Free chapter · Read without an account
13~14
by Khadija · D'A NA KOWA NE
ƊA NA KOWA NE
[RAYUWAR SAMHA]
MALLAKAR...
Mmn Amatullah(Sarauniyar Jarumai👸)
JARUMAI WRITERS ASSOCIATION💪🏻📚
Wannan page ɗin nuku ne,Alaweeyya da Mmn Aisha,, nabaku shi kyauta kuyi yan da kukeso da shi ina matuƙar jin daɗin comment ɗinku da addu'o'inku a gareni inayinku irin over ɗinnan one luv..
Tallah! Tallah!! Tallah!!!
TAURARI BIYU MASU HASKE✨✨
Albishirinku masoya littafan Haziƙar Marubuciyar nan MAMAN AMATULLAH dana Fasihiyar nan wato KYAUTA DAGA ALLAH wa innan taurari biyun sun shirya tsaf domin nishaɗantar da masoyansu da daddaɗan littafinsu mai suna KAICO! Labari ne mai ɗauke sa kiyayya soyayya yana ɗauke da ƙalubale na rayuwa yana tafe da tarin darissa na rayuwa ku biyomu 30 ga watan September akan kuɗi naira 300 kacal👌🏻 domin neman ƙarin bayani ku tun tuɓemu ta wa ɗannan lambobin *** ko ***
Tallah!
Inakuke masu San burge maza jensu Ina Me son ta Zama ƴar lelen mijinta kuma ƴar gaban goshi, to maza ku garzo ga kayan mata ƴan SOKOTO na musamman muna siyar da ɗaya muna bayar da sari, sannan muna da maganin sanyi sadidan karfa ki manta sanyi mugun ciwo ne duk gyaranki idan kina ɗauke da sanyi to barin gyaran shi yafi dominkuwa baze yi miki amfaniba domin Neman ƙarin bayani ku tun tuɓi wannan lambar ***..
Shafi na 13~14
Zaune yake shikaɗai,a kofar gida yana shaƙar iska mai daɗi ga dukkan alamu sun nuna yana matukar jin daɗin yanayin da ya ke ciki...
Sai dai wani gefen,na zuciyarsa yana cike fal,da kewar mama da Abba kamar yan da shima yake da tabbacin suna can cikin tashi kewar..
Ya yi nisa sosai cikin duniyar tinani.
Baba da ke tsaye a kansa tin ɗazu yana kiran sunansa amma Sam bejiba ,hannu ya kai ya taɓashi,tare da cewa "Faruq Allah dai yasa lafiya?
A lokacin da ya tsinkayi muryar baba ne ya dawo cikin hayyacinsa.
Murmushi yayi, tare da cewa "wallahi Baba babu komai kawai dai ina tinanin gida ne" Zama baba ya yi a kusa da shi,tare da faɗin "Haka ne kana da gaskiya tinani ai ya zama dole,amma kaɗan dinga sauƙaƙawa zuciyarka,kaga yau tsahon sati ɗaya kenan da farkawarka,amma jiki Alhamdulillah...Naga hannun ne ka ɗai ya rage,shima saura kaɗan idan ka dage da shafa magani,insha Allah kwana kaɗan,za ka karasah warwarewa sai kafara maganar tafiya gida" Baba ya kai ƙarshen maganar yana ɗan bubbuga bayan.Fatuq,...
Nisawa Faruq ya yi tare da cewa "Haka ne baba,ina ƙara godiya a gareka da irin ɗawainiyar da ku keyi a gareni ko nace ku ke kanyi"..
"Babu komai ai yiwa Kaine..
Fatana dai Allah ya bi da lpia'r jiki" Faruƙ ya amsa da "Amen baba"
Dubansa Baba ya ƙarayi tare da faɗin "Kaci abinci ko?
"Aa,
"To maza ta shi kaje kaci dan ina tinanin tin ɗazu. Samha ta ajiyemaka tashi mushiga ciki" Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa..
***************
Alhamdullah! ,zuwa yanzu mama ta rage yawan tinanin da take sai dai duk lokacin da tatina da.Faruƙ ko ya faɗo mata a rai takan ,zubar da hawayen rashinsa.
Sai dai bata tama bari Abba ya gani ba dan bataso ta dinga ganinsa cikin damuwa,,gakuma Alkawarin da tayi masa dan haka take ƙara tausasa zuciyarta..
Sai dai ta ɗauke duk wani.. Abu da zai saurin tina mata da. Faruƙ, tana ganin idan ba haka tayi ba bata,tinanin zata iya cika Alkawarin da taɗaukarwa Abba..
*********
Da sallama ɗauke a bikinta ta shiga ɗakin..Amsawa ya yi fuskarsa ɗauke da fara'a,tsugunnawa tayi tare,da cewa "Yaya Faruq, ina kwana?
Cike da kulawa ya amsa da "Lafiya ƙalau.Samha, ya ki ka tashi"
"Lafiya ƙalau"
"To masha Allah"
"Dama abin kari na kawo maka"
" ke dai bakya gajiya ko to na gode,yau banga baba a masallaciba,Allah yasa lafiya?
, "Wallahi yau ya tashi da zazzaɓi ne..Asha ai ban saniba,ai da naduba shi,,amma yanzu tashi muje na duba shi," To tace tare da ficewa yana binta a bayan..
Ko da suka shigo gidan,da sallama suka shiga..Mari dake zaune ko dagowa batayi ba balle susaka ran amsawa,,,
Gaisheta,ya yi,, amma ko ke da bakyanan dan ko dagowa batayiba ,gefe ya samu ya tsaya yana jiran samha tayi masa iso dan ya aan ba zata,amsa gaisuwarsa ba,shi dai be san me ya yi mataba,tin ba yan farkawarsa bata taba amsa gaisuwar Saba,,,
Da sallama ta shiga ɗakin baba ta sanar da shi zuwan Faruq, izinin shigowa da shi ya bata, komawa rayi tayiwa.Faruƙ iso..
Shiga sukayi a tare guri ya samu ya zauna yana gaishe da baba ,tare da yimasa ya jiki da cike da kulawa baba yace "Jiki da sauƙi Faruq ya naka jikin" "Alhmdullah da sauƙi sosai"
"Masha Allah"
"Sannan ina mai baka haƙuri,da halin mari dan duk inaganin irin halin da take nuna maka" "Babu komai Baba danni ban taɓa ɗaukansa,da wani manufa ba" Faruƙ ya faɗa yana sun kuyar da kai ƙasa..
" Na goda Allah ya yi Albarka"
In da sama take ya kalla tare da cewa,"ƴar baba har kinshirya fita kiwon ne?
"Eh baba na shirya"
"To maza kitafi kinga yau ke ka ɗai,za ki kuma ki dawo da wuri"
"To Baba amma baba dan Allah ka kula da kanka,har na dawo" Murmushi ya yi tare da faɗin "To ƴar baba karki damu ainamaji sauƙi" cike da jin daɗin abin da yace tace "To baba Allah ya ƙara lafiya"
"Ameen ƴar baba na gode"
Faruq da ke zau ne gefe,,yana kallonsu dan baƙaramin birgesa Samha takeyi ba ganin duk da ƙarancin shekarunta amma tana,matuƙar kula da mahaifinta,gashi kamar ya fuskanci,kamar tana zaman kunci a gidan amma tana da juriya da haƙuri....Maganar da Baba ya keyi ce ta dawo dashi daga duniyar tinanin da ya shiga..
"Tom ƴar baba ma,za je ki Allah ya kiyaye hanya"
"Amen baba"
Faruq ne ya dubi baba tare da cewa "Ai baba ba'ayi haka ba,,bari na rakata,gurin kiwon be kamata ta tafi ita kaɗai ba"..
"Aa ai da kabar shi kaga kaima bawata lafiya ce da kaiba kuma ta Saba tafiya ita ka ɗai,babu wani abu" "Aa baba ai babu komai tin da babu abin da nakeyi bari muje daga nan nima naga gari" Ya kai ƙarshen zancen yana miƙewa.
"To ai shikenan tin da kamatsa sekun dawo"
Tini samha tafito tsakar gidah,,,
Tana fitowa baba mari tace "ke zonan" Jiki na rawa ta ƙarasa in da take tare da cewa "Inna gani"
"Ke canake tin ɗazu na sakaki wancan aikin amma ki ka tsallake,kikatafi,ba kiyi shiba? baki,na rawa tace "Aa inna wallahi zanyi so nake naje kiwo na dawo sai nayi naga rana tayi"
"Eh lalai ne wuyanki ya yi kwari,har in ce ga abin da za kiyi kina bani uzurinki ko dan kin kwana 2 ban dakekiba,dama taraki nake,zonan" Cikin ɓarin jiki da rawar murya tace "inna dan Allah kiyi hakuri wallahi zanyi"
Tini hawaye sun fara zarya a fuskarta..
Hannu ta ɗaga da niyar saukewa a fuskarta muryar Malam ta tsinkaya yana faɗin "karki kuskura ki taɓata,tin da ke babu abin da kikeso kamar kiga kina dukan yarinyar nan,kamar wacce ta tare miki wani abu.Wallahi mari ki dingajin tsoron Allah ...Yanzu ace kamar wannan yarinyar ban da gaba daya aikin gidan nan da takeyi,ace ki kuma tila mata wanchan uban aikin kice tayi haba kidinga tausaya mata,mana, rashin uwa bafa hauka bane to bari kiji na faɗa miki,ni bazan hana samha tayi aikin gida ba amma wannan aikin da ki ka tilo mata,,bayan ta gama na gidah Sam bazan ɗauka ba na faɗa miki....Ke ƴar baba maza jeki kiwonki"
Bejira cewar mariba ya komawarsa ɗaki...Ƙwafa Mari tayi tare da cewa,, "Dani ki ke zancen za ki dawo ki sameni"
Samah jiki a sanyaye,tana share hawaye ta kaɗa shanu sukayi,waje zuciyarta cike da fargabar abin da zata dawo ta tara's..
Tana fita Faruq ya rufa mata baya zuciyarsa fal da tausayin ta sai yan zune ya samu amsar tambayarsa,,akan inna mari,,shi dai a iya zamansa a gidan ,abin da yaga tanayiwa samha ya tabbata babu,uwar da zatayiwa ƴarta hakan.
Tafiya suke,babu mecewa ƙala a cikinsu,in da samha,take ta faman share hawaye..
Gefen Faruq kuma ji yake,duk zuciyarsa babu daɗi,har suka ƙarasa gurin kiwo bata dena kukaba,guri ta samu ta zauna,ta cigaba da rera kukanta,..
Ganin Sam taƙi dena kukanne yasa Faruƙ zama a kusa da ita,tare da kiran sunanta cikin wata itiyar murya,be jira amsawar ta ba ya cigaba da cewa "Haba ƙanwata ki bar kukannan haka mana, ya Isa ko kinaso kanki ya yi ciwo ne ? bata ɗagoba balle ta dena kukan..
"To shikenan tin da ba za ki dena kukanba daga yau ni ba yayanki ba ne kuma mun ɓata" ya faɗa yana haɗe fuska tare da kautar da kai gefe,,
Da sauri ta ɗago,ta dubesa" Batare da ya kalletaba yace "Eh haka nace,,tin da bakyajin magana munɓata" ..
Da sauri ta goge hawayan ta tare da cewa"Wallihi Yaya Faruq na dena kaji,kayi haƙuri" yan da tayi maganarce ta ba shi dariya ,besan lokacin da dariya ta kwace masa ba ita ma murmushi tayi,ganin ya haƙura..
Sai alokacin yaji zuciyarsa ,tayi sanyi ganin yasata murmushi,kallonta ya yi tare da cewa "yawwa ko kefa,yanzu ba ni labari" ya faɗi haka ne kawai dan yasata ta manta da abin daya faru ɗazu..
"Ni dai bani da wani labari sai dai kai ka bani'' "To shikenan ni ina dasu kala-kala,ki karkaɗe kunnuwanki dan kisha labari..,,
Nan ya fara bata labarurruka masu ban dariy,aai tini samha ta manta da matsalar ,inna mari..
Kwanci tashi na Allah ne ,yau Faruq kimanin watansa 2 kenan,a rugar su samha,in da shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin sama da Faruq,,in dai samha bata aiki to tana tare da Faruq, dan zamanta da shi yana sa ta manta da irin halin da take ciki na ƙunci..
Yauma kamar kowanne loka suna zaune a kofar gida in da Faruq yaketa bata labari itakuwa babu abin da take sai dariya,sosai ya shagalad kallonta,dan shi besan me yasa ba duk abin da tayi yana yi mata kyau,sai yaji tana kara birgesa..
"Yaya ya naji kayi shiru ne? firgigit ya dawo daga duniyar tinanin,tare da cewa "Babu komai ƙanwata,kawai ina kallon yan da ki ke nishaɗi ne. ina jin daɗi sosai dan,bana son ganinki cikin damuwa,in na ganki cikin damuwa sai naji namafiki shiga damuwa"
Murmushi tayi tare da faɗin "Na gode yaya da sani farincin da ka ke"
"Babu komai ƙanwata,ai yiwa Kaine,
"To yaya kacigaba da bani labarin mana" Ta faɗa tana turo ɗan ƙaramin bakinta,gaba gani ya yi ta ƙara yimasa wani kyau na musamman besan lokacin da ya yi murmushiba tareda cewa "To ƴar shagwabar baba in dai ni ne bama sai kinyi kukaba dan zan cigaba da baki labari har sai kin ce ya isa" Cike da zumuɗi,tace "Allah yaya? yace "Da gaske"
"Amma kin ga yanzu yamma tayi,kibari sai gobe, sai muci gaba ko?"
"To shikenan Allah ya kaimu yaya"
"Ameen ƴar ƙanwata,shi yasa ki ke kara birgeni sabi da baki da musu yanzu maza tashi kishiga gida kinga har anfara kiran sallar magrib"
"To Yaya sai da safe"
"To Allah ya tashemu lafiya"
Tashi tayi ta nufi gida,in da Faruq ya bita da kallo yana jin wani gefe na zuciyarsa fal da nishaɗi
Alwala ya yi ya wuce masallaci,..
Alhamdullah zuwa yanzu Faruq ya warke garau,kai ba kace shiba ne ya yi wannan jinyar,in da zuwa yanzu har ya tsayar da ranar da zetafi gida wato sati mezuwa,insha Allah yake sakaran tafiya...
***********
Baba na hango,zaune a kofar, gida ya lula duniyar tinanin.. Faruq nr ya fito daga cikin gida ya hangosa,kai tsaye in da ya ke ya nufa da sallama ya ƙarasa ,amma sai ya ji shiru baba be amsaba,nan ya fahemci kamar yana cike da damuwa "Baba" ya kira sunansa tare da ɗan taɓa shi,kai ya ɗago tare da cewa "Aa Malam Faruq kaine? "Eh baba ni ne lafiya kuwa" Faruƙ ya tambaya yana duban baba..Hmmm nisawa baba ya yi tare da faɗin "Lafiya ba ƙalau ba Faruƙ" "Subahanallah! Baba me ya ke faruwa haka? guri baba ya nuna masa,tare d acewa,, "Zauna".
Dubansa baba ya ƙarayi a karo na biyu, tare da cewa "Faruq ba komai ya ke da munaba,sai irin RAYUWAR DA SAMHA takeyi a cikin gidannan,, tin da ta tashi a gidannan Sam batasan wani Abu wai shi farin ciki ba,kullum cikin k
ƙunci take da damuwa,kadubi irin ƙanƙantar shekarun yarinyar nan amma wai har ta,iya ɓoye damuwarta,a ranta,nayi,faɗan nayi masifar,amma.. Mari ba ta jin magana, daga zarar taga babu idona,tofa sai in da ƙarfinta ya kare, akan yarin yar da har yanzu da uwarta na da rai batawuci a tarairayetaba, toni duk ba ma wannan ba,tsorona Allah tsorona kada wata rana,wani ciwon ya sameta akullum idan na tina halin da take ciki abin yana ɗagamin hankali" Ya ƙarasa maganar cike da raunin zuciya...
Hmmm nisawa Faruq, ya yi tare da cewa, "To dan Allah baba kabar damuwa kaga yawan damuwar ze iya haifar maka da wata matsala..Allah ze kawo mata ɗauki addu'arka kaɗai take buƙata insha Allah... Allah zekawo mafita amma dan Allah kacire damuwa a ranka" ,"To shikenan faruƙ na gode zanyi yan da ka ce ɗin Allah yasa mu dace.Ya shirye- shirye'n tafiya anan ana yi ko? "Eh baba" "To Allah ya nunamana yau saura kwana 5 ko?
"Eh insha Allah"
"To Allah ya kaimu"
"Amin"
Nan dai suka cigaba da hirarsu..
***********
"Yanzu fa Yaya saura kwana 3 katafi ko?
"Eh ƙanwata"
"Shikenan idan katafi bazamu sake ganinkaba?
"Aa ai konatafi watarana zan zo a gaisa ai yanzu kun zama tamkar ƴan uwana dan ba zan taɓa manta alkairinku a gareniba,insha Allah ko da na tafi watarana zanzo mugaisa"
Cike da zumuɗi tace "Allah yaya da gaske za ka din ga zuwa muna ganinka" Yan da SAMHA tayi maganar kai kasan tana cikin farin ciki...
"Eh da gaske ƙanwata nayi miki Alkawari" ya faɗa yana murmushi..
"To na gode" Ta faɗa cike da zumuɗi,nan sukacigaba da firarsu cike da nishaɗi,...
Washe gari..
Yau tin da Malam y tafi masallaci sallar asuba be dawoba sakamakon rasuwar da akayi a makotansu,,
Wannan yabawa Mari dama ta ida wani nufinta,wan da tin tini ke riƙe dashi a ranta take kuma jiran irin wannan, ranar,,da Malam baya nan dan taci Alwashin sai SAMHA ta faɗawa " ƴan garinsu,ba dai malam ne yake hanawa a taɓata ba to yau bayanan, zataga me kwatar ta dan yau sai ta sauke duk wani fishinta a kanta..
Icen darbejiyar ta karyo mai rai da lafiya, kai tsaye ɗakin SAMHA ta nufa,wacce take kwance tana baccinta mai cike da daɗi,cikin baccinta taji wani lafiyayyan duka wata irin kara ta saki tare,da mikewa tsaye,,
"Dan ubanki,buɗe idonki nice nan,ba dai uban kine yake tare miki ba to yau baya nan sai naga wan da ze tare miki"
"Inna dan Allah kiyi haƙuri"
"Bashi ya kawoni ba"..
Ƙarar da tafasa ce ta farkar da Faruq, daga gajeran baccin da ya ɗau kesa,yana yin...AZKAR..
Dukanta ta fara kamar wacce aka aiko,,,SAMHA kuka take tana rokonta tayi haƙuri,ai kamar ma zugata take, dan ƙara azama tayi gurin dukanta kamar ta samu jaka...
Tin yana zaune yanajiwo kukan sama-sama kuma kamar SAMHA ya ke ji..,
Jiyayi kukan yana kara karuwa,kuma lallai samha ce ji ya yi zuciyarsa ta buga da ƙarfi,cike da azama ya fito ya nufi cikin gidan'
Shigowarsa tayi dai-dai da fitowarta,a guje daga ɗakinta tana kuka tana ganinsa da gudunta,ta faɗa jikinsa,tarirriƙesa tana kuka,,,tana cewa, "Yaya dan Allah ka ɓoyeni inni zata kasheni" idan ransa ya yi dubu,ya ɓaci,ji ya ke zuciyarsa tana yimasa suya..
Inna na fitowa in da SAMHA ta ke ta nufa, tana cewa "Ƙe kina ganin dan kinzo nan kina ganin kin ɓuya," ɗaga bulalar tayi da niyar ta sauke a kan SAMHA, charaf Faruq ya ri ƙe bulalar,dubansa tayi tare da cewa "kai waye da ina hukunta ƴata,za ka hana to wallahi kasakarmin tinkafin na ɓata maka rai",
In da yake atsaye,,ko motsawa beyiba kuma besakiba bekuma tanka mata ba,
Nan ta cigaba da masifarta,be dai sakiba kumah be tanka mata ba kuma ta kasa fizge bulalar..
Muryar Malam suka tsinkaya yana cewa, "A ina ta zama ƴarki,idan "yar kice ai ba za ki tasheta ,da wannan, mahaukacin dukan ba amma babu komai ai rayuwace,kuma daga yau ina mai tabbatar miki kin daki SAMHA duka na ƙarshe"
Daga haka be ƙarace mata komai ba ya dubi SAMHA yace "Maza je ki,ɗaki"
"Aa baba ni wallahi tsoro na keji,zata ƙara dukana" tafaɗa cike da tsoro,..
"Kina jina ƴar baba ki kwantar da hankalinki,komai yazo karshe da yar dar Allah,maza,je ki ɗakina ki kwanta"
Ya mayar da dubansa kan Faruƙ tare da faɗin "Faruq biyoni muje,inaso nayi magana da kai"...
Zama sukayi a ɗakin Faruq, Faruq ya duba tare da cewa, "Da farko dai inayi maka godiya dan da baka nan bansan mezefaru da Samha ba",
"Kai haba baba babu komai ai yiwa Kai ne ba sai ka godeminba "
Jin jina kai Baba ya yi tare da faɗin "Sannan Faruq idan babu damuwa inah Neman,wata Alfarma a gurinka ban saniba ko zan samu"
"Alfarma kuma Baba ai amatsayin uba na ɗaukeka,umarni kawai zakabani ni,kuma nabi,kafaɗa kawai baba babu damuwa insha Allah nikuma zanyi maka" Ya ƙarasa maganar yana sunkuyar da kai ƙasa..
Cike da jin daɗin kalaman Faruq baba ya ce "To na gode,da wannan karamcin da kayimin,dama Alfarmar da nake,nema ita ce, ina so idan babu damuwa kuma ban takura makaba, *na aura maka SAMHA*..... Da sauri Faruq ya ɗago ya dubi bab,, baba ya cigaba da cewa "Amma kada ka dauka wai dan na temaka maka yasa nace haka.. Aa sai dan na yar da da tarbiyanka kuma na San zaka riƙemin ita amana,amma fa duk hakan baze yuwuba sai ka amince,dan Allah idan baka aminceba,,karkaji kunyar sanar dani,, kuma hakan ba ze chanza alakarmu da kaiba"...
Hmmm, nisawa Faruq ya yi tare da cewa "Babu komai baba na amince,kamar yan da,na faɗa a baya cewa kai ɗin uba ne, yau ko da ace wata ce ka ɗauko ka bani ba SAMHA ba zan karba dan nasan baza ka cutar da niba to,balle kuma wacce,da ita aka haɗu akayimin abin da ba zan taɓa mantawaba babu abin da zance baba sai dai godiya"
Cike da matsanancin farin ciki baba ya ce "Na gode Faruq Allah ya saka da Alkairi..Allah ya faranta maka kamar yan da kayimin" ..
"Baba babu godiya a tsakanin mu, idan akwai wan da ya kamata ya gode ai ni ne..
Nan dai baba ya dinga saka masa albarka cike da farin ciki...
Bayan an idar da sallar azahar akashe da *auren Samha da angonta Faruq,,..
Tofa yanzu ne za'a fara wasan my fan's...
Ummu amsad ce😍