Free chapter · Read without an account

Chapter 9

by Ummulkhair Abba Muhammad · MIJIN MACE ƊAYA PART ONE

ALIYU YA SHIGA DAMUWA



  Aliyu ya kira Maimunat ba adadi ba ta ɗaga ba, ya shiga damuwa sosai, zaune yake a ɗakin mahaifiyarsa da abinci a gabansa ko buɗe wa bai yi ba. Da ya duba saman gado sai ya hango kamar kayan shopping na haihuwa da ya yi wa Maimunatu cike da mamaki ya ce, "Mama bisa gadonki kamar kayan shopping da na yi wa Maimunatu ba ta tafi da shi ba dama?"

 "Na ba ta kala biyu sun ishe ta ai ba cika maka gida za ta yi da yara ba da za ka sayo uban kayan nan ka ba ta, kullum ina hana ka almubazzaranci ba ka ji."

 "Umma, wannan ba almubazzaranci ba ne, to yanzu mene ne ribar hakan ga kaya a ajiye."

 "Ribar shi ne zan sayar da su."

 Ya haɗa kai da guiwa bai kuma cewa kanzil ba.



 Ta dube shi ta ce, “Na fuskanci tun da na raba ka da matarka ka saka wa rayuwarka damuwa, to damuwa ko za ta kashe ka sai dai ta kashe ka, kai da matsiyaciyar matar nan har abada. Kuma wallahi ka kuma yin wani shopping ka kai mata ban yafe ba..”


 “Mama ni ba rabuwa da ita ba ne ke sani damuwa, ba na jin daɗi ne.”


 Ta yatsina fuska “Oho dai, ga abincinka idan ka ga dama ka ci, idan ba ka dama ka shekara ba ka ci ba, kai ba ba karamin yaro ba ne da zan tilasta ka sai ka ci.”


 Aliyu ya tashi rai a ɓace ya fice ya bar mata ɗakin. Ta bi shi da kallo ta ce, "Ba za ka fahimci na yi maka gata ba sai arzikinka ya dinga haɓaka."

 Aliyu bayan ya koma ɗakinsa ya kwanta a gado yana kallon silin ya ce, "Allah sarki matata ashe Mama ta karɓi shopping da na yi miki amma ba ki faɗa mini ba. Da ban gani da idona ba ko shekara dubu za a yi ba za ki faɗa ba. Ka kyautatawa iyalinka ma ya zama matsala wurin Mama. Gaskiya Mama ba zan miki biyayya ba ko da ban mayar da aurena da Maimunatu ba har ta haifi abin da ke cikinta haƙƙinta na kaina. Ballantana da aure zan kyautata mata kuma ina da tabbacin Allah ba zai kama ni da fushinki ba."

 

 UMMA LAURE MAI IDON CIN NAIRA



 Umma Laure ta ciro kuɗin jakar gaba ɗaya, tana gani tana murmushi ta ce, "Safinat bari na shiga ɗaka ko da gudan 100 na ba ki ki yi kuɗin mota."



 Ta ce, "Umma ni da nake buƙatar 10k a kuɗin da na kawo."



 Ta zaro ido, "Ke Safinatu, kin san yadda boka mai aiki da cikawa yake tatsar kuɗi kuwa? Ba na tunanin abin da kika kawo ma zai kai labari."



 Umma Laure ta shige ɗaka sai ga ta da ₦100 ta ce, "Kin yi sa'a fa gaskiya banyi zaton ma zan samu 100 ba karɓa ki tafi."


  Safinat ta miƙa hannu ta karɓa.


 Ta ce, "Ba komai Umma ai ni in idan zan mallaki Mus'ab ko ba 100 a kafa ma na tafi gida.”


  “ Mus'ab naki ne, mijinki ne, ke ce uwar 'ya'yansa kina shiga gidansa za ki fara zazzaga 'ya’yan duk maza, ki gaje gidan baki ɗaya.”


 Feenah ta rangaɗa guɗa saboda maganar Ummanta ya mata daɗi, “Umma maganarki har ya ya sa ciwon kai na ya gushe.”


 “Saboda kin ji magana mai daɗi ko.”


 Ta ɗan sosa ƙeya, “ Umma ina tsoron koma wa gida saboda Yaya kin san halinsa.”



  “Na kira shi a waya ba abin da zai miki.”


  Safinat ta yafa gyalenta tana daf da za ta fice Ummanta ta ce da ita,


 “Safinat gobe idan na dawo daga wurin bokan zan kira ki da ki zo nan.”


 “Umma yaya zai bar ni kuwa?”



  “Dolen shi ni da kaina zan kira shi na ce ina buƙatar ganinki ai bai isa ya musa min ba.”


   “To shi ke nan Ummata, Allah ya kai ki lafiya ya dawo da ke lafiya, Allah ya ba mu ikon cimma burin mu.

 

Bayan ta fice ne ta tsaya a bakin titi ba tare da ɓata lokaci ba ta tsayar da a daidaita sahu (keke napep) ta ce da shi,. “Zan sauka a Maduganari by pass.”

  “Ki shiga.” Abin da ya ce da ita kenan.


  Safinat na zama, ta cire handset nata ta kira Habib, “Hello Baby na san ka yi ta try number ta ko?”


  “Eh mana, me ya faru ne?”


 “ Shutdown ya yi ga ba wuta gidan Umma na bayar da chargy sai yanzu na karɓa. Ita kuma Mummyna wayar nata ya lalace.”


  “Okay sai yanzu ki ce za ki koma gida?”


 “Eh Sweetheart.”


 “To bari na zo na kai ki.”


  “Na hau a daidaita sahu (keke napep) yanzu haka na kusa gida.”


 “To ai shi ke nan safe trip.”


 “Thank you dear.”



 “ Bye my baby i love you.”


 Ta mayar masa da “I love you too darling.” Ta katse wayar.

 

 GIDAN MUS'AB


 Mus'ab ya gaji da zaman bedroom ya fito parlour domin zama ya hango matarsa a zaune dirshan ta yi tagumi tana kuka.


 Shi ko Mus'ab ko a jikinsa bisa yanayin da take ciki, wani waje ya nema ya zauna, bayan zamansa ne ta miƙe ta zo gare sa, tana dunkaro inda ya ke ya fara yunkurin mikewa, zai bar wajen, da ta fahimci haka ta fara magana tana cewa, 


 “Mijin mace ɗaya, ba don ni ba don Allah da kuma soyayyar da kake yiwa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kuma darajar iyayenka nake so ka saurare ni.”

  

 Mus'ab na jin haka ya koma ya zauna, ba tare da ya ce komai ba, domin shi a rayuwarsa ko mene ne idan aka sa Allah da Manzonsa da kuma iyaye an gama da shi zai saurara idan na haƙura ne ma zai yi hakuri, sai isa Hafsy a duk lokacin da suka samu saɓani da Mus'ab salon da take bi ke nan don shawo kan mijnta.

  


 Guiwowinta a ƙasa ta dafa mijinta ta fara magana cike da nutsuwa da nadama tana cewa:


“ Mijina, ganinka cikin fushi da damuwa shi ne abu mafi muni da na tsana a rayuwata. Tabbas na yi kuskure wajen yi maka ƙarya, a tunanina yin hakan gyara ne, amma sai ya kasance saɓanin haka. Ka yafe mini tuba nake.”



  Mus’ab numfashi ya sauke ya ce, “Kina nufin Safinat ba da izninki ta fita ba?”



 “Eh wallahi MIJIN MACE ƊAYA ba da iznina ba, ta faɗa mini amma na hana ta, na yi maka ƙarya ne saboda kar laifuffukanta su yi yawa a wurin ka.”


 “Ga shi ke kin jawo wa kanki laifuka da fushin miji har ya furta miki abubuwan da ba su dace ba. Na ji wannan, ya batun shiga da take? Kamar yadda ta faɗa haka ne?


 “Shi ma ba haka muka yi da ita ba, yadda ka faɗa ni ma haka na faɗa mata, a take ta nuna mini ta amince, ashe ita shigo-shigo ba zurfi ne ta yi mini, Allah shi ne shaida idan har haka na faɗa mata ya Allah ka haramta mini aljannarka ka hana ni jin daɗi na duniya.”

“ Is okay my one and only an yafe miki, lamarin ne ya zo mini a ruɗe, wuni na yi ina mamaki. Lallai yarinyar nan ta iya kitsa munafurci.”



 Murmushi ta yi na jin daɗi mijinta ya fahimce ta "Ina godiya Allah ya ƙara girma da ɗaukaka. Allah ya kawar mana da fitina."


  "Ta ɗaga hannuwanta biyu sama tana cewa,  "Ya Allah ina gode maka da ka arzurta ni da miji mai fahimta. Ina kuma gode maka da ka sa muka fahimci juna ni da mijina cikin sauki.'




 MAIMUNATU



 Maimunat na zaune ta ji shigar saƙo wayarta tana duba wa sai ta ga Aliyu ne yana cewa da ita, "My dear kina hukunta ni da laifin da ban san da shi ba, to ki sani har an yi admitting na a asibiti saboda damuwarki. Yanzu saboda na ji ɗan relief ne ma ki ga saƙona. Ya Allah Idan har matata ba za ta daina fushi da ni ba ka ɗauki rayuwata da wannan rayuwar."


  Hannunta ne ya fara ƙarƙarwa da ta gama karanta sakon.


 "Ba za ka mutu ba Daddyn Teema."

 Cewar Maimunat a take ta yi try number shi yana gani ya ɗaga.

Bayan ta gaishe shi da yi masa ya jiki ta ce da shi;


 "My husband ka yi haƙuri bisa abin da na yi maka, ban taɓa tunanin abin da na yi zai jefa ka a irin wannan halin ba. A wanne asibitin kake na zo gare ka?"


 Sanyi ya ji a ransa, ya ce, "Kar ki damu ba sai kin zo ba, dare ya yi. Jin kalamankin nan ma ya gamsar da ni, na ji daɗi a raina sauki zai samu tun da wacce nake bege ta dawo gare ni."


 "Ni ka faɗa mini asibitin, idan ban gan ka ba zan iya runtsawa ba, ba daren da ya yi."


Ya numfasa "Shi ke nan, ina teaching hospital, Idan kika shigo ki yi mini waya Umar shi ne a kaina zai zo ya ɗauke ki."


 Ta amsa da to ta katse wayar ta sanar da iyayenta, da sun ƙi amincewa ta marairaice tare da magiya.


 "Amma kin san idan kuka haɗu da mahaifiyarsa da matsala." Cewar mahaifinta


 "Abba Umar ne a kansa haka ya faɗa mini.”



"To shi ke nan, kar ki daɗe, a dawo lafiya "


 "In sha Allah, na gode."


  Ta miƙe ta fice sai asibiti.


  GIDAN MUS'AB


   Mus'ab bayan ya yi shiru da ba zai wuce daƙiƙa ba ya sauke numfashi, daga nan ya ba wa matarsa labarin halin da ya ga Safinat a ciki ba tare da ya ɓoye mata komai ba.





Hafsy labarin ya tsuma ta ta ce, "Tabbas ɗan yau sai Allah one and only duk ƙoƙarin mu a kanta. Ni kam ina tunanin 'yar Aunt akwai masu hure mata kunne."



  Yana mai wasa da yatsun hannunta ya ce,  "Yau zan yi maganinta. Abin da nake so da ke duk wani hukunci da zan zartarwa Safinat idan ta dawo kar ki ce kanzil a kai ki bar ni da ita."


 Shiru ta yi na ɗan sakwanni, "In sha Allah zan yi abin da ka buƙata, amma na san kana cikin fushi ban da duka a yi mata nasiha."


   "Idan ta ɓata ta mini rai ko ta yi ƙoƙarin yi mini ƙarya, dole duka ya biyo baya saboda na san halin taurin kanta."



 GIDAN HAJIYA LAURE



 Kiran Hajiya Laure ce ya gani ya ɗaga wayar ta ce da shi, "Dama a kan Safinat ce, tana tsoro ta yi laifi ta fice ba tare da izninka ba, don Allah kar ka yi mata wani abu yanzu haka tana kan hanya."

 " Ba damuwa Umma ba dai tana kan hanya ba, komai ya wuce."

 "Yawwa ɗan albarka ka gaishe da Madam."  "To za ta ji." Ta katse wayar.


 Juyawa ya yi ya dubi matarsa ya ce da ita, “Honey a gaskiya ku mata ba kuna da matsala, 'yar ta ta yi laifi, tana ba da kashedin kar a dakar mata ɗiyarta.”


 “Mata kar ka yi jama'u ba dukkaninsu halin su ya zama ɗaya ba. Ita ɗin ma ba na tunanin tana da masaniyar abubuwan da Safinat take, kai ma ba don ka gani da idonka idan wani ne ya faɗa maka za ka ƙaryata..”


“ Haka ne, amma idan wanda na aminta ne ya zo mini da maganar zan gaskanta. Ba ki san Umma Laure ba wallahi ko ta sani ba za ta damu ba, ni fa idan aka ce tana daga cikin masu hure mata kunne ba zan musa ba. ”

 


  Sallamar Safinat ce ya sanya su kallon bakin kofar, Hafsy ce ta amsa mata amma shi Mus'ab ko kallonta bai yi ba.

 Ita ma da ta shiga ko gaishe su ba ta yi ba, ta tura baki tana cika tana batsewa ta nufi sashenta, abin ya ba su mamaki suka kalli juna Hafsat ta miƙe, ya dube ta ya ce,

 “Ina za ki?”


 Cikin sanyayyir murya ta ce da shi, “Zan kira wo ta ne mijin mace ɗaya.”

Mus’ab cikin fushi ya ce da Hafsat, “Ina mai ba ki umurnin ki zauna.”


  Wuri ta nema ta zauna ta yi tagumi.


 Miƙe wa ya yi yana huci yana cewa “Safinat! Safinat!! Safinat!!!” Ya ciji yatsarsa ya girgiza kai.

  


 Ya ja numfashi da ƙarfi ya nufi ɗakin Feenah.



 MAIMUNATU A HARABAR ASIBITI




 Maimunat tana isa harabar asibiti ta kira Aliyu ta sanar da shi ga ta ta iso.


 Aliyu murmushi ya yi ya dubi ƙaninsa ya ce, “Umar, Maimunat ce ta zo duba ni yanzu haka tana bakin gate, ka je ku taho tare.”


 Ya miƙe yana mai cewa, “To yaya.” Sai ya fice.


 Umar na isa wurin Maimunat cikin rutsunawa ya yi mata sallama tare da gaisuwa, ita ma cikin fara'a ta amsa masa.


 Suna tafiya suna hira har suka isa wurin da a ka kwantar da Aliyu.

 Sallama suka yi cike da fara'a Aliyu ya amsa.

 Ya tashi ya zauna daram yana murmushi. Ta gaishe shi tare da yi masa ya jiki, suka fara musayar kallon junansu sun manta da Umar na ɗakin.


 Umar, da ya fahimci suna cikin halin shauƙin juna ya girgiza kai ya fice ya bar musu ɗakin.


 “Mama me ya sa kika raba waɗannan masoyan? Tun da yaya ya rabu da Aunt na fahimci rayuwar shi ta fara susucewa. Ya Allah ka kawo musu maslaha a tsakaninsu.” Abin da Umar ya faɗa kenan yayin da ya fita waje ya jingina da bango.


 Aliyu ya sauke ajiyar zuciya, "Maman twins have a sit.”


 Ya nuna mata kujera da ke kusa da shi ta zauna.


 Bayan ta zauna ya miƙa hannunsa zai riƙe hannunta ta ja baya.


 “Haba dear, ya za ki yi mini haka! Shin akwai shamaƙi ne tsakanina da ke? Har yanzu fa mu a matsayin miji da mata muke.”


 “Haka ne dear, amma ka san ba mu san wanda zai shigo ba.”


 “Babu mai shigowa kuma ko an shigo ma ai ba abin haramun muke aikata wa ba.”


 Murmushi ta yi, “Haka ne, amma mu zama masu alƙunya ma yana da kyau.”


 “Gaskiya ne, amma ni dole ki ba ni hannun nan na riƙe na murza, saboda na yi missing, duk me shigowa na san zai yi nocking kafin ya shiga.”


 “Kai kam dai, to ga ka ga hannun ba dai iya hannu ba Bismillah.”


 “Ko ke fa ina shafa hannun matata ina murza shi, hirar zai fi tafiya cikin daɗi ga nishaɗi.”


Ta tuntsire dariya, "Ka ji da shi dai."


 GIDAN MUS'AB



  

 Da kafarsa ya tura kofar ya shiga ya tarar da Feenah kwance bisa matress wayar da ke jikin tv ya fizge tana gani ta miƙe ya ce, da ita, “Ina za ki? Koma inda kike.”


 “Ya yi mata wani irin kallo, a kufule ya juya ya sawa kofar sakata don saboda ya san halin matarsa, duk da sun yi da ita ba za ta ce kanzil ba, amma yana ganin zuciyarta ba za ta haƙura ta jure abin da zai yi ba.


Mus’ab ya dubi Safinat sama da ƙasa ya ce,


  “Gimbiyar mata ko in ce Sarauniyar mata mai iko da kanta haka sunanki yake ko?”


 Ta zazzaro ido yanayin da ta ga yayanta ya tsorata ta jikinta na rawa ta ce, 


 “Ba haka ba ne yaya.”


  “Haka ne mana, kin fita ba izini kin dawo kina ganin bayinki kika yi wucewarki."


  “Wallahi yaya kaina ke sarawa shi ya sa na zo na kwanta.”

 “ Gaskiya ne idan bai sara da gaskiya ba yanzu zai fara sarawar mai dalili .”


 Ya sharara mata wani gigitaccen mari wanda sai da shacin hannunsa ya zauna a fuskarta, ta zube ƙasa, ya finciko ta jikinta na rawa cikin tsawa ya ce da ita,


 “Da izinin wa kika fice a gidan nan? kuma ina kika je? “



“Yaya fitar ne ta zo ba shiri Umma ce ta kira ni, amma na faɗawa Aunt da izninta na fice.”


 Ya gwara kanta da a bango yana cewa, “Kin san abin da na tsana a rayuwa ƙarya, zan iya sumar da ke idan bakinki na furta karya a kaina ba da izinin Aunt ki ka fita ba, haka ne ko ba haka ba.”


 Ta gyaɗa kai alamar haka ne, ya ja kumatunta ya ce, 

 “Da bakinki za ki ba ni amsa ba gyaɗa kai ba.”


 “Tabbas Aunt ta hana ni fita.”



  “Ke kuma ga ki isashshiya kika fice da izinin kanki, zaman kanki kike ko?”


 “A’a yaya."


 "To faɗa mini inda kika je.”

 Cikin sheshshekar kuka ta ce, “Yaya gidan Umma na je gaishe ta.”


  Ya  ɗauki igiyar tv ya dinga zabga mata, “Ni na san inda kika je amma ba zan furta da bakina ba ke da kanki za ki furta.”


  Feenah saukar bulala take ji a jikinta ba ƙaƙƙauta wa, ita ko Hafsy sai buga kofar take  tana cewa, “Mijin mace ɗaya, ka yi haƙuri don Allah ya isa haka.”


 Shi ko Mus'ab bai ma san tana yi ba.

 Safinat ta yi jina-jina ta ce da shi, “Zan faɗa wallahi zan faɗa gaskiya.”


  Ya dakata da dukar, ta faɗa masa gaskiyar lamari shi ma ya faɗa mata yadda a ka yi ya ganta kuma ya dinga bibiyarta har inda aka sauke ki a gidan Ummanta.

 “Kuma nasan a zuciyarki za ki zargi Aunt ki ce ta faɗa mini, to kin ji yadda a ka yi na ganki, ita Aunty ta ki ma kare ki ta so yi, ba ta san ido na ya ga kazantar da kuke yi ba, ce mini ta yi pharmacy ta aike ki, da na kure ta ta faɗa mini gaskiya.”



 Cikin dashashiyar murya ta ce,  “Yaya ka yi haƙuri, tabbas na tafka kuskure ba zan kuma ba.”


 MAIMUNATU DA ALIYU A ƊAKIN JINYA



 Maimunat ta ce, "Daddyn Teema, yadda na firgita da na zo sai na ga jikin Alhamdulillah da sauki.”


 Ya sumbaci hannunta da yake wasa da shi “Eh da sauki amma gangar jiki ne kawai ta yi sauki, amma zuciya da ruhi rayuwarsu na cikin tsaka mai wuya. Saukinsu shi ne samun daidaito tsakanina da ke. Don Allah faɗa mini laifina."


 Ta runtsa idanuwanta kana ta buɗe, "Kafin na kai ga ba ka amsar don Allah mene ne musabbabin jinyarka?”


 Ya miƙe ya zauna a jikin bangon gadon, “Ke ce my wife, juya mini baya da kika yi ne ya haifar da hakan, na shiga damuwa ba na ci ba na sha, rana ɗaya jiri ya ɗebe ni na zube a ƙasa, daga lokacin ban san inda nake ba, kawai na buɗe ido ne na ganni a gadon asibiti. My love ki sani nisanta kanki da kika yi ya illata ni, don Allah my dear kar kina juya mini baya idan muka samu saɓani."



 Tana ƙwalla ta furta “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! My husband ka yi hakuri ban taɓa tunanin abin da na yi zai jefa ka cikin irin wannan halin ba. Zan faɗa maka laifin ka shi ne…………"

  

  


 Aliyu ya dubi matarsa ya ce, “Me ya sa kika dakata da abin da kike son faɗa mini.”


 “Ji na yi kamar ana nocking door.”


 “To kunnuwanki ne suka ji, faɗa mini ina sauraronki.”


“Dear me ya sa za ka aibata Mama a gaban Umma? Ba ka tunanin abin da ka faɗa zai ɗarsu a zuciyarsu su dinga yi mata kallon wacce take musguna wa 'yarsu.”

 “Ko ban faɗa musu ba yau da gobe za su sani, domin yanzu kiyayyar da Mama ke nuna miki ta yi ƙamari, domin yanzu ya taka matakin da a gaban kowa za ta iya nuna tsanarta”


 “Me zai yi don ta nuna, duk mai hankali ya san babu rayuwar auren da za ta ginu babu ƙalubale duk kallon daɗi da ake mata, ni na ɗauki abin da Mama ke yi mini shi ne jarabawar gidan aurena. Kowa da ta su jarabawar da za ka ji ta wasu ni tamkar ina cikin aljannatul firdaus ne., ni fa ka san Allah duk abin da take yi mini baya damuna, kuma ba na riƙe ta a zuciya daidai da second ɗaya. Wallahi na yi maka fushi ne kawai bisa aibata Mama da ka yi, ina fatan ba za ka kuma ba.”


 Ya ja gauron numfashi. "Mama yaushe za ki fahimci Maimunatu tana yi miki son da ya fi nawa ɗan cikinki. Mamata kyawawan halayyyarki shi ke sanya soyayyarki kullum na yaɓanya a zuciya. Ya sumbace ta i love You my wife."

 

 “I love You too hubby, mijina kar ka damu da yardar Allah da sannu za ta fahimta lokaci na zuwa da Mama za ta nuna mini so sama da yadda kake nuna mini.”

 “Murmushi ya yi ya ce, “Allah ya tabbatar da hakan, don zan fi kowa farin cikin kasancewar hakan.”

Aliyu ɗaga hannuwansa sama ya yi ya ce, “Ya Allah ka fahimtar da mahaifiyata ka arzurta ta surkuwa ta gari amma ta gaza fahimtar hakan.”


 Murmushi ta yi ta amsa addu’ar da amin.


  

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol