Free chapter · Read without an account

Episode 8

by Zulaihat S Kagara · KUSKURAN FARKO

KUSKURAN FARKO

BABI NA TAKWAS

NA

ZULAIHAT SANI KAGARA



Wasu hawayen takaici suka ci gaba da sauka bisa kuncinta," Lallai ma mutumin Nan, wai ni zai Yi ma wayau saboda ya ga zamu koma Kar su Gwaggo su gane bayan a gabansu ya nuna babu komi. Wai Wasa...." Ta janye jajayen idanuwanta daga kallonsa."Ai ni da Kai har abada babu yar Wasa!" "Na ga kamar baki yarda da Ni ba ne?" Ta Yi shiru. "To shikenan, tunda ba Wasa bane, ya tabbata Ni ke cinye mata na. Saidai ban san ta wacce hanya ba ce, saboda haka Ina jiran karin bayani" Tuni idanuwan ta ke kallonsa fuskar ta ta dawo abar tausayi," Ni fa ban ce maka ban yarda ba...." "To me yasa zan Yi magana ki wani dauke Kai ki Share Ni?" Ta dan cinno bakin nan da ke sa shi murmushi ko Bai so Yi ba." Ai ni ban San me Zan ce bane" Ta fada kamar mai kunkuni. Yayi yar dariya," Amma kin yarda mu abokan Wasa ne ko?" "I" " Dubi bakinta kamar gidan tsutsa! Wai I...Bakatsiniya kawai." Ta sunkuyar da Kai tana kunkuni" Dadin abin dai Kai ma....." Ji tayi ya katse ta, " Na fa Gaya miki ki dain hada Kai da zuciyarki kuna gulma ta!" Ba ta San lokacin da murmushi ya kwace Mata ba " Yauwa! Ko ke fa? Amma me yayi zafi da har zai tafasa jinin jikinki? A,ah ba haka Nuran Umma yake ba." Nan take ta Ji ran ta yayi sanyi, yar dariya tayi tare da sunkuyar da kai. Kan ka ce me hira ta tsinke ko kafin su shigo katsina ya gama cika mata ciki da dariya ba tasan lokacin da gaba daya damuwarta ta yaye ba. Zazzabin ma ko Ina ya je? Oho!

Tsayuwar su ke da wuya yaran da ke wasa a kofar gidan suka fantsama ciki suna tsalle tare da fadin," Ga su nan, ga su nan!" Su waye?" Ya tambaya. Tace," Duk jikokin su Gwaggo ne" "Masha Allah" A zaure suka hadu da iyayen yaran shewa kawai suke Yi suna mamakin ganin dan uwansu ya sauya. Ya Kara kyau matuka Kuma kallo daya za Kayi Masa ka gane Yana lokaci.Gaba daya cikin gida suka rankaya farin ciki kamar yau take sallah. A tsakar gida suka baje hira ta tsunke. Yayan kawu malam hudu ne duka Mata Kuma kowacce na dakin auranta. Shi kan sa kawun da shigo ya tartar da su ji yayi Hawaye sun kubce masa saboda Nan take ya tuno da yar uwarsa Sa'adatu. Haka suke bajewa ayi ta Hira duk lokacin da ta zo daga Gombe.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.