin goge hawayenshi yayi ya mik'e ya bud'e mata k'ofa, jikinta a sanyaye ta shigo tana binshi da kallo, ta fuskanci yana cikin damuwa, tana zama kusa dashi tace " kuka yi Malam?


Ta tambayeshi danta gane yayi kuka, tafi kowa sanin halin mijinta, ta yadda koyaya yanayinshi ya canja take ganewa, bayyi niyyar b'oye mata komai ba,

ya sanar da ita duk abinda ke faruwa tun daga farko har k'arshe, hawaye ta share da gefen zaninta tana fad'in " wallahi Malam daurewa kawai nake yi saboda kai,

amma Allah yasani daga ni har yaran nan muna cikin damuwa na rashin sanin takamaiman halin da Basmah take ciki, bai kamata mu yanke hukunci cikin fushi ba,

bai kamata muyi watsi da ita ba, hakan shike kawo sanadiyyar lalacewar mata da dama, yasaka su cikin mummunan hali, wasu daga nan suke shiga karuwanci, wasu sata, fashi da makami, wasu ma k'ungiyar asiri suke shiga,

ta k'arashe maganar tana fashewa da kuka, " ka gani na ganta Malam dan Allah, hak'uri na ya k'are, ta k'ara rushewa da kuka, " tashi muje, Ya Mu'allim ya fad'a yana mik'ewa.


K'arasawarsu Ya Mu'allim da Umma asibitin tayi dai-dai da fitowa da Basmah, Nurses na tura ta a gadon marasa lafiya, 

jikin Ammar na rawa yabi bayansu zuwa d'akin da za'a kwantar da ita, su Umma na biye dasu a baya,

likitan ya kalli Ammar yace " Alhamdulillah munyi nasarar cire cikin jikinta, anyi komai lafiya sai dai kasancewar ta zubar da jini da yawa yasa dole sai anyi mata k'arin jin.....,

tun kafin likitan ya k'arasa bayani Ammar yace " muje a d'ebi nawa zayyi mata, da kallo likitan ya bishi,

Ammar ya gane kallan da likitan kiyi mishi dan haka yace " jini na group O ne, direct lab suka ce, dukda haka saida aka k'ara gwada Ammar aka tabbatar jininshi group O ne,

sannan aka d'iba aka jonawa Basmah, gaba d'ayansu suna zagaye da ita, Ammar, Ya Mu'allim, Umma, Usman, Umar, Aliyu da Abubakar, 

a hankali ta motsa hannunta kafin ta d'aga hannunta marar canola ta dafe goshinta tana yamutsa fuskarta tana salati, gaba d'aya hankalinsu na kanta,

musamman Ammar jikinshi har rawa yake, bai damu dasu Umma na wajen ba, ya isa bakin gadon ya rik'eta gam yana kiran sunanta, 

saukar muryar a kunnenta yasata bud'e idonta a hankali dishi-dishi ta fara gani ta kasa tantance waye shi, a hankali idonta washe sarai a kanshi,

gau farinshi ya shigar mata ido tayi saurin rintse idonta, cikin sanyin murya yana shafa kanta yace " Basmah...! sai da aka d'anyi sakanni kafin yace " bud'e idonki ki ganni,

ni ne AMMAR....! d'inki, me sanki da k'aunarki tun kina zanin goyo, jin kalamanshi tayi kamar a mafarki dan haka tayi saurin bud'e idonta,

suka sauka akanshi a karo na biyu, bata tab'a zaton haka yake ba ko'a mafarki, idonta ta k'ara warewa tana kallanshi sosai,

murmushinshi me narkar da zuciya yayi mata had'i da d'age mata gira d'aya ya nuna mata su Ya Mu'allim da ido, da sauri ta tashi zaune tana murza idonta dan a zatonta mafarki take yi,

d'aya bayan d'aya take binsu da kallo kafin ta tsaida idonta akan Umma da Ya Mu'allim, k'ok'arin mik'ewa ta somayi Ammar yayi saurin mayar da ita, kuka ta saka marasa sauti kasancewar muryarta a dishe take bata fita " Abba Umma.... ta furta bakinta na rawa, a hankali Usman ya zauna kusa da ita,

had'i da rik'e hannunta gam cikin nashi, aiko ta k'ank'ame shi ta k'ara rushewa da matsanancin kuka tana fad'in " kuyi hak'uri ku yafe man,

naga bala'i da masifu kala-kala a rayuwata wad'anda ko a labari da film da littafi ban tab'a jin irinsu ba, nayi *SAKI RESHE....!* Abba dan Allah ka yafe min,

nayi maka alk'awarin ban sake sab'a umarninka har k'arshen rayuwata, Umma dan Allah kiyafe min, Yaya please ban sake sab'a muku,

ta fad'a fad'awa jikinsu, dukkaninsu hawayen sukeyi har Umma da Ya Mu'allim, suma suka rungume ta suna goge hawayensu,

" mun yafe miki duniya da lahira Basmah muma muna fatan Allah ya yafe mana dan muma masu laifi ne, Allah ya yafe mana gaba d'aya,

Ya Mu'allim ya fad'a yana k'ara rungume ta a jikinshi, ta kalli Umma tana kuka wiwi, tace " Umma kema ki yafe min, Umman tayi murmushi hawaye na gangaro mata tace,

" na yafe miki Basmah, ina fatan Allah ya yafe miki, ta juya wajen Yayyanta taja gwiwarta tun kafin tayi magana Usman ya d'agota ya rungumeta,

yana fad'in " i missed you so much lil sis, ta k'ank'ame tana kuka while tana murmushi, Umar, Aliyu da Abubakar suka sunkuya suka rungume ta,

bayan komai ya natsa Usman na zaune bakin gadon kusa da ita, Ammar yayi gyaran murya gaba d'ayansu suka kallanshi, yana sosa k'eya yace " amm....Abba da...dama,

sarai Ya Mu'allim ya gane abinda Ammar yake san fad'a dan haka ya d'an canja fuska, had'i da cewa " naga kamar kana san magana ko?


Kanshi ya shafa tare da sunkuyar da kanshi k'asa yace " Abba dama danaga Basmah bata da idda shine nace ko za'a d'aura auran yau?


Gaba d'ayansu baki suka bud'e suna kallanshi cike da mamaki, musamman Basmah data rasa dalilin dayasa bata san kallanshi,

duk lokacin data kalleshi sai gabanta yayi muguwar fad'uwa, musamman idan akayi rashin sa'a suka had'a ido, fuska Ya Mu'allim ya tsuke yayi kamar baiji abinfa ya fad'a ba,

ganin bashi da niyyar yin magana yasa Ammar sake langwab'ar dakai yace " Abba please mana,

" ka rabu dani Ammar...!, cewar Abba batare daya kalli Ammar ba, da sauri Ammar ya sunkuya kusa da shi ya d'ora hannayenshi saman gwiwar Ya Mu'allim,

yace " ina zan rabu dakai Abba, abari ya huce shike kawo raban wani, tun farko gangancin danayi kenan, Usman yace " kai Bros baka ko bari komai ya lafa ta sake samun sauk'i?


"Kaga ba ruwanka tunda ku bazakuyi min kara ku tambayar Abba ba, sai da na cire kunya nayi magana dakaina, ai ku ya kamata ku ari bakina kuci man albasa,

dannaga baku da niyya shiyasa na magantu, Umar, Aliyu da Abubakar da Usman suka saka dariya had'i da had'a bakin cewa " Abba muna nemarwa d'an uwanmu auren Basmah ,

mik'ewa Ya Mu'allim yayi yana fad'in " ko Ammar ya rasa mata babu abinda zayyi da Basmah, da sauri Ammar ya mik'e had'i da cewa " Abba Basmah ce fa,

Cikin fad'a-fad'a Ya Mu'allim yace " Basmah fa, kai yanzu nan har wani rawar kai da zumud'i kake yi akan macen data gujeka ta barka ta zab'i wani akanka?


"Saida taje ta gane shayi ruwa ne ta dawo kai kuma saboda rashin zuciya zaka kwasa wanda bai san mutuncin kanshi ba,

ka saurara kaji muddin ina da iko dakai bazaka tab'a auren Basmah ba har abada, kabi duk ka rud'e sai rawar jiki kake yi a inda ba'asan mutuncinka ba,

ka ma manta da yau aka d'aura maka aure kabar 'yar mutune acan tana jiranka salan kaja min zagin mutane dana duniya ace dan Basmah 'yata shiyasa nayi haka,

idan kai yaro ne soyayya ta rufe maka ido nina san me nake yi dan haka.......tim Ya Mu'allim yaji k'arar fad'uwar abu, tsayar da maganarshi yayi had'i da juyawa yana kalle-kallen abinda ya fad'i,

"Ammar! ya fad'a a razane yana nufarshi, su Aliyu suka rufar akan Ammar dake zube a k'asa kamar matacce.......

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol