Free chapter · Read without an account
Chapter 13
ƘARAMAR HUKUMA TAKAI (TSINTAR)
Ma'u kwance take idanuwanta sun yi ja tamƙar gonar tattasai ta fara tunano wani hirarsu Ahmadinta.
Tsaye suke a kofar gida ya fuskance ta ya ce:
“Ma’u, a dukkan lokacin da kika guje ni ko a ka yi ƙoƙarin raba ni da ke, to ki sani babu inda ya fi dacewa da na ci gaba da rayuwa a cikinsa face ƙabari, domin kuwa na san daga ranar duniya za ta zamo wajen zubar hawayena.”
“Ahmadina me ya sa kake son yawan furta kalmar rabuwa, ka san ni da kai babu rabuwa, ballantana na kai ga guje maka, har yanzu ba ka yarda da tsantsar soyayyar da nake maka ba ne? A har kullum ina ɗaukar kaina tamkar matar aure kuma ta Ahmadi, ba na ɗaukar kaina a matsayin ni budurwa ballantana na saurari wani ɗa namiji bayan kai, kamar yadda yake haramun ne matar aure ta kulla alaƙa da wani namiji, to haka yake haramun a kaina na saurari wani namijin face Ahmadina shi ɗaya tak."
Tattausar murmushi ya yi ya ce, “Na yarda da soyayyar da kike yi mini amma ki sani cikin kaso ɗari na soyayya kaso 90 suna fuskantar kalubale da shiga tasku, da wuya mutum ya faɗa soyayya ya kuma yi nasara a kai.”
“To ni da kai ba za mu fuskanci ƙalubale ba, ballantana mu shiga tasku, nasara a soyayya shi ke tare da mu.”
Ya duba agogon da ke ƙaramar wayarsa. "Dare ya yi ya kamata mu yi sallama ki je gida."
Ta juya za ta shiga gida ya ƙira sunanta. "Ma'u!" Ta dakata da tafiyar ya zo daf da ita.
"Ma'u ina jin wani abu a jikina dangane da soyayyarmu kuma yana tsorata ni, ko da kin ce na fassara miki abin da nake ji ƙwaƙwalwata ba za ta iya naƙalto shi ba. Ma'u ki sani son ki ba zai taɓa goguwa a zuciyata ba har cikin ƙabarina. Da son ki zan gama rayuwa, da kuma son ki zan mutu, kuma tare da soyayyarki zan tashi a ranar alƙiyama."
Ya sassauta murya, "Ma'u ko da ban aure ki ba, idan kika auri wani kuka hayayyafa ki ce da 'ya'yanki ni Ahmadi masoyinki ne da ya so ki sama da na mahaifinsu."
Tana zuwa daidai wannan gaɓar ta kuma rushe wa da kuka tana cewa, “Ahmadina abin da kake tsoro shi ke shirin riskar mu. Kaicona!”
BIRNIN KANO
Mama da Aliyu sun sauka a filin jirgin Malam Aminu, ɗan ƙaninta ta kira ya zo ya kai su gidansu da ke Tal'udu idan suka ɗan huta sai su nufi ƙaramar hukumar Takai.
SAFINAT DA UMMA LAURE
Safinat ta ce, “Umma ni so nake ki kira yaya ki nuna masa ya yi kuskure akan abin da ya yi mini ki ja masa kunne.”
“Hanzarin me kike, shi da kansa zai neme ni. Ubansa zan kira na faɗa masa duk abin da ake ciki.”
Shiru ta yi da zai yi daƙiƙa ɗaya a zuciyarta ta ce, “Kar kuma fa yin hakan ya fallasa abin da na yi.”
Sai wata sashi na zuciyarta ta ce da ita, “To sai me ye don an fallasa ke fa ba ki da matsala da mahaifiyarki.”
Ta amsa wa zuciyarta ta da tabbas ta ce da mahaifiyarta,
“Yawwa Ummata haka ya kamata ki yi.”
Umma Laure ta ce, “Ɗan ɗaga ni na shiga toilet.”
Safinat ta miƙe daga ƙishingiɗar da ta yi a jikin mahafiyarta.
Ta miƙe da kyar tana tangaɗi, Safinat ta dube ta ta ce, “Umma lafiya kuwa?”
“Ina lafiya.” Umma Laure ta ba ta labarin silar yin targaɗenta.
Safinat ta ce, “Allah ya kyauta, Allah ya kiyaye gaba.”
Umma Laure ta amsa da amin ta shiga toilet.
BIRNIN KANO
Aliyu da mahaifiyarsa bayan sun isa Tal’udu a ka yi musu tarba ta arziki bayan an gaggaisa ne sai a ka ba su wuri.
“Aliyu idan muka ɗan huta za mu nufi Takai mu ƙarasa Tsintar, don Allah kar ka watsa mini ƙasa a ido. Wannan zaɓin da na yi maka ba za ka taɓa nadama ba.”
Kansa a sunƙuye ya ce, “Ba damuwa Mama, ba zan taɓa watsa miki ƙasa a ido ba.”
Murmushi ta yi, “Yauwa ɗan albarka, ai kana aurar yarinyar nan arzikinka zai dinga haɓaka, 'ya’yan ƙauye ba su da damuwa akwai juriya, amma ka ga 'yan birnin nan idon su ya buɗe a kansu za ka dinga ƙarewa kuma kana yi ba su san kana yi ba, babu godiyar Allah da wata rana za ka gaza yi musu abin da ka saba cewa za su yi me ka taɓa yi mana saboda da tsabar butulci.”
Aliyu a zuciyarsa ya ce, “Na fahimci Mama ita mace ce mai kyashi da hassadar kar ɗan ta ya kyautata wa iyalinsa. Hakan zai yi wu kuwa? Shin ita lokacin da Abbanmu ke raye haka a ke yi mata.”
“Ka bar ni ina ta zuba kamar kanya ba ka ce komai ba, kamar ma tunani kake.”
Bayan ya miƙe ne ya ce da ita, “Ba ni da abin faɗan ne Mama. Bari mu ɗan ga gari da Saif.”
Mama ta bi shi da kallo a zuciyarta ta ce, "Wannan yaro sai na tashi a ƙansa na cire wannan maƙirar matar a zuciyarsa."
SAFINAT DA UMMA LAURE
Safinat zaune take cikinta na kur saboda masifaffaffiyar yunwar da ke addabar ya'yan hanjinta.
Mahaifiyarta ta dube ta, "Baki karya ba ne kika fito? Na ji cikinki na kukan yunwa."
“Umma tun da wannan saɓanin ya shiga tsakanimu zan fita na taya ta girki kuma ni ce ƙarfin aikin don minti kaɗan za ta leka mijinta ta shafe lokaci mai tsawo a wurin sa sai kuma ta dawo muna kammala wa za ta tattare gaba ɗaya wanda za ta bar mini ko yaro ɗan shekara uku idan ya ci ba zai koshi ba, ba zan kuma ganin ƙeyarta ba, sai kuma idan wani aikin ya tashi.”
Umma Laure ta riƙe baƙi ta ce, “To na ga tare kuke cin abinci ba.”
“Sarauniyar gidan ta ce da mijinta ya kamata ni ina ci ni kaɗai.”
“To ai idan haka ne sai ki daina taya ta aiki.”
Ta zaro ido, “Wacce ni! Mutumin da ya ce da matarsa me ye amfanina ya kamata ta huta ta bar ni ina aiki gabaɗaya. Tabɗijam! Na daina aiki ai zan kwashi ƙashina a hannu kana yi ma ba ka tsira ba ballantana a ce ka daina. Umma idan da kin ga inda ita da mijinta suke mini shouting akan abin da bai kai ya kawo ba ko 'yar aiki albarka. Allah ka raba mu da zama gaban waɗanda ba iyayemu Allah abin da ka ɗaura mana kar ka ɗaurawa 'ya'yanmu.”
Umma Laure ta tunzura sosai da karairayi da ɗiyarta ta furta mata
HAFSY A GIDANTA
Zaune take a falo ta miƙe ta leka ɓangaren Feenah shiru ba ko motsinta ta ce, “Anya 'yar Aunty lafiya shiru babu motsinta? Don muddin tana nan sai ka ji yo sautin music ko TV na tashi, bari na yi nocking.”
Tana zuwa daf da kofar ta ga key, ta duba sako da lungu na gidan babu motsinta nan ta tabbatar da Safinat ba ta gida. A take ta ƙira wayar Mus'ab ta shaida masa halin da ake ciki.
Bayan sun gama wayar a fili ya ce:
“Wato dai wannan yarinyar ba ta daddara ba kenan, i will teach you a lesson da ni kike."
UMMA LAURE DA SAFINAT
Safinat ta dubi mahaifiyarta tana marairaice murya, "Umma, yunwa fa na addabar 'ya'yan hanjina."
" Ni yanzu ba abinci a tare da ni amma ki shiga kitchen akwai sphagetti ki dafa akwai mai da yaji.”
Ta tura baki, “ Umma taliya fa kika ce kuma fara da mai, haba Umma.”
Harararta ta yi tare da yi mata dankwalo ta ce, “Ungo naki, taliyar ma ba babbar arziki ba ce da kika samu, ba a gidan Mus’ab kike ba, kina gidan uwar marayu ce, kin san kakudubar da nake yi kuwa? Don ma ban ce da ke ɗumame ba.”
“Amma Umma ina kuɗaɗen da nake kawo miki, ai ya kamata madara da bournvita da tea ba su yankewa a wurin ki..”
“Ina ni ina na ga cin daɗi, sai bayan mun cimma buri, kuɗaɗe da su nake amfani wajen ƙoƙarin inganta rayuwarki boka ke lakame su. Idan za ki ci taliya ki ci, shi ma sa'a kika yi akwai da sai dai ki haɗa garin kwaki.”
Safinat a hankali ta ce, “Lallai rayuwar gidan nan da matsala.”
“Me kike cewa?”
Cewa na yi “Duk jikina ciwo yake ga zazzaɓi anya zan iya girkin nan.”
“ Ai dole jikinki ya yi ciwo an duke ki kamar jaka, je ki kwanta zan girka miki.”
Feenah ta nufi ɗakin Ummanta daga tabarma ko katifa babu, ta gama wa ɗakin kallo ta ce, “Kullum dai idan ka shiga ɗakin Umma sai ka ga yana ta tsiyace wa, ba lallai abin da ka gan shi yau gobe idan ka kuma shiga ka gan shi ba.”
Zama ta yi dirshan ta ce, “Ni Feenah a nan zan kwanta da fa matsala rayuwar gidan nan, Allah ya kawo yaya gidan nan a yau asulhunta komai na tafi gwamma ƙalubalen zama gaban yaya da na gidan nan.” Ta karewa matsakaicin ɗakin kallo. "Tabɗijam! Wannan zai yi zafi da sauraye." Wani irin wari ta ji ya doki hancinta ta toshe tana dube-dube.
"Anya ɓera bai mutu ba a ɗakin nan? Lallai yau ana yin ta."
MUS'AB A WURIN KASUWANCINSA
Mus'ab ya tura calculator da takardar da ke gaban shi yana lissafi gefe ya yi jugum ya shiga tunani.
Ya ce, “To yarinyar nan ina ta shiga? Shin ko ta je wajen mayaudaran samarintan ne? A ina zan ganta? Ga shi na karɓe wayar hannun ta balle na kira ta na san takamaiman inda take.”
Riƙe goshinsa ya yi da hannunsa ɗaya yana tunanin ina Safinat ta tafi, sai zuciyarsa ta ce da shi, ya tuntuɓi Umma Laure ko tana gidanta. “
Ya tambayi kan shi kuma yana cewa “Anya za ta je kuwa?"
Number Umma Laure ya kira tana gani ta yi picking ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa. Bayan kare gaisuwar ce ya ce, “ Umma ko Safinat na gidanki?”
Ta ce da shi, “Cewa za ka yi baiwar da a ka ba ka amanarta ka ci amana ta zo? Don 'yata yau ina son sanin matsayinta a wurin ku jaka ko baiwa."
Numfashi ya ja, “Allah ya ba ki haƙuri, amma Umma yana da kyau kafin ki furta magana ki fara tambayar ba'asi.”
“To jakar ko baiwar tana nan ba ta mutu ba, ai wuya ba ta kisa sai kwana ya kare.”
“Umma amma ya kamata ki yi bincike a kan musabbabin faruwar duka.”
“Ashe ma ka san ka duki jaka, to ga ta gidan mahaifiyarta. Mus’ab kawai don yarinya ta zo wuri na ba da izininka ba ka yi mata haka. To idan har ka gaji da ita ni ina son ta, ƙaddara ce ta kawo ta wurin ka.”
“Umma bai dace da ke ba waɗannan nan zantuka suna fita daga bakinki, abin da nake so da ke ki tambayi Safinat shin a kan zuwa gidanki na duke ta.” Ya katse wayar da wannan furucin na shi.
Ƙwafa ta yi, “Lallai yaron nan, katse wayar ma za ka yi ba tare da na gama faɗin abin da raina ke so ba.”
Ƙara trying ta yi Mus’ab na gani har ya katse bai ɗaga ba.
Ranta ya yi mutuƙar ɓaci ta kuma latsa number, Mus’ab na gani ya ce, “Wannan matar idan har ban ɗaga ba za ta ce na raina ta ne, tun da ita komai laifi ne a wurin ta.”
Yana ɗaga wayar ga maganganun da suka fara shiga kunnuwar ta shi.
“ Mus'ab, ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba, ko 'yar tsintuwa ban tunanin za ka yi mata haka ballantana Feenah kanwarka jininka, ban yafe maka ba abin da ka yi wa ɗiya ta, idan har ka gaji da riƙon ta ai ba sai ka muzguna mata haka ba uwarta na raye sai ka kawo ta.”
“ Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Umma ba ni da laifi idan da za ki ji silar abin da ya jawo hakan za ki ce na hukuntata fiye da haka, kin gaza tambayata jin dalili, na ba ki damar tambayar 'yar ki kin ƙi, amma komai Allah zai bayyanar da gaskiyar komai.”
Cikin fushi ta ce, “Me zan tambaye ka, me zan tambaye ta, tun da duk na san amsoshinsu. Abin da ka yi ɗin nan sai na ɗauki mataki a kai.”
Ta katse wayar tare da jan tsaki.
Mus'ab tagumi ya yi, wasu irin zufa ke sauka a jikinsa. Take idonsa ya sauya suka yi ja saboda takaici.
BIRNIN KANO:
Tafiya suke a mota, amma babu mai tankawa ɗan uwansa, sai sanyayyir iskar AC ce ke ratsa jikkunansu.
Aliyu da shi ke ba shi yake driving ba, hankalin shi da tunanin shi gaba ɗaya na kan wayarsa suna chatting nasu da Maimunat.
Mama ce da ke zaune a baya ta katse hirar da cewa, “Saifullahi, mu yi hirar mu fa ka ga wannan yaron tun da na bijiro da maganar aurensa muke takun saƙa, idan ba ni na tanka masa ba baya kula ni. Ba zai gane ina son sa ba, kuma ni mai son haɓakar arzikinsa ba ne sai bayan ba ni.”
Ya ɗan shafa kasumbarsa. “Mama sai haƙuri, ki yi masa uzuri mu ai kullum albarkarku muke nema. Son albarkar ne ma ya sa bai yi jayayya da ke ba.”
“Ai ni gwamma ya yi jayayyar da irin wannan halin da yake nuna mini, ka ga fa yanzu ma yana jin mu ya yi kunnen uwar shegu. Na fahimci Aliyu a wurin sa ba ni da maraba da mahaukaciya”
"Subhanallahi Mama! Don Allah kar ki kuma furta haka."
Kiran wayarsa a ka yi ya ɗaga bayan ya gama amsa wa, kawai sai ya kunna ƙira'a yana bi don katse hirar da Mama ke yi masa.
Kamar karfe uku na yamma ne suka isa ƙauyen Tsintar, daidai wani gida mai gajeren gini da a ka yi shi da jar ƙasa suka yi parking na motarsu.
Suna fita yara da manya da ke wajen suka zuba musu ido.
Yayin da za su shiga cikin gidan dukkaninsu sai da suka sunkuyar da kansu kafin suka samu damar shiga kasancewar ginin gidan ba shi da tsayi.
Suna shiga aka fara musu sannu da zuwa suna amsa wa a haka har suka ƙarasa wurin yagwalgwalar su Aliyu.
“Lale marhabin sannunku da zuwa mutanen birni.” Tana shimfiɗa musu tabarma ne take faɗin hakan.
Bayan sun zauna an gaggaisa ne ta ce da jikarta "Mariya, tashi ki je kika wo wa baƙi ruwa.”
Mama cikin ji da kai ta ce, “ Yaya, ba sai ta kawo ba, mun yi guzirin ruwanmu. Ruwanku na ƙauye ai sai ku da kuka saba sha. Akwai ruwan roba wato faro a boot.”
Aliyu ya kalli mahaifiyarsa alamar bai ji daɗin abin da ta ce ba, ya ce, “Je ki kawo ruwan ni zan sha.” Mariya ta miƙe ta tafi cikin sassarfa.
MAIDUGURI BIRNIN SHEHU
Mus'ab bayan ya tashi a kasuwa bai tsaya a ko’ina ba sai gidansa.
Hafsy ta tarbe shi hannu bibbiyu kamar yadda ta saba a kodayaushe ta yi masa duk abin da ta san yana buƙata idan ya dawo gida.
Bayan ya samu nutsuwa ne ya dubi matarsa ya zayyane mata duk abin da suka yi da Umma Laure.
Ta dinga salati tare da mamakin yadda wasu iyayen yanzu ba su son laifin 'ya'yansu.
Mus'ab ya shaidawa matarsa akan zai bar Safinat ta ɗanɗana zama wurin mahaifiyarta tun da ta zaɓi haka, idan ma suna mata rana za ta fahimta."
Cikin tausasa murya ta langaɓe wuya ta ce da shi, “Nawa ni kaɗai, ni kuma ina ganin zama a wurin mahaifiyarta zai ba ta damar yin abin da take so, amma a hannunka karyanta.”
“Ina da wata manufa da na ce hakan, kuma ina mai tabbatar miki Safinat ba za ta jure zama a gaban Umma Laure ba, na bar ta ne ta zauna ta fahimci rayuwa, ina mai tabbatar miki in dai wannan gidan ne Safinat da kafarta za ta dawo nan. Ke dai ki zuba ido.”
“To shi ke nan MIJIN MACE ƊAYA nawa." Daga nan ta shi shawarar wannan al'amari ya kamata iyaye su sani. Shi ma ya amince da abin da ta faɗa masa.
Ta lakaci hancinsa tare da sumbatar shi ta ce, “Ka ga yanzu dai magariba ta gabato kana idar da Sallah ka nufi wurin su Abba.”
“Dama haka zan yi tawa ni kaɗai. Kullum kina ce da ni nawa ni kaɗai, ni ma zan fara cewa tawa ni kaɗai.”
Murmushi ta yi, “Kai ɗin ai ko ba ka faɗa ba ni ɗin naka ce kai kaɗai ba ka da abokin hammaya. Ko ka taɓa jin mace ta zama mijin maza biyu.”
“Ban taɓa ji ba, amma dai nasan akwai MIJIN MACE ƊAYA.”
Kyalkyale wa da dariya ta yi ta ce, “Wannan haka yake hubbyna kai don mace ɗaya a ka yi ka.”
Kiraye-kirayen sallah da a ke ya sanya dukkaninsu suka miƙe domin gabatar da alwala.
Bayan ya gama alwalar ne ya sumbaci kumatunta ya ce, “My pretty, idan na idar da Sallah zan wuce.”
Cike da shagwaɓa ta ce da shi, “ Allah ya tsare a dawo lafiya Allah kuma ya kawo daidaito a lamarin. Sannan a dawo da wuri idan ka ji ma zan bi sawu.”
Ya amsa da amin sannan ya ce ba ji ma wa zai dawo.