Free chapter · Read without an account
Part 5
*ƘULLALLIYA!*
[ _Littafin kuɗi N300_]
Labari/Rubutawa
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
[ _Meenat A Yandoma_]
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` 📚🖊️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*🥰
***
____________________________
*LITTAFIN ƘULLALLIYA NA KUƊI NE AKAN FARASHE MAI KAMA DA KYAUTA N300 KACAL! ZAKU TURO KUƊIN KU TA WANNAN ACCOUNT ƊIN AISHA ABUBAKAR 2151366600 UBA BANK, KO KUMA KATIN MTN NA 300 TA WANNAN NUBER *** KADA KI BARI AYI WANNAN TAFIYAR BABU KE.*
*LAST FREE PAGE👌🏻👌🏻*
*PAGE 9️⃣__🔟*
Last free page, daga wannan page ɗin free page sun ƙare, hanzarta ki biya 300 kin domin karatu cikin lumana, masu buƙata a riƙa tura masu ta pc 500 ne sannan in na gama masu buƙatar Document shima 500 ne.
*TALLAH!*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
...Jim! kaɗan bayan mamayewar duhun ihun ɗaliban tare dana Auntyn su ne ya biyo baya, yana yin yadda suke zabga ihu kaɗai ya isa ya sa ka fahimci tabbas suna ji a jikin su.
Fau-fau! Sautin ƙarar bulalai ke tashi, an ɗauki lokaci me tsayi kafin kaji komi ya lafa shuru babu ihun ɗaliban ƙarar bugun ma ta lafa, ruwan saman da ake sheƙawa kuwa ya ƙara ƙarfin tun sa'in da ake bugun ɗaliban, har yanzu ruwan ake sheƙawa babu ƙaƙƙautawa.
Ƙofar Clas ɗin ce ta buɗe kanta, haske ne ya haske ajin, nan na samu damar hango yaran kwakkwance suna maida numfashi da ƙyar! Auntyn kuwa tsabar buguwa da tayi ko numfashin kirki bata iyayi ta fita hayyacin ta domin wata ƴar ƙaramar suma tayi, kaf cikin Ajin Rumana ce kaɗai zaune ƙalau ba tare da wani abu ya sameta ba.
Ganin ruwan ya lafa yasa shugaban makatarantar Umurtar ɗalibai su fito domin Bus ɗinmu ta ƙaraso, kaf ɗaliban da Bus ke ɗauka sun shige daga cikin Bus ɗin Sa6anin ɗaliban Ajin su Rumana da har yanzu babu wanda ya fito, mamaki ne ya kama shugaban makarantar dan haka da kanshi ya kutsa kai cikin ajin, gaban shine yayi wata mummunar faɗuwa lokacin da majigin idanun shi suka hasko ma shi Aunty Sisilia kwance ita da ɗalibanta suna kwasar bacci.
A hankali ya riƙa tayar dasu suna farkawa, abin mamaki shine duk wadda ya kalla sai yaga fuskar shi ta sauya taji fushi ga idanun su sunyi jajur, Shugaban makarantar kauda duk wani mummunan tunani yayi ya ɗauka a ranshi cewa bacci ne yasa idanun su suka sauya, Aunty Sisilia kuwa cikin hanzari ta ƙarasa gaban Pc ɗin tare da Furta "Sir!"
Juyowa yayi domin ya lura tunda ya tayar dasu akwai magana bakim Auntyn.
Sisilia ce ta fara ƙoƙarin sanar dashi abinda ya faru, amma abinda zai baka mamaki shine yadda Sisilia taji komi ya 6ace mata abinda take son faɗa Harshenta yayi mata nauyi ta kasa furta komi.
"Yadai Aunty! Naji kinyi shuru."
Pc ya ƙarasa maganar tare da kafe ta da ido alamar tuhuma.
"Da ma...... Dama,,,, dama ce maka zanyi ba zani samu damar shiga Bus ɗin students ba, sakamakon kai na dake mani ciwo."
Sisilia ta ji bakinta ya furta ba tare da ta bashi izini ba.
"Ayya! Sannu, babu damuwa zaki iya tafiya."
Shugaban makarantar ya faɗa tare da ficewa daga cikin ajin.
Sai da aka tabbatar ko wane ɗalibi ya shiga Bus kafin driver ya tayar su hau hanya.
Ganin ɗalibai sun tafi nan sauran malaman suma suka hau shiri tafiya kamar yadda doka ta tanadar.
Rumana kuwa yau jinta take cikin farin ciki musamman yau ƴan class ɗin su tunda aka shigo Bus ɗin basu tsokame ta ba, domin su ma yau ta kansu suke."
Kasancewar Unguwar su Rumana ba kusa take ba sai da aka sauke mafi akasarin ɗaliban makarantar kafin a yi birki ƙofar gidan su.
Annurin fuskar Rumana ne ya 6ace sakamakon tozali da tayi da gidan nasu, da ace Rumana nada inda zata ja to kuwa tabbas da babu abinda zai shigar da ita gidan su.
maganar Driven ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula.
"Kina 6ata mana lokaci! Ke muke jira ki fice zamu yi gaba."
Driven ya karasa maganar cikin zafi domin ya lura tunda yayun ta suka fice amma ita ta kasa fita tayi togaciya bakin ƙofar motar.
A hankali ta zura kafarta waje tare da ficewa tamkar wadda ƙwai ya fashe mawa a ciki.
Sa'in da ta shiga gidan har Yayun ta sun shiga wanka, kai tsaye ɗakin su ta shige tare da yin wurgi da jakkar hannun ta faɗa kan gado, wani irin bacci ne taji yana firgarta tamkar yadda magana ɗisu ke jan ƙarfe, jin kaɗan bayan kwanciyar tabacci yayi awon gaba da ita.
Bayyana tayi a wata irin duniya me cike da abubuwan mamaki, ita dai wannan duniya kaf mutanen cikin ta a sama suke yawo tamkar tsuntsaye, duk da ƙarancin shekarunta amma ta fahimci wannan ba mutane bane, Sunan ta da taji an ambata ne ya sanya ta juyawa.
"IZMAH!"
Rumanah ta furta cike da zallar farin cikin ganin ta.
"IZMAH! ina ne nan? Dama haka kuke yawo a sararin samaniya kamar tsuntsaye."?
Rumana ta ƙarasa maganar tare da maida hankalinta akan halittu masu suffar mutum dake ta yawo a sararin samaniya.
"A duniyar mu kowa yana da ikon yawo a sama ne ko a ƙasa babu inda bamu shiga, kema kina so ki riƙa tashi sama tamkar tsuntsuwa"?.
Izmah ta jefa ma Rumana tambayar.
A tsorace Rumana ta girgiza kai tare da furta
"Aa! Bani so amma yana burgeni, sai dai in rufe idona ki ɗauke ni mu tashi."
Murmushi suka yi a tare.
Ƙarar busar da suka ji ce ta sanya Izmah firgita hankalinta ya tashi domin yau tasan abinda take gudu zai auku.
"Ƙarar mi ce ce wannan."?
Rumana ta tambayi Izmah.
"Ɗan Sarkin Aljannu na wannan nahiya ne zai wuce, dan haka mu duƙa bisa ƙafafunmu kafin ƙarasowar shi."
Izmah ta ƙarasa maganar tare da jan hannun Rumana alamar su duƙa.
Duk wata halitta dake wurin hatta waɗan da suke yawo a sararin samaniya duk sun sauko ƙasa domin girmama shugaban nasu.
Ingarman Aljanu daka-daka masu zubin samudawa ne ɗauke da wata ƙaragar mulki da ta sha ƙawa da kyawawan kayan alatu na wannan duniyar.
A hankali ya fara zuro kafafunshi kafin dukan jikinshi ya bayyana a waje, kirarin gaisuwa ne suka hau yi mashi cike da girmamawa.
Kyakkyawan aljani wanda kallo ɗaya zaka yi mashi ka fuskanci ya kai irin namijin da ko wace mace zata so zama dashi a matsayin abokin rayuwarta, amma fuskar nan tashi babu alamun imani a tattare da ita, mutanen shi ya fara bi da ido ɗaya bayan ɗaya karaf idanunshi suka sauka akan Rumana dake duƙe kusa da Izmah.
"Yake Izmah shin lokacin gabatar da aikin mu ne ya karato, lokacin ɗaukakar mune ya kusanto mu abinda nike ganewa idona"?.
Yarima Juzzam ya jefa ma Izmah tambaya.
Cikin girmamawa Izmah ta miƙe tare da duƙawa ta kwashi gaisuwa kafin ta fara bayani kamar haka.
"Tabbas ita ce, domin tun ranar da tazo duniya nike bibiyar rayuwarta na zama inuwa a gareta domin aduk inda zata kasance ni ce inuwar ta, na kawo ta ne domin na lura bayan mu akwai masu bibiyar ta kuma in muka sake suka ɗauketa burin shekare ɗari da sittin na wannan masarauta bazai cika ba ɗaukakar mu bazata tabbata ba inda muka yi sake abokan adawar mu suka ɗauke Gimbiya Rumana mai daraja, dan haka nike so a kira Babban Boka Gurmuz domin yayi mana bincike kafin mu fara gudanar da ƙudirinmu."
Izmah ta ƙarasa maganar cike da girmamawa.
Dogon nunfashi Yarima Juzzam Yayi domin tunda ya Jefa idon shi akan wannan ƙaramar yarinyar yaji sam bazai iya rayuwa ba tare da ita ba, tabbas lokaci yayi da burin su na shekaru ɗari da sittin zai cika.
Boka Gurmuz ne ya bayyana cikin shigarshi ta cikakken boka wanda ko cikin aljannu ake taƙama dashi.
Hatta yarima Juzzam sai da ya ɗuka domin girmamawa ga Babban Bokan, 6arkewa da dariya Boka Gurmuz yayi cike da farin ciki, domin tun yana saurayi sike tsumayin wannan rana har yau da yake da shekaru a ƙalla dubu biyu.
"RUMANA BINT AMMAR, tabbas ita ce, munyi babbar sa'a da muka gayyato ruhinta zuwa duniyar mu domin, domin a binciken da nayi na gano wasu boyayyun Aljannu suna gaf da ɗauketa, tabbas mun auna sa'a, dan haka a dai_dai wannan lokaci ta dawo ƙarƙashin kulawar mu a yanzu zamu ɗaura auren da ake da burin ɗaurawa tun shekaru ɗari da sittin da suka shuɗe tabbas a sannu burinmu zai cika."
A dai-dai lokacin ne aka ɗaura auren Mutum da kuma aljan wato Rumana da kuma Yarima Juzzam, wani sihirtaccen zobe aka sanya mata a hannu, wani garin magani boka Gurmuz ya watsama Rumana a fuska lokaci ɗaya bacci yayi awon gaba da ita.
"Mun ɗaura auren ka da Rumana, bisa sharaɗin bazaka tare da ita ba har sai ranar da ta cika shekaru ashirin da biyar."
Boka Gurmuz ya faɗa tare da bada Umarnin maida ruhim Rumana.
Har suka gama cin abincin rana amma babu rumana babu dalilinta, rashin kulawa da banzatar da rayuwar Rumana shiya haddasa ma ta faɗawa cikin wannan hali domin akwai wata ƙullqlliya dake bibiyar wannan ahali.
Har magrib Ruƙayya bata damu da rashin ganin Rumana ba, sai Ammar ne ya je ɗakin ya tadota.
Zaune suke a cikin falon ne su duka suna hira.
"Abbah!"
Rumana ta faɗa.
Tado kanshi yayi cikin rashin kulawa.
"Ya aka yi ne"?.
Abban su ya faɗa.
"Abba mine ne AURE"?.
Rumana ta faɗa.
A firgice iyayenta suka dubeta
"Mi kike fada Rumana, yanzu ba lokaci bane da zakisan ma'anar aure ki bari ki ƙara girma."
Ammar ya fada a taƙaice.
"Kai kama damu da har kake bata lokacin ka, wurin bata amsa."
Ruƙayya ta faɗa.
"Umma ɗazu aka ɗaura AURE NA, nima na zama matar Aure."
Rumana ta faɗa tana wasa da zoben dake hannunta.
Rukayya da ta ɗauki Cup ɗin ruwa ta kai baki babu shiri ta saki Cup ɗin ya faɗo ƙasa ya tarwatse......
_______________________
...Gangar jikin karen ce aka raba gida biyu tare dayin jifa da gawar shi gefe.
Duk wani me rai dake cikin falon ya kasa koda motsa yatsan shi ne tsabar firgici da tashin hankali.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, shikenan Jinnu sun shafi jikata, wannan aikin sihiri ne."
Inna Yalwa ta faɗa tana share hawaye.
"Ni abinda ke damuna shine shin waya kashe Karen nan, nidai naga bai ƙarasa jikin ASLAMIYYA ba aka raba shi gida biyu."
Inna Ladiyo ta fada cikin sarƙewar Murya.
Auwalu da mahaifin Aisha ne suka shigo gidan domin a yau ne mahaifin Aisha ya shirya komawa zazzau tare dasu Inna Yalwa.
Nan fa aka basu labarin abinda ke faruwa, cike da ruɗu suke kallon ASLAMIYYA dake kwance tana ƙare masu kallo, gefe ɗaya kuma ga gawar kare can gefe.
"Yanzu abinda za'ayi shine Auwalu ka nemi malamin addini a nema ma jinjirar nan Magani, domin al'amarin ta yana buƙatar addu'a tun kafin abun yayi tsayi ya kamata a tare shi da wuri, bayan haka a yau ne zamu koma gida zamu bar jinjirar a tare daku domin naga alamun bazaka iya rabuwa da ASLAMIYYA ba."
Mahaifin Aisha Ya karasa maganar.
Inna Yalwa ce ta ca6e zance da cewa.
"Bazai yiyu in bar jikanya ta a wannan gidan ba, Salmanu in kana so kaga zallar bacin raina to in sake jin kace abar ASLAMIYYA a gidan nan ƙafar mu ƙafar ASLAMIYYA."
Inna Yalwa ta karasa maganar cikin haɗe fuska.
"Babu inda za'aje mani da jikanya, mune dolen ASLAMIYYA, dan haka a gidan Ubanta za'a rene ta."
Inna Ladiyo ta fada tare da kafe Auwalu da ido.
Kan Auwalu ya rigada ya ɗaure domin harga Allah bazai iya bada abinda Aisha ta haifa ma shi ba.
"Inna Yalwa kiyi haƙuri! Amma ba zani iya bada ɗiyata aje wani wuri da ita ba, in na kalli ASLAMIYYA ina jin sanyi ne domin ina ji ne tamkar ina kallon mahaifiyarta, ina roƙonki da kiyi haƙuri ki zauna a tare damu, sai ku reni ASLAMIYYA keda Inna Ladiyo."
Auwalu ya ƙarasa maganar kanshi a ƙasa.
"Aa Auwal! Ba za'ayi haka ba zamu bar ASLAMIYYA a hannunku, babu damuwa Ubangiji ya rayata, maganar Mahaifiyata ta zauna tare daku bata taso ba, duk yau zamu wuce insha Allah."
Alh. Salmanu ya karasa maganar tare da fatan Allah yasa kada mahaifiyar ta shi ta 6otsare Ma abinda ya faɗa.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiu'un! Yau ni Yalwa ina ganin rayuwa, Salmanu kuna so ku raba ƙaunar dake tsakanina da ASLAMIYYA, to buɗe kunnenka ni Yalwa zama daram! Babu inda zani ina tare da jikata dan haka Salmanu ka fita idona in rufe."
Inna Yalwa ta ƙarasa maganar tare da haɗe girar sama da ta ƙasa.
"Hajiya kiyi hakuri, in dai zama gidan Auwalu ne na barki kiyi."
Alh. Salmanu ya karasa maganar cike da girmamawa.
"Yo Salmanu ko baka amince ba ai dole in zauna kusa da Jikalle ta."
Shuru babu wanda ya sake magana domin sun san kaɗan daga cikin aikin Inna Yalwa ne ta sa me su ta zage tas.
Babu yadda Alh Salmanu ya iya haka ya tafi yabar Mahaifiyarshi a gidan Auwalu.
Gida ya rage daga Inna Yalwa sai inna Ladiyo, sai kuma ASLAMIYYA.
Ko da dare yayi babu yadda Auwalu bai yi da tsoffin nan akan su bashi ASLAMIYYA ta kwana wurin shi, amma suka taru suka zage shi tas! Bawan Allah sai dai ya haƙura ya tafi ɗaki ya kwanta cike da tunanin matar shi.
Tsakar dare Inna Yalwa taji kamar motsin mutum, tayar da Inna Ladiyo tayi domin su tashi su duba.
Tashin hankali! Sun nemi ASLAMIYYA sun rasa, haske suka kunna cike da zallar mamakin wannan al'amari.
Inna Yalwa ita ta fara mugun gani cike da tashin hankali ta ta6o hannun Ladiyo, abinda Ladiyo ta gani ne ya sanya Numfashin ta tsayawa cak! Ta sulale a ƙasa sumammiya.
Inna Yalwa kuwa ji take ina ma ace ita ce ta suma, domin tashin hankalin da majigin idanuwan su suka hasko masu ba ƙarami ba, ba shiri Inna Yalwa tayi zaman ƴan bori tare da ɗora hannu saman kai zata kurma ihu sai ji tayi tamkar an sanya superGlue an daɗe mata baki ta kasa koda kwakkwaran motsi jikinta tamkar an ɗaure ta da igiyoyi......
Wace ce aslamiyya?
Shin mutum ce ko aljan?
Mike faruwa da rayuwar ta?
Wace irin ƙullalliya ce ta afkama sabuwar jinjira?
Ina labarin aure Rumana da ɗan sarkin Aljannu?
Shin aure tsakanin mutum da aljan yana yiyuwa?
Wane ƙudiri na akan wannan ƴan masarauta da suke iƙirarin zai cika bayan shekaru ɗari da sittin?
Shin iyayen Rumana zasu ɗauki maganar auren ta da muhimmanci?
Wace ce IZMAH?
Waye yarima Juzzam?
Shin su inna Yalwa zasu iya renon Aslamiyya?
Rumana zata ji tausayin jinsin bil'adam ko kuma zata tsane su ne kamar yadda suka tsane ta?
Shin aure tsakanin mutum da aljan zai ɗore???
*WADDA TA YI PAYMENT CE KAƊAI ZATA SAMU WAƊAN NAN AMSOSHIN, LOKACI BAI ƘURE MAKI BA KO YANZU ZAKI IYA BIYAN KUƊIN WANNAN LITTAFIN DOMIN KUWA WANNAN SHINE PAGE ƊIN ƘARSHE NA KYAUTA.*
*MEEN@RT.........✍🏻*
***