Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Hafsat usman waziri · ASMA’UL HUSNAH

~*_ASMA’UL HUSNAH_*~


NA 

~HAFSATOUAMJAD ~


_FREE PAGE _

03 


ASMA’UL HUSNAH na kudi ne it’s just 400 call or chart *** for more enquiry 



 ——————-✍️Da sauri su duka suka karasa bakin kofar Tuni hankalin su gaba daya ya tashi ,ganin Asma kwance babu alamun tana numfashi, da alamun taji abunda suke tattaunawa akai 

   Mamy har ta fara zubar da hawaye jikin ta in Banda rawa babu abunda yakeyi ,idan akwai abunda ta tsana Toh ya kasance shigar Asma cikin damuwa ko rashin lafiya itama atake rashin lafiyar yake kamata saboda tsananin yanda take qaunar ta , Ganin tana neman tada hankalin ta ne yasa Fahad da ya dauki Asma yace “Mamy please karki maida karamin abu babba babu abunda ya same ta ,nasan kawai shock ne and she be alright insha Allah “ 

   

   Cikin parlour ya dawo da ita ya shimfide ta a 3 seater ,suma gaba daya parlour suka dawo kowa zuciyar sa babu Dadi ,da sauri Anwar ya karasa medium fridge din dake parlour ya daukko ruwa a gora ,da sauri Fahad ya karba kafin ya yayyafa mata a fuskan ta wani karfaffen ajiyan xuciya ta sauke kafin ta saki wani marayan kuka tana jin bakin cikin abunda Ahmad ya mata har cikin k’ahon zuciyar ta , Ajiyar zuciya suka sauke atare gaba daya ganin ta farka amman kukan ta ba karamin kara daga musu hankali yayi ba , 


 Noor dake tsaye shima still abakin kofar ,shi kanshi abunda suka fada ba karamin shocking nashi yayi ba ,be taba tunanin Asma zaayi wa aure ba se yanzu da yaji cewa Saurayin ya fasa ,sosai yakejin shi cikin wani yanayi shi ba farin ciki ba Kuma ba bakin ciki ba shi kanshi baze iya fadar mood din daya shiga ba ,yanason Asma son da bazeso abun farin ciki ya sameta kuma wannan farin cikin yayi fading ba , Tattaro ragowar karfin daya rage mishi yayi sannan ahankali yayi sallama ,

  Mamaki ne ya kama su duka ,saboda basu San da wanzuwar mutum awurin ba se sallamar shi da sukaji , Ganin Noor yasa Fahad tasowa jiki asanyaye ya karaso yana murmushin yake , shima dole ya kakalo nashi sannan ya Mika mishi hannu sukayi musabaha “Yaushe ka shigo Noor “? “Tare muke da Asma “ waro ido yayi yana yin gaba sannan yace “Amman tun dazu kana tsaye sekace wani stranger ,Mesa baka shigo ba “? 

 Be ce mishi uffan ba har suka karasa cikin parlour da sautin dasashiyar Muryar Asma dake kuka ne kawai yake tashi ,Sosai yake jin zafin kukan da take .


  Ahankali ya zauna kan kujerar bayan ya gaida Mamy ,Murmushi tayi duk da tana cikin Matsala kafin ta amsa cike da kulawa ,gaishe sa Anwar da Kamal Sukayi ya amsa musu da karamin murmushi a fuskan shi . 


  Mikewa Asma tayi a hankali tana daidai ta tafiyar ta kafin ta shige Main parlour 

 Binta yai da kallo yana kara jin tausayin ta yana ratsashi 


 “Naji kace tare kuke da Asma a ina ka Samota “? 

Mamy ta katse mishi tunanin daya tafi ,

 Numfashi ya sauke sannan yace “Anan bakin layi na ganta zan wuce kamar tayi having accident , Toh sena dauke ta na kaita asibiti sukayi treating dinta bayan tayi resting ,shine yanzu na dawo da ita gida “ 

 Sanyayar ajiyar zuciya Mamy ta sauke tana kara godewa Allah ,da babu abunda ya samu Asma 

 Suma su Kamal hankalin su ya kwanta jin abunda ya faru ,kuma da hannun wanda ta fada sunsan Noor baze taba cutar da Asma ba saboda mutum ne shi me sanin ya kamata 

   “Mun gode sosai Noor Allah ya saka da Alkhairi ya baka mata ta gari ya...”

    Katseta yayi cikin hanzari yace “Haba Mamy mene na godiya bayan duk abunda nayi ban fadi ba ,koba Asma ba In naga wani acikin wani yanayi zanyi kokarin taimako shi daidai yanda zan iya kibar godiya “ 

 Jinjina kai tayi tana jin dadi cikin ranta tana kara gode mishi , 

  Mikewa yayi suka kuma musabaha da Fahad kasancewar shine abokin shi tun suna yara ,halin su ne be zo daya ba kasancewar Fahad Mutum ne me surutu da kutse kutse sabanin Noor da magana bata dame shi ba kuma rayuwar wani bata gabanshi, shysa tun daga lokacin da Fahad ya fahimce shi se ya zare jikin shi ,Amman sukan hadu time by time Sudan yi hira . 


   “Drugs dinta suna wurina zan ringa zuwa da kaina na bata “

 Yana gama fadar haka yayi gaba , Fahad ya rakoshi har bakin gate yana kara mishi godiya , seda ya fita sannan shi kuma Fahad ya dawo gidan .


    Zama yayi a parlour sannan suka cigaba da tattaunawa akan abunda ya faru , 

 Kamal ne yace “Toh Mamy mene dalilin fasa auren nasa atleast ai seya fadi abunda ya faru ko “?


 Jinjina kai Fahad yayi yace “Nima abunda nake tunani kenan ,Amman kar muyi saurin yanke hukunci ajira aji daga bakin iyayen sa “

 Kallon su Mamy tayi tace “Ni tunanina taya Zan fara fadawa Dadyn ku magannan nan this is painful “

  Sauke numfashi Anwar yayi sannan yace “Duk abunda ya samu bawa Muqaddari ne daga ubangiji,fasa Auren Ahmad bashi yake nufin Asma ta rasa miji ba har abada me yiwuwa Ahmad ba alkhairi bane shiysa allah be kaddara zamtowar su ma’aurata ba Mamy Addua kawai zamuyi kuma mu dauki dangana Dan Allah “

  Mamy da kanta yake sarawa tace “Allah yasa hakane yafi Alkhairi”

 Da Amin suka amsa su duka ,duk sunyi jigum 


Ganin haka yasa Mamy tace su tashi su tafi gidajen su dare yayi kar su shiga hakkin matan su .


 Mimikewa sukayi sannan sukayi wa Mamy sallama suka wuce , itama bayan fitar su mikewa tayi ta shiga main parlour ganin Asma bata nan yasa ta haura stairs , dakin ta nufa ,da sauri ta karasa cikin dakin ganin Asma kwance jikin ta in Banda rawa babu abunda yake hankali atashe ta taba wuyan ta ,Zafin da taji jikin ta yayi ba karamin daga mata hankali yayi ba “Innalillahi Asma Dan Allah karki jama kanki abunda ze cutar dake ,muma kisaka mu acikin tashin hankali “ 

  Asma da takejin Gaba daya jikin ta ya saki ,ji take kamar ana dadatsa gangar jikin ta juyowa tayi ahankali ta riko hannun Mamy tana tsiyayar hawaye “Mamy ki yafemin Dan Allah ,Mamy nasan bazan yi tsahon rai ba ,bana fatan ma na kara kaiwa koda zuwa gobe ne rayuwata bata da amfani , babu wanda ze ganni da mutunci da k’ima Dan Allah Mamy ko bayan rai na kiyi Alfahaari dani kuma ki ringa Min Addua “ 


 Saurin toshe mata baki Mamy tayi da Hannun ta tana jin tausayin ta har cikin ranta ,hawaye n suka fara zirya a fuskan ta a hankali tace “Asma waya ce Miki Mamyn ki bata alfahari dake ? A koda yaushe ina miki Addua kuma ina alfahari dake Ina matukar son ki ,rayuwar ki tanada amfani a garemu koda bata dashi awurin Ahmad karki kuma furta irin wadannan kalaman In ba haka ba zamu bata ,Dan an fasa auren ki bashi yake nufin jin rasa miji ba kenan har Abadan Allah yana kallon ki kuma yana tare dake ze kawo miki wanda ya fi Ahmad insha Allah Asma na “ 

 Sosai jikin Asma ya kara sanyi Mahifiyar ta tana kaunar ta sosai ko da iya wannan ya ishe ta rayuwa ,duk da tasan itada aure sunyi bankwana tasan babu namijin da ze aure ta a yanda take koda ya aureta In ya tabbatar bata tare da budurcin ta dole ya sauwake mata . 


 Rungume Mamy tayi tana karajin kaunar ta “ Na dena Mamy na Ina kaunar ki sosai “ 

   Itama rungumar ta tayi sosai tana jin soyayah ta na kara ninkuwa a zuciyar ta

    Seda taji kukan nata ya lafa sannan tace mata “Kinyi sallah “ 

  Girgiza kai tayi sannan Mamy tace “Oya tashi maza maza kiyi sallah “ 

   Mikewa tayi ahankali , sanann ta fara takawa kamar me koyon tafiya saboda yanda wurin yake mata zafi ga shi koya ta Gogi both cinyoyinta kamar ana kara mata zafin , ahaka har ta shige toilet din tana dafa bango ,seda ta tari ruwan dumi me Dan dama sannan ta shiga saurin toshe bakin ta tayi jin yanda Azaba ta Ratsa ta da sauri ta mike daga cikin ruwan ta lafe ajikin bangon bandakin tana goge hawayen da suke tsere a fuskan ta, girgiza kanta ta farayi tana me kokarin danne kukan da yake neman kufce mata ,kuma komawa cikin ruwan tayi wannan karon kam kukan yaki boyuwa dole ta fara rera kukan ta mara sauti kasancewar muryan nata baya fita ko kadan , ahaka dakyar ta iya minti 3 acikin ruwan ta fito watsa ruwa kawai tayi bata iya sakawa jikinta soso ba saboda yanda takejin jikin ta yana saki ,alamun zazzabi yana gab da kamata saurin saka towel dinta tayi ta fito a toilet din tana harde kafa, wanka tayi ta dauro alwala sannan ta fito daga toilet din da towel daure ajikin ta ,data fito Mamy bata nan Amman ta shimfida mata sallaya da Babban hijjab se gefe flask din tea ne da plate da abinci kadan aciki da maganani agefe ,share hawayen da suka zubo mata tayi ta shirya shap shap cikin kayan baccin ta sannan ta rama duka sallolin da ake Binta duk da bata iya yin sallah a tsaye ba saboda Jirin dake dibarta ga kuma zafin da kafafuwanta keyi wanda. Ko kwakwaran motsi bata iyawa,ta dade a sallaya tana Addua har Mamy ta dawo ,seda ta shafa adduar Mamy ta Tayata da Amin murmushi tayi daya tsaya iya fatar bakin ta , dole Mamy ta tilasta mata tasha tea din amman kasa cin abincin tayi saboda gaba daya bakin ta babu taste, bayan tasha Magani Mamy tace ta kwanta ta huta ,seda ta tofa mata Addua sannan ta kashe mata fitila tana mata Seda safe .ko kadan Mamy bata soma yi mata maganar fasa auren ba saboda batason tagan ta cikin wani hali .



 Duk yanda Asma taso ta rintsa a daren nan abun ya gagara koya ta rufe idon ta abunda ya faru ne yake dawo mata sabo fill ,tayi kukan tayi harta gaji zuwa lokacin hawayen idon ta sun kafe ,se kukan zuci da take ga wani hamshakin zazzabin da ya kuma rufeta tana kallon maganin Amman bazata iya koda mika hannun ta ba alokacin duba da yanda jikin ta yake rawa ,sunayen Allah kawai take kira . 


 Akan idon ta akayi kiran sallar asuba na farko kuma har lokacin zazzabin be sauka ba , Se karfe 7 sannan ta samu wahalallen barcin da batayi shiri ba ya tafi da ita, har Mamy ta shigo dakin ganin yanda take baccin a takure ya tabbatar mata da ,da zazzabi ta kwana 

 Kashe mata Ac dakin tayi gaba daya sannan ta kara gyara mata bargon data rufa dashi ,ta saki duka labulayen dakin sannan ta fita .


  Bata wani dade tana baccin ba ta tashi , Alwala tayi da ruwan dumi sannan ta kabbara sallah tana daga zaune saboda yanda jiri yake kwasar ta addadafe ta idar da sallah ta kuma hawa gado ta kudunduna.


  11 Mamy ta kuma shigowa dakin da breakfast a hannun ta ,Fahad dasu Ammar abayan ta 

 Ganin Halin da take ciki ba karamin daga musu hankali yayi ba ,Mamy ce take rarrashin su akan zazzabi ne kawai amman inta ci abinci tasha magani ze sauka , suna zaune dukan su suna mata zolayan da suka saba duk bakin cikin da take ciki dole ta biye musu sukaita dariya saboda tanason hankalin yayyun nata ya kwanta ganin yanda duk suka rikice, 

 Dole taci Abinci Tasha maganin da Mamy ta bata dazun, ita da kanta ta danji saukin jikin ta , basu bar gidan ba har seda Mamy ta tilasta musu sannan suka tatatfi aiki aka bar Ammar Dan yace yau baze fita ba yana kusa da Crime patner din shi , Ahaka suka wuni a tare taji sauki sosai har game suka buga da Ammar , duk wani abu da ze saka ta tunani Ammar ya hana , sede lokaci zuwa lokaci takan tuno dukda bata bari Ammar ya gane, 


 Ana kiran Magrib Ammar yabar dakin ita kuma ta mike tayi sallah , Half vest da wani short niker ta daukko ta saka tanajin Boobs dinta da su kai tsami suna mata wani zafi , saboda yanda aka mata matsen magun ta aka kuma shasu har suka fita daga kamin su, Zama tayi agefen gado tana hawaye tare da Dan mamatsa boobs din , 


Sallamar Mamy ne yasa tayi saurin sauke hannun ta , 

 Karasowa Mamy tayi da sauri tace “Asma me ya same ki “ ganin ta rude ne yasa tace “Mamy Boobs dina suna Min ciwo ne “ 


Saurin rike bakin ta tayi ganin baranbatamar da tayi , ta saba sharring ko wani moment da Mamy shiyasa a komai batajin nauyin fada mata abunda ke Damun ta 

 Kallon ta Mamy tayi tanason karantar yanayin ta sannan tace “Garin yaya suke miki zafi “

 “Uhm daman jiya da aka bige ni ne har yanzu sukemin zafi”

   Kallon ta tayi tsaf tana son gasgata abun da ta fada , mikewa tayi ta fita batare data tanka mata ba ,dandanan gaban Asma ya fara faduwa hawaye ya cigaba da zuba “Nashiga uku Mamy ta gane ni,innalillahi wainnailahi rajiun “ abunda take ta fada kenan tana kuka , Shigowar Mamy ne yasa ta tsaya cak da kukan kamar anyi ruwa an dauke 

 “Oya remove the shirt “ Mamy ta bata umarni babu alamun wasa 

 Jiki na rawa ta cire rigan ta koma ta zauna , kallon Boobs din nata Mamy tayi tana examining nasu ganin yanda sukayi jaa sosai har nipples din ya wani tattare wuri daya ,kuma ga alamun Kumburi nan attatare dasu 

 Sauke ajiyan zuciya tayi sannan tasa Asma tayi flat, Pain reliever hannun ta ta bude sannan ta fara massaging Boobs din nata tana Dan mamatsa mata ahankali ,duk da zafin da takeji bata bari Mamy ta yi noticing ba ,seda ta gama shafe mata duka sannan tace ta mayar da rigar ta , dauka tayi ta mayar Mamy tace “Gashinan ki ringa amfani dashi yanda kikaga na miki ,saura Zafi ya hanaki shafawa kinga In ya fara ciwo se a yanke miki a huta “ 

 Zazzaro Ido Asma tayi tana dafe kirji jin Mamy tace zaa yanke mata Boobs ,tun lokacin da wata kawar Mamy ta yi breast cancer aka yanke mata nata Da Asma akaje dubiya kwana tayi tana kuka shysa take matukar tsoron ace zaa yanke mata Boobs , duk yanda Mamy taso danne dariya ta seda tayi Murmushi Dan already ta riga ta gano lagon Asma “Ai haka nace idan bakya shafawa,in kina shafawa kinga ze warke Toh babu abunda zaa miki “ sauke ajiyar zuciya Asma tayi tana Dan murmushi 

  “Sako hijjabin ki ki saukko “ 

 Mamy ta fada sannan ta juya ta fita 

Wadrope dinta ta buda ta daukko well iron jalbab dinta peach color daya haska kyauwun fuskarta , ta saka sannan ta Saukko tana tafiya a harde domin kuwa babu abunda ya ragu aciwon nata,wurin Mamy ta karaso tace “Mamy gani “ 

 Kije Sit room kinada bako 

Juyowa tayi da sauri ta kalli Mamy hawaye har sun fara tara mata ,Karde ace shine ya dawo wurin ta kuma Haryana da karfin halin shigowa gidan su ,har yace a kirata me ze ce mata ? Bayan yaudarar tada yayi kuma ,ko

Kuwa d wata sabuwar yaudarar yazo lalle ta kara yarda maza basu da kunya “Ba Ahmad bane “

 Mamy ta katse mata tunanin ta ,se a sannan ta fara tunanin to waye take dashi dazezo gidan su itadai tasan batayi da kowa zezo gidan su ba , 

  Ba ta Kuma magana ba tayi hanyar da ze sadata da Sitting room ,tunda ta doso hanyar gaban ta ke bugu zuciyan ta yana bada sautin LUF DUF a bakin kofar ta tsaya ta daidai ta numfashin ta sannan ta shiga da sallama 


  Tana sako kai cikin sitting room din wani sanyayyan kamshi ya bigi hancin ta lumshe ido tayi saboda yanda take tsananin kaunar kamshi.

  Idanunta ne suka shiga nashi , dauke kanta tayi gefe daya alokacin daya taji kunya ya rufeta, idanunta har sun fara kawo ruwa 


 Deeply yake kallon ta yana jin babu dadi yanda tayi reacting kamar dai bataji dadin ganin sa ba ,ko Kuma ganin sa na tuna mata da abunda ya sameta shi kuma abunda baya so ta ringa tunawa kenan shysa yake ganin duk yanda zeyi dole yayi dan ya rabata da duk wani damuwa.


  Rausayar da kai yayi sannan ya bude mata hannayen shi cikeda tausayi yace “Come on “.

  Batare da ta tsaya bin shawarar zuciyarta ba ta tafi da gudu ta fada faffadan kirjin sa tare da fashewa da kuka 

 Har cikin zuciyar sa yake jin kukan nata , hugging nata yayi sosai yana bubbuga bayan ta ahankali sannan ya fara rarashin ta jin taki yin shiru ne yasa ya fara mata waka slowly acikin kunnen ta “ I will never ever ever do you wrong! I will always always do you right , I will treat you like a queen ! I will buy you diamond rings , I swear my baby I say no be like ! I love to hear you laugh and watch you smile ! I will give you all the finest things of life ! You’re the angel of my life ! The loml! I love my baby dance my baby I will treat my baby right “.

  

   Wani sanyi taji har cikin zuciyan ta yana ratsata ,tsigan jikin ta ya fara mikewa jin yanda yake rera wakar har yafi wanda yayi wakar I yawa ,dumin numfashin sa na shiga har cikin kunnen ta shiru tayi tana sauke ajiyan zuciya sede zazzabin da yake damun ta yanzu yafi komaI Dan kuwa jikin ta yayi zafi rau , shima da take jikin shi yaji yanda zazabin yayi zafi sosai dagota yayi yana kallon ta sanann yace “What’wrong baby “ ?

  Sunkuyar da kanta kasa tayi batare da ta mishi magana ba 

 Sallamar hajara ce ta katsesu ,gaishe shi tayi sannan ta ajiye babban tray din dake hannun ta.

   Ruwa ne aciki da lemo se fruit salad , Hajara na fita ya mike da kanshi ya janyo tray din gaban shi sannan ya buda bowl din 

  Fara sha yayi sannan ya Debo ya kai bakin ta make kafada tayi ta Kauda kai gefe, “Indai biki shaba zamuyi fada “ 

  Jin yanda yayi magana in a serious tune yasa dole seda ta karba , karnin madarar dake ciki ne yasa zuciyar ta Yafara tashi ,datse bakin ta tayi jin amai yana taho mata tashi zatayi ya rikota , bude bakin ta tayi da niyar mishi magana ta fara mishi Amai ajikin shi ,seda ta amayar da duk Fruit Salad din sanann ya zaunar da ita tana numfashi cike da galabaita tace “Kayi hakuri Dan Allah so.. nake.. nace... maka .. zanyi amaiiiii... ka rikeni “ ta karasa muryan ta na cracking .


 Seda ya gama jin ta sanann ya dage mata gira yana murmushi, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jin wani iri .


  Mikewa yayi ya nufi toilet din dake sitting room wipes ya saka ya goge duka aman sannan ya goge inda ta bata ya goge mata baki ya zuba a dustbin din toilet din ya wanko hannun shi ya fito , kallon shi kawai take da idon ta dake lumshewa ganin yanda ya gyara wurin , sannu ya mata sannan ya daukko maganin ta daya zo dashi ya Balla mata babu musu ta amsa tasha duka , ganin babu karfi ajikin ta yasa yace ta koma cikin gida shi Kuma ya fita bayan ya mata peck a goshin ta.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol