Free chapter ยท Read without an account
5-6
๐๐RAYUWAR FAHEEMAH๐๐
_by Noor Eemaan_๐โ๏ธ
free novel
Life is so confusing,what we want we don't get, what we get we are not satisfied with, what we expect never happens &what we hate generally repeats.....
***
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
(not edited)
5-6
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Faheemah nada shekara Tara Jameela nada shekaru sha daya inda babu shakuwa atsakaninsu domin mami(hajara) bata Barin suyi wasa tare idan ma faheemah taje dakinsu da kuka take dawowa domin mami taki jinin ganin Faheemah, hakan yasa ummie(haleema) hana ta zuwa kullum suna dakinsu saboda kaucewa fitinar mami.
โ โ โ Mami ce zaune da kawarta hajja hindu wacce suka hadu akasuwar sabon Gari suka kulla kawance kasancewar halinsu yazo daya.
"Wallahi kitashi tsaye akan wanna kod'add'iyar kishiyar taki da yarta, amma da anyi magana sai kice bakya son shige-shige bin yan tsubbu"
" hmmm kedai bari hajja hindu babu abinda yafi damuna kamar cikin jikinta"cewar mami.
" ai bama wanna ba kina ganin idan wanna yartata mai suffan aljanu ta Kara girma suka kai munzanin aure aka ajiye faheemah da jameela kina ganin za'a dau yarki ne?"
Bata rai mami tayi jin abinda hajja hindu tace.
" kiyi hakuri fa kawata kinsan gaskiya ce saina fada..."
Suna a haka saiga jameela ta shigo ta dawo school ta fada jikin mamin, "ke baki ga uwar taki ba?' Sai data turo baki kana ta juyo tace "Ina wuni" amsawa hajja Hindu tayi, hadi da mikewa sanna ta Kara jadaddawa mami tayi tunanin akan maganarsu kana ta fice
"Mami meyasa faheemah ta fini fari da gashi da kyau? kowa a makarantan mun sonta yake har malamai sonta suke saboda ita ce take zuwa na daya ajinsu" cewar jameela cikin jin haushin Faheemah saboda mami tariga ta datsa mata kiyayyar faheemah a azuciyarta tun basu girma haka ba, kara turo baki tayi kana tace "kuma wallahi dan dai abbuh yace mu dinga tafiya tare school da na daina saboda na tsani hada komai da ita" jameela ta kara faษa cikin jin haushin faheemah.
Ran mamine ya kara baci hassada na cinta ta ko ina haleema da yarta su musu nisa dole ta tashi tsaye akansu domin bata so ace RAYUWAR take hangowa yarta yazama Faheemah ce zata samu...
*FAHEEMAH*
"Ummie dan Allah idan kin haifa min baby zaki saka masa suna FU'AD"
tafada cikin shagwaba da yarinta.
murmushi ummi tayi kana tace "Faheemah a Ina kika ji sunan nan?"
Murmushi daya bayyana milk color hakoran ta tayi kana tace "Da muka taho yanzu daga makaranta, Ina tsayen jikin wata mota ina jiran aunty jameela tazo mutafi shine naji murya wata yarinya tana cewa "please ya Fu'ad kaga mai agwaluma can ka siyamin" Faheemah'n ta fada tana kwaikwayon yanda yarinyan tayi, dariya ummie tayi kana tace "ke yanzu banda shirmenki daga jin suna shikenan kice asawa baby?"
"Allah ummie yana da kyau, kuma yana kirki, ya siyawa kanwarsa agwaluma kinga sai suyi kama da baby mun a halayya"
" kinga ni tashi kiyi shirin islamiyya" cewar ummi
"dan Allah ummi kinji" tafada tana bubbuga kafa irin na shagwaba, tasan faheemah bazata barta ta huta idan ba wayo ta mata ba, "shikenan na yarda zan fadawa abbuhnki ya duba ma'anar sunan" murna faheemah ta kama yi , Murmushi ummie tana jin kaunar yartata...
*Bayan wata biyar*
ummie ce zaune da katon cikinta haihuwa ko yau ko gobe, faheemah na mata tausa saboda kafafunta dasuka kumbura.
"Faheeta!"
"na'am ummiena"
"inaso kiyi hakuri da duk yanda rayuwa zata zo miki, kada kiyi wasa da sallah, duk sanda kika kai ga shiga damuwa kiyi karatun alkur'ani. Sannan kibi umarnin duk abinda maminku zata ce miki matukar bai tsaba addininki ba, kada ki raina jameela ita din gaba take dake, kinji ko?"
"Toh ummie" ta amsa a hankali.
Amma haka nan gabanta ke faduwa yau kwana uku kenan kullum sai mami ta mata nasiha, duk da karancin shekaratunta ta fahimci abinda ummienta kecewa saboda yarinya ce mai nutsuwa.
"ummie toh ba kina nan kullum ba, sai ki dinga fadamin abinda zan dinga yi kullum kinji" cewar faheemah murya asanyaye.
Murmushi ummie tayi kana tace "zanso kasancewa tare dake y'ata, amma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi...
โ โ โ
da safe ummie ta fara nakuda inda faheemah tasa kuka sai antafi da ita asibitin.
Bayan 3hrs ummie ta haifi da namiji murna sosai abbuh yayi haka ma faheemah an mata karin jini saboda ta zubar da jini da yawa.
"Dan Allah ki Kiran min yata da mijina" cewar ummie cikin sanyin murya
"ok" nurse ta ce kana ta kirasu tana fadin
"banda hayaniya please".
Bayan sun shigo, ummie tace "Faheeta baki zo kinga FU'AD din naki ba"
Abbuh ne ya musu kallon karin bayani, Murmushi ummie tayi kana tace "dan Allah kacikawa faheemah burinta tana matukar son sunan"
abbuh murmushi yayi yana mamakin wayon faheemah wai har tasan ta zabawa kaninta suna, daukan jaririn yayi hadi da rada masa sunan domin ya San sunan yana da ma'ana mai kyau.
kallon faheemah yayi hadi da cewa "Allah ya raya mana FU'AD"
Murna sosai faheemah tayi, babu jimawa ummi ta fara tari sosai,Bayan wasu minutes tarin ya lafa, cikin galabaita tace "Faheeta ki kula da kaninki sosai kinji, sanna kiyiwa maminku biyayya ki kula da addininki, banda wasa da Sallah, ki kula da mutuncinki , naso kwarai naga mijin faheeta... sai tayi murmushi kana ta cigaba , na so na bashi amanarki da hannuna sai ,dai bana jin zanga wanna lokaci" ta karasa hawaye masu dumi na gangaromata,
"haleema me kike cewa haka ne? ba abinda zai same ki, har fu'ad sai kin aurar kinjiko? kin ga faheemah na kuka" cewar abbuh a rikice domin maganarta ta matukar taba shi.
"zo nan faheeta"
da gudu ta fada jikin ummie tana kankameta hadi da fashewa da kuka duk da karancin shekaratun, amma tana jin kamar ummie tafiya zatayi ta barta, tafiyar da ba'a dawowa. "Inasonki ummiena dan Allah karki barni kinji?"
"nima inasonki yar albarka, kimin alkawarin zakiyi dukkanin abinda nace kiyi"
" zanyi ummiena namiki alkawari"
" Shukran ,ya binti (nagode diyata)"
cewar ummie saboda tasan faheemah na matukar so tayi mata magana ta labarci a wasu lokutan, ta kuwa yi dariya tana runguman ummie.
"Alhaji maminsu bata zo ba?"
Kai kawai ya gyada mata, saboda duk maganganun ta ya Sanyaya masa jiki.
Murmushi ummie tayi cikin karfin hali ta ce "kace Ina gaisheta, sanna ga amanar su faheemah ta kulamin dasu".
Shak'uwa mai karfi hadi da salati ummie tafara wanda ya daga hankalinsu, da gudu ya fice domin kiran doctor...
Cikin kwarewa doctor ya shiga duba ummie har ma da baby ya tabbatar wa abbuh da cewar rai yayi halinsa.
( kullun nafseen za'ikatul maut. Allah ya jikan wandanda suka riga mu gidan gaskiya, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kalmar shahada) suman tsaye abbuh yayi, domin cikin mintuna kalilan ace sun mutu? jiyayi maganar kamar saukar aradu , jiyayi kamar karya doctor ki yi, rufesu doctor yayi hadi da yiwa abbuh kalamai masu kwantar da hankali, ganin doctor ya rufe ummie da baby ne yasa faheemah fuskantar abinda yafaru domin tana gani a TV , sai idan ya mutu ne ake rufesa, ihu ta saki hadi da yaye rufin da aka masu tana jijjiga su tana kuka kamar zata shide, janye ta abbuh yayi cikin karfin hali, kana ya daga waya da kyar yafara sanarwa yan'uwa da abokanan arxiki.
Bayan sun koma gida abbuh da kansa yayi mata wanki ita da baby aka sallacesu kana aka tafi kaisu gidan su na gaskiya, ganin haka Faheemah ta fasa kara kana ta suma.
Mummyn zaynab ( kamar yadda faheemah ke kiranta) data kasance kanwar ummie ita tayi karfin halin yayyafa mata ruwa.... hakika mutuwan ummie ta daki mutane dayawa kasancewarta mutuniyar kirki, mami ma ba laifi taji mutuwar za'ace.
Daga wanda ranar Faheemah ta dawo shiru shiru, wanda hakan ya kara taba zuciyar mutane musamman abbuhnta,wani soyaaya mai matukar zafi yake mata.
*Bayan kwana arba'in*
yan'uwan ummie suka ce zasu tafi da faheemah, abbuh yaki, saboda yace itace zata dinga debe masa kewar haleema saboda suna matukar kama, basu ja dashi ba saboda abbuh'n ya matukar basu tausayi.....