Free chapter 路 Read without an account

3-4

by 饾櫧饾殬饾殬饾殯饾櫢饾殩饾殜饾殫 路 Abraham


馃崌馃崌ABRAHAM馃崜馃崜


*First edition*




*WATTPAD*

@NoorEemaan







***


Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din





Chapter 3-4


(Not Edited)


Sosai tsoro ya bayyana a fuskar madam Gloria, domin abu ne wanda bata taba gani ko ji ba, ta yaya dan cikin Nonye ke motsi bayan ta mutu? Sosai murnan cikar burinta ya ragu

Mai da kallon ta tayi ga Anty Sarah data yi mutuwar tsaye, sosai nadama da tsoron Allah ya rufe ta, domin abinda ke faruwa yanzu ikon Allah ne mai yin yanda yaso.




"Sarah kina ganin abinda nake gani kuwa ko mafarki nake yi?" madam Gloria ta fada a rude, tana jijiga anty Sarah



"ba mafarki kike yi ba kawata, da gaske ne, amma ga shawara daya" ta fada tana satar kallon madam Gloria, fatan ta ta amince da tunanin daya zo zuciyar ta yanzu, domin ta hakan ne kadai zata samu sasaucin tsantsar mugunta da suka yiwa Nonye.


"meye shawarar ki Sarah fadi ina jinki" madam Gloria ta fada a kage.


"mezai hana mu fita da ita ta kofar baya inda ba security sai ki kira Emma ya hayo mota daga nan mu kai ta asibiti ayi operation kana a ciro dan cikin kafin gari ya waye mun dawo, idan ba haka ba matukar mutane suka Lura da dan cikin Nonye na motsi za a samu matsala domin abinda bakya so ne zai faru, ma'ana Dan Abraham zai rayu" anty Sarah ta fada tana fatan kawarta ta amince.



Jinjina kai madam Gloria ke yi cikin gamsuwa domin ta yarda da shawaran Kawarta dari bisa dari, babu bata lokaci ta kira Emma ta sanar dashi abinda take bukata, mintuna ashirin kacal ya kawo Emma unguwar wordbank, Kiran madam Gloria yayi yace ya iso, ta fada masa cewa ta Bude kofar baya ya shigo domin su biyu baza su iya daukar Nonye ba





Bayan su ukun sun fita da Nonye cikin sanda suka saka ta a mota Emma na mata kirarin har ta cika aiki ta masa banza domin yanzu damuwarta a cire dan cikin dake ta motsi, har Emma zai ta da mota anty Sarah ta fita tace ta manta Abu, cikin Sauri ta koma ta shiga dakin Nonye da Abraham wasu abubuwa wanda Allah kadai yasan me ta dauka, cikin wani Jakarta ta saka kana ta fito ta fada mota, ta tarar madam Gloria na mitar basu da lokaci fa, me taje dauko wa ne? Hakuri kadai ta bata domin bazata so ta San abinda ta dauko ba....


Bayan sun isa wani karamin asibiti inda da

farko likitan yace sai anyi bincike, hankalin madam Gloria ya tashi abinda tayi gudu Kenan shiyasa basu je babban asibiti ba, take ta siye likitan da makud'an kud'ad'e inda ya amince, aka shigar da ita aiki bayan sunyi gwaji ya tabbatar musu da Nonye ta mutu



Cikin awa daya aka ciro lafiyayyun kyawawan y'ay'an cikin Nonye maza biyu , dayan sak ubansa tamkar yayi kaki, dayan kuma sak Nonye.



Masu iya magana sun ce zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzuru Ana shawo sai yayi...





Sun kansu likitocin Sun Jinjina ikon Allah, domin abu ne wanda bai taba faruwa a asibitin su ba, a cire rayayye daga matacce, gasu kuma yan biyu...




Su madam Gloria sun kansu sun girgiza da abinda ya fito a cikin Nonye, yayinda hankalin ta ya kara tashi, fatan ta kadai a fito da yaran ta shake su har lahira, yayinda anty Sarah ke tunanin hanyar tsiratar dasu....






Likitoci suka fara aikin dinka Nonye yayinda

Nurses suka yanka cibiyar su hadi da goge jikinsu da olive oil aka nade su a wani babban towel domin babu kayan saka musu, bayan komai ya kammala, anty Sarah ta saci jiki ta je wajen babban likitan tana kuka tace ya mata Alfarman tseratar da Rayuwar yayan, domin madam Gloria bazata bari su rayu ba, da fari likitan bai amince ba, amma ganin yadda take kuka bilhakki da gaske ya sanya shi amincewa, kana yace zai ajiye record din komai daya faru a yau din saboda ko da bincike ya taso watarana, take anty Sarah ta amince



Y'ay'an aka bata, likita yasa nurse ta bi da ita ta wata kofar inda ma'aikatan asibitin kadai ke bi har ya sadata da bakin gate, direct tasha ta nufa inda ta ji conductor's suna Kiran garuruwa masu yawa, ta rasa wanne zata shiga daga karshe taji anje GOMBE sauran mutum d'aya






Babu bata lokaci ta fada ciki, duk da bata San ko ina a arewancin Nigeria ba, amma ta San cewa yaran zasu yi nesa sosai da madam Gloria ta inda bazata taba kawowa ranta cewa suna arewa ba, duk da bata San abinda likitan zai fada mata game da yaran ba, bata kuma damu ba tunda burinta ya cika ta tseratar da Rayuwar yaran.....



Likita ke tsaye gaban madam Gloria yana sanar da ita cewa yaran sun mutu sakamakon ruwan haihuwa daya shiga kansu inda basu Lura da wuri ba, sosai murmurshi ya bayyana a fuskar madam Gloria wanda bata San cewa ya subuce mata ba, take Likita ya gasgata maganar anty Sarah ya kuma godewa Allah daya bata yaran ta tafi dasu, ganin duk ma'aikatan na kallon ta ya sanya ta ankara da abinda tayi, sai tayi saurin sanja fuskar ta zuwa ta zallan damuwa inda ta Riga ta makaro, tabbas madam Gloria ta cika shu'uma.



"Likita Allah ya jikan su, amma bazan iya kallon yaran ba, da wanne zan ji da mutuwar Nonye ko da rasa Y'ay'an dana saka ran zasu maye mun gurbin Nonye" sai ta saka kuka kana ta cigaba "a binne su kawai a makabartan asibitin nan, amma bazan juri ganin gawar su ba" ta karasa tana sakin sheshekan kuka...





Biyar saura na asuba aka basu gawar Nonye suka saka a mota, sai a lokacin madam Gloria ta Lura babu anty Sarah amma bata tsaya neman ta ba, domin bata so gari ya waye basu koma gida ba, a cewar ta Sarah zata zo gidan tunda ba bakuwar ta bane....


Wanna karan da kyar Emma da madam Gloria suka shigar da Nonye, suna yi suna hutawa har suka kaita dakin ta, hadi da rufe ta da bargo, falo suka fito ta sallami Emma ya tafi, kana ta koma dakin ta, tana fatan gari ya waye sosai domin yanzu karfe Biyar da mintuna ashirin ne.



*WASHEGARI*


Kamar yadda madam Gloria ta fada karfe shidan safiya ta gwala ihun mutuwar Nonye


sosai take kuka tana birgima a kasa tamkar gaske, hakan yasa ma'aikatan gidan suka shigo part din halin tashi, suma kuka suka saka sakamakon Jin abinda madam Gloria take fada, "ewooooo Nonye yata kin tafi kin barmu, tayaya zamu kasance cikin farinciki bayan babu ke, kin tafi kin barmu da son(ABRAHAM) ya zamu yi da rashin ki, bayan kece cikon farincikin mu, mutuwa kin min yankan kauna " sosai take maganganu cikin fitar hayyaci kai ka rantse da gaske take




Kowa na gidan yaji mutuwar Nonye matuka, domin macece mai son kowa, bata raina mutum komin kaskancin sa, haka zalika tana da son mutane sosai...



Kamar yadda yake a al'adar inyamurai idan mutum ya mutu basa binne shi a take, mortuary ake kai shi zuwa wasu lokuta kafin ayi bikin binne shi, hakan yasa madam Gloria da ta sanja shiga zuwa bakake tare da wasu yan'uwan su.


Haka al'adar su take idan anyi musu mutuwa komai na jikinsu yana kasancewa baki ne har izuwa wasu kwanaki.






*GOMBE STATE*


Bayan anty Sarah ta sauka a garin GOMBE ta shiga raba Idanu domin babu inda ta sani, ga yaran Allah ya basu wani mugun hakuri domin har yanzu basu yi kuka ba, daga karshe ta yanke hukuncin fara tafiya, tayi tafiya mai dan nisa kana ta shiga wani layi, gida na hudu idonta ya sauka a kai, haka kawai taji gidan ya kwanta mata a rai, shiga gidan tayi inda ta tarar da wata k'yakyawar yarinya fara sol hadi da iyayenta dake zaune a gefen ta suna hira cikin annushuwa






Da kallo duk suka bi anty Sarah ganin ta shigo musu babu sallama, "lafiya baiwar Allah" uban yarinyar ya tambaya a tausashe.





Jim anty Sarah tayi domin bata ji ko kalma daya daga abinda yace ba, dan haka tace "please can I use your toilet? Am really pressed"



Duk shiru suka yi domin babu mai Jin turanci cikinsu gwara-gwara baffa ya fahimci kalmar toilet din cikin abinda tace Dan haka yace "shalelen baffa zuba mata ruwa a buta"



Take yarinyar ta yi yanda yace kana ta kalli anty Sarah tace "gashi"


Amsar butar tayi, duk da a yawan lokuta idan fitsari zasu yi basu fiye amfani da ruwa ba, shiga bandaki tayi da jariran inda babu wanda ya lura cikin su Baffa cewar yarane sabuwar haihuwa a hannunta



Ta kai mintuna biyar a ciki kana ta leko ta kofar langa-langan inda ya huje ta ga baffa da Inna(matar baffa) sun shige daki, ya rage saura k'yakyawar bafulatanar yarinyar nan mai suna Aysha, ita ma daga karshe mikewa tayi zuwa nata dakin, duk anty Sarah na kallon su...



Ganin babu kowa a tsakar gidan ya Sanya ta ajiye jakar hannunta hadi da jariran a kasa cikin bandakin, kana a hankalin ta Bud'e kofar cikin sanda ta fito, sai da ta je soron gidan ta fara sauri-sauri gudu-gudu domin barin Layin.....








Ga wacce take bukatar ayi adding dinta a group chat this num馃憞

***



NoorEemaan 馃





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or

*460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.


*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 0806626851

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol