Free chapter · Read without an account

Chapter 21

by Na'ima sulaiman Sarauta · KWAILA CE

Zare Idanu Salame tayi lokacin da ta ji bakin Zain,He was kissing her mouth in peace and taking a breath. Idanun Zain har wani rufewa ya ke, duk yadda Salame taso ƙwace kanta kasawa ta yi sai kawai ta daddage tare da sakar masa wata uwar tosa wacce ita kanta bata san tayi ta ba.


Duk da haka Zain ƙin sakinta ya yi, sai da ya sha bakinta son ransa Sannan ya saketa tare da mirginawa ya kifa kansa a pillow yana mai da Numfashi, He doesn't love her, Amma yana jin wata matsananciyar sha'awar ta na addabar sassan jikinsa. Her soft black skin intrigued him.


Salame ta rushe da kuka tana faɗin.

"Allah ya isa wallahi sai na faɗawa Mami ka sha min baki, wlh sai na faɗa mata ka ƙara yi min ciki, yanzu ban san adadin yaran da suke a cikina ba, ko wanne ubansa daban innalillahi ni Salame jikar Inna tashin ƙauyenmu yaya zanyi da wannan masifa?"


Jikin Zain ma rawa ya sakko da ga kan gadon, bai san ta ina zai fara ba, bai kuma san mene zai ce ba, amma ba ƙaramar bugawa zuciyarsa ta yi ba, lokacin da salame tace ko wanne ɗan cikinta ubansa da ban. Zubewa ya yi gabanta yana ƙare mata wani irin kallo kafin yace.


"Ciki kuma?" Da sauri tace "Wlh fa, yanzu haihuwa ce abin ji, dana haihu kowa zai je na kai masa gantallan ɗan sa, yanzu gashi ka shanye min baki ban san adadin yaran daka zuba min acikina ba" Zain was shock da kalaman Salame amma yanzu abin dry bama ba shi, gane cewa har yanzu KWAILA CE ita. A hankali yace.


"To yaushe za'a ban nawa?"

Wata uwar harara ta watsa tace "ko zan bawa Kowa wlh ba zan baka ba, ɗan iska mai shanye bakin mutane" haɗe fuska Zain ya yi cikin kakkausar murya yace "ki ka sake cemin ɗan iska zaki sha mamaki, bakin banda wari babu abinda yake daman shanshanawa nayi" baki ta sake tana shinshina iskar bakinta amma sam ba taji warin ba kamar yadda ya ce.


Miƙewa tayi tana murguɗa baki "Kuma babu ni ba kai, duk abinda na yi maka kai ne ka siya da kuɗin ka, dan kaji nace ina sonka ai banta da wulaƙancin da kayi min a gaban a bokanka ba, ni yanzu bana sonka bana ƙaunarka ba zan taɓa...."


"Shut up.... Shiru"

Zain ya faɗa cikin ƙara ji yana dakawa Salame tsawa, sosai kalmar bana sonka ta daki tsakiyar zuciyarsa. sai da taje bakin ƙofa ta juya tace.

"Kuma dan kaji na fara nono"

Tana faɗin hakan ta juya da sauri kafin ta ƙarasa ficewa ta tura masa ɗuwawu Haɗi da sakar masa tosa wacce tasa Zain saurin toshe hancinsa.


Salame na fita suka haɗa idanu da Zannur da sauri ta dafe ƙirjinta tana faɗin "Na shiga uku, Alkur'an na manta da kai" Murmushi kawai ya yi mata ya ce "Shi ya sa kika daɗe ko?" Ta zauna tana zabga tagumi irin abu ya isheta ɗin nan kafin ta buɗe baki tace.


"Wlh kunyarka na keji"

"Kunya? For what reason?"

"Ba ance Yaa Zain ya sakeni ba? Ke nan ni ba matarsa bace gaba ɗaya?"

Zannur ya gyara zama zuciyarsa na bugawa na tsoran abinda zai fito da ga bakin Salame, domin zuciyarsa dab take da bugawa akan soyayyarta.


"Ba mijinki bane, ba mijinki bane domin ya sakeki baki da haɗi da shi" ihu ta fasa tana ɗora hannunta aka tare da faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, na shiga uku wayyooo Allah Innata kina kizo ki taimakeni Wlh ɗan iska ne ya yi min iskanci ya saka min bakinsa a nawa ya zame min wando......


Arewabooks ai comment 😂

Anyi wa Zain ƙarya


Follow my account

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol