Free chapter · Read without an account

Episode 6

by Zulaihat S Kagara · KUSKURAN FARKO

KUSKURAN FARKO

     BABI NA SHIDA

          NA

ZULAIHAT SANI KAGARA

  Dole shima ya dawo da baya daidai lokacin da take wa mahaifin ta bayanin ko waye bakonsu. Da sauri ta ga ya mike har yana tuntube da kujera,"Ki ka ce Nuran Gombe?" Ko kafin ma ta bashi amsa ya ga zahiri, Alh. Nuran ne tsaye a kofar ofishin. Bakinsa kamar tsage saboda tsantsan farinki"Nura!" Ya amsa"Kawu" ya karaso da sassarfa ya rungume shi" Haba Nura, kamar ba da kowa? Me ya sa ka manta da kannin mahaifiyarka? Ba haka Yaya sa'a ta ba ka tarbiyya ba, me ya sa ka ka sauya daga inda ta ajiye ka?" Kalaman kawu karami suka tilasta ma haywayensa garzayowa waje babu shiri. Ya dago ya dube shi" Ku yafe min kawu, na san ban kyauta ba amma Allah ne shaida na kullum kuna cikin raina." Ya kamo hannunsa  suka Yi cikin gida yana tambaya" Saukar yaushe?" " Wallahi jiya, ai ni nace wa kawu malam kar ya gaya maku na zo saidai ku ganni kwatsam" Dariya sosai yayi " Kai lale marhabin! Ba ka ji farin cikin da nake ciki ba" 

  Jikin Nur ya mutu murus ganin sun manta da ita a tsaye sun wuce abin su, "Me yasa kowa ke son yaya Nura ne? Dubi yadda Baba ya kidime saboda ganinsa? Lallai ya zama wajibi a gare ni in kiyayi kai na domin ban San me zai faru ba muddin Baba ya ji laifin da na Yi Masa." Idanuwanta suka kawo kwalla, cikin tausayin kanta ta taka zuwa cikin gidan.

   Kamar zasu cinye shi haka taras da kowa ya fito kwai da kwarkwata kowa na fadar albarkacin bakinsa, ganin hakan yasa ta silale ta shige dakin matar Baban ta. Shi kan sa Alh. Nura ya San cewa yau ya shigo danginsa ma su matukar kaunarsa Kuma da gani suna cike da kewar sa, shi yasa ya ke jin sa tamkar wani hamshakin basarake. Kan ka ce kwabo an baibaye shi da abubuwan ci da na sha kala kala, daga kowacce sasa kowa Yana kawo abinda Allah ya hore Masa. Sai da ya numfasa kafin ya tuno da yar rakiyarsa," wai Ina Nur? Ta shigo gidan Nan kuwa?" Mama suwaiba ta amsa " Eh Tana nan cikin daki ta ce min kan ta son yayi mata ciwo shine nace ta Sha ko fura ce in bata magani." Yace" Ka ji rguwa, daga katsina zuwa nan shine ta wani narke?" Suna dariya kawu ya ba shi amsa" Nur ce fa! Allah ya hada ka da yar rakiya na san yau ka sha sakarci iri-iri ko?" Yayi Dan murmushi, "Eh to Dan kadan tayi min wai Sai yanzu ta yarda Kamar mu daya. Nace har sunan mu ma iri daya ne.kenan ta tabbata Mai kama da maza" Dariya sosai ya ba su." Nura kenan, to ya hakurin rashe rashe?" Ya amsa," mun gode Allah." Da tausayawa kawu ya Kara fadin " Allah ya taushi zuciya da imani, tabbas ka fuskanci jarabawa domin niKai na bani mance ranar da Halima ta tafi ta bar ni da Nur cikin tsumma. Ni ma kenan Mai guda daya Ina ga kai mai uku?" Ya dan runtse ido ya bude su Jajir," Abin baa cewa komi kawu amma mun gode Allah tunda mu na istigifari." "Haka ne, Amma kana Nan kwana biyu ko?" "Eh zan kwana biyu don na ma gaya wa kawu Ina son ayi family meeting. Duk zuri'a za mu hadu a gana ayi zumunci." "Wannan shawarar tayi kyau sosai Nura."

   Haka suka shagala da hira har aka kira sallah suka Yi alwala suka wuce masallaci hakan ya ba Nur damar sulalewa daga gidan don ko alama bata marmarin sake bin Alh.Nura. Babu wanda yasan ba ta a gidan sai bayan la'asar lokacinda Alh.Nura yayi Shirin tafiya domin kowa yana zaton Tana daya daga cikin sassan gidan. Babu ma Mai takan ta saboda murnar ruwan tsarabar da Alh. Nura ya jibge masu. Kamar Wasa fa aka lalubi Nur babu ita ba dalilin ta.Haushi da takaici kamar kawu karami ya Ari baki ya na ta sababi. Ana cikin haka Hassan da Hussain suka shigo, kannin ta ne da suke uba daya"Wai anti Nur ake nema?" Inji Hassan. Hussain yayi fit yace," Ta fa ce Kar mu fada har ta ba mu naira goma-goma." Kawu ya Kai ma Masa dakuwa," Ka ci gidanku! Za ki gaya min in da kuka gan ta ko Sai na sa an dauko min dorina!" Jiki na rawa suka hau bayani,"mun dawo Kai nika mu ka gan ta zata shiga mota wai wajen Inna za ta je Amma ta ce Kar mu fada min gan ta." Wani karkarfan ajiyar zuciya Alh.Nura ya sauke don tuni ya gano inda ta dosa. Kawu ya Kara fusata," Ka ji sakarcin ko? Yanzu Tana nufin ka jira ta ko Yaya?" A sanyaye ya amsa," Kwantar da hankalinka kawu, Ina ne inda Innar take? Sai mu je da wani na dauko ta." Yace, "Can Yan tumaki ne." " Au Ashe ma ba nisa kuma ai bisa hanya ne.Kawai a bani yaro ya nuna min gidan in ya so shi Sai na sa shi a motar haya ya dawo." Kawu yayi kwafa" Wannan yarinya wanna yarinya! Zan ga ranar da za ta daina sakarci!" Alh Nura ya shafa Kai yace a ransa," Ni ne Nan zan Yi maganin ta!"

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol