Free chapter · Read without an account
49-50
by 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗 · kyautar koda
🍇🍇ƘƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)
*WATTPAD
@NoorEemaan
***
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
EDITING IS NOT ALLOWED❌
Page 49-50
Cikin fushi shi ma minister ya katse Daddy da cewa "oho! Wato sai yanzu ka san cewa fadeelah bata son auran Jameel din ko? Shi dan gidan alhajin son shi tace maka tana yi? Toh wallahi....."
Kit daddy ya katse kiran, domin baya son su yi batacciya da minister Sa'id din.
Babu jimawa ya nufi part din Grandma ya sanar da ita komai, bata ko yi masa fada ba, sai ma nuna murnan ta a fili domin babu wanda bai san alhaji Sufyan Rufa'i ba kaf kasar nan dama wajenta, nan aka cigaba da shirye_shirye gida na kara cika, yan'uwa da abokanan arziki na ta zuwa tun kafin ma satin bikin ya kama...
******. ******. ******.
"Daddy wallahi bazan hakura da Fadeelah ba never! Ta ya ya ma professor zai mana haka, yanzu ɗan alhaji Sufyan Rufa'i zai bawa fadeelah? Bayan na jima ina kaunar ta, gaba daya yanzu zai bata min budget, matukar ya hana ni Fadeelah, toh sace ta zanyi mu bar kasar gaba daya ma kowa ya huta"... Jameel ke wanna maganar tamkar zai fashe da kuka.
Murmushi mai ciwo minister yayi yace " kai yaro ne my son, ɗuƙ inda kake tunanin wayon professor ya wuce nan, childhood friend dina ne, nasan shi in and out, bare yanzu daya kara security masu yawan gaske Ta yaya za a iya sace ta? ka kuma san duk inda zata tana tare da bodyguard's dinta..... "
Mummy'n Jameel data cika tayi fam tace "yanzu minister haka zamu bari ya ci bulus, gaba daya ya kunyan ta ni gaban kawayena, bama ni kadai ba, gabadaya mu abin kunya ne a garemu, gaskiya kayi wani abu kai, akan wata can dana bazai shiga mayuwancin hali ba, ƙalli fa tun safe ƴa ƙasa cin abinci"
"Calm down! Calm down!! Dole zan yi wani abu a kai, domin duk na fi ku jin ciwon abinda ya faru, kamar ni professor zai yi wa haka?" Ya fada cikin takaice, nan dai suka cigaba da tattaunawa kan maganar....
*WASHEGARI*
Yan'uwa da abokan arziki sun cika falon Mommah mai yalwa sai kallon lefen Fadeelah suke, fadin yawan su bata lokaci ne, domin su kansu masu hannu da shuni sun yaba kwarai da akwatunan ɗa uɓan ƙayan ciƙin sa.
Kaf kayan babu na kasa da dubu dari biyar, duka kayan masu tsadar gaske ne, duk nacin mutum da son ganin duka kayan baya iya wa, domin akwati daya ma yawan kayan bazai fadu ba, bare in aka hada duka guda hamsin din.
Sosai wani akwati Madaidaici ya ja hankali mommah, haƙan yasa ta bud'e, take zanen hotunan fadeelah kala kala da aka yi masa kamar enlargement ne a cikin akwatin, ƴawan su zai ƙai ashirin, sosai hakan ya birge jama'a abinda ba a taba samu ba, a ciƙin lefe kenan...
Nan mutane suka fara daukar akwatunan hoto ɗa video suna watsawa a social media, kafin dare comment, like, da share kamar zai fasa wayoyin jama'a, abin gwanin burgewa, Grandma baki yafi rufuwa ganin jikarta mafi soyuwa a ranta tayi goshi, ɗomin tasan bikin ya zo ɗa wani salo mai kayatarwa, ta kuma san biƙin zai kafa tarihi wanda shekaru masu yawa anan gaba mutane zasu dinga tattaunawa akai...
Duk abinda da ake yi, fadeelah bata sani ba, tana kudundine a dakin ta, tana kuka, domin ta rasa madafa, ita kam bata son wani d'a namiji idan ba Fadeel ba, duk da taji sauki ganin an fasa bikin da Jameel, amma still hankalin ta bai kwanta ba, domin bata san waye wanna da zata aura ba, bata kuma damu da tambayar kowa, ko magana yanzu bata son yi, amma tana kokari matuka wurin boye damuwar ta tunda yanzu gida ya cika da jama'a...
Wanna kenan.
*******. ********. *******.
TWO WEEKS LATER
*RANAR DAURIN AURE*
Zaune take a dakin Mommah, tana sanye da wata tsadaddiyar material wanda fadin kudin sa bata lokaci ne, a yau shine karo na farko data fara saka manyan kaya (in kun tuna shigar Fadeelah english wears ne, amma ba matsatsu ba) wanda yayi mata kyau ainun, duk da cewa tayi rama sosai saboda damuwa da fargaba da take kwana take tashi dashi, amma hakan bai boye kyawunta ba.
Light makeup ne a fuskar ta, kana hannu ɗa kafar ta ya sha jan Kunshi wanda duka sai da taga bacin ran Mommah sannan ta yarda aka yi mata su.
Tunda aka fara event din bata ko saka ango nata a ido ba, domin an sanar cewa baya kasar, sai daurin aure da zai hallata, duk inda ka shiga labarin bikin da event din ake Saboda uɓan dukiyar da aka narka wurin gabatar da kala- kalan event din.
Wanda kaf ba a taba irin bikin ba a fadin Nigeria, abinda mutanen ke ta fada kenan.
Babu abinda take ji sai faduwar gaba mai tsanani, domin ta san cewa ta rasa masoyinta Fadeel har Abadan kenan, hak'ik'a basu cikawa Mahmah burinta ta ba. Take wasu hawayen masu zafin gaske suka zubo mata.
Babu jimawa yan daurin aure suka fara dawowa, inda aka d'aura auren akan sadaki naira na gugan naira har million biƴar, sosai gidan ya cika ɗa hayaniya, saboda yalwar jama'a.
A hankali ta mike ta zuge labulen Mommah, nan ta hango tarin jama'a da ba za su fadu ba cikin shigar fararen kaya...
Ganin hayaniyan jama'a sun fara yawa a part din Mommah, hakan yasa ta bi ta kofar baya ta koma part din ta, domin wani mugun ciwon kai ke barazanar tarwatsa kanta.
Tsaye yake tare da alhaji Sufyan Rufa'i cikin shigar tsadaddiyar shadda fari kal Yayi dinkin babban riga. agogo, takalmi, hula, duka mai tsadar gaske ne, babu abinda ke tashi a jikin sa sai k'amshi, sosai yayi kyau mai tarin yawa ya kuma fito saƙ a angon sa....
Cikin marairaicewa yace "Alhajina I want to see her, kaji yanda k'irjina ki dukawa Saboda da ita"
Murmushi alhaji Sufyan Rufa'i yayi, fuskar sa fes cikin annushuwa domin ya cika masa alkawari, kamar ƴaɗɗa ƴayi wurin taimakon sa ɗomin mallakar muradin ransa, yanzu duk abinda zai biyo baya a shirye suke...
Hannu sa ya kamo yace "for sure zaka je gareta, domin ita din taka ce yanzu, mallakin ka ce, Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa, ina tayaka murna sosai, mu ma anjima zamu koma abuja in Sha Allah"
Rungume alhajin yayi yana jin kwallan farincikin ya cika idanunsa, sai dai sam bai basu damar zubowa ba, Saboda tarin jama'a dake wurin ...
A hankali ya motsa labb'ansa yace "Alhajina Kalmar godiya tayi kadan in yi amfani da shi wurin gode maka, domin kaine silan wanna farincikin nawa na yau..."
"Shhhhh! Ka cancanci haka, babu godiya a tsakanin mu, maza je ka gareta kaji" alhajin ya fada yana raba jikinsa da nasa.
Wani security daya zo gifta wa alhaji ya kira shi yace "ina ne part din amarya?"
Sanin cewa saurayin dake gefen alhajin shine mijin ma'am din su, hakan yasa cike da girmamawa yace "muje zan nuna masa yallabai"
Jinjina kai alhajin Yayi, ya kalli dan nasa yace "all the best the young billionaire ku je"
Murmushi saurayin ya sakar wa alhajin kana suka tafi da security'n. Suna zuwa daidai kofar da zai sada mutum da part din Fadeelah'n security ya tsaya cikin girmamawa yace
" nan ne kofar shiga part din ta"
Murmushi wanna saurayin ya sakar wa security kana ya murda kofar ya shige.....
Kwance fadeelah take tayi rub ta ciki tana kuka sosai, Idanunta sai yaji suke mata Saboda tsananin kuka ga uban kumburin da suka yi, kuka taƙe tana surutu cikin fitar hayyaci, ga jikin ta daya dauki zafi da alama zazzzabi na shirin saukar mata...
Cikin nutsuwa ya murda kofar bedroom din ya shiga, lumshe idanun sa yayi sak'amak'on dad'add'an k'amshi turaren ta daya kama dakin, kana ya ware idanun sa da suka sanja launi zuwa ja a kanta...
Wani abu tamkar mashi ya soke masa k'irjin sa sakamakon jin kukan ta, da alama bata ma san ya shigo dakin ba...
Ya jima yana kallon ta, ba tare da ya iya furta wata kalma ba, ganin bata daina kukan ba ya sanya shi ware kyawawan labb'ansa ya furta
"my darling Fadeeeeeeeeeelerh"
Cak! Kukan ta ya dauke sakamakon jin muryar da ko a wani hali take zata gane, sai dai sam bata yarda shi din bane, tafi yarda cewa gizon da kunnewan ta suka saba yi mata ne.
Cigaba tayi da rera kukan ta, wani murmushi daya taho da hawaye ya saki kana ya kara cewa
"Fadeeeeeeeeeelerh! It's me your Fadeel"
Wata zabura tayi ta sauko daga kan gadon kasancewar ta bawa kofar baya ne ɗama, waro ido tayi cikin mamaki.... Shin da gaske fadeel abin kaunar ta ne ke tsaye a gabanta ko a'a? Shin ba gizo ko mafarki data saba yi bane?
Murza idanun ta tayi da dukkanin hannun ta, still yana tsaye a gabanta, hawaye da murmushi dauke a fuskar sa...
Ganin kamar tana tamtama ya sa shi ƙara cewa "my Darling nine! your Fadeel da gaske ni ne a gabanki" Fadeel ya fada yana ware mata hannuwan sa, kana ya kare maganar cikin muryar sa da amon sa ke fidda aji, so, kauna, kewa, hadi da matsanancin tausayin ta.
"Fadeeeeeeeeeeeeeeeeel"
tace cikin zunzurutun mamaki hadi da zallan farinciki kana ta buga tsalle ta rungume shi, a karon farƙo tun da suka fara soƴaaƴƴa, ta fashe da kuka sosai harɗa shesheƙa...
Cikin wani zafin nama ya taro ta, domin da ba dan yayi namijin kokari ba, da sun zube a kasa domin babu kwari a jikin sa, Saboda da dukkanin k'arfin ta ta rungume shi.
Hugging dinta so tight shi ma yayi, ya kasa controlling hawayen dake zuba a idanunsa, yalwataccen gashinta ɗa ya rufe fuskar ta ya mayar baya, kana ya dora lips d'insa cikin kunnen ta yace......
*Team fadeel and Fadeelah, Fadeel is back! I know you guys are happy, dan haka ina son jin ra'ayinku akan page din yau*
Shin Ta yaya Fadeel yayi arziki?
Daddy zai amince ɗa auren kuwa idan ya san cewa Fadeel daya dauka dan alhaji Sufyan Rufa'i ne, ba kowa bane face wanna talaka fakirin daya raina?
Sannan Jameel zai hakura kuwa?
ƴa ƴa Mommah zata ji, idan ta san cewa Fadeel din fadeelah'n ta ne angon? Da dai sauran su....
Muje zuwa fans😚
Thank you for reading my Novel *Kyautar koda*
NoorEemaan ce
***
#Share fisabilillah
#Comment
#Vote
show me love😍
please vote and follow me on wattpad @NoorEemaan
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *****