Free chapter · Read without an account

2

by Badeelah Yakubu Mahdi · JINNUL KAMIL(A TRUE LIFE STORY OF ALISHA)

Da gudu ta Shiga Kitchen, ta ciro miya a firji ta d'aura shi akan electric cooker, food flask d'in da ta sa sakwarar d'azu ta d'auka a jiye a dining, ta kuma komawa ta d'auko juice d'inda mummy ta had'a Kan ta tafi Shima ta ajiye ta koma ta d'auko plates ta jera su Suma, miyar da ta d'aura taga yayi tayi saurin juye shi a karamin flask ta kai dinning, ta Kuma d'auko pepper soup na ganda ta d'uma sannan ta dawo ta ajiye shi Akan dinning, ajiyar zuciya tayi, sannan ta koma d'akin ta, duk a cikin minti biyar tayi abubuwan nan sabida a tsorace take. Bata bari ya d'au zafi da zaran ya d'anyi dumi Saida sauke.





Tana Shiga d'akinta tayi saurin fad'awa ban d'aki ta watsa ruwa sannan tayi alwala, tana fitowa ta sa kaya sannan ta Fara sallah, ta Kai raka'a d'aya Kenan taji mummy na Kiran ta.




Mummy kuwa jin bata amsa ba ga gidan shiru tace "Yan iska babu abinda suka iya sai bacci" cikin 'bacin rai ta nufi d'akin Alisha, Bud'e kofar d'akin tayi had'e da fad'in "Alisha ba kyaji ina Kiran ki?"




Hango ta tayi Akan sallaya Tace "Kinci sa'a."

Alisha na idar da sallah, bata tashi ba Saida ta jero azkar d'inda ta saba, kana ta Mike  ta nad'e sallayar, juyowar ta ke da wuya ta hango mummy a bakin gadon ta a zaune ta d'aura kafa d'aya a kan d'aya.




Murya Chan ciki Tace "Mummy welcome(sannu da dawo was)"

Murmushi tayi ba tare da ta amsa gaisuwar ba Tace "Ina Daddyn ku?"

Cikin Rawar murya Tace "Ban sani ba ina ga ya fita"

"Ina ta Kiran shi bai d'aga ba,amm......"

Turo kofa akayi had'e da fad'in "Mamana kina Nan?"




Mummy da Alisha a tare suka kalli kofar, Daddy na ganin Mummy ya yace "Har kin dawo?"

"Eh" kawaii Tace Masa ta fice daga d'akin har tana kokarin ture shi. Tana tafiya Tace "Ki fito ki Kira kannen ki a ci abinci"




Daddy yace "Me kikeyi tun d'azu baki yi sallah ba? Ko anyi la'asar ne?"

"Wallahi daddy bacci ne ya d'auke ni ban San Lokaci ya tafi haka ba"

"Ki kula ki daina sallah a makare, ki fito kuci abinci"

"To daddy,insha Allah Zan kiyaye." 




A dinning room ya tarda mummy tana zaune, sai faman danna wayar ta take, daddy na Zama ta Mike tasa mishi abinci, yace "Thanks" Murmushi kawaii tayi ta sawa kanta.




Zamanta yayi dai dai da shigowar su Alisha da Fa'eez da Hisham, plate ta d'auka ta sawa ko wannen su, sukayi godiya, tunda suka fara cin abincin Babu Wanda yace kala har suka gama, da taimakon Alisha mummy ta gyara Kan dinning table d'in, bayan sun gama suka koma d'akin su, daddy kuwa parlor ya nufa ya na kallon TV, Mummy kuwa ta d'auki mayafin ta, ta koma shagon ta ba tare da ta kula kowa acikin suba.




 *TUSHEN LABARI*

Abdulhameed Adam 'dane ga Adam Abiodun, Asalin 'dan garin Lagos ne bayarbe ne shi, ya na Aure Amina Abdulmalik, duk da cewar su Yarobawane Amma sun Riki addinin su da hannu bibbiyu, Amina da Adam auren Soyayya sukayi, sun d'auki tsawon shekaru ashirin ba haihuwa ko 'batan wata ne Amina bata tab'ayi ba, hakan baisa Adam ya juya mata baya duk da cewar a ko da yaushe Yan uwansa suna cikin zaginta cewar ya auri juya, zagin yau daban na gobe daban, Babu yanda ba suyi dashi ba akan ya rabu da ita ya kara aure amma yaki,ita kanta Amina tayi rarrashin duniya Akan ya Kara auren amma yaki,a fad'in sa idan ya auro wata zata Raina mishi mata shi Kuma bazai lamunci Hakan ba, ganin Basu da niyar barin zancen ya rabu da matar sa hakan yasa ya nemi transfer a gun aikin sa ya dawo garin Gombe da aiki.





Dawowar su Gombe da Shekara d'aya Amina ta tashi da zazza'bi Mai zafi sosai, Adam ya rikeci sosai hakan yasa ya kaita Asibiti, ai kuwa likata na duba ta ya shaida Masa cewar matar sa na d'auke da ciki har na tsawon wata uku, yayi farin ciki sosai.





Amina kuwa tana jin cewar tana da ciki ta fashe da kuka, Adam Zama yayi a gefen ta yace "Amina kukan me kuma kikeyi? Bayan burin mune ya cika abinda muka dad'e muna nema sama da shekaru ashirin, Kuma naga kina Kuka why?"





Cikin muryar kuka tace "wannan kukan Farin ciki ne ba na bakin ciki ba,ina matukar farin ciki, farin cikin da nake ciki bazai misaltu ba"





Sa hannu yayi ya share mata hawayen yace "na fahimta my dear wife, Zan Kira Mama na fad'a mata yanzu" yana maganar yasa hannu ya zaro wayar sa, da sauri ta rike hannuna sa had'e da girgiza Masa kai Tace "a a please Kar ka Kira ta.




Cike da mamaki yace "meyasa?"

"Kawai so nake sai munje su gani da idanun su"

"Kina nufin zamuje gida?"

"Eh a chan nake so na haihu"

Girgiza kai yayi yace "Baza ki haihuwa a gida ba, kin manta abubuwan da suka miki ne? Idan ke kin manta ni bazan manta ba"




"Ka fahimce ni, Yan uwan Kane su, hakan yasa nima sun Zama Yan uwana, yau shekara ashirin harda biyu da auren mu Amma ban tab'a haihuwa ba they have all the right to be mad at me"






"Su Basu San kaddara bane? Lokacin rabon namune Bai zo ba, gashi Allah ya kawo shi yanzu, ai ba laifin ki bane yin Allah ne, Kuma Allah kad'ai ya bar wa kansa sani, Amma duk da hakan babu irin wulakancin da basu miki ba, Amma Kuma ke da ke marar zuciya ce har kike fatan zaki koma, Ni nayi alkawarin bazan sake komawa chan ba, haka kema baza kije"





Mikewa yayi yace " tashi mu koma gida an sallame ki" Bai tsaya jinme zata ce ba yayi ficewar sa, Murmushi tayi ta shafa cikinta Tace "Kana jin baban ka ko, ko ince baban ki, Kar ki d'auko irin Wannan fushin nasa."





Mayafinta ta d'auka ta yafae ta Fice, ta samu Yana zaune a mota yana jiran ta, gidan gaba ta Bud'e ta zauna, tana Zama ya fisgi motar ba tare da yace mata komai ba.







Cikin dare, ta tada shi cikin salo da lallama ta shawo kansa har ya amince zasu je gida, Amma sai ta kusa haihuwa tayi ta murna, ta masa godiya sannan tana jin so da Kaunar mijin ta na ninkuwa a birnin zuciyar ta.







Cikin Amina na wata takwas suka kama hanyar Lagos ta wahala sosai duk da cewar da motar su suka tafi ba na Tasha ba, Adam ke Jan Motar, kafanta ya Kumbura tim, Kai tsaye gidan su Adam sukayi, horn yayi sai da Mai gadi ya leka don ganin wane ne, yana ganin d'an gidan ne da Rawar jiki ya Bud'e masa gate.






Mama na zaune a yar karamar gadin dake gidan, tana ganin ya cike da mamaki ta mike, tana ganin Amina kuwa tayi tsaki ta zauna, cikin sauri ya nufi Amina don yasan tafiyar wahala yake bata, bayanta ya tallafa yana mata sannu, Mama cire eye glass d'inta tayi ta zaro Ido don tabbatar da abinda idonta ke gane mata.






Har suka isota kallon cikin Amina take, kallon Adam tayi Tace "Adamu me Zan gani haka? Kamar ciki nake gani a jikin yarinyar nan"







Ba tare da ya kalle ta ba yace "Eh Mama ciki ne da ita"

"Alhamdulillahi" riko hannun Amina tayi ta zaunar da ita akan plastic chair dake gun tana mata sannu, sa hannu tayi Akan cikin Amina tana dannawa Amina ta sa kara, razane ya yace "Mana what's the meaning of this? So kike ki kashe min d'a?"

Dariyar tayi tace "Ah ahhh don't be angry my son, so nake na tabbatar da cikin ne ko tsunma, I mean no harm"

Ta Maida kallon ga Amina tace "You're Welcome my daughter(sannu da zuwa 'yata), Allah ya raba Lafiya" ta fad'a da yarobanci, Amina ta amsa da amin.




Da taimakon Mama Amina ta shiga d'aki, Mama na Rawar jiki ta had'a mata ruwan wanka,bayan tayi wankan Yan uwa da abokan arziki, da magulmata sai kaiwa suke suna kawo wa.




Mahaifiyar Amina na Jin Labarin cewar yarta ta zo kuma tana da ciki gud'a ta shigayi tana rawa tana godewa Allah, ba ta tsaya 'bata lokaci ba ta je gidan, mahaifiyar Adam na ganinta taji kamar ta nitse kasa sabida Babu irin cin mutunci da ba ta mata ba, Gori Kam sun Shashi dai dai gwargwado.




Kannen Amina kullum suna hanyar zuwa duba Yar uwarsu, haka zalika kanne da yayun Adam kullum cikin yi mata hidima suke, sabida Adam ne kad'ai 'da na miji agidan nasu,shi Kuma Adam bayan sunyi sati d'aya ya koma Gombe, bazai dawo ba har sai ta Shiga watan haihuwar ta.




Kula take samu ta ko ina har ta shiga watan haihuwar ta, wata ranar jumma'a Adam ya shigo gari, yana kwance Yana hutawa sabida ya kwaso gajiya Mama da gudu ta Shiga ta Sanar dashi tsabagen tsorata da yayi jallabiyar da yasanya a jikin sa da baibai ya sa, ya d'auke ta ya sata a bayan mota, Mama kuma ta d'auki duk abubuwan da za a bukace shi a asibiti.




Suna Isa asibiti bata dad'e ba ta haifi santalelen d'anta, murna agun Adam bazai misaltu ba haka ma mama, Nan da nan batun haihuwar ta ya zaga Kan dangi, tun Kan a sallamesu wasu suka Zo duba su.




Bayan sun koma gida kuma Banda Shiga da fita Babu Wanda abinda ake a gidan, kyaututtuka Kam sun samu, a ranar suna yaro yace suna *Abdulhameed* anci ansha, namomin kaji da Naman shanu kamar zasuyi magana, sakwara kuwa anci shi abun ba a cewa komai sai Masha Allah, a ranar sunan ma sun samu kyauta sosai daga ita har d'anta.




Bayan haihuwar ta da wata d'aya, Adam ya ce ta zasu koma Mama na Jin Haka ta hana, Amina baza ta koma ba har sai jikinta yayi karfi, Kuma d'an ta yayi karfi, Kai da ya Kama ka koma sai ka koma. 



Ba don yaso ba ya koma Gombe, sun d'auki tsawon Watanni uku a gida Amma duk da hakan Mama ta hana, har Saida baba ya sa baki a maganar ya dawo ya d'auki iyalin sa.



Abdulhameed ya taso cikin gata, soyayya da kuma kulawa,bayan shi Amina bata sake haihuwa ba amma duk da hakan cikin godewa Allah take da ya bata Abdulhameed.




Abdulhameed yarone kyakkyawa ba farine bane sosai sannan ba baki bane wannan ba, dogone Mai faffad'an kirji, a ko da yaushe fuskar sa a sake take zaiyi wuya kaga 'bacin ransa, duk abinda yake so shi akeyi Masa.




Duk da ya kasance shi kad'ai ne d'an su hakan bai sa sun 'bata shi ba kamar yanda wasu iyayen keyi, kullum cikin karatu yake, ba a iya Boko ya tsaya ba harda karatun muhammadiya 




Tun yana d'an shekara goma sha biyar yayi saukan alkur'ani, bayan ya gama secondary School yayi jamb, sannan ya nemi admission a Gombe state university, anyi sa'a Business Admin yake so Kuma ya samu.




Nan da Nan aka masa registration, ya Fara zuwa yana aji biyu ya had'u da wata yarinya mai suna Haleema, daga abota suka fara sannan tare suke karatu dake department d'insu d'aya.




Haleemah 'yace ga Alhaji Abdulrazak Basi da Hajiya Hajara Abdullahi, mutanen cross river suma ne Yarobawane, aikine yasa suka dawo garin Gombe, Haleemah da Fiddausi sune kad'ai 'ya 'yan Abdul'razak da Hajara, Alhaji Abdulrazak ba mai kud'i bane sannan ba talaka bane suna da rufin asiri dai dai gwargwado da buga bugan sa har ya samu ya biya wa kansa da matar sa hajji.




Haleemah da Hameed soyayya suke sosai, har ya kai ga iyayen su sani uwa uba kowa yasan Yarobawa wasu su suna da kabilanci, ganin dukkanin su yaren su d'aya suka samu goyon baya d'ari bisa d'ari daga gun iyayen su.




Bayan sun gama makaranta, Abdulhameed ya Fara aiki a kamfanin Mahaifin sa don zuwa yanzu ya samu cigaba sosai a business d'insa, hakan yasa 'dan sa bai sha wahalan neman aiki ba.




Bayan gama makarantar su da shekara biyu aka d'aura musu Aure sannan suma Suka tare a anan garin Gombe, a Shekarar da sukayi auren Bata Kai wata d'aya ba ta samu ciki ta samu yarta mai suna Alisha, bayan Shekaru uku ta haifi Fa'eez, bayan Shekaru biyu ta haifi Hisham, sai Yar autar ta Mai suna Nawal wacce kwatakwata bata wuce shekaru goma ba a yanzu.




Haleemah na matukar son 'ya'ayan ta duk wani abu da ya dace uwa tayi wa 'ya'yan ta tanayi, Hameed ganin tayi karatu kuma tana son business sosai ya bata jari ta Bud'e boutique, kayakin ta masu kyaune daga Dubai take order d'in su, hakan yasa ta sanu sosai, Bata dade ba boutique d'inta ya bunkasa ya Zama shine boutique d'in da yafi ko wanne a garin Gombe sabida tana aikinta da kwarewa. Boutique d'in nan shine mafarin rushewar farin ciki da kwanciyar hankali a gidan Abdulhameed.






Tun daga Wannan Lokacin ta daina Zama cikin iyalan ta, Bata sanin farin ciki bare bakin cikin su, 'bacin ransu, idan kaga ta musu magana to fa na fad'a ne ko Kuma duka.

_____________________________

Please comment and Share

Milhat ce

Yar Terawa ✍🏻

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol