FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Labari ne mai cike da cin Amana, makirci, da kuma fashi da makani.
Sample · ZAINABU ABU
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨ Na ZAINAB A BARDE*GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION* { _Marubuta masu garkuwa da alƙalami domin fadakar da al'ummah_}Free page 1 nd 2Juyi kawai takeyi, saboda hayaniyar yaran da suka hanata bacci, bargon ta jawo ta tura kanta a ciki wai ko zata daina jiyo hayaniyar yaran, amma ina kamar a cikin dakin suke hayaniyar, dagon tsaki taja tana fitowa daga ciki bargon, fitowa waje tayi inda yaran suke zagaye da wata tsohuwa, "Anna ni ta hamsin za'a bani","Anna ni kuma ta ashirin","Anna wllhi ni za'a fara bawawa, ai na rigasa zuwa","wllhi baku isa ba ni za'a fara sallama","duk kuyi hakuri za'a sallami kowa yanzon nan" bayan ta karewa yaron kallo da kowa burinsa a sallame sa, wani takaici ne ya rufeta na tashinta daga daddadan bacin da takeyi, tsaki taja a karo na farko, ai da sauri yaran suka jiyo ganin wacce ta fito yasa sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su, lokaci daya suka natsu saboda ganinta, Anna kuwa jin shirun yayi yawa yasata dagowa, murmushi tayi ganin ashai dodonsu ce ta fito, daya daga cikin yaran ne yayi tsuru tsuru, irin na mararsa gaskiya.Shako masa wuya tayi, "dan buhun ubanka wana kama, dama na gaya maka zaka shigo hannu, wato ranar saboda kaga a gaban uwarka ne harda zagi na ko aiko yau zaka gayawa yan garinku" marinsa tayi aiko yaro ya fashe da kuka, wani marin ta kuma kifa masa, aiko nan yaro ya fadi kasa yana kuka, duk da haka bata kyalesa ba saida ta kuma marinsa, hakan ma ta kyalesa ne saboda maganar da Anna takeyi mata, aiko yana ganin ta kyakesa ya zura a guje yana fadin "Wllhi saina gayaki da mamana" dariya ta barke da ita, "yoo uwar takama in tayi lakada mata na jaki zanyi banlantana kai karankada miya, ku kuma kallon mai kukeyi min" ai dandanan suka sunkuyar da kai kasa, "kuma bari kuji na fada muku wllhi daga yau, in kukazo siyan waina kuka cikamu da surutu, wllhi sai naci uwar mutum kai harda uban ma, ko bakuji mai nace ba" ta daka musu tsawa, A firgice yaran suka hada baki wajan fadin, "munji","karma kuji jikin mutum nai dai zaiyi tsami, ehhe","kekam Allah ya shirya min ke, na kula so kike ki korar mun yara, su daina zuwa suna siyan waina ta","yoo dan ubansu su daina zuwa mana, suga yadda zanje har gaban uwar yaro inyi kuli kulin kubura dashi" girgiza kai kawai Anna tayi, tama rasa abinda zatace, nan dai ta sallami yaran, hada kwanikan tayi, ta kaisu wajan wanke wanke, daganan ta share gidan sab, wanke wanken tayi, tare da sharo dakunan, saida ta gyara gidan sab sannan tazo ta zauna a kusa da Anna, "Jikalle ta maz...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.