Free chapter · Read without an account
Chapter 8
CI GABAN TATTAUNAWAR ALIYU DA IYAYEN MAIMUNATU.
Aliyu ya ce, “Abba idan har kun amince na yanke hukunci zan nisanta matata da mahaifiyata ina nufin zan kama mata gida Damaturu sai ina zuwa a ɓoye tun da ba mu da nisa, mahaifiyata ba za ta taɓa sani ba, kuma na yi alƙawarin zan kula da Maimunat zan sauke mata dukkanin haƙƙoƙinta da ke kaina, kuma ita ma hakan zai fi mata kwanciyar hankali.”
Bayan ya sauke ajiyar zuciya. “Gaskiya ban yarda da wannan hanyar ba, ba zan raba ka da matarka ba, amma magana ɗaya da zan yi ka shawo kan mahaifiyarka ta yarda da 'ya ta a matsayin surkuwarta.”
Aliyu ya durkusa yana fuskantar Abban Maimunat ya ce, “Abba ka tausaya mana, wallahi Ummata tana da ƙafiya idan har ta nuna ba ta yin abu babu wanda ya isa ya sa ta, tun da abin da za mu yi bai saɓa wa Allah ba ka amince.”
Miƙe wa ya yi ya ce, “Aliyu akwai dangin mahaifiyarka a cikinsu ba za a rasa wanda take jin nauyinsa ba, ka tunkare shi/ta maybe za ka yi nasara. Wannan shi ne shawarar da zan iya ba ka amma batu da ka zo da shi ban amince ba.”
Yana gama furta maganar ya fice.
Aliyu wani irin zufa ne ya karyo masa ya juya kan Umma yana cewa, “Umma don Allah ki rarrashi Abba ki jawo hankalinsa ya karɓi batun da na zo da shi.”
“Aliyu idan har kai kana da ƙarancin tunani to namu mai zurfi ne. Ta ya za mu bar ka ka yi wannan ɗanyen aiki. To Bari ka ji maganar duniya ba ta ɓuya duk yadda ka ɓoye mata wata rana dole ta sani. Idan ta sani me kake tunanin zai biyo baya?”
“Umma wannan maganar daga ni sai ku ne ba wanda zai ji.”
Ita ma miƙewar ta yi ta ce da shi, “Ka je ka yi abin da Abban Maimunat ya ce da kai in har kana son matarka, mu kuma za mu saka ka a addu’a da yardar Allah za ka yi nasara a kanta.”
Ita ma tana furta hakan ta fice. Aliyu cikin sanyin jiki shi ma ya fice.
GIDAN UMMA LAURE
Safinat ta cancaɗa kwalliya ta feshe dukkanin jikinta da turare, mahaifiyarta da ta ganta, ta ce, " 'Yan mata adon gari, irin wannan kwalliya haka kamar wacce za ta wurin gasar sarauniyar kyau."
Wayar Hajiya laure ne ya fara ringing tana dubawa sai ta ga Mus'ab ne ƙira ta ce da Safinat, "Kin ga Yayanki ke ƙira."
Finat na jin haka ta yi tsaki, ta ce, a zuciyarta, “Ba za ka ɓata min budget ba ka ji Yallabai."
Bayan Umma Laure ta ɗaga wayar suka gaisa cikin girmamawa ya ce, "Umma ina buƙatar Finat ta dawo gida yanzu."
Safinat ta zurawa Mahaifiyarta ta ido dan jin abin da zai fito daga bakinta.
Umma Laure ta ce da shi, "Lafiya?"
Ya ce, "Lafiya lau Umma ni dai ta dawo."
Mus'ab na gama faɗin haka ya katse wayar.
Umma Laure ta dubi ɗiyar nata ta ce, "Safinat Yayan ki fa na neman ki, ya ce ki koma yanzu-yanzu."
Ta ce, "Yaya kuma Umma, ta ya ya san ina nan?"
Ta ce, "Au ba ki faɗa masa ke nan za ki zo nan ba?"
"Ban faɗa ba Umma, ni bai ma san ba na gida ba, amma na tabbatar munafukar matarsa ce ta faɗa masa na fita."
Hajiya Laure sake baki ta yi tana kallon ɗiyarta, ta ce, "To na fara fahimtar wani abu a lamarin, amma kin san meye kinyi sauri ba yanzu ya kamata ki fara ba, sai sun shiga hannu tukun."
Ta ce, "Umma ke nan me ya rage?"
“Ni na fi so ki shiga jikinta ki nuna mata kina yin ta, amma sai kina mata zagon ƙasa.”
“Umma zuciyata ta tsane ta, sai isa ba za ta iya yi mata abin da kika buƙata ba, ni ina da yaƙinin kina zuwa wurin boka zan samu kan Mus’ab, wanne biyayya zan mata, na baya ma da na yi ina nadamar yi.”
“Eh kuma fa gaskiya ce, ai kishiya ma ba abokiyar zaman lafiya ba ce.”
Safinat ta fuskanci mahaifiyarta ta ce, "Umma yanzu ya za a yi da batun Yaya, ga kuma zuwa wurin Alhaji."
Ta taɓe baki "Wa yake ta Yaya, zai ba mu 100k a yanzu nan take ne?"
“Ina Umma ai ko 10k ba zai fito a hannunsa ba, amma da matarsa ce ko 1 million ta buƙata zai dire mata."
“Manta da shi, zan kira shi a waya ke dai je wurin Alhaji ki yakato mana Allah ya bada sa'a"
Safina ƙyalƙyalewa da dariya ta yi, ba tare da ta ce komai, ta sa kai ta fice.
Bayan ficewar Finat ce, Hajiya Laure ta yi dialing number Mus'ab yana gani ya yi picking ya mata sallama, bayan ta amsa ne ta ce, "Mus'ab kana ji na ba na jin daɗi, Safinat ba za ta dawo gida ba har sai ta gama mini aiki saboda haka ka yi hakuri."
"Umma don Allah ki yi hakuri ta dawo ina da muhimmin magana da ita ne, ko gida zan yi wa su Umma waya su turo wata ta yi miki aiki."
"Mus'ab ni da kai shin waye babba? Shin mahaifiyarka idan ta buƙaci ka bar ma ta 'yar ka na wani lokaci za ka furta mata abin da ka faɗa mini? Shin ban san da 'ya’yan wasu ba ne sai ka faɗa mini. To ka kiyaye ni, bakinka ya san abubuwan da zai dinga furtawa."
"Allah ya ba ki hakuri Allah ya huci zuciyarki."
"Kai ka san wannan kuma."
Umma Laure ta katse wayar.
Bayan ta ajeye wayar ne ta ce, "Yaron nan ina ga alama kana takurawa yarinyar nan to ka fita a idona na rufe. Idan ba za ka janye takurarka gare ta ba, tabbas za mu fara takun saƙa. Yaran yanzu suna son takura ne aka faɗa ma, ina daf da shata maka layi."
Umma Laure ta mike ta nufi kitchen.
Safinat na fita ta tsayar da a daidaita sahu (keke napep) ba a dire ta a ko ina ba sai a harabar hotel ta miƙawa mai a daidaita sahu kuɗinsa ta shige dama already ta san a room da yake ta gama da ma'aikatan ta nufi sashensa tana nocking a ka ce da ita, shigo tana buɗewa ta ga Alhaji daga singlet sai gajeren wando yana ganinta ya fara washe baki, yanayin da ta gan shi ya sa ta ji wani iri ta yi saurin kawar da fuskarta.
Alhaji ya fara washe baki yana cewa, "My baby have a seat." Yana mata nuni da wata kujera.
Safinat ba tare da ta kalle sa ba ta ce da shi, "Ba zama ya kawo ni ba, kai dai kawai miƙo abin da muka yi da kai za ka ba ni."
Murmushi ya yi ya ce, "Ikon Allah, ba gaisawa ma kenan."
"Na fa faɗa maka ina tare da mara lafiya, Please dont waste my time."
“Tabbas kina tare da mara lafiya, but irin wannan cancaɗa kwalliya da kika yi ya tabbatar mini da jikin na ta bai yi worst ba, da ya yi worst a birkice za ki zo gare ni, saboda haka sai kinyi wasting time da ni for 3 to 5 hours sannan za ki samu 100k."
A wannan gaɓar ne Safinat ta waigo ta fuskance shi cike da mamaki ta ce da shi, “Ban fahimce ka ba, me kake nufi?."
“Da yaren da kike ji na yi magana. Amma ba damuwa zan yi miki sharhi, ina nufin ba zan iya ba ki 100k ba sai na amshi virgin ɗin ki, idan kin amince fine idan kin ƙi you are free to go kin yi asarar 100k."
Safinat furucinsa ya razanata da mamaki take kallonsa don ko a mafarki ba ta taɓa tunanin zai zo mata da irin wannan maganar ba, da girmansa ga kuma shekaru sun miƙa, siffarsa idan ka gani za ka jera shi a layin dattijan arziƙi kuma kamalalle.
"Ya kika yi shiru, me kike shawarta wa?" Abin da ya ce da ita.
Sunkuyar da kanta ta yi cikin tsarkewar murya ta ce, "Alhaji don Allah ka janye wannan ƙudirin, tun da nake a rayuwata ban taɓa yin zina ba. Ina dai yin shashanci ne kawai.”
Cikin ɓacin rai ya ce, “Me ye marabar dambe da faɗa. Yanzun ma shashancin nake buƙata mu yi idan kuma ba za ki yi ba kina iya tafiya, Allah ya haɗa ki da wani ɗan asara ya ba ki ba tare da ya mora ba, amma ni Alhaji Tanimu ba a cin kuɗina a banza."
Safinat shiru ta yi na wasu daƙiƙu, cikin sanyayyiyar murya ta ce da shi, "Na amince."
Ya ce, "Yauwa ko ke fa, ai na san ke 'yar hannu ce, kawai dai kina so ki ɗan nuna mini kina fa da sauran mutunci, dama haka kuke nuna wa namiji a farko.”
Ta ce, "Ni ba 'yar hannu ba ce, kai ne dai namiji na farko da za ka fara lalata mini rayuwa.”
“Komai ki ce game da ni, amma ki sani 100k ba karamin kuɗi ba ne 5hrs za mu yi."
ALIYU DA MAHAIFIYARSA.
Aliyu durkushe yake a gaban Ummansa ta ce,
“Aliyu ka nuna mini ban isa da kai ba ko?”
"Kamar yaya? Haba Umma isar taki ce ma ta sa duk abin da kika yi mini umurni nake biyayya wajen yi.”
“Ina ban isa da kai ba Aliyu da na isa ba za ka kai ƙara na ba, wurin kawu Musa ba, a kan hukuncin da nazartar a kanka.”
“Umma ki yi haƙuri da ma……”
Cikin tsiwa ta ce da shi, “Rufe mini baki! Saboda ina jin nauyinsa na ce na amince da lamarinka, amma ka sani a zahiri a zuciyata ban amince ba, yanzu zaɓi ya rage gare ka, ka bi son zuciyarka ka mayar da matarka amma ka sani babu ni babu kai, kuma har na mutu ba zan daina fushi da kai ba, ka yi mini biyayya kuma ka haƙura da matarka. Ta shi ka ba ni wuri.”
SAFINAT DA ALHAJI.
Safina ta ce a zuciyarta “Wannan bawan Allah alamu ya nuna babu mutunci a tattare da shi.”
Shi ya katse mata maganar zuci da cewa, “Ina sauraronki.”
"Haba Alhaji na fa ce maka da mara lafiya muke, kuma idan ba a ajeye kuɗin nan ba sun ce ba za su taɓa ta ba, ya kamata ka yi min uzuri ka rage awannin."
Ya kurɓi ruwan tea da ke gabansa. "A gaskiya a wannan ɓangare ba na uzuri, muddin zan rage awanni kuɗi ma za su ragu. Me ruwanki da awanni ki yi duba kawai da kuɗi da shi fa za ki yi solving problem naki mahaifiyarki ta samu lafiya. Ya kamata mu bar jayayya mu yi abin da ya dace.”
Safinat, tuni ta fara cire ɗan kunnaye da awarwaraye da tsarka, ya ce, "Ko ke fa, abin da ya dace ki yi dama tuntuni.”
GIDANSU MAIMUNATU
Aliyu ya koma wurin surukinsa ya shaida masa duk abin da ya waƙana tsakaninsa da mahaifiyarsa.
Mahaifin Maimunatu ya sauke gauron numfashi. “Aliyu tun da haka ya kasance ni a ganina ka haƙura ka yi ma mahaifiyarka biyayya ka san girman iyaye.”
Cikin rarraunar murya ya ce, “Abba tabbas biyayya ma iyaye wajibi ne, amma ka sani idan na yi mata biyayya rayuwar da zan jefa kaina a cikin saɓa mata ya fi sauki. Don wallahi ba zan iya rabuwa da matata.”
“Kai Aliyu me ya sa ba ka fahimtar abin da kake so ka fahimta ne. Ba za ka iya rabuwa da matarka ba idan mutuwa ta ɗauke ta ya za ka yi? Kai ba Musulmi ba ne ba za ka karɓi ƙaddara ba."
Aliyu ya goge zufa da yake da handkchief, "Abba idan mutuwa ce zan karɓi dangana saboda nasan ba ta nan, amma yanzu ina ji ina gani muna son junanmu da matata a raba mu ba zan iya ba. Ni Musulmi ne na yarda da ƙaddara amma ƙaddarar rabuwa da Maimunatu za a iya sauyata ta koma ƙaddarar Allah ya kuma haɗawa."
Alhaji ya miƙe, "Aliyu ka fara zarewa."
Aliyu ya ce, "Abba, ba zarewar da na yi kalau nake ka koma ka zauna mu tattauna. Don Allah Abba ka tausaya mana ni da Maimunat muna kaunar junanmu, raba mu zai haifar da na dama.”
“Aliyu ba zan yi abin da kake so fa.”
“Shi ke nan Abba, gobe ka zo jana'izata, zan kashe kaina ba zan iya rayuwa ba, muddin Maimunat tana numfashi.”
Maimunat duk hirar nan da ake tana saurararsu tana jin kalmar mutuwa, ba ta san lokacin da ta shige tana cewa,
“Aliyu muddin ka kashe kanka ni ma zan kashe kaina. Ni da kai mun san babban laifi ne mutum ya kashe kansa da kansa, amma iyayenmu sune silar faruwar hakan Allah zai tuhume su domin suna da damar amince mana da yin abin da bai saɓa wa umurnin Allah ba, amma sun ƙi.” Ta fashe da kuka, "Abba ni macece mai kunya amma yau na zare kunyar na furta abin da ban taɓa tunanin zan iya furta shi a gabanka ba ya kamata ka yi na'am da abin da ya zo da shi."
Tana gama furta hakan ta bar wajen. Alhaji ya tsirawa silin ido yana ta'ajibi.
SAFINAT DA ALHAJI A ƊAKIN HOTEL
Alhaji ya kyalkyale da dariya ya ce da Safinat, “Ba ni wayarki.”
Safinat ta miƙa masa, ya yi switch off, ya dube ta ya ce, "Sai dai ki yi haƙuri wayarki sai after 5hrs za a kunna haka tsarina yake."
Ta ce, “Don Allah, da ka bar mini wayata a kunne sai ka sa a silent."
Cikin tsiwa ya ce, "Safinat don Allah in har ba za ki iya ba ki fice mini da gani.”
“Abin bai kai ga haka ba, Allah ya huci zuciyarka.”
“Ke fa kika kawo kanki ba ni na kawo ki ba. Dole ki yi accepting na duk abin da na zo da shi.”
Tsaki ya yi ya ɗauki wayar shi ya kashe ya ajeye a gefe.
Alhaji Tanimu ya duba agogo ya ce, "Ya kamata ke ma ki duba time ba cuta ba cutarwa 5hrs na yi haƙƙinki ya sauka."
Safinat ba ta ce kanzil ba kawai ta ba shi kanta da ya yi abin da ya yi niyya.
WANNE HALI HAJIYA LAURE KE CIKI?
Hajiya Laure hankali ya tashi ta ka sa tsugunne ta ka sa tsaye sai safa da marwa take Safinat ba ta dawo ba har ana kiraye-kirayen Salla tana kuma try number a na cewa currently switch off.
Ta ce, "Ni Lauratu na shiga uku! Ko dai Safinat da ɗan yankan kai ta haɗu daga zuwa karɓo kuɗi shiru, awanni nawa har yanzu ba ta iso ba. Ga number ta baya shiga, yau idan a ka tuhume ni ina Safinat wanne amsa na tanada zan faɗa, lallai kwaɗayi mabuɗin wahala ne." Ta sharce gumin da ya karyo mata a saman goshi.
ALHAJI DA SAFINAT
Alhaji sai da ya yi 5hrs kamar yadda ya ce sannan ya bar Finat, ta sauka gado da niyyar shiga toilet ya dube ta ya ce, "Ina kuma za ki nufa?"
Ta ce, "Zan je na yi wanka mana."
Ya dube ta sama da ƙasa a wulakance sannan ya ce, "Ni duk mace da na yi sex da ita a ƙa'ida ta a gidan su take wankan janaba ba.”
"Haba Alhaji...."
Ya miƙe cikin ɗaga murya ya ce, "Dakata yarinya ban gaji mutunci ba fa, yanzu sai na juya miki kamanni a baya ina ɗan biye miki saboda ina kwaɗayinki yanzu kuwa na ci moriyar ganga sai na lakaɗi jaka ki taya mahaifiyarki jinya idan har da gasken kike ba ta da lafiya."
Ya watso mata kayanta a fuskarta ya ce, "Yi sauri ki sanya su stupid girl kuma ki ɓace mini da gani."
Finat da ta fahimci da gaske yake zai iya yi mata rashin mutunci ta ɗauki kayanta ta sanya ya watso mata 100k a fuskanta ya ce, "Ga tsiyarki idan da gaske Umma ba lafiya a kai wa doctor idan ma karya kike ni dai na ba ki haƙƙinki ki ba ni wuri."
Murmushi ya yi ya ci gaba da cewa, , "A duk ranar da talaucinki ya ƙara motsawa kina iya tuntuɓa ta zan yi zan biya, don kina da test."
Ita dai ba ta ba shi amsa ba ta gama tsince kuɗinta ta zuba a jaka ta yafa mayafinta za ta fice, ya ce, "Sweetheart babu bye-bye ne?”
Safinat ko waiwayarsa ba ta yi ba ta fice.
Ya ƙyalƙyale ya dariya ya ce, "Yarinya ke ce da asara, just ko da hot kiss ki yi a ba ki 2k kin ƙi asararki.”
Alhaji kyakkyata dariya yake bayan fitarta ya ce, "Ga ni wawa in ba ki 100k a banza, sa'a ta ma kika yi ni a 20k ma 24hrs a ke yi mini, ke ma don yau na farko ne, amma next time in kin kuma zuwa farashinki ya faɗi ƙasa wanwar."
Alhaji ya shige toilet ya yi wanka.
MAIMUNATU DA ALIYU
Abban Maimunat ya ƙira ta, “Maimunatu dawo."
Ta dawo kanta a ƙasa, ya sauke ajiyar zuciya, ya ce, " Na amince Allah ya datar da mu. Allah ya sa hakan da za ku yi ya zama alheri, Allah ya ba ku zaman lafiya Allah ya karkato da hankalin mahaifiyarka ta fahimci daidai ina yi muku fatan alheri.”
Ya juya ya kalli Aliyu, “A duk lokacin da ka gama shirye-shiryenka ka zo ka ɗauki matarka. Allah ya ba ku zaman lafiya.”
Jin kalamansa suka kalli junansu suna murmushi.
Aliyu ya durƙusa har ƙasa yana godiya
Alhaji ya murmushi ya yi ya fice ya bar su a zuciyarsa ya ce, “Wannan soyayyar taku sai Allah, bai kamata ana shiga tsakaninku ba.”
Bayan fitarsa Aliyu ya yi sujudush shukur bayan ya miƙe ya juyo yana fuskantar Maimunat ya ce, “My wife ya kamata ke ma ki nuna wa Allah godiyarki”
Ta jefe shi da muguwar harara, "Ba sai ka faɗa ko ka sani ba, na fi ka sanin yin haka, Abban Teema ka yi mini babban laifi wanda da wuya ka samu yafiyata, ƙirarin za ka hallaka kanka ne kawai ya kai ni fansarka a wurin Abba, ba wai don ina yin ka ba.”
Tana gama faɗa ta sa kai za ta fice, ya ce da ita, “My heart beat don Allah ki tsaya ki sanar da ni laifina.”
Tsaki ta yi ta fice ba tare da ta ba shi amsa ba.
Aliyu ya dafa kansa a bango yana cewa, “Na kashe wannan wutar, ga kuma wata wutar ta kuma ruruwa. Wanne laifi na yi wa Maimunat wanda ban san da shi ba?”
BAYAN FICEWAR SAFINAT
Safinat da ta fice zuciyarta cike da taƙaicin irin rashin mutuncin da Alhaji Tanimu ya yi mata tana tsaye a bakin titi tana maganar zuci tana cewa, "Tabbas Alhaji ya cika mara mutunci ka gama fasikancinka da ni buƙatarka ta biya ka wulakanta ni, ba laifinka ba ni na kai kaina wurin ka.”
Murmushi ta yi ta ce, "Duk fa akan na samu damar mallakar Mus'ab na yi haka, ba damuwa in har zan mallake ka Mus'ab zan yi abin da ya fi na yau, zan kuma jure duk wulakanci da cin mutuncin da za a yi mini."
Adaidaita sahu (keke napep) ta hango ta tsayar da shi ta ce, "Gomari airport za ka kai ni."
Ya ce, "Ki shiga."
Safinat ta shiga ta zauna mai a daidaita sahu ya ja suka tafi.
Hajiya Laure ta gagara yin salla sai zagaye gida take ta jiyo sallama tana hango Finat ta zo a guje ta ce, "Alhamdulillahi Safinat, ina kika shiga? Na gama tsorata fa."
Safinat, ta miƙa mata jaka, Hajiya Laure ta fara jan ZIP tana cewa, "Allah dai ya sa buƙata ta biya."
Umma Laure tana buɗewa da ta ga kuɗi ta ce, "To da sauki tunda na ga bugun Abuja ga kuma kin dawo gida lafiya, gaskiya ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu."
Ita dai Finat ba uffan kawai ta shige toilet ta yi wanka tare da alwala ta gabatar da salla.
Bayan ta idar da sallar ne Ummanta ta ce da ita, "Safinat me ya sa tunda kika dawo na ganki a sanyaye ina dai fatan lafiya?"
Safinat ta ce, "Kalau Umma, ba komai."
Ta ce, "To ai shi ke nan ga abinci ki ci."
Ta ce, "Na koshi."
Hajiya Laure ta ce, "Kai, kar ki ce kin ci kaji a wajen Alhaji."
Ta yamutsa fuska, "Umma kenan ni kam kaina ciwo yake ina buƙatar tafiya gida."
"To sannu Allah ya sauwake."