Free chapter · Read without an account
🔟
🔟
*TOP-NOTCH WRITERS*
Eh toh me zata ce? Me zata gaya mishi? Cutar dajin ya kamata ne tun da jimawa ko kuma ta gaya mishi gaskiyar maganar cewa cutar cin amana ce da rashin soyayyar shi ya haifar da haka ko me zata ce masa? Tsintar Muryan shi tayi daga sama ya ce mata.
"Baki ji ba ne?" D'ago idanun ta tayi ta zuba Mishi, shima ita yake kallo cikin wani irin yanayi, a karon farko da yake jin tausayin Yaran shi da ita kanta, janye idanun shi yayi tare da lumshe su, yana kara jin babu dad'i sama da shekaru sha suna zaman dan marina.
Bin shi take da idanu, kullum shekarun shi kara boyuwa yake, wallahi idan ba kasan yawan shekarun ba, sai ka dauka yaro karami ne, wato irin matasan nan yan kwalisa da iya daukar wanka.
"Tun cikin Junaid" ta fad'a muryan ta yana rawa. A hankali ta fashe da kuka, shi kan shi yasan yayi kuskure babba ya kasa sauke nauyin da yake kan shi. Ya tuna wannan cikin jikin ta, a ranar da yake da yakinin samun shi. A ranar da ba zai manta ba, barin ta da cikin kamar sayawa yaran shi tick din zama marayu ne, sai dai rabata da cikin kamar yanke mata kauna daga abu me darajar da take so ne.
"Taf! Taf!! Taf!!!" Ta ji takun takalmin shi, inda yayi taku uku ya iso bakin gadon, matsawa tayi tana kallon shi, zuciyar ta yana wani irin bugawa kamar wacce take kwasar gudu me nisan kilomita 80, kamshin turaren shi ya sa ta, birkicewa. Hawaye na zuba a idanun ta kamar an bude famfo. Zama yayi ya riko hannunta yana jin tausayinta sabida albarkacin Yaran da ke tsakanin su.
"Me yasa kika saka min magani a cikin abincina?" A hankali ta sauke idanun ta kasa jini na d'igowa daga hancin ta. Very slowly tayi kasa da muryan ta.
"Ka yafe min"
Wannan kalmar Billahi azim da za a bude zuciyar shi ji yake, kamar ya mutu domin cuta fa Meryam ta gama cutar shi, amma Albarkacin Nadiah yake jin ya yafe mata.
Dumin jikin da ya d'ago daga hancin ta. Yabi da sexy eyes din shi, yana wani irin lumshe su.
"A kira likita" zaman da take a jikin shi da yadda ya rab'ata a jikin shi yafi mata likita da Nurse din da xai kira mata, dan haka ta rike shi gam. Tana murmushi hawaye na zuba mata.
"Kayi hakuri, ina son jin dumin ka nasan ban cancanci zama da kai ba, amma ka bani aron lokacin ka, don Allah."
Mika kyakyawar hannun shi yayi, idanun shi na kanta ya ciro audiga ya tushe mata hancin. Itama kallon shi take cikin wani kaunar shi yana bin jini da jikin ta.
"Nayi Kuskure babba nayi laifi mara iyaka. Sai dai nasan na cancanci hukuncin Allah. Baya barin hakkin wani akan wani. Cin amanar da nayi Allah ba zai tab'a yafe min ba..."
Hannun shi ya daura a bakin ta, yana goge mata jikin da ya b'ata mata baki.
Ya rasa Meke mishi dad'i a duniyar shi, ya rasa meke damun shi duniyar shi, baki daya ji yake a kuntacce yana kokarin pretend ne domin hankalin ta ya kwanta amma ji yake kamar yana rab'e da wuta. Meryam tana da duk wani abin da d'a namiji me lafiya yake bukata ga mace, sai dai abu daya ne ya durkusar da kome a idanun shi. Mummunan laifin da ta aikata musu.
"Nasan kana tare da ni ne Alatilas, nasan banda Hajiya Mama da take tsaye akan mu da yanzu bana tare da kai. Mehd kasan me ake kira soyayya? Soyayyar bangare guda?" Hawaye ne ya zubo mata. Ta kuma k'amk'ame hannun shi cikin nata.
"Ban tab'a samun damar da ya wuce ta yau ba, wallahi ko auren ka da nayi ina tunanin naci banza sai na fahimci ashe hanci a banxa ba. Ga Mehd Junaid, Mainar Hajiya Mama amma ya zame min hoto. Karka manta kai ne sabon Sarkin Maradi nan gaba "
Hannun shi daya yasa yana shafa bayan ta, hancin shi yana saman kanta yana shakar Lady Gaga shampoo, wanda take wanke kanta da shi.
"Duk inda son zuciya ya bayyana dole kyashi da hassada ya bayyana, ni da ita mun rayu cikin soyayyar juna, ban tab'a ganin mutum me hakuri da juriya irin na Inna Isa ba. Ban san lokacin da kuka kulla ba, amma nasan nice sanadin rushe ku. Maina gaya min idan na mutu xan shiga Aljanna?" Ta fada cikin shashekar kuka.
Wallahi ya gaji, matukar gajiya ji yake kome ya dawo kamar da can. Ji yake kamar ya dawo da mutunci da zumuntar su.
Amma ina tun daga ranar da ta bude baki ta ce mishi.
*Ya Mehd!! Ina son ka babu abin da zai sauya Inna Isa kuwa ka saka a ranka kamar mafarki kayi domin ta tafi kenan har abada*
Wani abu yaji ya tsaya a wuyar shi, a hankali ya hadiye yawun da yake bakin shi. Shi kan shi daga baya ya fahimci abubuwa da dama bayan auren su da ya ajiye ta kamar madubi kishi yasa tayi ta fallasa sirrin su,.tayi ta gaya min shi abin da ta aikata dan yaji haushi ya daina tunanin Inna Isa, amma haka ya faskara domin Inna Isa wata shashi ne na rayuwar shi. Ko lokacin da ta fara saka mishi abu a cikin abin karyawa lokacin farkon auren su. A ranar kamar zai yi hauka haka tayi ta bashi wahala kafin ya samu biyan buƙatar shi wanda ita ce sanadin bashi kwaya. Tun daga lokacin bai kuma kusantar ta ba, asalima sai ya zama kamar wani abin kunya yayi inda babu shiri suka bar ƙasar shi da Selim. Koda ya dawo bayan wata biyu ta kuma hakka mishi gadar zare ya fada, a wannan lokacin zai iya cewa aka samu cikin Nadiah. Tun daga lokacin ta shiga harkokin cikin ta idan yana nan oho idan baya nan Oho, ita kan ta samu abin da take so. Haka ma cikin Eman sai da ta bashi kwayar sannan zai iya cewa haka cikin Junaid. Cikin jikinta nan ne yasan shi da kan sa ya nime ta. Domin a lokacin yana tuna abin da yake gaya masa.
*Daadan Nadiah don Allah kar ka min haka, jiya nayi wankar tsarki bani da lafiya*
Lumshe idanun shi yayi ya bude, domin ranar ne ya nime ta da kan shi, ya kuma ji nutsuwar da kowani d'a namiji yake ji, a ranar ya fara ganin hawayen da ya gaza gane na meye. Tana kuka akan zamantakewar su. Amma bai tab'a ganin tana hawaye sosai tare da shiga tashin hankali a lokacin ba, shi dai da ya gama abin da zai yi ya nufi ban daki domin a ranar zai yi tafiya ne zuwa America, domin harkan kasuwancin shi na Ma'adinai. Kuma akwai babban taro da xa ayi na duniya a birnin Chicago.
Wayar shi tayi kara a aljuhun rigar shi, a hankali ya saka hannu ya ciro wayar. Sannan ya kurawa wayar idanu yayi, sannan ya kwantar da ita a nutse. Kallon shi tayi tana rike da hannun shi.
"Ina zaka" nuna mata screen din wayar yayi.
Tab'e baki tayi tana me juya mishi baya, yasan haka zai faru.
Fita yayi dakin ya nufi can wajen asibitin.
"Masu ruwa sune da kifi!" Aka fada mishi haka ta wayar.
"Hm"
"Ya kwana biyu, ban ji ka ba sannan dazun Mr Robert yake gaya min kun soke zaman da yan kasuwan nan?"
Shaƙar iska yayi tare da sake shi a hankali yana shafa sajen shi.
"Maina kana cikin damuwa ne?"
Abokin ya kuma tambayar shi.
"Eh A'a!" Ya fada mishi, yana kallon birnin London.
"Maina me yasa baka da tawakkaali ne? Maina baka yarda da ƙaddara bane? Yaci a ce ka saba da halin da ka tsinci kanka a ciki amma yin haka da kake kamar kana kalubalantar Ubangiji ne!"
"Hmm Mansur ya zaka ji idan aka ce maka matar da kake aure tana dauke da cutar Daji na tsawon shekara goma ya xaka ji?"
"Innalillahi wa inna alaihil raji'un allahumma ajirni fii musibati wa'akhlifni khairan minha, Mehd kuna ina yanzu?"
"Hmm muna London din ba." Mehd ya furta a hankali yana dunkule hannun shi, tabbas yana jin wani abu da ya aikata marasa kyau akan iyalin shi.
"Maina ku dawo gida ko kuma a turo wani ya kula da ita da Yara" wani abu yaji ya tsaya mishi a ran shi.
"Hmm Mata ta ce fa! Kana tsammann ba zan iya bata kulawar da ya dace ba ne?"
"Allah ya baka hakuri. Ba haka nake nufi ba kayi hakuri don Allah, idan ta samu lafiya ka duba sai a dawo da ita" Mansur ya fada cikin lallashin sa.
"Hmm" ya fada kafin ya lashe bakin shi ya ce mishi.
"Tana da juna biyu shine ya tab'a lafiyar ta. Amma sun ce a cire tace tana bukatar abin cikin" ya fada kamar me ciwon baki.
"Fisabilillahi Mehd haka zata zauna da ciwo? Ka gayawa Hajiya Mama?" Mansur ya tambaye shi.
Kamar yana ganin shi ya girgiza mishi kai yana faÉ—in.
"A'a"
"Toh don Allah jiran me kake yi da ba zaka fada mana ba, Mehd idan ban tambaye ka ba haka zan gaya wayata baka gaya min halin da Ke ciki ba, Haba Maina."
Baki daya sai yaji ya muzanta, domin ai shima bai san da batun ciwon ba sai jiya aka kira shi aka gaya masa. Ita kanta me ciwon bata gaya masa tana da ciwon ba, amma baki daya shi yake amsar laifin da ba na shi ba. A hankali yayi kasa da muryan shi.
"Ban san yadda zan maka baya ni ba, amma duk yadda ka dauka daya ne, zan koma wurin ta" daga haka bai bawa Mansur damar magana ba, ya kashe wayar ya saka a cikin aljuhun rigar shi. Sannan ya nufi dakin da take. Tana kwance ya tura kofar ya zauna ganin kamar tana barci yasa shi komawa ya zauna a sofan dakin tana yana me daura kafa daga akan daya, ya jingina kan shi saman kujeran yana me kallon sama.
Bayan kamar awa daya aka buga kofar dakin, d'ago kai yayi yana faÉ—in.
"Yes"
Bude kofar aka yi nurse suka shigo da wani likita. Mika mishi hannu likitan yayi suka gaisa sannan ya juya wurin Meryam.
"Mrs Junaid ya jikin naki?"
" Da sauki Doctor"
"Jinin yana d'iga ne?"
"Eh ya zuba sai da ya saka min audiga ya tsaya "
"Yayi kyau ya maganar cikin?" Satar kallon Mehd tayi wanda yana jin su amma hankalin shi yana kan wayar shi. Itama so take taji me zai ce amma yayi shiru kamar ba shi ba.
"Sabida lafiyar ki da sauran kwanakin da suka rage miki ya dace a rabaki da cikin" a hankali ta rike zanin gadon tana jin wani irin ciwo mara iyaka, me yasa Mehd ba zai yi magana ba? Me yasa ya bar ta da halin ta. Me yasa yayi shiru ta zata zai tsaya mata ne? Sunkuyar da kai tayi tana kokarin É—aukar takardan ta cika. Jikin ta ya a rawa, ta kuma satar kallon shi tayi a karo na biyu, ta dauki biron da nurse din ta ajiye mata, hawaye na zuba mata, sai jan kuka take.
"Dr a bar cikin tana son shi" cak ta tsaya hannun ta yana rawa, amsar takardan Nurse din tayi.
"Amma Mr Junaid "
"Allah zai kawo mafita, amma a bar cikin tana son abinta"
"Shi kenan" likitan ya fada bayan sun bata magani, suka fita yana jin yadda take shashekar kuka, shi da zai samu halin kukan wallahi da yayi ita da take kukan dadi.
Kuma dan tsiya yaki rarrashinta ta cigaba da abin da yake yi, yana jin kamar ya bata baki yana kuma jin toh uwar me ya mata da zai bata baki ita taga zata iya kukan Allah ya bata sa'a sai tayi ta yi.
Wurin karfe daya ya tashi ya fita, can wajen asibitin a can yayi sallah duhur, sannan ya shigo a bakin asibitin ya hadu da Yaran shi farin cikin shi da gudu suka tawo gare shi...
_Books din da zasu zo kamar haka_
1- Sahla A Paris
2-Bani Da Laifi
3-Abin Da Ya baka tsoro.
Dukkan su Uku 1k
_Guda daya_ 350₦
_Guda Biyu_700₦
_Guda Uku_ 1k
_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_
_and send evidence to does number_
*+234 ****
Or
**** or ****
_Dukka zaku iya tura shaidar biya_
_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_
**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
*+22784506476*
_Welcome ta Top-notch Team_