Free chapter · Read without an account

Chapter 18

by Ummulkhair Abba Muhammad · MIJIN MACE ƊAYA PART ONE



 *WANNE HALI MAIMUNAT KE CIKI?*



 Zaune take dirshan a ɗaki ta miƙe ƙafafu zama da kyar ta shi da kyar.


  Bayan ta shanye lemon da ke hannunta ta dubi mahaifiyarta ta ce, “Umma wayar Daddyn Teema da baya shiga lamarin ya ɗaga mini hankali. Anya lafiya?”


  Shiru ta yi na ɗan wasu sakwanni, zuwa can ta sauke numfashi tare da kallon ɗiyarta ta ce, “Maimunat kina ba ni mamaki shi ya kamata ya damu da ke ko ke. Ka bar mace da tsohon ciki yau ko gobe ba za ka tuntuɓa ka san ya take ba.”


  Riƙe kugunta ta yi ta ce, “Wayyo! Bayana.”


  Ta runtse idanuwanta tare da cizan laɓɓanta ta ce, “Umma ki yi masa uzuri ina ga da dalili.”


Tsaki ta yi kawai ba tare da da ta ba ta amsa ba, tana yunkurin miƙe wa ta ce, “Ina ga fa ya kamata mu tafi asibiti yanayinki na yau ɗin nan.” Waya ta fara ruri.


  Maimunat ta ce , “Umma ki ɗaga ba zan iya amsa wayar nan ba. Wash Allah!.”


  Tana duba wa ta ce, “Ɗan halaƙ ka ƙi ambato.”


  Ta ɗaga tare da yin sallama, bayan sun gaisa ya ce, “Umma ya Maimunat?”


  “Ga ta dai jiki ba daɗi ka ƙira zuwa an jima yanzu ina hanzarin kai ta asibiti.”  Ta katse wayar.

  

   Aliyu tsaye yake ƙarƙashin wata bishiyar dogon yaro, kana ganin fuskarsa kasan yana cikin damuwa ya dafa bishiyar ya ce, “O my God! Maimunat haihuwa ce don wannan watan ne edd nta, kamar na yi tsuntsu na ganni kusa da ke. Ya Allah ka sauki matata lafiya. Ka raya mana abin da ka arzurta mu da shi.”


  “Me kake yi a nan Aliyu kai kaɗai? Duk an haɗu ana hira ana annashuwa amma babu kai a ciki Aliyu. Na fahimci kai a rayuwa babu abin da yake maka daɗi irin kana bakanta mini rai. Na gode.”


  Mahaifiyar Aliyu ke nan da ta tutsiye shi a gabanta.


 Yana sosa keya ya ce, “Mama ki yi hakuri wani ɗan wurin aikinmu ne ya kira ni a waya shi ne na fita na amsa kirar.”


 Dogon tsaki ta ja tare da dalla masa harara ta yi gaba shi ma ya bi bayanta.


 *MU WAIWAYI SAFINAT:*




 Tun da Feenah ta shiga ɗaki don kwanciya ta yi bacci, bacci ya gagara sai juyi take tana tuna maganganu Ummanta a zuciyarta ta ce:

 “Shin Umma me take nufi? Tana nufin hotel-hotel zan dinga bin maza suna fasikanci da ni in haɗa kuɗin da ta buƙata? Ni ba sana'a ba, ba aiki ba a ina zan haɗa kan kuɗin nan cikin sati. Na bi mazan da sai sun gama wulakanta ka kafin ka more su.”

   


  Hawaye ne suka fara sauka a fuskarta ta ce, “Alhaji Tanimu kai ne namiji da ka fara lalata mini rayuwa, kuma kai ne ka buɗe kofar da nake ga shi ya dace da ni a yanzu. Ba don Habib ya fita ƙasar waje karatu ba yaushe zan saurareka.”



  Miƙe wa ta yi ta zauna tare da rafka tagumi ta ce, “Amma ni na sani idan ba da ministers ko senators ba zan yi harka 400k in a week ba zai haɗu ba. Allah ga mu gare ka.”



MUS'AB A GADON ASIBITI



 Hafsy zaune take tana kallon Mus’ab yadda a kasa masa drip yana bacci.



 Likita ne ya shigo ya dudduba shi.


  Ta dubi likitan jikinta a sanyaye cikin rarraunar murya ta ce, “Don Allah likita yaushe zai farƙa?”


  Murmushi ya yi ya ce, “Ki kwantar da hankalinki ke ma ki kwanta ki yi bacci. Zai iya farkawa a kowane lokaci.”


  Girgiza kai ta yi ta ce, “Likita ba zan iya runtsawa ba.”


 Ya duba agogon da ke hannunsa ya ce, “Ki yi haƙuri kar ki sa damuwa a ranki just pray for him, bari na je na duba wani patient.” Ya fice ya bar ta.

  Riƙe hannunsa ta yi ta ce, “*MIJIN MACE ƊAYA* nawa ni kaɗai, Allah ya ba ka lafiya.”


  Motsi ta ga ya fara ta kuma damƙe shi, a hankali ya fara buɗe idanuwansa sai ya ga matar shi ta zuba masa idanuwanta a kansa, ya kuma bi ɗakin da kallo ya ce, “Ina ne nan?”


  Ya duba hannunsa ya ga an saka masa drip nan ya fahimci a asibiti yake.


  Ya fara yunkurin tashi Hafsy ta agaza masa ya miƙe ya zauna yana dafe da bango.


 Murmushi ta yi tare da furta kalmar alhamdulillah tana yi masa sannu.


 MAIMUNATU A ƊAKIN HAIHUWA (Labour Room)


  *WASHE GARI:*



  Da misalin ƙarfe shida na safiya 6:00am Allah ya sauki Maimunat lafiya da santala-santalan tagwayenta (maza). Dukkaninsu suna cikin koshin lafiya.


  Duba wayarta da ke silent ta yi ta ga 20 missed call na Aliyu tare da sakon kar ta kwana kamar haka:


 “Matata ina cikin damuwa na nesa da ke da na yi ko runtsawa ba na yi tun da na tafi kullum da tunaninki da begenki nake kwana nake tashi. Na shiga tashin hankali sama da koyaushe da Umma ta shaida mini halin da kike ciki. Amma zan kwana ina yi miki addu’ar Allah ya raba lafiya. Fatan za ki yi mini flashing a duk lokacin da kika karanta saƙona. Ina son ki matata uwar 'ya'yana.”



 Tana gama karantawa ta sake tattausar murmushi ta yi kissing ɗin sako, kana ta kira shi yana ganin kiran ya yi rejecting ya kira ta.


 Bayan sun gaisa ta yi masa albishir da ya samu twins, Aliyu ya yi murna mara misaltuwa. Daga nan ya ba ta hakuri na rashin kiranta da ba ya yi ya shaida mata a lokacin yana ƙauye ne ba network. Amma bai faɗa mata an ɗaura masa aure ba.



“Allah sarki mijina dama na yi maka uzuri jin ka shiru da na yi na san da dalili.”



  Murmushi ya yi ya ce, “Tabbas haka ne matata, yau in sha Allah za mu taho, yadda nake zumuɗinki da twince kamar na yi tsuntsuwa na ganni.”



 “Mijina sannu-sannu ba ta hana zuwa, ni dai addu’ta Allah ya dawo da ku lafiya.”



  “Amin matata, in sha Allah ma yau muna hanya, yadda nake zumuɗin nan zan lallaɓa Mama a hau jirgi don na ji mota take batu. Shi kuma ba za mu iso da wuri ba.”



  “Kai dai ko a ƙafa ta ce za ku zo kar ka yi jayayya da ra'ayinta ka yi addu’a da fatan zuwa lafiya.”



 “Shi ke nan matata, ki wuni da lafiya ke da twins ɗina a gaishe da Mummy da Daddy da ɗawainiyarsu a ce ina godiya kafin na zo. Sannan a tura mini hoton twins ɗina ta WhatsApp kafin na zo na gansu.”




  Ta amsa da za su ji, bayan ya katse wayar a take ta ɗauki jariran a hoto ta hau WhatsApp ta tura masa, kana ta ci gaba da bibiyar group da take tana karanta abubuwan da aka tura. Sallamar da ta ji ake yi ne ya sanya ta kashe data da ajiye wayar a gefe, cike da fara'a ta amsa sallamar.

 Abbanta da Mahaifiyarta ne suka shigo, bayan sun zauna an gaisa, mahaifiyarta ta ɗauki jaririn ɗaya ta miƙawa mijinta, yayin da ita kuma ta riƙe ɗaya suka yi wa jarirai addu'a suka ci gaba da hira a tsakaninsu.


 

 Aliyu, ya ƙira wayar Umar ya sanar da shi haihuwa, Umar ya yi murna sosai da jin wannan labari, kasuwa ya nufa ya yi wa jarirai har da Mahaifiyarsu shopping na gani na faɗa ya nufi asibiti.



MUS'AB DA HAFSAT


  Mus’ab na zaune yana shan tea Hafsy ta dube shi ta ce, “Hubby ko zan kira mutanen gida a sanar da su halin da kake ciki?”


 Girgiza kai ya yi ya ajiye cup na tea da ke hannunsa tare da ajiyar zuciya ya gyara zama ya ce, “No, ban son kowa ya san abin da ya same ni, ke ma ban son ki tambaye ni me ya haifar da faruwar abin da na riski kaina a ciki.”


  Ɗago kanta ta yi ta kalle shi yayin da idanuwanta lokaci guda yanayinsu suka sauya, cikin sanyayyir murya ta ce da shi, “Mijina na ji ba zan sanar da kowa ba, amma mene ne hikimarka na hana ni sanin silar abin da ya same ka.”


 Lumshe ido ya yi ya ce, “Saboda babu fa'ida a faɗan na san ki ba kya jayayya da ni, saboda haka mu tsaya a abin da na ce.”



  Nocking na kofa da a ke ne ya sa dukkaninsu suka mai da hankalinsu wurin mai shigowa.


 Likita ne ya karaso inda suke bayan an gaisa ya ce, “Dube ta sai washe baki take, amma jiya da daddare duk kin ruɗe.”


 Murmushi ta yi ba ta ba shi amsa ba ya dubi Mus’ab ya ce, “Za mu sallame ka yanzu, amma don Allah ka daina sa damuwa a ranka.”



  Ya juya kan Hafsy ya ce, “Madam ni na san halinku na mata sai a hankali ku yi abu idan ya ɓaci ku fi kowa shiga damuwa, ki daina ɓata wa mijinki rai idan har kina son rayuwarsa ta inganta. Zaman aure sai ana haƙuri da juna a ke cin riba.”

 Ita da Mus'ab suka kalli juna kawai.

 Ya miƙa mata wata ƙaramar paper, “Magunguna za ku saya, Allah ya ba shi lafiya, mun sallame ku.”


 *BIRNIN KANO*



  Aliyu yana gama waya da Maimunat ya shiga toilet domin yin wanka.


Farin shadda da ya sha aikin zubi ya sanya, yayin da rigar shape ɗin ta ɗame shi hakan ya daɗa fito da cikakken kirjinsa. Agogon sarka mai launin golden ya ɗora a hannun shi, ya sanya hula da ta yi matching da zubin kayan da ke jikinsa. Ya sanya bakin takalmi sau ciki mai zallar fata, ya kuma sanya bakin glass ya feshe jikinsa da turarurruka iri-iri ya ɗauki jakarsa yana ja a ƙasa. Shigar da Aliyu yau ya yi ko a ranar auren shi da Ma’u bai yi irin ta ba.


  Falon da su Mama suke ya tunkara yana shiga da ya yi sallama duk hankalinsu ya koma kansu.



 Saif ne ya zo kusa da shi ya ce, “Ɗan uwa irin wannan shiga haka! Ko jiya ranar angwancinka ba ka yi irin shi ba.”


 Murmushi ya yi kawai ba tare da ya ce komai ba, Saif ya kuma cewa, “To mu ƙarasa ka zauna.”



  Mama zaune take bisa lallausar kujera, sanye take da doguwar riga atamfa ta hakimce kamar sarauniya tana kallon talabijin da tuffa a hannunta. Aliyu na shigowa da ta ɗaga ido ta kalle shi ta kawar da kanta ta ba wa telebijin muhimmanci.


  Aliyu ya durkusa har ƙasa ya ce, “Mama an tashi lafiya?”


  Sai da ta cinye tuffa da ke bakinta ta amsa masa da “Lafiya ka lau.” Ba tare da ta kalle shi ba tana kallon talabijin.

  Ya juya cike da girmamawa ya gaishe da dukkanin wanda ke zaune a ɗakin. Ma'u ne ta shigo tana ganinsa ta ji wani gabanta ya yi ras! Ba tare da ta kalle shi ba ta ce da shi, “Barka da safiya.” Ta yi gaba ta shiga ɗakin da a ka tanadar mata ba tare da ta tsaya sauraron abin da zai fito daga bakinsa ba.


 Dama ita tun da suka zo a ka nuna mata masaukinta a nan za ka same ta kodayaushe ba ta shiga cikinsu.


 Aliyu ya sosa ƙeyarsa ya ce, “Mama na san tun ɗa zu ni kuke ta tsimaya na gama za mu iya tafiya.”

 

 Juyowa ta yi tare da sauke numfashi ta dube shi ba tare da sakin fuska ba ta ce, “Tafiya zuwa ina?”


  Kan shi a ƙasa cikin nutsuwa ya ce, “Mama koma wa gida mana.” 


 A fakaice ta ɗan kalle shi ta ce, “Ai kai da Maiduguri sai bayan nan da kwana goma za ka koma, saboda za mu yi ziyarce-ziyarce dangi su ganmu muma mu gansu shekara nawa ba a haɗu ba.”


  Jin Waɗannan furucin Aliyu nan take ya haɗa zufa ya ɗaga kai ya kalli mahaifiyarsa yana ƙoƙarin motsa laɓɓansa ta yi caraf ta ce, “Sai ka kira 'yan ma'aikatarku tun da duk ƙarƙashin ikonka suke su ci gaba da gudanar da ayyuka.”


  “Mama…….”


 Cikin tsawa ta katse shi ta ce, “Ta shi ka ba ni wuri.”


 Aliyu ya miƙe jiki a sanyaye ya fice Saif ya bi shi a baya.



 Wata kujera ya gani a ƙarƙashin bishiyar zaitun ya nufi wajen domin ya zauna.


  Bayan ya zauna a kan kujerar ya fesar da wani irin numfashi mai ɗumi, take ya ji ƙansa ya fara sara masa.


 Saif ne ya dafa kafaɗarsa ta baya ya ce, “Bros ka yi hakuri, kwana goma kamar yau ne fa idan da rai.”


 “Ɗan uwa akwai dalilin da ya sa na zaƙu da tafiyar. Madam ta haihu kuma twins, Mama ta bijiro da wata magana ba za mu koma sai after ten days.”


  Wayarsa ce ta fara ruri ya cire sai ya ga Abban Maimunat ne. Ya ɗaga cikin girmamawa ya gaishe shi.


 Bayan sun gama gaisawa cikin hikima ya sanar da shi abin da Maimunat ta haifa ɗaya ya koma.


 Zumbur ya miƙe! Kamar wanda a ka tsiƙara da tsinin mashi yana mai furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!


  Abban Maimunat ya katse wayar. Saif ya kama ɗan uwansa yana cewa, “Bros lafiya kuwa kana salati?”


 Cikin dashashiyar murya ya ce, “Saif zan tafi Maiduguri yanzu ko Mama tana so ko ba ta so.”


“Ka faɗa mini me ya faru?”


  Kwace hannunsa ya yi ya fice, Saif na ƙwalla masa ƙira da ya dawo ya yi gaba ya bar shi.


  Saif ya yi tagumi ya ce, “Ikon Allah! Aliyu daga waya ka gigice lokaci guda da dalili. Ina kyautata zaton wani abu mara daɗi ne ya faru.” 


  Cikin sassarfa ya doshi falo ya bankaɗe labule ya shiga tsaye ba tare da sallama ba, ganin yanayin da ya shigo ne ya sa ilahirin waɗanda ke zaune a falon mayar da hankalinsu gare shi 


  Tsaya wa ya yi a gabansu, wata irin buga wa zuciyarsa ta fara yi, ƙanin shi ne Kabir ya taso ya zo daf da shi ya ce,  “Yaya lafiya!”


  Ajiyar zuciya ya yi wanda har sai da Kabir ɗin ya ji sautin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciyar da ya sauke.

   

 Cikin kasalalliyar murya da ke bayyana mood ɗin da yake ciki ya ce, “Aliyu ne……” Ya dakata ba tare da ya ƙarasa abin da yake son faɗa ba.


  Mama ce ta miƙe zumbur cike da kaɗuwa ta ce, “Me ya faru da Aliyu Saif?"


Ɗago kansa ya yi ya dubi Mama kana ya kuma sunkuyar ya ce, “ Muna tare da Aliyu a ka kira wayarsa, na jiyo shi yana furta innalillahi, hakan ya tabbatar mini da abu ne mara daɗi ya faru. Bayan ya gama wayar na fahimci yana cikin ɗimuwa na tambaye shi me ke faruwa bai ba ni amsa ba, kawai dai ya ce shi Maiduguri zai nufa yanzu-yanzu ya fi ce a gigice.”


 Mama kana ganin yanayinta za ka fahimci ita ma ta kiɗime, a zuciyarta ta ce, “Tabbas gagarumin abu ne ya faru tun da Aliyu ya kiɗime lokaci guda kuma ya ce zai koma gida a yau. To me ya faru?”


  Wayarta ta zaro ta fara ƙoƙarin kiran wayar Aliyu ta yi sa’a ya shiga amma a ka ce da ita a kashe (switch off). Ta ja tsaki ta dafe forehead nata.



   

 MAIDUGURI:



GIDAN MUS'AB



 Kanwarsa ce ta zo gidansa, ya bayar da wayar da kayan sawan Safinat a ka kai mata.

  Ƴar aike na tafiya, Feenah ta yi try number Alhaji da ya tozartata, da shike ɗan bariki bai da kunya, har sun kara haɗa appointment, don ta gama tunaninta duk cikin samarinta shi ne kaɗai zai iya ba ta mai ɗan kauri.


 Suna zaune da Ummanta ta ce, "Umma dama ina da magana."


 "Ina jin ki." Ta lankwasa wuya tare da marairaice murya, "Umma kema idan kina da wata hanya na haɗo kan kuɗin nan don Allah ki duba, ban son ki dogara da ni na gaza ko shi yaya ko kawu ki yi musu wata karya ki ɗan wawuri wani ɗan abin a hannunsu.

 

  "To shi kenan ba zan ki ta taki ba amma yayanki yadda ta kaya tsakani na da shi a kanki ba zan iya tunkararsa ba, amma zan tuntuɓi wasu."


 Murmushi ta yi, "Yauwa Umma Allah ya sa a samu, ni ma yanzu Alhaji da ya ba ni 100k da shi za mu ƙara haɗuwa."


 Ta washe baki, "Kai don Allah? To Allah ya sa wannan haɗuwar ki samu 200k ko sama da hakan."


 Cikin zuciyarta ta ce, "Ke dai Ummata burinki a samo kuɗi ba ki damu da sanin ta wacce hanya zan samo ba. Allah ya kyauta!" 


Wayarta ce ta so ma ringing ta yi picking "Okay, eh, to ka ba ni 30mins." Tana gama faɗin haka sai ta katse wayar.

 Ta juya dubanta ga Ummanta, "Alhaji ne ya kira a kan mu haɗu."


 "To ai sai ki shirya kije."


 Haka Feenah ta miƙe ta je ta kintsa, Hajiya Laure ta dube ta tana dariya, "Amaryar Mus'ab kinyi kyau fa, Allah ya tsare Allah ya ba da sa'a abin da aka fita ne."


 Murmushi ta yi, "Amin uwa ba da Mama ba, Umma wannan ƙwalliyar da ba abin a zo mu gani ba har da kyasawa."


 "To abin ka da santaleliya kyakkyawar mace ko ya kika ɗan zizara sai kin haska." Safinat ta sheke da dariya ta fice tana cewa, "Ni dai nagudu."


 Bayan fitar Feenah ce, Umma Laure ta ɗauko waya ta ƙira yayanta wato mahaifin Mus'ab, bayan gaisawarsu sai ta kashe murya ta fara magana, "Yaya, dama na je asibiti ba na jin daɗi da na faɗawa doctor abubuwan da ke damuna, ya ce ina da buƙatar a yi min blood test, sannan akwai scan kuma za a ɗauki photo kirji na idan na gama dukkan abin da ya ambata sai naje da shi a nan zai fahimci abubuwan da ke damuna, na yi sati bana iya bacci."


 " Ikon Allah, Allah ya ba ki lafiya." Ta amsa da amin ta ci gaba, "Da na je a ka yi calculating abubuwan da za a yi mini da magungunan 200k ya kama."


 Ya ce, "To, 200k duk a gwaje-gwaje, wannan a asibitin a gida Nigeria ne za a yi ko dai ƙasar waje ne? "


Shiru ta yi, sannan ta ce,"Yaya, kamar ba ka yarda da abin da na faɗa ba, da girmana ta ya zan ɗorawa kaina cuta."


 Dariya maganarta ta ba shi sai ya ɗan yi murmushi.

 "Ta yaya za ki ce kamar ban yarda ba, ke ma dai akwai fassara mutum."

 Ya sauke ajiyar zuciya, "Laure, ni kam kin san irin wannan kuɗin wane mutum, amma ki kira ɗan naki Mus'ab ku gama za ki samu a hannunsa."


 Ta marairaice murya, "Yaya kenan ba ka da labarin mun samu saɓani da shi akan Safinat ba?"


 "Haba! Ban ji ba yaushe a ka yi haka? " Bai faɗa maka ba kenan?"


 "Ai kin san halin ɗan naki zurfin ciki." "To yanzu ko za ka ji."

  Ta faɗa masa karya da gaskiya, ita ba ta san ya san duk abin da ake ciki ba.

 " Shi Mus'ab ɗin ya yi miki haka zai zo ya same ni."


"Yaya rabu da shi, ni ka ganni nan cin mutuncin da ya yi mini har na manta kar abin ya dame ka, yarintace zai zo ya yi hankali, ni dai kawai ka same shi saboda zai ji maganarka ya ba ni wannan kuɗin da kaina zan zo wurinka na karɓa na wuce asibiti."

 "To ai shi ke nan duk yadda muka yi zan sanar da ke."


 Cikin jindaɗi da ke bayyana a fuskarta ta ce, "To babban yaya ina godiya Allah ya ƙara girma da ɗaukaka. "

 Ya amsa da, "Amin, amma akan batun Safinat da kika yi magana ina buƙatar da ke da Mus'ab ku zo mu zauna a yi magana a kai." Ta ce, "To yaya amma sai na gama da harkar asibiti." 

 " Ba damuwa Allah ya ba ki lafiya." Ta amsa da amin ta katse wayar.


 Hajiya Laure nan fa ta dinga kiran numbers na handset na ta tana zuba karyace-karyace kowa da salon karyar da take masa, wasu a take suke ce ta tura account number, wasu ko ce mata suke zasu neme ta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol