Free chapter 路 Read without an account
7-8
by 饾櫧饾殬饾殬饾殯饾櫢饾殩饾殜饾殫 路 Abraham
馃崌馃崌ABRAHAM馃崜馃崜
*First edition*
*WATTPAD*
@NoorEemaan
***
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
_note wanna ba sabon typing bane, reposting nake, so duk mai so ya fara bi yanzu ba sai nayi nisa ace daga farko ba_
Chapter 7-8
Yana shirin yin magana Kenan yaji muryar madam Gloria na fadin
"son munyi rashi, munyi rashi babba, Nonye ta tafi ta barmu, tafiya ta har abada, Nonye is gone for ever son" ta karasa tana fadawa jikinsa hadi da rungumeshi, yayinda sautin kukan ta ya karade gabadayan falon.
Tamkar wanda aka watsawa barkono haka ya runtse idanunsa, ji yayi gabadaya dakin na juya masa, sosai gabansa ke faduwa tamkar zata Faso kirjin sa ta fito
Nonyen sa ta mutu, ta tafi, tafiya ta har abada? abinda madam Gloria ta fada ya Shiga dawowa kunnuwansa , a karo na biyu madam Gloria ta kara cewa "ta haifi yan biyu wanda suma a take suka mutu, wayyo ni Gloria ya zanyi da raina" wanna karon k'wak'walwar Abraham ce ta daina gane komai sak'amak'on abinda madam Gloria ta kara fada, wanda ya sanya guiwowin sa yin Sanyi har ya gaza daukar gangar jikinsa, tilas ya sulale kasa, gabadaya jikinsa ya dauki rawa tamkar wanda yake cikin kankara, sabanin hakan gumi ne ke keto masa, na zallan tashin hankali, ga gashin kansa sun mimmike, duk da cewa babu ko digon hawaye a jajayen idanunsa, amma dole dukkanin wani mai tausayi da imani ya tausayawa halin da Abraham yake ciki a yanzu.
Rikeshi madam Gloria tayi tana kuka hadi da bashi hakuri, ko kala ya gaza furtawa domin nauyi da labb'ansa suka yi, hannu biyu ya sa ya rike kanshi dake barazanar fashewa, haka ya kasance cikin wanna halin fiye da awa uku kuma ko motsi bai yi ba, banda zuciyarsa dake bugawa da sauri虏 mutum zai yi tunanin matacce ne....
*GOMBE STATE*
Ba tare da su baffa sun lura da jariran dake kasa ba suka riketa hadi da cewa "aysha lafiya meya same ki, yi magana meya same ki aysha? " suka fada a tare suka duba jikinta...
Idanunta ta runtsa, sakamakon hakan hawaye ya zubo kan kyakyawar fuskar ta, hannu ta mika ta yiwa su baffa nuni izuwa ga kasan bandakin inda babies din ke kwance wanda zuwa yanzu sun fara mutsu虏 sak'amak'on sanyin ruwan bandakin daya fara ratsa ta cikin towel din zuwa fatar jikinsu, a tare suka zaro idanun su ganin abin al'ajabi, da ba dan kada su kara firgita tilon diyar su ba, da ihun suma zasu zunduma, a take kuma k'wak'walwarsu ya tariyo musu sanda anty Sarah ta shigo da farin towel din nan, amma basu taba tunanin cewa abu mai rai ne a ciki ba, a tunanin su ko wani kayan ta ne bata son ajiyewa a waje shiyasa ta shigar dashi bandakin.
Sosai mamaki da al'ajabi ya rufe su, babban tambayar su anan shine menene dalilin ajiye yaran da anty Sarah tayi? Domin basu ga alamun tabin hankali ga anty Sarah ba, bare su ce rashin cikakken hankali ne ya sanya ta manta yaranta a Bandakin, shakka babu wanna babban al'amari ne ya shigo cikin Rayuwar su...
Baffa da tausayin yaran ya gama rufe shi ya tsunkuya, amma gabansa na faduwa, amma ya dake, domin abu ne wanda bai taba ji ko gani ba ne ya ratsa gidan sa, sosai ya dake gudun kada ya kara firgita su Inna, addu'a dauke a bakinsa ya hade yaran a jikinsa, kana ya kalli su Inna yace "ki dauko jakar nan ku fito daga bandakin hakan nan" ya fada yana barin bandakin, sai a lokacin indo ta Bude idanunta dake ziraro da hawayen zallan tsoro, cikin tsoro Inna ta sanya hannu ta dauki jakar hadi da riko hannun indo suka fito daga bandakin....
Direct dakinsa baffa ya nufa da yaran, hakan yasa cikin muryar tsoro indo ta ce "wayyo baffa nah! kada ka shigar dasu dakin ka, Kar su cutar da mu, kila ba mutane bane, ni gaskiya bazan iya kwana a gidan nan ba, Dan Allah baffa ka fitar dasu daga gidan nan, muje mu nemi matar mu bata yaran ta " ta karasa cikin zallan tsoro mai hade da kuruciya hadi da sakalci....
Itama Inna irin tunanin Indo ne a ranta na cewa
Yaran ba mutane bane, amma bata furta ba, sai sai tsaf baffan ya karance ta, hakan ya sanya shi sakin murmushi, ya kuma girgiza kansa, tabbas duk shekarun mace da kaifin tunanin ta namiji ya fita koda bai kai ta yawan shekaru ba, ba tare da kuma yayi magana ba ya ida shigewa dan karamin dakin sa, ya kuma san cewa zasu biyo bayan sa domin basu taba ketare umarnin sa...
Wata jibgegiyyar kodaddiyyar malum-malum baffa ya janyo cikin kayansa ya saka yaran a ciki ya lullube su kana ya kwantar dasu kan gado irin dai na kauyen nan, towel din ya fitar waje ya saka cikin roban wanki ya saka kilin da ruwa ya jika shi, kana ya saka kilin ya wanke hannunsa sosai sannan ya koma dakin....
Gyaran murya yayi hadi da mai da duban sa ga Aysha Indo yace "shalelen baffa ina so kwantar da hankalin ki, ta ina kike tsamanin zamu ga matar? Wacce hanya tabi? Ba mu sani ba, Allahu masani.
Sannan ba fa manta yaran tayi ba, ko mai tabin hankali ta san kaunar abinda ta haifa, Allah ka dai yasan dalilin daya sa ta ajiye mana yaran, wadannan yaran mutane ne kamar mu, ki cire tsoro a ranki kinji, Allah kadai yasan dalilin daya sanya wadannan bayin Allah shigowa cikin Rayuwar mu, ko nace kaddarar mu" ya fada yana nuna yaran kana ya cigaba "domin akwai gidaje bila adadin a unguwar nan, amma nan gidan yaran suka fado, Dan haka nayi alkawarin kula da yaran nan har sanda zan daina numfashi, ina fatan zan samu goyan baya daga gareku"
Jinjina kai inna ta yi, wanda tsoron ya dan ragu sak'amak'on maganganun da baffan yayi, zai kara magana yaji an kwala Kiran sallar magriba a wani masallaci hakan ya sanya shi barin dakin da sauri yana gayawa su inna suma su hanzarta yin alwala kada su rasa jam'i domin su kan bi jam'i domin masallacin yana kusa da gidan su, wanda baffa shine Limamun masallacin....
Bayan an iddar da sallah da kamar mintuna talatin baffa ya shigo hannun sa dauke da bakar leda, kallon inna dake kokarin yin tarke/talke yayi, Cikin sauri yace "da kin fara yi wa yaran wanka da ruwan zafin nan, idan yaso sai a sake dora na tuwon" ba musu ta ajiye kayan tuwon, wani tsaftataccen bokiti ta dauko ta juye ruwan, kana ta zuba wani, hadi da gyara wutan, dakin baffa ta nufa da bokitin, kana ta fito ta nufi dakin ta domin dauko roban wanka wanda tun na indo ne amma yana nan da sauran kyansa da sabunta(kun San fulani akwai iya ajiya馃ぉ)
Sai da ta wanke roban wankan kana ta dan sirka ruwan zafin kadan, kan gado baffa ya zauna, jariran na hannunsa yayinda indo ke gefe tana raba idanu wanda zai tabbatar wa mutum cewa har yanzu tsoron bai barta ba.
Ledar da baffa ya kawo inna ta zazzage, kayan jarirai da na Sanyi, sabulun yara da so so, man shafawar su, mataji(comb) hadi da hular Sanyi. Ba laifi siyayyar tayi daidai talaka...
Sosai inna ta wanke yaran ta kuma gasa musu jiki sosai, sai a lokacin jariran suka canyara kuka tun lokacin da suka shaki iskar duniya....
A kuma daidai lokacin ne Indo taji wani mugu_mugun tausayin yaran ya ratsa jikinta, wani Sanyi ya fara ratsa ko wani huda na gashin jikin ta, sak'amak'on hakan tsikar jikinta ya fara tashi, haka nan ta ke Jin wani yanayin na mussaman kan yaran Wanda bakinta bazai iya furtawa ba...
Ajiyar zuciya ta sauke, kana ta mai da duban ta ga yaran Inda zuwa Yanzu Inna ta shirya su cikin kayan da baffa ya kawo, sunyi kyau sosai gwanin sha'awa, karon farko da Indo taji tana son daukan yaran ta rungume su, hakan yasa ta fara takawa domin isa garesu....
*yanzu Abraham ya soma, yawan comment dinku shi zai bani kwarin guiwar cigaba da typing, idan ba comment nima bazan yi update ba*
*Sannan mai son nayi adding dinta a group ta yi chatting dina up ta lambar nan*馃憞
NoorEemaan馃
***
Share fisabilillah
Comment
Vote
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851