Free chapter 路 Read without an account
SHAFI NA 09
```ZUMUNTA 馃 KO MUGUNTA 馃懞...鉁嶏笍
MARUBUCIYAR...鉁嶏笍
**Bayan wuya **
**Ashe ba so ba ne**
**Zumunta ko mugunta? on typing...鉁嶏笍
BY - Fatima Zara Alhassan 鉂わ笍
(拼ar mutan Argungu)
ARGUNGUN WRITERS ASSOCIATION 馃挄
GARGADI!!!
kagaggen labari ne,sabo da haka idan ya yi dai-dai da rayuwar ku, toh akasi ne. Littafi na ba na sayarwa ba ne,wallahi duk wanda ya saida shi ban yafe ba!!!
GODIYA馃憣
Ga mabiya karatun lattafai na, Allah ya saka mu ku da alkhairi 馃グ
JINJINA
Ga yan uwa na Allah ya kara dankon zumunci, ameen 鉂わ笍鉂わ笍鉂わ笍
FREE BOOK 馃摎
SHAFI NA 9
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
************************************************Akwana atashi asarar mai rai, ga shi har anyi bikin Abubakar da Atika. acikin shekara daya Atika ta haihu, zo kuga murna awurin Iya, yaro ya ci sunan Tukur watoh mahaifin Atika, sabo da tsaye tayi ta ce atafau, ba za a saka ma yaronta sunan kowa ba, sai na mahaifin ta. Iya ido rufe ta ce a saka...
shekara daya tsakanin haihuwar Tukur, ta sake haifo wani yaron kuma ,haka ta murje idanuwan ta, wallahi sai sunan da ta ke so za a saka, hakan ya sa suka yi rigima sosai da Abubakar, sabo da shi ya na son a saka sunan mahaifin sa. Haka iya ta lallaba Abubakar ya yi hakuri a saka wanda ta ke so. Ita ma iya yanzu abun na Atika ya fara ba ta haushi.Haka aka yi suna yaro ya ci sunan Adamu.
Haka Atika ke ta murza mulki a cikin gida, gori da habaici ba wanda Zainaba ba ta gani ba, don ma wata rana malam Abubakar na taka ma ta burki idan ya na nan. Murnar iya ta koma ciki, sabo da Atika ba ta barin yaranta su je wajen iya, tun abun na ma ta ciwo, har ta zubawa sarautar Allah ido. Wasa-wasa har Atika ta yi shekaru shida agidan malam Abubakar. kwatsam! Sai ga ciki ya bai yana ga zainaba, zo ku ga murna wajen malam, kamar ba a taba haihuwa a gidan sa ba. Haka ita ma iya, ba a barta a baya ba, duk wani abu da zainaba ke so jiki na rawa ta kawo ma ta shi. Aka ce "rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya", toh hakan ce ta kasance a gidan malam Abubakar, zainaba ta haihu lafiya, ta samu Yaro... Ranar suna aka sa ma yaro sunan mijin iya watoh Abdul'aziz, amma su na kiransa da Abdul. Sabo da iya ta ce kar a boye sunan. Haka yaro ya taso cikin gata, duk abun da ya ke so, iya za ta sai da dabbobin ta, ta saya mishi. Malam Abubakar kuwa arxikin sa ya karu, ba bu inda ba asan malam Abubakar mai noma ba. Haka ya tattara yaran sa, ya saka su a makarantar boko da na islamiyya.
Bayan sun gama primary school, ya kai su boarding school KANTA COLLEGE. Ya yin da ya'yan Atika su ka gama, shi kuma Abdul na ss1, iya ta rasu...Haka malam Abubakar ya sa ka suTukur da Adamu gaba, akan dole su ci gaba da karatu, san nan kuma su ci gaba da noma, sabo da gadon gidan su ne kuma dai ai sana'ar hannu ce. Amma su ka yi tsaye suu sam, ba za suyi noma ba, sabo da aikin wahala ne,haka innar su Atika ta daure musu kar suyi noma. Malam abubakar bai ce musu komai ba ya kyale su.Bayan takad dun su sun fito ya tura su Alieru university, Tukur na karanta law, Adamu kuma likita. Da farko sun mai da hankalin su akan karatun su, amma daga baya su ka biyewa yan iskan abokai, su na shekara ta biyu aka koresu, amma malam bai sa ni.Ranar da malam ya ji an kore su, ran shi ya mugun baci. Duk da haka ya ba kowan ne su gona, ya ce su je su yi noma, ba zai sake hasarar kudaden sa, tun da ba karatun su ke yi ba!
Bayan Abdul ya gama KANTA COLLEGE shi ma ya wuce UNIVERSITY OF ALIERU Ya na karantar Agriculture. Ashe karar sa ta karshe ne ya hadu da Haleema,yar jahar katsina ce, a BARHIM ESTATE iyayenta su ke da zama... alokacin ta na 300 level.
KAR KU MAN TA DA YI MIN, COMMENT, SHARE,VOTE AND FOLLOW
Domin shawarwari ko gudunmuwa
pls ***
yar mutan Argungu``` 鉂わ笍馃摎