Free chapter · Read without an account

Kuliya Kuliya...

by Azizat Hamza · SAHLA a Paris


TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

006... "Kuliya Kuliya cinye min kashina" inji Sahla...

Yau Alhamis tunda na dawo daga school na fara kokarin yin assignment ɗin English da aka bamu dan gobe da safe za a karɓa. Ina son darasin English saboda shine kaɗai ko ban yi karatu ba na kan taɓuka abin kirki.

"Sahala tashi ki karɓo min Abinci tunda ke yunwar bata ishe ki ba"

"Kaka Dan Allah ki bari na karisa rubutun nan"

Can kamar minti ɗaya Kaka ta sake yi min magana. Na shareta.

"Sahala wai sai hanjina sun gama nannaɗewa ne kan za ki kawo min abincin ne"

"Kai Kaka" na dangwalar da littafin na je ɗaya ɗakin na ɗauko cooler na wuce sashin Anty Amarya. Na rike ranan girkin kowacce a cikinsu kamar yadda na rike irgen kwanaki.

Ina nufowa ɗan karamin gate da ya raba ɓangarenmu dana matan gidan na fara jin hayaniya. Muryan Anty Amarya ne ke tashi. Ban taɓa ji tana masifa irin haka ba. Ina zuwa kofarta na tarar da kaya jibge a wajen. Hayaniyar ta ciki ne. Na kutsa kai na shiga.

Fitowa kawai take da kayanta daga ɗaki tana jibgawa a falo. Su Mama da Ummi na wajen suna bata hakuri amma sai masifa take.

"Ni zai nunawa ya san Amana. Ya san sarai inda ya ɗaukoni ba gidan matsiyata bane. Aure shekara goma miya tsinana min. Dan ban haihu ba nina ke hana kaina haihuwan ne. Yau zan bar masa gidan. Bani da kowa a gidan nan amma wani irin bauta ne bana yiwa 'ya'yan gidan"

"Sai hakuri dai Rafee'ah" Mama ta faɗa tana kokarin matsar mata da akwati gefe dan Anty Amaryan ta samu ta ajiye jakar da ta fito da shi.

"Zan bar masa gidansa. Alhamdulillah tunda ba wajen zama na rasa ba"

Shegu sai hakuri su ke bata amma babu wanda yai yunkurin hanata tattare kayanta. In da babu munafurci ai Kaka zasu kira ta zo ta hanata tafiya amma suka makale suna bata hakurin karya.

"Anty Amarya Dan Allah ki yi hakuri"

Allah na gani na fi sonta duk cikin matan gidan nan. Idan ta tafi ya zamu yi ni da Kaka.

"Matsa min a waje kiga" ta ɗan bugeni kaɗan ta wuce da wasu akwatunanta waje.

"Wai ina Hamza ne?"

Mama ta ɗan karkatar da kai wajen Ummi tace " ni kam Akwatunan Rafee'ah nawa ne? Wancan kam ba irin akwatin lefen Firdausi ba"?

"Irinsu ne fa. To yaushe ta sauya akwatuna"

Shigowar Anty Rafee'ah yasa suka yi shiru. Na yi mamaki ma da annamimiyar gidan bata shigo ba, kila bata nan ne.

Na fito daga falon na nufi ɗakinmu. Yadda Anty Amarya ke fitar da kaf kayanta bana tunanin ta yi girki yau.

"Ina abincin? Ko bata gama ba"

Ashe ma na bar kular tamu a chan.

"Kaka, Anty Amarya fa yaji za ta yi. Gata chan tana tattara kayanta"

"Yaji kuma?. Miya faru?"

"Ni ina zan sani"

Kaka ta mike daga tabarmar da take zaune tace mu je. Na bita a baya dan nima ina son sanin abinda ya faru.

Lokacin da muka je Kaninta Hamza ya zo yana ɗaukan mata kaya yana kai mata zuwa motarta. Dama duk gidan ita ke da mota ta kanta, sauran kam sai dai su yi amfani da motan gida na Alhaji.

"Rafee'atu ya haka? Mi ya kawo maganan yaji"

"Hajiya Kaka kiyi hakuri ki tambayi ɗanki"

"Rafee'atu ban san ki da rashin kunya ba. Mu shiga ciki ki gaya min abinda ya faru"

"Babu bayanin da zan miki. Abu ɗaya nake so ki min, Dan Allah ki sa Alhaji ya aiko min da takardata gidanmu"

"Ina shi Kabirun?"

Ummi tayi caraf tace " ya fita tun safe"

"Munafukai, ina gidan nan Rafee'atu tana kwashe kayanta ba za ku zo ku gaya min ba. Aishatu kira min shi Kabirun"

"Hajiya ko an kira shi ma ba ɗagawa zai yi ba kila yana masallaci"

" kira mini shi na ce" Kaka ta daka mata tsawa

"Bari na je na ɗauko wayar"

***

Paris, France

"Aly come here. Come closer. I'm waiting"

Yaron ya ja baya hannunsa na rawa, fiskarsa cike da hawaye yana girgiza kansa tareda faɗin "No, please no"

"Please Nooooooo"

A firgice ya tashi daga bacci fiskarsa ya jike sharkaf da gumi duk da cewa a zahiri ɗakin akwai sanyi.

Ya kunna fitilar ɗakin haske ya karaɗe katafaren bedroom ɗin.

Matashi ne da ba zai wuce shekaru

Talatin da uku zuwa da huɗu ba. Dogo ne kuma ba shi da jiki.

Yaye farin duvet ɗinsa yai sannan ya sauko da kafafuwansa kasa, ya dafa kai yana sauke numfashi a hankali. Kusan sakan goma yana haka kafin ya mike ya wuce banɗaki.

A gaban madubin dake banɗakin ya tsaya yana karewa kansa kallo.

'Komai zai daidaita, abubuwa zasu chanja' abinda yake ta maimaitawa a ransa kenan.

Ya jima a haka kafin ya samu ya watsa ruwa sannan ya fito.

Sai da ya shigo ɗakin ne ya dubi agogo ya ga karfe biyu da rabi na dare shi da bacci kuwa sai wani daren dan idan yace zai sake kwantawa ma ba iyawa zai yi ba. Daga shi sai bathrobe ya wuce ɗakin karatunsa. Buɗe computer ɗinsa yai ya fara aiki. Kusan kowanni dare aikin kenan. Zai kwanta, zai yi mugun mafarki, zai tashi yai wanka ya zo yai aiki ko kuma ya fara karatun littafi...

Washegari da safe yana haɗawa kansa breakfast wayarsa ta shiga ringing. Sayyidah ce.

"F Kay ka kira Dad ka mishi magana. I can't take it anymore. Zan aikata abinda zuciyata take so, and i don't give a damn"

"Calm down SD. Zan sake yi mishi magana"

"Iyayen Irfan suna jiranmu. Bamu da lokaci"

"Zan kira shi. Ki kwantar da hankalinki"

Yana ajiye wayar ya shiga nazari. Alhaji yana so Sayyidah ta yi aure amma kuma baya so ta auri mutumin kasar Pakistan, wannan kuma so yake ya take mata 'yancinta na zaɓin wanda take so.

***

Kwana biyar kenan da yajin Anty Amarya. Dake ina makale da Kaka na samu information akan dalilin tafiyarta.

Duk maganar akan Sayyidah ne. Wai ita Sayyidah ta nace wani ɗan India za ta aura ko ana so ko ba a so. Shi kuma Alhaji tunda Uncle Faruku ya masa maganar lokacin bikinsu Anty Firdausi yace bai yarda ba. Ta dawo gida ta auri wanda aka san asalinsa.

To akan maganan ne Anty Amarya ta yiwa Alhaji magana akan ya hakura da zaɓin Sayyidah tunda shi mutumin da take so musulmi ne. Shi kuma Alhaji ya tuhumeta da cewa ita ke hurewa Sayyidah kunne. Shikenan Anty Amarya ta ɗau zafi ta ringa mita, shima Alhajin da yake a tunzure yake sai ya biye mata.

A bisa majiya mai karfi wai Anty Amarya tace tunda ya mata gorin haihuwa ita ba zata dawo gidansa ba sai dai ya aika mata da takardarta.

A wata majiyar kuma ni da Kaka mun samu rahoton cewa shi Alhajin yana neman wata bazawara ne, shine zancen ya isa kunnen Anty Amarya ita kuma ta ɗauka yana mata gorin haihuwane shiyasa yake shirin sawwake mata ya auro wata.

Koma minene dai ni da Kaka muna jin jiki a hannunsu Mama dan yanzu kaf ɗinsu sun haɗa baki wajen rage mana kason abincin da ake zuba mana.

Kaka ta yiwa Alhaji magana akan ya je ya dawo da Anty Amarya amma ya ki. Yace idan ta ga dama za ta dawo da kanta tunda ba sakinta yai ba...

*

"Waye ne a nan? Waye ke kaɗa min gwaiba"

Na yi shiru ina cigaba da kaɗo gwaiba. Ga gwaiba nan sun yi ɓula-ɓula amma Kaka ta hana a cire wai basu gama kosawa ba.

Bishiyar a bayan ɗakinta yake kuma duk cikin bishiyoyin Gwaiba dake gidan wannan ɗin tafi yin mai kyau kuma manya.

Cakwal-cakwal sai ga Kaka ta fito daga ɗaki a fusace ko zani bata gama ɗaurawa ba. Wannan bishiya kamar ranta ne a jiki dan yana ɗaya daga cikin abinda ke haɗamu faɗa da ita.

"Sahala ina magana kina shiru. Ba nace sai karshen watan nan za a cire Gwaiban nan ba"

"Kaka da yau da karshen wata duk ɗaya ne. Ni kam Wallahi ba zan jira ba, kika sani ko na mutu kafin lokacin"

"Sahala ki kiyayeni. Ya isheki haka nan"

Ta kama sandan ta rike.

"Kaka ki bari na kaɗo wannan daga ita shikenan"

"Na ki ɗin. 'Yar banza kina ganin duk nacin Abbas na hana shi taɓa gwaiban nan amma dan munafurci kika biyo baya kina satan min"

"To sai ki yi ai"

Na ɗauki na karshen da ta faɗo na wuce wajen famfo, kamar jaraba Kaka ta biyoni tana faɗin sai na nuna mata nawa na ɗauka.

Da muka gama darun fa da ita aka zauna aka ci gwaiban na ci biyar ta ci uku.

Da Isha cikina ya ruɗe na nufi banɗaki zan buɗe na ji anyi gyaran murya.

"Kaka ki fito kashi zan yi"

"Nima ita zan amma ta ki fitowa"

"Kaka Allah rabin minti na baki ki fito"

Na tsaya jikin kofa ina ɗan jijjiga jikina kaɗan-kaɗan ko kashin zai tafi. Chan na tuna da wakar da muke lokacin muna yara. Na fara rerawa a hankali.

"Kuliya Kuliya cinye mun kashina"

Na sake buga kofan " Kaka ki fito mana"

Maimakon tayi magana sai tayi gyaran murya.

" Kaka ki fito fa. Zan miki kashi a ɗaki Allah"

Na tsugunna a wajen na rike ciki ina jijjiga jikina ina yin wakar da karfi.

Chan kusan minti goma sai Kaka ta buɗe kofa.

Hawaye na gani a idanun Kaka.

"Dama na gaya miki Gwaiban nan bata gama kosawa ba"

"Kaka ni kam ki matsa"

Na wuceta na shige banɗakin.

Na zauna a toilet seat ɗin ina jira na ji zurrrrr sai na ji wani zafi a takashina. Ina nishi ina tura kashin amma ya ki fita. To ko dai takashina ya toshe ne?

Na sake yin nishi ina turawa amma abu shiru. Can wani mai tauri ya fara fitowa amma sai ya makale shi bai faɗi ba shi bai fito duka ba.

"Wayyo Kaka nima yaki fitowa"

Inaga na yi minti ishirin a banɗakin nan ina nishi, ga Kaka sai buga min kofa take.

Na fito haka nan ba tareda na samu biyan bukata ba.

Ni da Kaka muka tsaya kallon kallo.

"Ke sabulu zamu saka zai fito "

"Sabulu kuma Kaka"

"To ki kunna mana risho mu turara takashinmu da ruwan zafi"

"Allah ya kiyaye Kaka"

Ai kuwa duk option ɗin da Kaka ta kawo sai na ce bai yi ba. Karshe nace barin je na karɓo mana magani a wajen Mama ko Umma Bilki na san ba za a rasa ba.

Na je na karishi zagayena wai babu maganin ciwon ciki.

Na dawo na samu Kaka ta kunna stove ta ɗaura ruwan zafi a tukunya.

Ko mi tsohuwar nan ke shirinyi oho.

Ni dai na tsugunna gefe na cigaba da wakata 'Kuliya Kuliya cinye min kashina"....

Litattafan TOP-NOTCH

Abinda ya baka TSORO---Ramlat MaiDambu

Bani da LAIFI--- Shatuu

SAHLA a Paris---Azi_zat

Guda ɗaya 350

Biyu 700

Uku 1000

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.