Free chapter · Read without an account

Chapter 15 nd 16

by Zainab A Barde · ZAINABU ABU

✨✨ ZAINABU ABU ✨✨

                 Na

   

       ZAINAB A BARDE


   ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITERS ASSOCIATION

   (A.Y.T.W.A)


Page 15 nd 16

****

Da wannan hirar suka karaso gida, ko zama basuyi ba Zainabu ta kwaso kayan wankin su, ta fara wanki, itako Anna girki ta dora masu, tana masifar an takura wa jikar ta a cikin garin nan, "daga yau zan fara mana tarun kudi wllhi, danni ba gantalalla bace da zan zauna inda ba'ason jikata","ni dama Anna na jima dason mu bar wannan banzan garin","karki ji komi jikata, aini duk abinda kike so shi nakeso, karki wani damu, kisa aranki gari kamar mun barshi ne","yauwa Annata shiyasa a koda yaushe nake kara sonki.


Zaune yake a kan kujerar dake cikin office din shugaban gidan marayun, "yallabai, bamu da bakin yi maka godiya da wannan dawainiya da akeyi da marayun nan, saide muce Allah ya biya maka bukatun ka na Alkairi" kayataccan murmushi yayi, wanda hakan ya kara fito da tsantsar kyawun sa, saboda ba kasafai ya ciki yin murmushin ba, gyara zama yayi akan kujerar ya dora kafa daya kan daya, magana ya fara cikin daddadar muryar sa mai dadin sauraro, cikin natsuwa yace, "na dade da fada maka, ka daina kirana da Yallabai, call me with my name, MUHAMMAD KABIR, dani dakai duk daya muke a wajan Allah, babu wanda yafi wani, sai wanda yafi bauta masa","ayimin afuwa, zanji nauyin kiran sunan ka kai tsaye ne shiyasa","babu komi ka fada kanka tsaye ba wani abu bane","To Muhammad Kabir muna godiya sosai, Allah ya saka da alkairi","babu komi nidai abinda nakeso daku shine, ku cigaba da rike amanar da Allah ya baku","insha Allahu"


Mika masa hannu yayi, yana mikewa tsaye, har bakin motocin sa ya rakosa, da sauri masu tsaron lafiyar sa suka bude masa mota ya shiga ya zauna sannan suma suka shiga tasu cikin azama suka hau titi, duk inda suka wuce motocin ake kallo, saboda tsabar haduwar su, motoci ne jere guda goma ko wacce mota tinted ce, baka iya ganin na ciki, tafiya suke cikin natsuwa, saboda baya son ya shiga hakkin mutane, kowa yaga lambar dake cikin motocin wato *MK* saiya masa fatan Alkairi saboda taimakon sa ga Alumma, ko ina suka wuce hannu kawai ake daga musa, a haka har suka karaso gida, gida ne daya amsa sunan sa gida, bawai muna gida ba, kaida ka kalli gidan kasan mamallakin sa ya tara, motocin na tsayawa da sauri bodyguards dinsa suka fito suka bude masa kofa, fitowa yayi, ya nufi kofar shiga gidan, da sauri daya daga cikin yaran nasa ya ruga ya bude masa kofar, har ya shiga ya dawo, "kuje ku samu wannan mutumin daya kwace wa wadan nan marayun gidan su, tell him that I want to see him, and if he refused, ku dauko min shi ta karfin tsiya","an gama Sir" daga haka ya shige ciki.



Yana zuwa Company ya tarar da uban aiki jiya kawai da baizo ba, PA din Abee ne ya shigo, "Sir Muhammad Kareem yazo office, shigowar sa kenn ma, nace bari na sanar maka" nannauyar ajiyar zuciya Abee ya sauke, yaji dadin shigowar Muhammad Kareem office, duk da cewar yasan bazai taba fada masa magana ba yakiyi masa biyayya, yasan tunda yace masa lallai lallai yazo Company yasan zaizo amma mutum yana iya chanzawa a koda yaushe, "nasan cewa Muhammad Kareem shine bangon wannan Company, muddin kuwa ya daina zuwa, to abubuwa zasu tabar bare, Company zai lalace","gaskiya ne Sir, Muhammad Kareem yana matukar kokarin ya jajirce akan yaga wannan Company yaci gaba, kuma ya samu daukaka","na sani PA, Allah yayi masa Albarka","Ameen ya Allah","ka shirya yanzo zamu fita","owk sir" ya fada yana fitowa daga office din.


Shima fitowa yayi, da sauri PA ya bude masa bayan mota ya shiga, shi kuma ya shiga wajan mai zaman banza, driver yaja suka bar Company, saida suka hau kan titi sannan ya tmby Abee ina zasuje, "ma'aikatar Alhaji Bukar zanje" ta cikin mudubi PA ya kalli Abee, maiyasa zaije chan, bayan bakar gabar dake tsakaninsu, ko sun shirya ne banida labari, yayi zanchan a cikin zuciyar sa amma babu mai basa amsa, wayarsa ya dauko ya turawa wata lamba test massage, akan gasu nan zuwa ma'aikatar su, ni kaina bansan number wane ko wacece ba, babu jimawa aka dawo masa da reply, ashai yau muna da manyan baƙi, murmushi PA yayi ganin abinda aka rubuta, kashe wayar yayi ya maida ta aljihu,



Suna zuwa da sauri PA ya fito ya budewa Abee kofa, tunda suka shigo ma'aikatar ake kallonsu bare ma wandan da suka san baƙar gabar dake tsakanin Alhaji Bukar da kuma Abee, bai jira an masa jagora ba, ya fara tafiya, ko tsayawa a basa izinin shiga baiyi ba, ya bude kofar office din, dagowa Alhaji Bukar yayi, murmushi dauke akan fuskarsa, shi duk a tunaninsa Abee yazo ne dan suyi sulhu, su cigaba da tsohuwar abotar su, shiko indai da hakan yazo, to ya shirya tsaf da irin wulakanci, da kuma korar karan dazaiyi masa, zama Abee yayi dan bashi bukatar a bashi izinin zama kafin ya zauna,


"Nazo ne in fada maka, kajawa yarinyar wajanka kunne akan ta rabur min da ɗana, if not, zan maka ku a kotu, no need of having any relationship da Wanda bashida tsoran Allah, kuma macuci,maha'inci, kuma Azzalumi","kaga dakata Malam, bangane abinda kake nufi ba, what the hell my daughter will do da wannan gunkin dan naka, she is not his mate anymore God forbid, kaidai zaka jawa danka kunne bani ba, kama je kaja masa kunne tun dare baiyi muku, okayyy is that what you said? "Yeah ni Alhaji Bukar haka nace" Abee bai sake cewa komi ba ya fito daga office din ransa na suya, sai baza babbar riga yakeyi, mota ya shiga yana fadin "let's go home"


Yana fitowa shima Alhaji Bukar ya shiga mota, ya nufi gida, yau sai yaji dalilin da yasa Shahida zatayi soyayya da dan makiyinsa, kuma uwarta ta sani amma basu sanar dashi ba, suna zuwa gida ko parking bai bari driver sa ya gama ba ya fito, yana kwala kiran sunan, Shahida! Shahida!! Shahida!!! Umma ce ta fito tana fadin Abban Shahida lfy kuwa, kake kwala mata irin wannan kiran","ki kyale ni tukunna I'll get back to you.













Shere fisabilillah.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.