Free chapter · Read without an account
SHAFI NA 03
```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺📖?
MARUBUCIYAR...✍️
Bayan Wuya
Ashe ba so ba ne
Zumunta ko Mugunta📚
BY- Fatima Zara Alhassan ❤️
ƴar mutan Argungu
GARGADI!!!
ƙagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata, su juya mi ni littafi, ba ta re da izini na ba!! Sabo da haka a kiyaye👂!!!
JINJINA
Ina jinjina ga mabiya littafai na, nagode sosai Allah ya barmu ta re🥰💛💙
SADAUKARWA
ga yan' uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma qara hada kanmu, mu yi zumunci🤝❤️
MY FANS WANNAN SALON NA DABAN NE. KAR KU BA RI ABAR KU A BAYA🤪
Free pages
SHAFI NA 3
BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM
Ya gane nufin ta shiyasa ya ci gaba da cewa...
Sunana FU'AD BAQER JAMEEL,dan sarkin Aljanun FARISa. Mahaifina sarki Baqeer ya na da mata biyu, sarauniya AYRA da kuma SARAUNIYA SaMEE. Sarauniya Ayra ita ce uwar gida,ta na da yara biyu, yarima fu'ad da kuma gimbiya Hoor.
sai Sarauniya Samee, ita ba ta haihu ba,amma ta na ruƙon ɗan uwan ta. Wato Aasim, ƙanene a wurin ta.
Sarauniya Samee, yar uwar sarki Baqeer ce, auren zumunta aka yi mu su, while sarauniya Ayra Auren soyayya su ka yi. ita yar sarkin misra ce( Egypt). Ta kuma gaji sarauta gaba da baya, shiyasa duk wata hauka da sarauniya samee ke yi akan mulki ba ya damunta...
lokacin da kakana sarki Jameel ya bar duniya sai a ka nada mahaifi na ya zama shi ne sarkin farisa. Shi kuma kawu Aasim aka ba shi waziri. Wannan abun ya yi wa sarauniya samee ciwo ainun, domin ta so ace ƙanenta aka ba sarki,ba mahaifi na ba, Shi ne ya cancanci ya yi mulki ba mijin ta ba, sabo da ita tun farko mulkin ta ke so ya dawo hannunta shiyasa ta Auri sarki Baqeer. wannan kenan...
Shiyasa ta haɗa kai da ƙanenta su kashe sarki. Haka su ka bi duk dakarun sarki su ka saye su ba ki ɗaya...
Duk wani abu da sarki Baqeer zai yi toh waziri Aasim zai ce be yi daidai ba. Shiyasa duk wani abu da waziri zai zo da shi, sarki Baqeer zai karba sabo da a zauna lafiya,amma fa matukar bai sabawa addinin sa ba.
Ashe ba nan gizo ke saka ba, duk wani tanadi na halaka sarki ya ta na de shi.
Wata rana ana zaune a fada, sai ga waziri Aasim ta re da makaman yaƙinsa,ya ce lallai sai mahaifi na ya sauka daga karagar sa , shi ya hau. Wannan magana ta bata ran mahaifi na sosai!!! "kai Aasim ka natsu kasan agaban wadda ka ke yin magana!!! Dan haka ka gyara kalaman ka, ko kuma yanzu insa ayi min kasakasa da kai a nan wurin...!!!! Wata yar iskar dariya Waziri Aasim ya ke yi, ta re da nu na sarki Baqeer ya na cewa, haba dan uwana kuma sarkin Farisa...waiii tsohon sarki zan ce, ta re da bushewa da dariya... sai can ya tsagaita dariyar sa, ba dai tun yanzu ka karaya ba? kar ka damu idan ka barmin sarautar zan barka da lafiyar ka amma, matukar ba ka bar karagar nan ba, toh wallahi ni ne ajalinka...!!
Mai ku ke tunanin zai faru da sarki Baqeer? Shin ku na ganin zai sauka daga karagar sa, ko kuma zai yaki waziri Aasim?
DOMIN GUDUMUWA KO SHAWARWARI PLS
***
Dan Allah kar ku man ce da yi min
COMMENTS
SHARE
FOLLOW
E.T.C
YAR MUTAN
ARGUNGU``` ✍️📚