Free chapter · Read without an account

1-2

by 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗 · Papi ne!

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓


Written by

Noor Eemaan


Wattpad

@NoorEemaan




In the name of Allah most glorious, most merciful.


Wanna labarin ƙirƙirarren labari ne, ban yarɗa a juya min shi ta ƙowacce siga ɓa idan ƙunne ya ji....




Alhamdulillah dukkanin yabo sun taɓɓata ga ubangiji mai sammai da ƙassai, a ƴau gani tafe da saɓon novel har ɓiyu ƙamar haƙa PAPI NE DA ƘƳAUTAR KODA ban san ya zan yi muƙu ɓayanin books din ba, sai dai shaƙƙa babu zaku ji ɗadin books ɗin in sha Allah, ƙuɗai ku cigaba da ɓina ɗan jin ƴanda ɗoguwar tafiyar da zamuyi ɗani ɗaku zata ƙasance. Banyi alkawarin yin typing kullum ba...



sannan ga masu son shiga group dina sun min magana ta wanna lambar *** inyi adding din su, domin na rufe link din, saboda maza masu shiga groups nagode.




Wanna Littafin Sadaukarwa ne Gabadaya ga dukkanin Maraya(orphans) Dana gidan Marayu da ma ko ina Suke a duniya...




Page1-2


*SOKOTO STATE*


Misalin k'arfe takwas na dare ne, unguwar shiru tamk'ar babu halittu a unguwar, wanda hak'an baya rasa nasaba da ruwan saman da ake tsulawa tamk'ar da bak'in k'warya, mafi ak'asarin gine_ ginen unguwar na marasa k'arfine domin mutum na ganin tsarin gidajen unguwanin zai san cewa na talakawa ne...


A hank'ali wani yaro mai k'imanin shekaru goma sha biyar a duniya ke tafiya, duk da uban ruwan da ake tsulawa hak'an bai dame shi ba, ga wurin fak'ewa da yawa amma bai yi hak'an ba. Duk da kananun shekarun sa yana da tsayi sosai, wanda mutum zai iya tunanin ya kai irin shek'arun ashirin nan.


Wasu kod'add'un jeans da riga ne a jik'insa sai wani snickers a kafarsa, yana da k'yau, da alama idan ya zama babban saurayi za a yi k'yak'yyawan gask'e da yanmmata zasu yi ruɓuɓɓin sa, yana daf da shan k'wanar da zai saɗashi da layinsu ya ji k'ukan jariri, cigaɓa yayi da tafiyar sa ba tare da ya ko kalli inda k'ukan ke tashi ba...


Har ya kai kofar gidansu, wanda ya k'asancewa na zallan jar k'asa ne, ya ji Hank'alin sa ya kasa k'wanciya d'omin tunda ya taho sautin k'ukan jaririn ke amsa k'uwwa a k'unnewan sa. Runtse ido yayi kana ya juya da sauri har da guɗun sa....


Abun mamaki har yanzu k'ukan jaririn ke tashi, A hankali ya karasa gaban k'wallin da jaririn ke ciki add'ua dauke a bak'insa yayind'a wani tsoro tsoro ke k'ok'arin shigar sa, sai dai yaki ɓawa tsoron daman samun muhalli a zuciyar sa...


Har ya kai hannu cik'in k'wallin da niyyar dauk'a, sai kuma ya sauk'e hannun, ya fara k'ok'arin daukan k'wallin gaba daya, a tunanin sa na gidan yaje kofar gida ya buɗe, faduwar gaba ce ta saukar masa d'aid'ai lokacin da kwalli ya rabe kansa sak'amak'on ruwa daya jik'a k'wallin yayind'a k'yak'yyawan baby'n yayi gefe yana daf da shan kasa...


Cik'in wani sauri da bai san yana da shi ba ya cafko ta, k'asancewar ak'wai cak'walli sosai a wajen yasa ya fadi kasa, runtse idanun sa yayi sak'amak'on ɓugewa da kansa yayi jikin wani dutse, sai dai ya rike baby'n gam gam a jik'in sa, yama rasa wani jinsi zai b'awa wanna baby'n shin _jariri ne ko jaririya ce_

Sai d'aya dauki tsahon mintuna goma kana yaji k'ansa ya dan daina ciwon kana ya mik'e tare da baby'n a jik'insa wanda zuwa lok'acin ruwan ya fara tsagaitawa kadan da kadan, Kara kallon kwalin yayi yaga ya dame da kasa saboda tsananin jikewa, bayan haka babu komai a tare da baby'n domin ko riga babu a jik'inta sai jini da bai gama fita a jikin ta ba har yanzu da alama haihuwar yau ce...


Cik'in tsananin tausayin baby'n dake ratsa zuciya da jik'insa ya mik'e ya fara tafiya bayan ya shigar da ita cikin jikin sa, a dalilin sa na son tareta daga ruwan saman dake dukan naked body d'inta har yanzu, duk da dai babu abinda rigar tasa ta karewa baby'n domin a jike take sosai, baby'n kuwa wani damke fatar k'irjinsa sa tayi tana k'ok'ari tsota, wani sabon tausayin baby'n ne ya sake dirar masa...


Cikin sauri_sauri gudu_ gudu yake tafiya har ya isa bak'in kofar gidan nasu, tura kofar gidan yayi wanda ya kasancewar na zallan langa langa ne, shiga yayi kana ya sanya sakata... 'Dakuna biyu ne kacal a gidan sai bandaki, daga can gefe akwai wasu manya manya dutsina uku, da kuma wani tuk'unya akai wanda aka k'washi tuwo a ciki da alama nan ne maɗafa, tsakar gidan ba wani babban bane, kana jar kasa ce wanda ya sake ca'bewa saboda ruwan saman da aka yi, ga robobi reras a jira cike da ruwa da alama ruwan sama aka tara cikin su...


Daki dake a farko ya nufa, hadi da daga labulen ya shige... wata tsahowa mai k'imanin shekaru hamsin da tara zaune kan gadon ta irin na bunun nan ga tudu da laushi, wani kallo ta jefa masa kana cikin fad'a ta fara cewa......




Ya kuka ga wanna labarin? Shin in cigaba ko in dakata? yawan comment dinku ne zai sa na cigaba da suburbudo muku shi...✍


Don't forget to share

Comment and

Vote me on wattpad @NoorEemaan



Noor Eemaan na muku sahihiyar kauna🥰

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.