Free chapter Β· Read without an account

25-26

by π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš— Β· Abraham

πŸ‡πŸ‡ABRAHAM πŸ“πŸ“



*First edition*





*WATTPAD*

@NoorEemaan





***

Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.





_Am so sorry for keeping you guys waiting, na San ba dadi, kun jira ni da yawa, amma ba laifi na bane, ban ji dadi bane kwana biyu, ga ba lokaci, amma kuyi hakuri in sha Allah bazan kara jimawa irin wanna ba, har in gama Abraham, ngd sosai da kokarin jirana da kuka yiπŸ™ much luv masoyan NoorEemaan_😍





Chapter 25-26



Cak! ya tsaya a lokacin ya isa bakin k'ofar dakinta, inda a yanzu amon sautin zazzak'ar muryar ta ya fi tashi, hannu yasa kan handle din kofar a kokarin sa na son bud'e kofar, sai kuma yayi saurin d'auke hannun sa hadi da murza su cikin na juna, a hankali ya jingina bayan sa da kofar dakin ta, sannan ya Lumshe k'yawawan idanun sa yana cigaba da sauraron kira'ar ta mai dadi....



Sosai ko wani mahuda na gashin jikin sa suka kara bude wa, kasancewar yanzu yafi kusanci da ita, wani yanayi mai kama da zubar tsigan jiki, da Sanyi ya shiga ratsa shi...




*40 Minutes later*


Wanda yayi daidai da lok'acin da Aysha ta rufe qur'anin ta, kana ta shiga yin addu'oi'nta...


A kuma lokacin ne Abraham dake tsaye a bakin kofar ya sauk'e wata k'arfaffar ajiyar zuciya, kana a hankali ya bud'e lumsassun idanunsa da suka dan rine sak'amak'on jimawa da suka yi a rufe.




Cikin yanayi mai kama da rashin jin dadin ya yamutsa fuska tamk'ar yaro dake son wani abu daga mahaifiyar sa, haka nan yaji ba dadi a dalilin daina jin amon sautin muryar ta dake rera karatun qur'ani.

A karo na biyu ya kara sauk'e numfashi kana cikin tafiyar sa ta ingarman na miji mai ji da lafiya da kuruciya ya bar wajen...




Aysha kuwa bayan ta iddar da addu'o'in ta ta Mike, a gaggauce ta shirya kana ta sauko kasa ta fara shirya musu had'add'en breakfast mai rai da motsi tamkar ba Indon baffa ba.




*********




9:00am.


ABRAHAM tare da madam Gloria ke zaune a had'add'en dinning area suna jiran Aysha tayi serving din su, a hankali cikin takun nutsuwa Ayshan ta fito daga kitchen hannun ta dauke da plates na tangaran da zata yi serving dinsu dashi...





Jin kamar ana kallon ta yasa ta a hankali ta dago kanta idanunta suka fad'a cikin nashi, gaban ta ne ya bada dam! Domin tun lokacin da ta fara serving madam Gloria abinci yau ne karon farko data ganshi a dinning table, gabadaya ji tayi idanun sa na yawo a jikin ta wanda hakan yasa jikin ta fara rawa domin sosai yake ladabtar da ita da sexy eyes d'insa masu masakaicin girma, hannunta ne ya fara rawa, ba tare da zato ko tsammani ba plates din suka kufce daga hannunta suka tarwatse kan tiles din...



A zabure madam Gloria ta mike, hadi da daga lukutan hannunta da niyyar marin Aysha da ta k'amk'ame jikin ta sannan ta runtse idaunta...




Ganin yasa Abraham mikewa, taku biyu kacal yayi ya kamo hannun madam Gloria ya sauke, kana ya kalle ta, ba tare da yace komai ba ya koma kan kujerar sa ya zauna, yana k'ark'ad'e hannun sa saman dinning table din...





Da kallo ta bishi kana tace "why son? Meyasa zaka hana ni? Daka barni na nunawa wanna Bush Village girl din hankali"


Juyawa tayi ta ga Aysha tace "ke! Baki da hankali ko? what's your problem? Hannun ki ciwo yake? Kina abu kamar zararriya, bari in gaya miki, this should be the last time da zaki kara fasa min plate, kin San nawa each one?... β€œ





" mummy plssssssssss" Abraham ya fada a dake, yana rike da kansa, haka nan yaji fad'an da take wa Aysha na bata masa rai, be San mai dalili ba, baya ga haka shi mutum ne mara son hayaniya...





Shiru madam Gloria tayi, ta zauna tana sauke hucin bacin rai, amma ba halin magana, domin ta San Abraham kaifi daya ne, sannan ta yi Controlling kanta ne domin kada tsanar da take wa Aysha ya fito b'aro-b'aro, saboda har ita kanta Ayshar bata so ta San cewa ta tsane ta, ta kuma tsara hakan ne domin plan din ta ya tafi daidai yanda ta tsara...






Indo kuwa runtse idanunta tayi tana jiran sauk'ar mari, jin shiru ne yasa ta Bud'e idanunta cikin mamakin rashin marin da madam Gloria bata mata ba, cikin sheshek'ar kuka ta dauko Abin shara da Abin kwashewa ta shiga tattare fasashen plates din, cikin rashin sani ta taka wani fasashen plate...


Kara ta saki, inda a tare ita da Abraham suka runtse idanun su, wanda shi kanshi bai San yayi hakan ba.....




Saboda d'auriya irin na Aysha, ta kuwa Mike ta karasa tattara wajen ba tare da ta damu da cire broken plate dake tafin kafar ta ba.




Cikin k'ok'arin shanye zafin da take ji ta koma kitchen din ta dauko wasu plates din, wanna karon Sam bata yarda sun hada ido ba, duk da yanda take jin idanun sa na yawo a kanta, a nutse ta fara serving dinsu, amma tayi kokari matuka wurin controlling kanta domin sosai hannun ta ke rawa....






Bayan ta gama, ta jaa kafar ta zuwa sama tana zub da hawayen da bata San koma menene ba, domin indai fada da zagin madam Gloria ne ta fara sabawa, har hakan bai fiye damun ta ba...




Kan mad'aid'aicin bed dinta ta zauna tana sauke nishi, kafar ta daya ta d'ora kan dayan da niyyar cire k'walban, amma ta kasa saboda zafin daya ziyarci k'wak'walwarta....




Kwanciya tayi a gadon ta cigaba kuka, har wani wahalallen bacci da bata shirya zuwan sa ba ya dauke ta....




Ta bangaren Abraham kuwa, hakan nan yaji ransa ba dadi a dalilin abinda ya faru, duk da dadin dandanon da abincin ke dashi akan bai sa yaci da yawa ba, ruwan black tea yayi sipping kana ya goge bakinsa da tissue, sannan ya mike...




"wait! Son don't tell me you re full?" ta fada cikin rashin jin dadi da kulawa kamar gaske.




"yes mum! Am going out"


ya amsa a takaice kana ya haura sama cikin abinda bai fi 7seconds ba...

da kallo mai tattare da zallan tsana hadi da muradin cika mugun nufin ta a kanshi ta bishi, kana ta dawo da kallon ta ga plate dinta mai shake da chips with fried eggs, a hankali tace "shege mai taurin rai, dama kayi accident a hanya ka mutu idan ka fita, kaga ka sauk'ak'e min aiki, na rasa me yasa har yanzu na kasa cika burina akan ka, tabbas nayi kuskuren barin Dan zaki ya girma" ta fada cikin yaren igbo hadi da cizon yatsan ta mai dauke da artificial nails...



*ABRAHAM*

Har ya murda handle da niyyar shiga part dinsa, sai kuma ya tsaya cak! Sak'amak'on brain din sa daya tariyo masa lokacin da fasashen plate din nan ya caki kafar ta da karan da ta saki, Lumshe ido yayi a hankali ya furta "is it still in her leg? β€œ(ko har yanzu yana tafin kafar ta).



Tamkar wanda ake ja, haka ya nufi hanyar dakin ta, a hankali ya tura kofar ciki...


Kwance ya hangota, jin bata motsa ba yasa shi fahimtar bacci take, wanda hakan ya bashi kwarin guiwan zuwa gareta duk da bugawar da kirjin sa ke yi...





Tafin kafar ta da yayi jaa ya kurawa ido, a hankali ya dire guiwar sa kasa, kasancewar rub da ciki tayi ya bashi daman ganin kafar da kyau, a hankali yasa karfaffan hannun sa mai laushi ya kamo kafar ta, sannan ya a hankali ya fara zare fasashen plate din...

motsa kafar tayi wanda yasa shi dakatawa, hadi da fatan kad'a ta farka har ya gama...




Sai daya bari baccin ta ya kara nisa kana ya cigaba, inda yayi nasaran cirewa, ajiyar zuciya amma boyayye ya saki, kana ya cilla fasashen plate din cikin wani karamin dust bin dake dakin, da haka ya Mike ya bar dakin zuwa nasa, inda cikin mintuna arba'in ya shirya cikin wani Turkish suit ya bar gida zuwa ginin company dinsa daya kammala, inda a cikin satin nan za a yi bikin bude shi....





*AYSHA*

Awa biyu ta d'auka cikin baccin da bata jin dadin sa ba Sam, kana ta farka...


mikewa tayi zaune tana marairaice fuska saboda zogin da ta ji daga kafar ta, a hankali ta kamo kafar, yayin da kwalla ta cika idanun ta, sai dai rashin ganin alamun fasashen plate din ya bata mamaki kwarai, a hankali ta kai hannu ta shafi daidai wajen ciwon, taji wayam babu alamun plate din a tafin kafar ta, sosai hakan ya tsaya a ranta domin iya tunanin ta bata cire da kanta ba, toh waye? ganin kanta ya fara tsarawa sak'amak'on tunanin da ta fara yasa ta mike tana Jan kafar ta har zuwa toilet....




*Bayan kwana biyar*


Zuwa yanzu Aysha taji sauki sosai a kafarta, domin tana yawan dannawa da ruwan zafi,, kuma tun daga lokacin da Abin nan ya faru bata sake ganin Abraham ba, wanda hakan yayi mata dadi, domin idan ta ganshi rasa nutsuwar ta take yi, ko gyaran dakinsa sai ta tabbatar baya nan take shiga ta gyara masa....





*madam Gloria*


Zaune take kan gadon ta, tana k'ark'ad'a kafa hadi da sakin murmushin zallan nasara, Bud'e tafin hannun ta tayi, inda wani karamin roba mai dauke da guba, wanda wanna gobar ke da hadari sosai, domin daga India tayi order din sa, inda ta hanyar sirri tayi har ya iso gareta, domin hadarin da gubar ke da shi, saboda idan aka yi kuskuren kamata tata ta kare, hakan yasa tayi taka tsantsan k'warai wurin ganin cewa ba a samu matsala ba har poison din ya iso gareta...



Duba agogo tayi ta ga karfe 5:30pm inda a yanzu ta San cewa Aysha ta gama dinner, ko tana daf da gamawa, mikewa tayi ta fito zuwa kitchen, inda maganin na tamk'e cikin tafin hannun ta....





Share fisabillah


Comment for more typing...




Thank you all for reading my novel πŸ‡Abraham πŸ“






#NoorπŸ¦‹




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or

*460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.


*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 0806626851

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol