Free chapter · Read without an account

75-76

by 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗 · kyautar koda

🍇🍇ƘƳAUTAR KOƊA🍓🍓

(Its all about love, scarifes, hatred, and destiny)



*Wattpad*

@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌



***

Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.





Page 75-76



Ya fada yana daga ta cak izuwa bandaki domin su yi wanka...


Bayan sun yi wanka, ya gasa ta sosai, suka yi sallar asuba a makare, pain reliever ya bata ta sha, kana ya kwantar da ita, shima kwanciya yayi domin dukkanin su basu yi bacci mai yawa ba a daren jiya.




Karfe takwas Fadeel ya farka, kallon fadeelah yayi yaga tana baccin ta cikin nutsuwa, murmushi yayi ya sumbaceta a labe kana ya sauka daga kan gadon a hankali gudun kada ta farka.





Toilet ya shige yayi wanka, hadi da yin brush, drying gashin sa yayi a toilet domin bayason karan hand dryer ya tashe ta.




*FOGG MEN* body lotion ya shafa a black skin din shi mai kyalli kana ya fesa body spray, Riga armless baki na Adidas ya sanya kana ya saka 3quarter ash color, sosai yayi kyau...





Kara kallon Fadeelah yayi ya ga tana baccin ta cikin nutsuwa, murmushi ya saki har fararen hakoran sa suka bayyana kana ya fice yana jin shi sakayau kana cikin nishadi.





Porridge din Irish potatoes(faten dankalin turawa) daya ji zallar kaza, green beans, carrot, red bell, da dai sauran spices masu saka dandono da kamshi ga abinci ya saka a faten...




Bacci take tana kara bud'e kofofin hancin ta sak'amak'on k'amshin girkin Fadeel dake ratsa kofofin hancin ta.




A hankali ta bude lumsasun kana gajiyayun Idanunta ta sauke su tarrrr a dakin, a hankali ta yunkura ta mike tsaye tana yamutsa fuska, domin har yanzu akwai sauran radadi, amma ba kamar dazu ba...





Toilet ta fada ta sake gasa kanta sosai, domin tabbas taji dadin jikin ta dazu da Fadeel ya gasa ta, brush tayi ta fito, wani rigar sa fari mai layi_layin ja ta janyo, dogon hannu gare shi kana akwai botira jere a gaban rigar.





Sakawa tayi ta makala botiran, ya sauko mata zuwa saman cinya, head band ja ta dauka ta saka a kanta, tamkar yar baby haka ta d'awo dan kyau. *FOGG INTENSE AROMATIC ta fesa sama-sama kana ta fito, tana taku a hankali.





Jin motsi a kitchen ya sanya ta nufar wajen, ta kuwa hango shi a tsaye yana kokarin kashe gas din.





Sai data bari ya kashe kana tayi saurin rungume shi ta baya tace "Good morning Fadeel"






A hankali ya juyo da ta, ya zamana suna kallon juna. "Meyasa baki bari na zo nayi miki wanka da shirya ki ba?"




Murmushi tayi tace "naji sauki, gwanda na dinga yin wasu abubuwan da kaina domin jikina ya ware da wuri...





Jinjina kai yayi yace " yeah it's true, amma bakya jin zafi ko, ya daina?"


"Yeah" ta ce masa tana murmushi domin taga gabadaya ya damu kansa.


Ajiyar zuciya ya sauke yace "alhamdulillah naji dadin haka" kana ya kama lallausan labb'anta ya fara kissing di'n ta, tamkar zai cinye mata lebe, sosai fadeelah ta bashi hadin kai hakan yasa suka dauki tsahon lok'aci suna abu daya.




Kanta ta kwantar a jikinsa, tana sauke numfashi, haka zalika shima, sun dauki mintuna biyar a haka, kana ya bud'e fitinanun idanun sa...





"You look beautiful fadeelah" ya fada yana kallon yanda rigar yayi mata das a jiki, duk da bai kamata ba.




"Thank you my handsome Fadeel" ta fada kana ta dora da cewa "tun cikin bacci nake jin k'amshin girki, hakan yasa ni tashi ba shiri"



Siririyar dariya yayi yace "girki nake wa 'yar albarkar matata taci idan ta tashi, domin nasan jiya na gama jigata ta"




Murmushi ta saki, ta sani cewa Fadeel dinta romantic guy ne, amma bata san ya wuce tunanin ta ba, tuno first night din su ya sanya ta sakin murmushi, duk da ta wahala iya wahala, amma hakan bai hanata fahimtar salon sa ba.




Iska ya hura mata yace "tunanin me kike?"

"Ba komai" tace tana kallon shi da murmurshi.





Plate mai dan girma ya dauka ya hada musu abincin a kwano d'aya, ya sanya spoon guda d'aya.






Lemo da ruwa ya daukar musu duka ya jera a tray, fadeelah zata dauka ya hana ta...





Falon suka zauna kasan carpet, tana jikin sa ya shiga ciyar da ita, ta ci sosai fiye da rabi, kana ta sha ruwa kadan domin ta koshi sosai, ragowar ya cinye ya sha lemon da ruwa, take yaji cikinsa ya cika shi ma.



Kitchen suka koma, yana wanke-wanke tana dauraye kwanon, yayinda suke hirar soyaayar su gwanin burgewa...





***********






Satin su daya a gidan, suka koma gidan sa, kamar kullum komai a gyare tsaf-tsaf duk da basa nan amma ma'aikatan suna aikin su yanda ya kamata.






_WASHEGARI_



Da misalin karfe 4 na yamma dawowar Fadeel kenan daga aikin zanen hoton wani babban hotel da za a gina, bayan motocin sun faka, suka yi saurin bud'e masa kofar mota, daya daga cikin tsad'add'en wayar sa ya shiga latsa wa, karawa yayi a kunne yace "my Darling am back! Kina wani sashe ne?"



"Alhamdulillah! welcome back mijina, ina part B" ta bashi amsa kamar yadda suka saka wa ko wani part suna a gidan Saboda girma da yawan su.





"Alright" yace yana katse Kiran, sauka yayi, ya nufi part din, ya kuwa sameta zaune...





Da gudu ta tashi ta dane Shi, dariya yayi yana bubbuga bayanta yace "easy easy fadeelah! Da alama kin warke ko? Irin wanna gudu haka" ya karasa a zolaye.





Dariya kawai tayi, domin ta fahimci abinda yake nufi, zai sake magana aka kira wayar sa, ganin number babban security dinsa ya sanya shi dagawa...





"Hello boss! Ga wasu mutane suna ta zuwa neman ka, yau kwana hudu kenan muke sanar musu baku nan, gashi kuma sun dawo yau"..





Mamaki ne ya kama Fadeel, domin bai yi da wasu zasu zo ba, katse Kiran yayi yana kallon Fadeelah dake kallon sa itama.





"Kace su barsu su shigo, kila akwai abu mai muhimmanci da ya kawo su" domin taji abinda security'n ya fada.



"Kina ganin haka fadeelah?" yace yana kallon ta.




"Yeah! Ka basu dama ka ga ko su waye, am sure alkhairi ne in sha Allah"





"Allah yasa" yace yana sake dialing number security


"Let them in" yace yana katse Kiran.




Kallon Fadeelah yayi ya ga doguwar Riga yar kanti ce a jikinta company'n *Valentino* Yayinda tayi rolling da karamin mayafin sa.





"Kinyi kyau sosai, fiye da yanda bakina zai furta" yace yana manna mata kiss a lebe.




Itama kissing dinshi tayi tace "thank you!" Ta karasa tana zagaye hannun ta a kugin shi, idanunsu sarke dana juna, yana dan juyi da ita.





Alarm da aka danna ya sanya su dauke idanun su daga kan na juna, hannun fadeelah ya ja suka zauna ya bada umarnin shigowa.



Gabadaya suka shigo jiki a sanyaye, mata biyar, maza shida. Bayan sun gama shigowa security daya musu jagora ya fita, Fadeel bai dago ba hankalin sa na kan wayar sa, yana duba massage din daya shigo masa ta e-mail, Wanda wani shahararren attajiri ya bukaci yayi masa Zane na wani industry, mutumin mazaunin jahar kwara Ilorin ne.



Fadeelah ce ta Mike tace "bismillah ku zauna, sannu ku da zuwa"


Zama suka yi a sanyaye, ta gefe ta dan mintsile shi alamun ya dago ya kalli bakin na sa.



"Zan rama" ya fada a hankali ba tare da ya kalle ta ba, yana ajiye wayar a gefe.





"Fadeel danmu" daya daga cikin mazan ya kira shi, wanda ya kasance wan mahaifin sa ne.





A hankali ya dago jin wata murya mai kama data mahaifin sa, ya sauke su tarrrr kan yayan mahaifin nasa.





Kankance ido yayi yana kallon su cikin zallan mamaki! Dama suna raye? ya aiyana a ransa.





"Me ku ka zo yi a gidana? Wallahi Dana san kune babu abinda zai sa na bari ku shigo min gida, And yanzu zaku bar min gidana" ya karasa yana kokarin danna wa security kira.





Kwace wayar fadeelah tayi, domin ta fara fahimtar ko su waye. "Give me the phone" ya fada muryar sa na rawa alamun baccin rai...





"Bazan baka ba, what are you trying to do huh? they are your family" ta fada ita ma a dame.





"Family! Did you just said family?" Dariyar takaici yayi kana yace "Fadeelah bani da wani family, my family are dead! Suna ina a lokacin da mahmah na take bukatar taimako? Ina suke? Gabadaya sun yi watsi damu, idan ma Mahmah ta kai ziyara wulakanci suke mata, Saboda suna da arziki?"




Numfashin bacin rai ya sauke yace " look you guys should live my house kafin raina ya baci"




"A enough please Fadeel! A enough! Nasani cewa hakan ba dadi, kayi hakuri kaji, just forget and forgive" FADEELAH ta fada tana dan jijjiga shi domin taga ranshi ya baci matuƙa kana ya fara fita a hayyacin sa.





Daya daga cikin matan data kasance kanwar mahmah tayi saurin cewa "eh dan nan kayi haku'ri dan Allah! Mun san cewa bamu da zumunci bamu kuma kyauta ba, amma hannun ka baya ribewa ka yanka ka yar"




"Sai dai idan hannun bai ishe ka da radaddi ba" ya katse ta, a zafaffe.




Nan fa gabadaya suka hada baki wurin bada hakuri, amma ina Kamar kara tunzura fadeel suke.





Daga Karshe ma ya bar falon a fusace zuwa sama, sosai fadeelah ta tausaya masa, amma hakan bazai hana ta fada masa ya yafe musu ba, tunda sun gane laifin su.




"Ina zuwa" tace tana bin shi a baya da sauri, kwance ta tarar da shi yayi rub da ciki, hannunta kan k'irjinta ta karaso gaban gadon, kwanciya tayi a jikin shi tace





"fadeeeeeeel".....






_tnx my readers for the love and support_😘




SHARE



COMMENT





NOOR✍️🥰




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call *****

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.