Free chapter 路 Read without an account

Chapter 3

by Ummubasheer 路 CUTAR KAI

```CUTAR KAI....```馃拲



{ _Labari ne mai cike da nadama, yaudara, tausayi, tsantsar k'auna mai tab'a zuciya_ }


_Story And Written_

        ```By```

```UMMU BASHEER

   &

MAIMOUNATH O.G```


*Wannan labarin k'irkira ne, bamu yarda a sace ko ayi mana copy and paste ba, duk wanda yayi kuma bamu yafe ba*


Page 03


Nadrah ce sanye cikin doguwar riga na atamfa dinkin A Shape yayi Mata kyau tayi dauri tare da yafa veil Black colour, simple make up tayi ta feshe jikinta da turaruka,ta sanya flat shoe black, Wayarta ta d'auka ta nufa Parlour Daddyn su dama nan ake sauke bak'i akwai k'ofa ta waje,dama already ta riga ta shirya mai snacks sai drinks saboda da Daddare ba kowa ke son cin abinci mai nauyi ba, K'amshi ne kawai ke tashi a Parlour,Kira ne ya shigo wayar ta, d'auka tayi cikin sanyin Murya ya sanar da ita gashi ya shigo gidan,Tace Ok Hisham ta kira tace ya shigo dashi,tana zaune kan Kujera ya shigo Parlour, Hisham kuma tun a k'ofa ya juya,Wani irin kallo yake binta dashi cike da soyayar ta, Sunkuyar da kai tayi tare da gaishe shi zama yayi yana amsawa"Baby yau dai gani ga ki,Ina farin ciki Sosai"


Murmushi tayi tare da D'aukar glass cup ta zuba mai Coke mai sanyi,Ta Mik'a mai karb'a yayi tare da rik'e hannun nata da sauri taja cikin tsoro,Shi kuwa wani irin abu yaji na fisgar shi,wow soft skin,ya fad'a a ranshi, meatpie tasa a karamin plate ta ajiye kusa dashi domin bata son hannun ya k'ara haduwa domin wani irin shock taji,yana sipping Coke din amma eyes dinshi na kanta,can yace"Baby ashe kinfi kyau a fili,dama ranar dana fara ganin ki ban kalle ki sosai ba sai share ni kike kinki bani damar ganin Fuskar ki mai kyau"


" Uhm"tace domin wani irin kunya da nauyin shi take ji ganin shi a zahiri, dawowa yayi Kujerar da take ya zauna kusa da ita Cikin tsoro ta matsa da sauri, murmushi yayi"Baby tsoro na kike,nifa ba abinda zan miki ba cinye ki zanyi ba Matsoraciya"ya fad'a cikin dariya.


 Warwaro da Ummu'n shi ta bashi ya ciro tare da cewa ta rufe idon ta, tambayar shi tayi mene ne yace kawai ta rufe idon ta,rufewa tayi ya ciro warwaron tare da rik'e mata hannu,jin ya rik'e hannun ta yasa tayi Saurin bud'e ido sai taga yana kokarin sa mata Bangles,sai D'aukar ido suke kasancewar hasken daya cika Parlour,sa mata yayi yace"Mahaifiya tace ta bani tace insa ma surukar ta sanann kuma in fad'a Miki cewa tana welcoming dinki cikin family mu"


Murmushi tayi cikin farin ciki" Ina godiya sosai,Dan Allah ka taya ni godiya,naji dad'i Sosai da wannan Kyautar"


Dariya yayi"karki damu indai Ummu ne zata iya Baki abinda yafi haka ma domin tana son duk abinda nake so,Matar Sufyan"ya fad'a yana d'aga mata gira.


 Ita dai duk a takure take jinta,haka ya dinga mata hira ita dai sama sama take amsawa kasancewar su kusa da juna yana jefa ta cikin tsoro shi kuma yana jin dad'i saboda yasan Nadrah kamilaliya ce,ba irin wasu y'an matan yanzu bane da sai suyi ta shishige ma saurayi, Lokacin da zai tafi ya ajiye mata rafar y'an dubu,tace ya barshi amma yace ba zai d'auka ba sai dai idan rainawa tayi hakan yasa tayi shiru, Sannan tace bari ta kira mommy su gaisa,Da Sauri ta nufa bedroom din Mommy cikin farin ciki ta sanar da ita, Mommy wacce ke duba wani litafin Azkhar ta Mik'e tasa doguwar Hijab dinta suka nufa parlour,yana ganin mommy ya durkus'a k'asa ya gaishe ta ta amsa Cikin sakin fuska da tambayar shi mutanen gidan yace Alhamdulillah,daga nan tayi mai sallama ta koma ciki, Nadrah ya kalla yana kashe mata ido"Baby tohm azo a raka ni"


Rufe Fuskar ta tayi cikin Kunya,har gurin motar shi ta raka shi yana ta Mata hira irin ta massoya ko a gurin motar sun dad'e yana cewa kamar kar su rabu,haka dai sukayi sallama,Cike da K'aunar juna ita kanta ji take kamar kar ya tafi, Komawa tayi parlour tare da D'aukar kud'in daya bata tayi ta nufa gurin Mommy tare da bata kud'in tana cewa shine ya bata,ta Ciro warwaron ta bata shima,tace Maman shi ce tace a bata, Mommy tayi mamakin ganin warwaron zinare sai bata rai tayi"Meyasa zaki karb'a Nadrah?"


"Wallahi Mommy nace ya barshi yace wai sai dai idan rainawa nayi shiyasa ni kuma nayi mai godiya"ta fad'a cikin marairaicewa.


" Shikenan anjima idan Daddy ku yazo Zanyi mai magana,amma next ki kiyaye,karki k'ara karb'a wannan ba irin tarbiyyan dana baki kenan ba karbar kud'in saurayi"


Mike'wa tayi tana cewa" Inshaallah Mommy kiyi hakuri"


"Jeki gyara Parlour'n,kizo ki had'a min furar nan"


Amsawa tayi tare da nufar parlour ta kwashe komi ta kai kitchen ta gyara gurin,Tana kitchen tana had'a ma Mommy fura sai ga Hisham"Yauwa Aunty Nadrah,idan kin had'a ki zuba min pls"


" Na Mommy ne, wai kai ba d'azu ka gama shan wani ba"


D'aukar cake yayi yana ci" Bai ishe ni bane, Yauwa Aunty Nadrah, Yaya Sufyan din nan kamar zaiyi kirki fa, ba kiji yanda yake tamin hira ba ya sake dani wlh sai fara'a yake min da zan rako shi zuwa Parlour"


Murmushi tayi cikin jin dad'i" Ai kad'an ma ka gani kirkin shi ya wuce nan, Ina son shi sosai wlh"ta fad'a tare da dafe Daidai heart dinta.


Dariya Hisham yayi suna ta hira irin na Yaya da Kani, har ta gama ta kai ma Mommy tana Zuwa dakin ta kiran Sufyan ya shigo wayarta,cike da farin ciki ta d'auka"Baby nah I'm missing you"


Murmushi tayi tana jin k'aunar shi cikin zuciyar ta" Dafataan ka isa gida lafiya?"


"Alhamdulillah Baby sai kewar ki data adabi Zuciya ta"


 " Don't worry indai nice ai taka ce"ta fad'a cike da kunya.


 Ba karamin farin Cikin maganar ta yayi ba sun dad'e suna waya.



Kasancewar Daddy baya nan yayi tafiya hakan yasa Mommy ta bar maganar sai ta dawo ta fad'a mai,


Tun daga wannan Lokacin Sufyan yana zuwa gidan su Nadrah haka kuma soyayar su sai k'ara karf'i take, Lokacin da Daddy ya dawo Mommy ta same shi da maganar d'an jim yayi kad'an can yace"Amma meyasa ya fara zuwa gidan nan ba tare da na sani kuma na bashi izini ba, yaushe ma yarinyar nan ta fara soyayya?,banso ta kula saurayi ba har sai ta gama Secondary tukuna"


 Gyara Zama Mommy tayi" Amma Daddyn Nadrah a gani nah yanzu ya dace ta fito da miji a tsayar da magana,nafi son tana gamawa sai ayi auren ni bana son mace ta shiga University ba tare da aure ba"


"Zanyi bincike akan yaron in gani" ya fad'a cike da nazari.


 

" Yauwa mace darajar ta da Mutuncin ta Shine gidan miji" Haka dai suka Cigaba da tataunawa.



 Nadrah Sosai ta dage da Karatu sun rage waya da Sufyan saboda gabatowar WEAC ,yakan zo su sha hirar su sau dayawa ya kanyi yunk'urin rik'e mata hannu sai ta dinga k'wacewa ko ya zauna kusa da ita suna gogar juna,basu tab'a haduwa da Daddy ba,Shi kuma Daddy a nashi bangaren yayi bincike,Baban Sufyan babban mutum ne sannan kuma shi kad'ai ne d'an su bai samu wani bayani akan neman matan da Sufyan yake ba tunda iyayen shine kawai suka sani, yakan yi a b'oye.



Nadrah ta Kamala exams dinta sosai take farin ciki,An shirya musu Graduation Party a school dinsu, Nadrah da Yusrah har lalle su kayi,akayi musu make up,ana gobe graduation dinsu taje gidan su Yusrah domin karbo dinkunan ta da tailor yayi musu,har yammah tana jiran Bala driver amma shiru bai zo ba duk ranta ya b'aci bata son hawa Napep, Sufyan ne ya Kira ta bayan sun gaisa yake tambayar ta tana ina ne,sai tace gidan su Yusrah,yace yaushe zata tafi tace driver take jira amma bai zo ba,ai da Sauri yace ta bari zai zo ya maida ta gida,cewa tayi"No Sweety ka bari,zan hau Napep"


Da Sauri yace" No Baby bazan bari ki hau Napep ba,kina matar Sufyan" tura mai address din gidan tayi,ya tashi ya shirya tare da shiga Motar shi sai zuba k'amshi yake,dama ya dad'e yana son su d'an fita outing da ita amma ba dama, saboda ba'a barin ta fita,yanzu ma sa'a yaci.


Har ga Allah ita Nadrah tsoro take Daddyn ta yaga Sufyan ya maida ta gida zai iya mata fad'a na shiga motar shi, Yusrah ganin ta damu tace"Besty karki damu wlh ai yanzu ba Lalai bane Daddyn naku ya dawo"


 " Nidai wlh dama ban fad'a mai ina nan ba,baki san halin Daddy bane"ta fad'a Cike da damuwa


 "inshaallah nothing will happen just pray"


 "Tohm shikenan Besty ina godiya" 


 Suna cikin hira ya kirata gashi a Kofar gidan,sanye take cikin Abaya light brown,tayi rolling veil ta d'auki leda bags, Yusrah tasa Hijab ta raka ta har zuwa gate, cikin wata Bakar Benz ya fito, Yusrah ta gaishe shi ya amsa da fara'a,tare da bud'e ma Nadrah front seat,ta shiga tare da ma Yusrah sallama,shiga motar yayi ya fara driving wak'a yasa na Akon Na just me and you, Nadrah shiru tayi ita dai bata saba da kid'e kid'en nan ba,Can ya waiga ya d'an kalle ta"Baby nah kinyi kyau,Sarauniyar Zuciya tah..." Maganar shine ya katse ganin Kiran dake shigowa wayar shi Rejecting yayi,


Ganin yayi wani hanyar bana Unguwar su ba yasa da sauri tace"Ina zamuje"


 "Siyar dake zanyi" ya fad'a yana b'ata rai


Shiru tayi ganin Kamar ranshi ya b'aci,tana lura sai kiran shi ake a waya amma yak'i d'auka,bata sake cewa komi ba,shi kuma yana ta janta da hira,humm ko hmmm take cewa,a haka suka isa Wani Babban Shopping Mall,da Mamaki ta kalle shi.


 Yace su shiga ciki baya son tambaya,suna zuwa yace ta zab'a duk abinda take so,ita dai ta kasa d'auka karshe shine ya dinga jiddar mata kaya na sawa dasu chocolate, biscuits,Drinks,sosai yayi mata shopping kamar baya jin ciwon kud'in,sai data dinga cewa ya bari haka ta gode sanann ya bari suka shiga mota,har Cikin gidan ya shiga da ita,gaba d'aya ita kuwa a tsorace take gashi har magrib yayi,suna shiga taga motar Daddy nan hankalin ta ya Kara tashi,ganin duk ta damu yasa ya rik'e hannun ta yana matsawa a hankali, kallon shi tare da Saurin k'wace hannun ta domin gani take kamar Daddy zai fito ya gansu.


 "Calm down, why duk kika shiga damuwa?"


Daddy ta hango da Hisham sun fito da sauri ta bud'e motar ta fito,Sufyan ma ya fito ganin Hisham da wani mutum wanda yake kyautata zaton shine Daddy,



Daddy yana sauri zasu wuce massalaci sai ganin Nadrah yayi ta fito mota,ranshi yayi mugun b'aci, Sufyan ya k'arasa har gaban shi tare da gaishe shi, Daddy amsawa yayi yana kallon Sufyan,Hisham ne yace "Daddy Ya Sufyan ne"


D'an sakin fuska Daddy yayi suka k'ara gaisawa,Nadrah ma ta Gaishe shi,a hankali ya amsa tare da nufa hanyar gate shida Hisham, Nadrah da sauri tayi ma Sufyan sallama ta shige gida,duk a tsorace take,Sufyan ko tab'e baki yayi yaga kamar Daddyn baiji dad'in ganin su ba,ya kira mai gadi yasa shi kwashe kayan a booth ya bar gidan.



Lokacin da Nadrah ta shiga mommy na sallah a Parlour kawai sai ta shige d'akin ta tana zuwa tayi alwala ta tada sallah.



Gaba d'aya Nadrah ta kasa fita bayan ta gama sallah, mommy ce ta shigo d'akin fuska a d'aure,"ke sai yanzu zaki dawo,kuma wancan lodin kayan da aka shigo dashi na mene ne?"


 A rud'e Nadrah tace" Mommy dama Bala bai zo d'auka ta ba,Uhmm..toh...shine..."ta fad'a Cikin in Ina.


Tsawa Mommy ta daka mata" shine mene?"


Ba zata iya ma Mommy karya ba kawai ta fad'a mata gaskiya, Sosai Mommy tayi mata fad'a,daga nan tace bari Daddyn nasu ya dawo, Nadrah duk taji hankalin ta ya tashi.



 Sai bayan isha'i Daddy da Hisham suka dawo,koda ya shigo baice komi ba, Mommy da Nadrah dinne suka had'a dinner akan Dining Table,Duk suka zauna yin Dinner,Nadrah hankalin ta a tashe yake ta kasa cin Abincin sai cakula shi take,Duk Daddy na kula da ita.



Bayan sun gama cin abinci ne,Daddy yace Hisham ya basu guri,yana tafiya Daddy ya Nadrah wacce ta sunkuyar da kai"Wato yanzu har shiga motar saurayi kike ashe?"


 Da Sauri ta D'ago kai domin yin bayani bai saurare ta ba yayi mata fad'a Sosai, Mommy ta fad'a mai siyayar da Sufyan yama Nadrah din,nan Daddy ranshi ya k'ara baci, Nadrah tasha fad'a,Daddy yace tunda aure take so zaiyi mata.


Kuka ta fara tana bashi hakuri,yace ta wuce d'aki,bayan tafiyar ta,Daddy ya kalla Mommy"Yaron nan hankali na bai kwanta dashi ba,zan k'ara bincike akan shi,kuma daga yau kisa mata ido sosai bana son ta k'ara fita idan ba Islamiyya ba"


 Ajiyar Zuciya Mommy ta sauke" Gaskiya gara kawai ka k'ara bincken idan yaso sai ya turo magabatan shi asa ranar auren nan ayi tunda ta gama makarantar.



Nadrah kuwa tana shiga d'aki ta fara kuka,ba wai auren da Daddy yace zai mata bane yanda akayi mata fad'a ne gashi kuma tana jin gaban ta yana fad'i, wayar ce ta fara ringing ganin Sufyan ke kira sai kawai ta kashe wayar gaba d'aya domin bata jin zata iya magana.



Bangaren Sufyan kuwa Bayan ya fito gidan su Nadrah wayar shi ta sake ringing cikin b'acin rai ya d'auka"wai meye kin ishe ni da kira are you mad"ya fad'a a fusace.


 Rai a b'ace daga d'ayan Bangaren tace"Kar kayi min ihu Malam,kiran ka nayi domin in sanar maka cewa ina d'auke da ciki one month...."


Tsawa ya daka mata" will you just shut up,Ni zaki raina ma hankali kije can ki nema wanda yayi miki ciki bani ba....."


 " Kam bala'i Wallahi Sufyan kayi kad'an, cikin nan naka ne kai kace kar inyi tarayya da kowa sai kai na tsawon wata biyu kuma ba wanda na kula,kai kan ka you know that"


Tsaki yayi" Naji naji kawai ki zubar dashi Zan turo miki kud'in mtttsss"ya kashe wayar.


Haka ya cigaba da driving rai b'ace


Jamy kuwa wacce sukayi waya dariya tayi ta tafa da K'awar ta,tace"wato y'an iska ashe haka ake musu" K'awar ta Dariya ita ma tayi tace"da zarar kana son kud'i sai kayi Cikin karya kinga Dole su biya kud'i a cire idan ba so suke asirin su ya tonu ba"


" Gashi kuwa naga zahiri"Cewar Jamy budurwan Sufyan.


Koda Sufyan ya koma gida bayan ya huta zuwa ya tura ma jamy dubu d'ari biyu, Sannan ya danna mata waya yace ta cire cikin kuma daga yau babu shi ba ita kar ta sake neman shi ya kashe wayar tare da blocking number ta,nan ya kira Nadrah bata d'auka ba k'arshe ma wayar is switched off,sam baiji d'adi ba sai hankalin shi ya tashi.haka ya hak'ura zuwa safe acewar shi ya k'ara trying, Jamy Abinda ya fad'a Mata ya bata mata rai wato shi ya d'auki mata kamar kayan canzawar shi ko ai kuwa sai tayi Maganin shi.wato yanz baya bukatar ta tunda ya mata ciki, alhalin ma bai san cikin karya bane.


Washegari su Nadrah sukayi Graduation,amma sam bata wani cikin walwala haka akayi pics dai aka ci aka sha taro ya watse ko Sufyan bai zo ba,ba taji dad'i ba anma sai ya bata Hakuri tare da aiko mata da gifts.



Bayan y'an wasu kwanaki



Sam Daddy hankalin shi bai kwanta da Sufyan ba,Dan haka ya tsanan ta bincike sosai akan shi domin hakkin iyaye ne su samar ma y'ayan su miji nagari,ana cikin haka ne ranar kawai yaga an turo mai video da Bak'uwar number,koda ya bud'e hankalin shi ba karamin tashi yayi ba,rai a b'ace ya nufa d'akin Mommy, Fitowar ta wanka kenan ta gama shirya sai ganin Daddy tayi yana Mik'a mata wayar, cikin rashin fahimta ta karb'a tayi yace ta duba kawai"playing video tayi amma abinda ta gani yasa tayi Saurin rufe ido Sufyan ne da wata tsirara suna aikata Zina, Mik'a mai wayar tayi tana fad'in Innalillahi wa'ina illahir Raji'un.


 Cikin b'acin rai yace"dama ni hankali na bai kwanta da Yaron nan ba,dan haka dole ne Nadrah ta rabu dashi wannan sam bai dace da ita ba.



Nadrah na d'aki Mommy ta same ta cewa taje Parlour Daddyn su yana kiran ta,Tana zuwa Ta samu guri ta zauna Daddy ya kalle ta"Nadrah a matsayina na mahaifin ki daga yau ina son ki rabu da Yaron nan Sufyan!"


A matuk'ar razane ta Mik'e tsaye,yace" Umarni nake baki,daga yau na yanke duk wani alak'ar dake tsakanin ku,kar ya k'ara zuwa gidan nan kuma kar ku sake waya,domin shi din ba miji ne nagari ba,dan haka ki rabu dashi"



Nadrah kuka take tana girgiza kai" Daddy Sufyan mutumin kirki ne, dan Allah kar ka raba mu, wallahi muna son junan mu...."


Tsawa ya daka mata" kina hauka ne,har ni mahaifin ki zaki dinga fad'a ma haka"


Mommy cikin fushi tace" Nadrah meye haka,kina da hankali wato saurayi ya hure Miki kunne ko...."


Da Sauri tace"Aa Mommy kuyi hakuri amma nasan komi aka fad'a akan Sufyan karya ne...."


Cikin fushi Daddy yayi kanta yana cewa"wato mu ne muke karyar Koh"


Mommy ce tasha gaban shi tana bashi hakuri,tare da cewa Nadrah ta wuce ta basu guri,haka Nadrah ta koma d'akin ta tana kuka cikin tashin hankali,da sauri ta d'auki wayar ta tare da kiran Sufyan yana zaune yana tunanin ta sai ga kiran koda ya d'auka kawai ta fashe mai da kuka, hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, tambayar ta yake mene ne amma ta kasa magana da k'yar ta iya fad'a mai abinda ke faruwa Sosai ya Shiga tashin hankali, hakuri ya fara bata yana cewa ba zasu rabu ba kar ta damu, hankalin shi duk a tashe yake kawai dauriya yake domin Kwantar mata da hankali,a daren ba suyi bacci ba.




Nadrah gaba d'aya ta rame ta shiga cikin damuwa sosai, kullum cikin tunani domin an raba ta da Sufyan har wayarta Daddy ya k'wace,gashi sun gama school, Islamiyya kuma anyi hutu kullum tana cikin gida cike da damuwa,taba mommy Hakuri amma mommy tace ta rabu dashi Kawai Domin neman mata yake,ranar da Mommy ta fad'a Mata hakan hankalin ta ya tashi haka ta ari wayar Hisham ta kira shi,sosai take mai kuka da k'yar ya rarashe ta tayi Shiru nan take fad'a mai abinda aka ce akan shi Sosai ya razana da jin maganar ta amma sai yace shari ne Kawai ake mai,daga nan dai suke d'an yin waya a b'oye amma basu hak'ura da juna ba,shi kuma yana jiran Dawowar baban shi daga Cairo domin aje neman mai auren ta,yasan idan iyayen shi suka je Daddy zai Amince domin shi bai san video da aka tura ma Daddy ba,so kawai za'a ce Shari, Yusrah haka take ba Nadrah Hakuri idan tazo gidan ko sunyi waya a wayar Hisham sosai Yusrah take tausaya ma Nadrah.



A wannan Lokacin ne akayi auren K'awar ta Yusrah ta auri dan uwa ta da ya dawo k'asar waje Abuja aka kai ta, can zata zauna,Sosai sukayi kukan rabuwa da juna,yanzu kusan 3weeks da Bikin Yusrah,Daddy ya samar ma Nadrah da Admission a Kasuu inda zata karanci Law amma bata fara zuwa ba kasancewar ba'a fara lectures ba ta gama Registration din ta dai.
















UMMU BASHEER

      &

MAIMOUNATH O.G

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol