Free chapter · Read without an account
Episode 7
KUSKURAN FARKO
BABI NA BAKWAI
NA
ZULAIHAT SANI KAGARA
Gian Innar Nur Bai da nisa da bakin hanya.Alh.Nura ya faka lafiyayyar Jeep din sa suka fito tare da munir kanin Nur, muna iya cewa shi yake bin ta domin shine da na farko a wajen mama suwaiba."Munir shiga ka gaya wa Innar ta Yi bako" ya wuce Yana amsawa. Har dakin Inna munir ke ta zuba sallama tana amsawa. Ta na zaune bisa sallaya da carbi a hannunta tana ja, can bisa gado ya hango Nur kududune cikin hijabin Innar ko zufar gari ba ta ji. "A,ah munir ne? Hala ka biyo yar uwar ka ne?" Ya amsa" Eh tare mu ke ma da bako yana waje." Jin haka yasa Nur ta Kara kudundunewa, zazzabinta ya karu,"shikenan ya gano inda nake da na sa ni Ruga na tsere" Hawaye masu zafi su ka malalo bisa kuncinta.Ita kuwa Inna mikewa tayi tana fadin," To je ka ce ya shigo mana" kafin su dawo ta baza Tabarma. Ya kwararo sallama ya shigo, cikin Nur ya Kara murdewa ji ta ke kamar zata Fara gudawa.Karon farko da ya dubi inna ya gane bafullatanar asali ce, hatta hausar ta da mutum ya ji ya san cewa harshen fulani ne. A haka take ta Yi masa barka da zuwa.Bayan sun gaisa ya bayyana mata ko shi waye, Nan take ta hau sallallami,"lkon Allah Nura am ka sauya gaba daya." Yar darya yayi kafin yace," Dama yar rakiya ta na zo dauka." "A,aha, wai dama tare da Nur ka zo? Ai Ni Bata gaya min ba ka gan ta Nan zazzabi mai zafi ya rufe ta saida kawunta ya Kai ta kemis." Sai a lokacin ya lura da ita bisa gadon kamar an nade kayan wanki. Sosai gaban sa ya tsitstsike ya fadi,"zazzabi?" Bai San lokacin da ya isa gaban gadon ba ya yaye lullubin. Kai tsaye kasan wuyanta ya cusa hannunsa. "Inna lillahi wa Inna ilaihir Raji,un! Ke Nur tashi mu Yi sauri mu koma mu je asibiti! Inna tashe ta mu tafi da sauri" "Anya zata iya kuwa jikinta fa har karkarwa yake Yi." Nan da nan ya goce da fulatanci ba tare da ya sani ba" Inna ba zan iya barin Nur a Nan ba, ki bari mu lallaba mu je likita ya duba ta don Allah inna!" Ita kan ta ba zata iya Hana shi tafiya da ita ba yadda taga ya marerece. Hannu biyu tasa ta tarairayo ta," Daure ki tashi ku tafi ya Kai ki babban asibiti kin ji yar Inna?" Ba ta iya yin musu ba itama bata san dalili ba duk da zuciyar ta ba ta son bin sa, ko dama can ita ba mai gardama ba ce.Duban tausayi yayi Mata, gaba daya ta fada ta Yi dan duhu shi yasa ya kasa cewa komi har Inna ta gama gyara ta ta jawo mata takalman ta daga kasan gado," Ungo sa, Allah ya kara sauki."
Har gaban mota inna ta rako su ta sanya ta ciki Tana masu fatan alheri. Yan dubu dubu guda goma ya mika wa inna sannan ya ba munir dubu biyu yace ya shiga mota. Gaba daya godiya suke zubawa har ya ja ya wuce. Sun jima shiru a motar, shi kan sa ya rasa Mai zai ce,duk Shirin da ya kwaso don ya ci gaba da firgita ta, Nan take ma ya ji sun bace masa. Ya dube ta a Karo na barkatai, tana nan makure kamar yar kyanwa. Ya numfasa q hankali yace," Sannu Nur." Ki ta Yi wasu hawayen shagwaba sun malalo bisa kuncinta, da Kai ta iya amsawa," ki daina kukan haka mana, ai ya isa haka ko?" Ta sa hannu ta dan goge kwallan tare da numfasawa." Don girman Allah Yaya Nura ka Yi hakuri laifin da nayi ma ka." "Wai dama saboda shi ne duk wannan zazzabin?" A shagwabe ta amsa da Kai, wasu kwallan suka sake watsowa ta share da bayan hannu. Dan murmushi yayi yana kada kai, Kamar ba zai ba ta amsa ba kafin yace," Lallai bako ya ci dan gari, Gombawa kenan, baa kwana da mu ba a tashi da mu! To ki Kwantar da hankalinki komi Wasa ne!" Ya Karasa maganar Yana kallon fuskar ta. Itama zuru tayo Masa tsantsan mamaki ya Kama ta.