Free chapter · Read without an account

33-34

by 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗 · Papi ne!

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓



*WRITTEN BY*

Noor eemaan




*WATTPAD*

@NoorEemaan








EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌



*pls&pls sisters kuyi following dina a Wattpad @NoorEemaan*




(Kila kuga typing error😎)


33-34


........Salati kaka ta sanya ganin yanda Nu'aiym ke jan kafafun sa, ga kumburin daya yi. "Nu'aymu hatsari kayi? yaushe haka ta faru? Ko aljanu ne suka biyo dare suke son kassara min jikana?" Kaka ta fada cikin iyakar gaskiyar ta, sannan cikin damuwa.




Bai kula ta ba, sai zama d'aya yi yana cije lebe, domin zuwa yanzu azaba iya azaba ta ishe shi.





" ''yar nan ya akayi haka ta faru? Tunda ubanki dan ganin dama ne, yaki kula ni"




Nu'aiymah dake share hawaye tace "ji...ji...ya da...ya...dau...koni...da...ga... wa...jen...pa...party...mu...ka...fadi...daga...kan...lifan" ta faɗa cikin rawar murƴa tana fashe da kuka domin yadda hannu da kafar Papi tayi dole mutum gaji tausayin sa.





"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" kaka tace tana tafa hannu


"Amma ''yar nan baki kyauta min ba, idan shi zuciyar dutse da shi yaki fada, ai ke kya gaya min a kira mai gyara tun a jiyan"



"Sannu! Sannu!!" Kaka tace tana dan latsa inda ya kumbura, runtse idanun sa yayi, duk da azabar dayake ji bai hana ta ba, Nu'aiymah ce ma tace "wayyo! Kaka ke daina taba masa akwai zafiiiii fa"




"Toh masu uba, ai ni bana kaunar sa ƙenan dole ki ce haka, karshen kaunar daya kamata ki nuna shine ki sanar da ni a kira mai gyara tun a jiyan, sai yanzu zaki yi min wani iyayi, toh bari kiji gojewar kashi yayi, dole aje gun mai gyara ya d'awo da kashin daya goce saiti, sannu Nu'aiymu bawan Allah, hada mana karin kumallo mu karya sai aje wajen malam Danliti, ya gyara masa "





Wasu hawayen Nu'aiymah ta share, ta fara hadawa kaka, domin tasan bata da haku'ri kan yunwar Cikin ta, sai Nu'aym da zallan black ta siyaya masa tunda baya son madara a shayi.



A sanyaye ta ce "Papi gashi"



Idanunsa a lumshe ya mika hannu ya karba.


Shiru falon ya dauka sai sautin taunar kaka dake tashi, sai data sake kai wasu chips dazai kai 10 bakinta kana ta kalli Nu'aymah tace "A'a Nu'aiymahtou ya naga bakya ci?"




A raunane tace "ba komi na koshi" domin ita damuwarta Papi ya daina fushi da ita, ko yunwar bata ji.


Kaka zata sake Magana ya bud'e idanunsa fess kan Nu'aiymah, fuska a dan daure yace "zuba, and eat up now"




Bata musu ba ta hada black tea, domin itama bata fiye son madara ba, sai chips data debi kadan tana ci tana hawaye tana kallon papi, amma sam bai kalleta ba.



Kaka data kai kofin tangaran bakin ta mai dauka da tea daya sha breavages, kofin manne a bakin ta tace "kwa ji da karyar Engilihi(English) dinku"




Babu wanda ya kula ta, har suka gama breakfast din, duk da kaka tafi kowa cika cikinta dam ƙuwa.





Bayan kaka ta saki gyatsa tace "Alhamdulillah! Nu'aymu ya kamata aje gidan malam Danliti a duba ka, domin kara tsami yake faa"



"Toh" ya amsa mata




Kaka ta kara cewa "anya zaka iya tafiya? Kodai a kira mai adaidaita sahu, domin bana jin zaka iya tuka babur lifan din nan ƙo?"



Jinjina kai yayi, domin ba ma zai ma iya tukin ba.



Nu'aiymah tayi saurin cewa "kaka na iya mashin, zan iya kai shi tunda ba nisa" (kasancewar Nu'aiym na koya mata)



"Kinga rufa ni ki saya ni, kar ayi biyu"



Amma ina Nu'aiymah tace "Allah kaka zan iya, ki tambayi Papi ma" tana fadin haka ta koma dakinsa ta d'auko key, kana ta shiga dakin ta ta sanya dogon wando baki, Saboda zaman mashin, sai rolling data yi da dankwalin k'anta kasancewar yana da girma...



Dan babur din ta haye ta kunna hadi da nufar waje, kaka ta kalli Nu'aym tace "daure ka tashi, kaga ita har ta fice, ooh wanna yarinya da zuciya take ko tsoro bata ji, ni ina zan iya tuka babur, ko hawa ma bazan iya ba, domin jina zan dinga ƴi kamar a kwalta nake shawagi".




Danne dariyar sa yayi, ya lallaba ya bar gidan, tana zaune kan babur din, kasa dauke idanun sa yayi daga gareta domin wani bala'in kyau tayi kan mashin din, har yau yana mamaƙin saurin girma ɗa ciƙa da baby'nsa tayi. Da suka hada ido kuwa ya sakar mata harara, ta tabe baki zata yi kuka, ya dauk'e kai kamar bai gani ba...




Kan Babur din ya hau, da kyar ƴana cije leben sa, da suka yi mugun jaaa kamar ya shafa jan baki.... ai fa take suka gefe luuuuu, zasu fadi, Nu'aiymah har da dan ihun ta, tama saki babur din tana jiran ta jisu a kasa...




Cikin wani k'arfi dabai san yana da ragowar sa ba, ya kama babur din ya dawo dashi ɗaiɗai, ƴana cije leben azaba, kana ya kalli Nu'aiymah yace "lazy type, dama bazaki iya ba, kika fito da mashin din?"



Shagwa'be fusk'a ta yi tace "Papi na iya faa, daka hau ne abin ya fi k'arfina"



tabe baƙi yayi yace " Wai ba munyi fada ba? Karki ma kula ni, mara jin magana kawai"



"Kukan zallan shagwa'ba ta sakar masa tace " Allah Papi na daina, please ka daina fushi da ni"



"Ohh really? Dama kina gudun bacin raina? My friend mu tafi"



Wani hawayen sakalcin ta share, amma taji dadi, tunda yayi magana mai dan tsayi da ita, da alama ya fara saukowa...




Ba musu ta fara driving din a hankali, duk inda suka gifta sai an kallesu, wasu har suna gulma a tsakanin su wai mace ta hau mashin, wasu kuma burge su sukayi, dama haka rayuwa take...




Isar su kofar gidan malam Danliti yasa ta faka mashin din, kallon ta yayi yace ta fara sauka, kana shima ya sauka cikin taka_tsantsan.




"Shiga kiyi sallama da shi" inji Nu'aym



Ba musu ta nufi cikin gidan, ta tarar da mata uku wanda da alama matan malam Danlitin ne.



Kasa tayi cikin girmamawa tace "ina kwanan ku" bayan taƴi sallama.




Hada baki sukayi wurin fadin "lafiya kalau"


"Am... malam yana nan kuwa?" Inji Nu'aiymah.



"Eh yana nan, lafiya dai 'yar nan ko?" Babbar cikin matan ta tambaya.





"Eh lafiya, mahaifina ne yayi gocewar kashi, shine muka zo ya duba shi"








"Ai yo, Allah ya kiyaye gaba" kana ta nufi dakin malam din, babu jimawa ta fito tace "gashi nan zuwa" ga kujera zauna mana" matar ta fada tana nuna mata kujera yar tsugunno.




Murmushi daya bayyanar da wushirya ta tayi kana tace "a'a nagode"



Daidai lokacin malam Danliti ya fito rike da wata babban sallaya a hannunsa, matan suka hada baki wurin fadin "barka da fitowa malam" ya amsa. Itama Nu'aiymah har kasa ta gaishe shi, ya amsa a sake, kana ya shimfud'a sallayan a soro yace Nu'aymah ta fada wa Papi ya shigo.




Fita tayi waje tace "Papi wai yace ka shigo" bai ce komai ba, ya shigo tsoron yana lafiya da kyar domin ji yake tamkar an dora masa bulu inci takwas a kafar, ga matsananci azaba da zugi......





Nasan yayi kadan, kuyi hkr pls, wallahi na gaji😓



Share fisabilillah

Comment

Vote

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.